5
by @oumfatima33
💞💞💞💞💞💞💞💞
*AMATURRAHAMAN*
_*By*_
*_OUM FATIMA_*
_*(Hakimar D. A. W. A)*_
💞💞💞💞💞💞💞💞
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S📚ASSOCIATION*_
_*TEAM*_
_*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*_
BOOK 1
*PAGE 5*
_*بسم الله الر حمن الر حيم*_
Kai tsaye Asibitn Babbar Riga dake Katsina suka nufa, inda aka amshi Mukhtar aka shiga bashi taimakon gaugawa kafin likitan da zai duba shi ya ƙaraso.
Bayan gwaje-gwaje da binciken ƙwa-ƙwaf da akayi wa Mukhtar aka tabbatar da yana ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki wato (HIV AIDS) sai kuma hunhunsa da ya lalace sakamakon hayaƙi Cigarette da yake banka masa. Koda likita ya gama yiwa Umma da Kawu Isa wannan bayanin kuka ta fashe dashi tana jin wani irin ɗaci a maƙogaromta, shi kuwa Kawu Isa kai yake gaɗawa yana faɗin "Nasan za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya. Yo idan ƙanjamau bata kama Mukhtar ba wa zata kama a duniya? Mutumin da banda iskanci ba abinda yasa a gaba, hum ai yanzu da ya ɗebo ciwon da zai kaishi lahira ya dawo ya ya tsuguna don dole."
Ita dai Umma batace komai ba sai kukanta da yake daɗa tsananta, likita ne ya katseta ta hanyar yin gyaran murya yace "kiyi haƙuri Madam zamu ɗora sa akan magungunan da suka dace, zai ji sauƙi in sha Allah." Shiru ya yana nazari kafin ya ƙara cewa "Matarsa ce ke ɗin?."
"Eh". Ta faɗa cikin sanyin jiki.
"Da bukatar kema a bincika lafiyarki." Ya faɗa yana ɗaukar kan wayar dake saman table ɗin gabansa ya saka kira, ana ɗagawa daga can ɓangaren yace "Meet me in my Office right now."
"Ok Sir". Ta faɗa daga ɗayan ɓangaren, ya aje wayar. Ba'a daɗe ba sai ga wata siririyar budurwa sanye da daren kaya ta shigo da sallama. Umma ya nuna mata yace "Kije da ita ayi mata gwajin HIV."
"Ok Sir". Ta faɗa tana duban Umma data miƙe jikinta na rawa gabanta na matsanancin bugu jin abinda likita yace, ficewa suka yi gaba ɗaya har Kawu Isa da yake son ganin abinda zai turewa buzu naɗi. Shi kuwa Doctor jingina yayi jikin kujerarsa tausayi matar na kamasa"Allah ya kyauta." Ya faɗa yana ci gaba da aikinsa.
Tunda aka ɗibi jininta a ɗakin awon jini aka shiga aunawa take zaune a wurin da aka tanada don hakan, tsoro ne cike a zuciyarta da fargabar sakamakon da za'a samu. Ya'yanta sune na farko da suka fara zuwa a ranta, idan ya tabbata itama tana ɗauke da wannan cuta mai karya garkuwar jiki shikenan bazata yi tsawon raiba, bazata samu damar ci gaba da kulawa da su ba ta basu ingantaccen ilimi kamar yanda take fata, musamman ma Amahh daya kasance burninta tayi karatu mai zurfi. Itace ƙarama duka shekarunta goma ne a yanzu amma tana da zurfin tunanin daya zarce na Ƴarta data bata shekara shida.
Maganar da Nurse ɗin da suka zo tare ce tayi mata yasa ta farkawa daga dogon tunanin data faɗa "Muje ko?" Shine abinda ta faɗa tana yin gaba, gyaɗa kai kawai Umma tayi ta bita suka nufi Ofishin likitan.
Kawu Isa ma binsu yayi don so yake ayi komai a gabansa yanda bata isa ta ɓoye musu gaskiyar abinda ke faruwa ba. Umma kuwa juriya da dakiya irin tata ce yasa har yanzu take riƙe da kanta bata sume ba tsabar fargabar dake ranta.
Koda likita ya gama duba sakamakon ɗagowa yayi ya kalli Umma cike da tausayi, amma sai ya dake ya fara da yi mata nasiha kafin sanar da ita tana ɗauke da cutar, ya kuma ɗora da kwantar mata da hankali akan cewar in ta kiyaye dokokin maganin da zai rubuta mata zata samu lafiya harma tafi wanda baya ɗauke da cutar.
