1
by @maidambu41
*❤️🩹SO da CIWO❤️🩹*
*WOW*
Women's of Words
®©Ramlat A Manga
Mai_Dambu
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai,
Allah ka bamu ikon rubutun lafiya kamar yadda muka fara, Alhamdulillahi Ubangiji ka bani ikon rubutu ta hanya madaidaiciya, bana ce ba amma tabbas kowa yaga zabuwa da zanenta ya ganta,
*🚫Ina gargadi da jan kunne don Allah kada a tab'a min labarina ko a sauya mishi fasali yin haka laifi ne babba! Banyi don cin zarafin wata al'umma ko kabila ba, haka ban yi don b'atanci ga kowa ba, idan yayi dai-dai da rayuwarki arshi ne!*
Paid book
01
Rano local government, Kano Nigeria.
Gundumar Rurum sabon Gari.
-------------------------------------------
Gidan fura.
Tun daga nesa zaka iya hango cincirindon al'ummar da suke zaune a kofar gidan, wasu a taburma wasu a kujeran rabo fari. A rumfa kofar gidan ya cika ya ɗinke da al'ummar Musulmi. Kowa ka gani a wannan lokacin kasan yana cikin wani irin yanayi na damuwa. Can gefe wani wasu matasa ne da suke tsaye, kafin can Yara ne da suke tsugune, kasancewar yau kwana biyu kenan da rasuwar, amma har lokacin rasuwar bata fita jikinsu ba. Mikewa wani dattijo yayi ya nufi wurin matasan, ya karasa yana faɗin. "Ayuba ina dan uwanka?" Fitowa yayi ya ce mishi. "Ya fita dauko abokan aikinsa." "Tow dama dama, so nake na gaya mishi yau gidan fa sai a hankali. Domin masarar da aka kawo tun ranar rasuwar Abu Babba ya ƙare." "Shi kenan zan gaya mishi!" Ayuba ya fada ranshi a hade, don ya fahimci renin wayon ya fara wuce gona da iri. Wucewa Dattijon yayi ya koma cikin mutane, idan ka ganshi sam babu nutsuwa a tattare da shi.
A cikin gidan kuwa da yake cike da mata da Yara, yan mata da matan aure, iyaye da da Yara, ko ina ka gani zaka ga cike yake da al'umma. Babban gida ne irin wanda ake kira gidan gandu, sannan gidan a rabe yake domin kana shiga cikin gidan zaka ga inda ya raba kowani ɓangare. Sannan a cikin gidan akwai bangaren da yafi kowani bangare kyau da haduwa ginin zamani ne, wanda ya haɗa kome kamar kana unguwar manya, sannan akwai kofar da aka fitar ta can bayan gidan, sai yar karamar kofar da aka fitar ta cikin gidan. Wancan babban kofar an fitar da shine saboda ajiye mota da mashin, kasancewar mammallakar ɓangaren suna da waɗanda ababen hawan.
Babu cunkoson mutane sosai a bangaren, yan mata uku ne suka nufi bangaren daya daga cikinsu ta ce mata. "Me za mu yi a gidan Inna? Kun ko kun manta abin da Ya Ayuba ya fada ne? Kada ya kara ganin kafar kowacce mu!" "Kai Jamila Allah kin cika tsoro, yana can wurin zaman makoki" dayar me rawan kan cikinsu tayi magana. Juyawa ita jamilar tayi zata bar wurin daya yarinyar ta ce mata. "Don Allah ki zo muje na ga matar Yaya Iro, ina son naga me tafi mu da shi har ya tafi can ya dauko ta!"
Jin ana bude ƙoƙarin buɗe kofar gidan suka kwasa da gudu, tare da barin kofar shiga gidan, fitowa wata babbar mace tayi sanye take da doguwar riga da hijab iya gwiwa, bayanta wasu mata ne masu kananun shekaru, daya zata kai ashirin da biyu daya kuma ba zata wuce ashirin zuwa sha tara ba. "Hajjo kyale Bintu da kofar muje." Cikin yar kunya wacce aka kira da Hajjon ta ce. "Tow Inna!" Ta fada tana gyara rikon Babyn da ta mishi ado, yana tashin wani sassanyar kamshi, baka ce amma kuma tana da kyau, sannan itama Binta yanayinta fara ce amma ba can ba, ita ce kusan Autar Inna, tana da kimanin shekaru ashirin da daya. Juyawa Inna tayi ta ce. "Hajjo bani shi!" Mika mata shi tayi cikin girmamawa. Har suka fito daga ɓangarensu, yan matan nan na tsaye suna kallonsu, babu wacce ta iya bude baki ta gaishe su, sai da Binta ta juya ta kalle su. Dake sun santa bata da kirki idan aka fusatatta. "Ina wuni Inna? Ina wuni Adda Bintu!" "Lafiya lau! Tsayuwar uwar me kuke yi anan?" "Babu!" Suka fada suna masu barin wurin, babbar budurwan cikinsu ta kalli Hajjo sama da kasa, ganin yadda hankalinta yake kan waya, ta ja tsaki ƙasa ƙasa,bata san me yasa Ya Iro ya tsallake gidansu nan ya dauko wannan yarinyar ba, a cire hassada suma sun san Hajjo ta hadu, ga yanga irin na yaran manya ajeboti . "Hello My Man!" Ta dauka a yangance, irin ya zame mata ma natural idan bata yi shi ba kamar ba ita ba. "But why?" Can yayi magana a sanyayye, "My Man na gaya maka Innah she need us, taya zan cd mata zan tafi daga zuwa jiya-jiya, Inna she isn't my mother in laws, she is my mother too, please ka daina jin ba dad'i don zamu kwana daga gobe sai mu tafi ko!" Dake sun yi gaba sun barta. "Ok ai na gaya maka Asibiti sun bani hutu ai nayiwa Daddy magana ya ce a bani hutu." "Thank God I have you in my life, so shi kenan!" Ta kashe wayar, tana kallon yadda suka mata zuru da idanu, yaran sun cika reni, zata cigaba da tafiya,sai ga Ayuba. Murmushi yayi mata yana faɗin. "Mom Amjad muje na kai ki wurinsu!" Ya juya yana kallonsu Jamila. "Uban me kuke nima?" Simi-simi suka wuce kamar an watsa musu ruwan sanyi, suna Bala'in tsoron Ayuba. "Kai ku zo nan!" Dawowa suka yi, kamar munafukai. "Uban me kuka zo yi?" "A'a kawai mun zo gaida Aunty Hajjo ne!" "Yaushe aka koya muku gaida mutane bana ce kada na kara ganinku a bangaren nan ba ne ko kun manta yadda muka yi da Baba Yusuf akanki ke Labiba!" Sunkuyar da kai tayi tana faɗin. "Kayi hakuri!" "Idan na kara ganin kafarku sai na karya yarinyar wuce ko nayi kallo da ku, yan iska marasa kunya." "Ayub me ya faru!" Tsaki yayi ya saka su a gaba yana bata labarin, shiru tayi tana kallon yaran basu waju girma ba, amma yadda suke abu daka ɗauka sun kai shekarunta.
Bangaren da aka yi rasuwar ya mata jagora. Yana shiga yaji ana magana sama-sama, kowa yasan Ayuba bai da dad'i kamar ya make mutum yake idan ya shige mishi harkan sa. "Eh ai wasu kunyar ce a duniya ba a santa ba." Wata mata ta fada tana watsa hannu kana ganinta, ka ga kasungumar jahila domin tayi wani butu-butu da ita, yanayinta kawai idan kana da saurin amai zaka yi, don irin mutanen nan ne, da basu da kyan gani ba wai na jiki ba. "Inna!" "Kai karibu wuce ka bani wuri, Allah ya kiya shemu abin kunya." "Inna" yaron ya kara kiran sunanta, ta kalli matan da suke dankad'en garin masaran da Ayuba ya kawo za ayi tuwon wunin ranar. "Ai Ina gaya miki Malam yana kokari, ba a gani ne don kawai Allah ya saka ana ganinsu kamar wata tsiya." Shi kan Ayuba tuni ya fita yasan abin da Inna Lantana take yi dasu take. Amma yadda Innarsu ta gaya masa ko me za ayi babu ruwansa, na shi idanu.
A dakin Mamaciyar Yaranta mata ne, Hajiya Altine, tana aure a kano, da Yaranta sai Hajiya Sa'adatu da take aure a Katsina. Da yaransu, yan gayu da su. "sannu Boɗɗo! Rayuwa yau gashi kema kin hada naki ahalin Allah sarki Baba Bello da yana raye da shima da na shi iyalin." Murmushi Inna tayi tana jan Yar karamar casbinta. "Boɗɗo yanzu shekarunshi zasu kai talatin da bakwai ko?" Sunkuyar da kai tayi tana faɗin. "Eh jibi watan bawa rasuwar Malam shekaru talatin da bakwai da wata goma sha daya, watan sallah zai cika shekaru talatin da takwas." "Ikon Allah! Shekara kwana kuma haka ne da rayuwarshi da ta Yaya kwanaki ne, Allah ya musu rahama." Zuciyarta tayi nauyi yadda har yau bata manta labarin mutuwar sa.
A waje kuwa kasa da murya Inna Lantana tayi, tana faɗin. "Waye ya sani ko yanka kai Yaron yake, taya za a ce a kasa da shekaru huɗu yaro kamar Ibrahim yayi arziki haka. Hmm ke dai gaskiya ce ba so." "Inna!" wata ƙatuwar budurwa ta taso yaron da bai wuce shekara bakwai ba. A gaba tana make keyarshi. "Wallahi sai naci mutuncinka, Inna wallahi na gaji kullum aikina ne na wankewa Ma'aruf kashi, dubi dan banza kullum bashi da aiki sai kashi a jiki yaro kamar Maaruf sai an wanke mishi kashi!" Ta fada tana hayayyakowa Uwar, cikin takaici ta ce mishi. "Haba Sailuba, maza ki je ki wanke mishi, kai kuma kada ka kara." "Tow Inna kashin ne yake zuwa min ban sani ba!" Ya fada yana share kwallar da take zuba mishi. "Tow uwar masifa tsigai kin ji bai ma san yana kashin ba, fita da shi kada su Hajiya su gani hankalinsu ya tashi." Juya kan yaron tayi suka fita tana mita. "Sailuba Sarkin lalaci, yaron nan dai zan kai shi gidan mai magani don na lura so ake a saka min hannu, idan wani ne ma yake nimanta da sharri zata hwad'a kanshi ban nemi kowa da alkaba'i ba."
Fitowa Bintu tayi tana waya, muryanta a kashe tana faɗin. "Sugar ka iso ne? Muje ɓangaren Inna idan kun gama gaisauwa." Wani kallon shekeke, suka bita da shi kana ganinta kasan yar gayu ce, sannan tana tafiya kamar ba zata taka kasa ba. Kwafa Inna Lantana tayi, a bakin kofar Bintu ta matsawa wata mata itama kana ganinta kasan yar bala'i ce amma dattijuwa ce. "Mtseew, lalatacciya waye bai san abin da uwarku ta yi ba, ina shima kafirin Ubanku Habibu haka ya mutu a wulakance ai kowa ya tab'a Ilimin Muhammadiyya sai yayi mutuwar ƙare!"
Dariya Bintu tayi mata tace mata. "Yadiko Allah ya baki nisan kwana ne domin ki ga yadda Yaran Habibu da Boɗɗo sun zama damina uwar albarka, idan maganinki ya kare ki gayawa Inna zata gaya min, Allah ya baki lafiya domin ina miki fatan lafiya da nisan kwana yadda zaki ga abin da zai dame ki." Ta fita tana dariya idan dai wannan halin ne ai ba sabo ba ne, sai dai har yau tana mamakin yadda dangin Abba suka tsane su. "Maraba lale Yadiko!" "Sannu Lantana, yau ma dai kin fito kamar an koro ki, haka Isuhu yayi hakurin zama da ke har yau baki canza ba!" Ta fada tana tafiya a hankali, dakin Marigayiya, Abu babba. Kasancewar tana fama da laluran idanu, sai da glass take gani haka yasa tana isa bakin kofar ta sake baki tana kallon Innar Ayuba, da take rike da jikanta na uku. Domin Bintu tayi aure shekara shida kenan. Yaranta biyu mace da namiji, mijinta yana da rufin asiri sosai, domin a Kano take zaune kuma abin dad'i tana koyarwa makarantar sakandare, domin tana candy ta aka uzura mata. Musamman dangin Mahaifinta da suka ce hannunsu bai cudi baya ba, ba zasu iya mata kome ba, basu da ƙarfi.
Wani haɗe rai Yadiko Marka tayi tana faɗin. "Hajiya Sa'ade." "Yadiko ki shigo mana." "Tow!" Ta wani kwab'a fuska. Ta shiga tana hararan Innar Ayuba. "Ina wuni Yadiko!" Innar Ayuba ta gaidata. "Lafiya !" Daga haka bata kara magana ba. Har lokacin Yaron Ashraf. "Ina wuni!" Cikin son cusawa Innar Ayuba takaici ta ce mata. "Ba zan amsa ba, ina Uwar Mijinki bata koya miki tarbiyyar da zaki zo ki gaishe ni, taga miki nice uwar gidan Malam Bello kuwa!" Kan Hajjo a sunkuye, "ko shi Iron bai gaya miki matsayina ne." "Eh bai gaya mata matsayinki ba, domin kakarmu da muka bata matsayi Hajiya Abu Babba ce, kuma ta rasu. Allah ya mata rahama Hajiya Inna ga Babansu Arif sun zo da abokansa." "Tow mara kunya me fama da bakin Uwa!" "Wa? Ni ai wallahi Yadiko kin san ma'anar wa yake fama da bakin Uwa, Uwata bata barci domin kullum niman lahira take akanmu. Bata watsar damu ta zabi wani akanmu ba." "Sai naci kaniyarki Bint!" Tura baki taya tana faɗin. "Fisabiilillahi sai na kyaleta tana gaya min magana, kuma wallahi yallabai yana shigowa kika yi wani shirme idan ban bugawa mala'ikan Mutuwa ya zo ya dauke ki ba, mu da muke kiran shi ya dauke ki ya dauke mana, Hasken gidan nan!" Ta fita tana me faɗin ta sake jin tayi tari. Shiru yadiko tayi bata kara magana ba, domin a duniyar nan idan aka kira mata mutuwa duk bala'inta sanyi take. "Hmm!" Ta fada tana gyara zaman glass dinta. Tun daga tsakar gidan muryan manyan maza yake tashi, har suka iso bakin kofar suka durkusa suka gaishe shi. Tare da musu ta'aziya, Bintu tana kallon mijinta da ya sha manyan kaya. "Allah ya muku albarka, hmm! Kayi ta hakuri da ita. Domin ni." Kallon Bintu Yadiko tayi ta rike bakinta tana faɗin. "Iyatu nayi shiru!" Murmushi suka yi, daya daga cikinsu yayi ta addu'a suna Amin Amin. Kamar wacce aka matse ta cikin damuwa ta ce mishi. "Yaro don Allah, ka gayawa Mutuwa kada ta dauke ni da wuri." Dake yasan da batun Bintu ta gaya mishi, sauran abokanshi suka yi sororo, Innar Ayuba kamar ta nutse.
"Yadiko ai babu maganar daukarki da mutuwa zata yi,muna tare da ke." Ya fada yana murmushi, haka suka fita cikin damuwa ta kalli Hajjo ta ce mata. "Matar Iro kin ga nayi kama da wacce zata mutu? Ance kune malaman jinya kuna gane wanda zai mutu!" "Kada ki fada hajjo, ba dai halinta rashin mutunci ba ne ba a fada ba!"
"Boɗɗo ki gayawa Yarinyarki ta fita idanuna." "Ummi ki daina Please!" Tura baki tayi tana faɗin."mutuwa na kan kowa idan lokacinta yayi babu tsimi babu dabara." Ta ajiye mata kudin tana cigaba da cewa. "Gashi Inji Babansu wai ki ci goro!." Murmushi ta sake tana kallon Hajiya Altine ta ce mata. "Altine Yaran Habibu yan albarka ne, gidan na cire wancan kafirin." Wato Ayuba, don tun tasowarshi ya bata wahala. Mikawa Hajiya Sa'adatu kudi me yawa Bintu tayi tana faɗin. "Wannan na sadaka ne, suka bada bari na sallame shi nazo!" "Allah ya bada lada, ya cika mizani." "Amin Ya Allah!
"
Fitowar da Bintu tayi ta samu Lantana tana tangale, kallon juna suka yi ta tab'e baki, tana faɗin. "Da bamu san asalin balbale ba, da sai muce daga masar take amma mun san kome." Murmushi Bintu tayi tana faɗin. "Inna Lantana, kina tunawa da baya dai." Ta fita, abinta. Cikin rashin mutunci irin na wanda ya samu wuri ya fara ruga Ash'aria kamar zata daki wani, abin da yayi sanadin fitowar Iyalan mamaciyar kenan, suna tambayar ba'asi. "Ni ake tambayar ko ita yar magajiyar ? Ni Bintu zata zaga?" "Amma dai Lantana kece kika fara kika ce da ba'a san asalin balbale ba da zata ce daga masar take, ita kuma ta ce ki tuna ba ko ba haka ba?" Inji Sahura wacce bata shiga harkan kowa tunda ta san irin zaman mutanen gidan, ta kame kanta. "Sahura zaki ga Ma'aikin Allah kuwa? Koda yake dole ki fadi haka, tunda Iro ya dauki nauyin karatun Dahiru!" Tana fadar haka ta buga zaninta tana faɗin. "Idan dai ni Lantana kuke fada da ni, ku shirya zaku ga rashin mutunci." Ta juya tana me barin bangaren rasuwa.
Haka ta nufi bangarensu tana fada da sababi, tana shiga bangarensu babu kowa, sai Maaruf da yayi kashi ya bata jikinsa har lokacin Sailuba bata gyara mishi, nufar bakin rijiyar bangarenta tayi ta fara kokarin jan ruwa, bayan ta janyo ta zuba a wani bokiti, sannan ta wanke mishi jiki ta hade da garin Klin tayi mishi wanka. "Maaruf kashin kan nan, ya fara yawa baka da baki ne da ba zaka gaya mana zaka yi kashi ba?" Shiru yayi yana kallonta. Idanunshi cike da kwalla. "Assalamu alaikum! Lantanas ya zaki bar aikin da kika fara?" Juyawa tayi tana kallon Larai da ta shigo cikin son munafunci ta cigaba da cewa. "Ke dai Larai raina ne ya b'aci, amma ko yanzu ai zan koma." "Gaskiya gara ki koma kin san Laraba bata nan, wannan shine damarmu na kane-kane akan kome, Batun Boɗɗo da Yaranta, ki barshi zamu ji da kome."
Shi kenan muje, ba don ke ba ai.." ihu ta kwala tare da kad'e jikinta tana ihu. Itama Larai ihu take tana faɗin. "Kadangare ne." Garin kade shi kuwa ta buge da jikin kofarta, sai ga Hannunta daga kafad'arta ya kwabe, wani irin azaba yasa Lantana tsalla ihu tana faɗin. "Wayyo Allah na mutu na lalace!" Ta zube kasa, tana ai kuwa kadangare ya sauka da gudu ya nufi hanyar waje. Tana kallonshi, cikin azaba da raɗaɗi ta fashe da kuka tana faɗin. "Tabbas na fahimci kome, ture aka min." "Innalillahi wainnalihir rajou! Yanzu me kika ci musu da zasu miki irin wannan lamarin? Bari na kira Malam!" Ta fita da gudu zuwa bangaren da aka yi rasuwar ta shaidawa Sahura. Sannan suka fita zuwa soron gidan ta kira karamin Yaron Sahura. "Minka'ila maza kira min Babati!" "Tow Inna!" Ya tafi da gudu,.har inda Babati yake wato Malam Isuhu. Tasowa yayi ya nufi soron gidan. "Malam ka shigo, Lantana ta fadi ba lafiya " "tow Innalillahi wainnalihir rajou,garin yayya?" Ya tambaye ta yana nufar cikin gidan shima, a tsakar gida ya same ta a yashe tana nishi, "Ya Salam, Lantana? Taya haka ya faru?" "Malam ture aka min, ina ganin an so ya ga bayana ne Allah bai nufa ba ga Larai nan yadda muka yi ta kokuwa da shi kafin na fyad'a dan banza da ƙasa!" Ta fada tana zubda hawayen azaba, Larai dai ta san ba ayi haka ba, amma saboda munafunci da son kara samun fada a wurin Lantana domin danta yana fatakwal yana mata aika, kayan more rayuwa don ma ita ba mai adana bace, amma yaci ace ta zama wata, amma ina kome ta samu yana wurin Malamai da yan bori.
(🤔 ko waye yayiwa Lantana ture oho)
#RamlatAManga
#Mai_Dambuce
#Wow