Salatin da Kawu Isa ne ya ɗauka yana tafa hannu kamar wani Mace yasa Umma miƙewa jiri na kwasarta amma ta kasa tsayawa, tana zuwa bakin ƙofa ta yanke jiki ta faɗi a sume. Cikin sauri likita ya kira Nurse aka ɗauketa aka kaita saman gado aka shiga ƙoƙarin dawo da numfashinta, tana farkawa cikin juriya da dakiya ta miƙe ta nufi ɗakin da Mijinta yake taci gaba da kulawa da shi.
Kawu Isa kuwa tafiyarsa yayi gida tun ma kafin ta farka bakinsa cike da gulma, ko tausayin halin da suke ciki baya yi burinsa kawai yaje ya fesar da abinda ya guntsa.
Umma kuwa haka ta danne fargaba da tashin hankalinta taci gaba da kula da Mijinta cikin juriya da ƙarfin zuciya, duk kuwa da cewar itan ma lafiyar bata isheta ba tana buƙatar kulawar amma ta daure take kula da shi tunda jikin ya tsananta. A duk lokacin daya buɗe ido bashi da aikin da ya wuce kuka da bata haƙuri "Ki yafe min Asiya, don Allah ina roƙon ki da kiyi haƙuri ki yafe min. Duk ni na saka ki a wannan halin, sai dai kuma ba laifina bane ƙaddarata ce a haka ba yanda zan yi. Ki kula da yarannan ki basu ingantaccen ilimi idan kin yi tsawon rai don nikam tawa ta ƙare, sannan idan Allah yasa kin haɗu da Halima ki bata haƙuri kice ta yafe min!." Mukhtar ke wannan maganar cikin raunin zuciya.
Umma dake zaune gefensa kuwa banda aikin share hawaye ba abinda take, gaba ɗaya ta rame ta ƙare tas sai iyayen ƙasusuwa kamar ka riga su, kamar ba Asiyar Mukhtar ta shekarun baya mai tashen kyawun fuska dana sura ba. "In sha Allah zaka samu lafiya Malam." Shine abinda take ce masa duk sanda yake irin waɗannan magan-ganun.
***
MATAZU...
Isar Kawu Isa garin Matazu ko gida bai ƙarasa ba ya fara yaɗa cewar ai Mukhtar ashe ƙanjamau yaje ya ɗebo, ya kuma gogawa Matarsa ita ma. Duk wanda yaji haka sai kaji suna faɗa ba abin mamaki bane ai tunda kowa ya san abinda yake aikatawa ba ɓoyayye bane.
Lokacin da Nafisa da Amaturrahaman suka samu wannan labarin a tsakar gida, haka aka riƙa nuna su ana musu habaici. Nafisa da bata barin bashi haka aka kwashi dambe da ita da Furera ɗiyar Kawu Isa.
Duk da ƙarancin shekarun Amaturrahaman abin ya daki zuciyarta, haka suka shige ɗaki suka yi ta kuka ita da ƴar'uwarta.
*****
KATSINA STATE GORUBA ROAD...
Wasu tsala-tsalan baƙaken motoci ne suke tsala gudu saman shimfiɗaɗɗiyar kwaltar dake malale a layin, basu tsaya ko ina ba sai gaban wani danƙareran gidan da girmansa ya kusa cinye rabin layin ta ɓangaren dama.
ALHAJI MUHAMMAD DOKAJO MENTION!.
Shine abinda ke rubuce a jikin wani kyakykyawan signing bord dake kafe a ƙofar gidan, ganim Motocin dake tunkaro wa yasa jami'an sojojin dake tsaron babbar ƙofar saurin buɗe ƙaton gate ɗin daya matuƙar haɗuwa.
Gaba ɗaya ƙamewa sukayi suna sarawa na cikin Motar da ba'a ganinsa sabo da tinted glasses ne gaba ɗaya a motocin, sai da Motocin suka gama wucewa kafin suka koma wurin zamansu suna fadin kowane tsagera sai ya shiga taitayinsa sabo da Babansu ya dawo.
Shimfiɗaɗɗiyar kwaltace ta miƙe tun daga babban gate ɗin har ƙarshen ginin, sai da suka tsallake gidaje uku daga ɓangaren dama kafin aka buɗe musu ƙofar na huɗu suka shige, lafiyayyen ginin gidane daya gama haɗuwa. Shuke-shuken dogayen flowers ne masu kyau suka zagaye ginin gidan tako wane ɓangare, masha Allah ginin ya tsaru tako wane fanni tamkar ba hannu ne ya gina shi ba.
Motocin basu tsaya ko ina ba sai da suka je makeken wurin da aka tanada don ajiye Motoci, cikin saurin sojan dake cikin Motar tsakiya ya fito daga gaba ya buɗe gidan baya inda sauran sojojin dake cikin sauran Motocin duk suka fito suka ƙame wuri ɗaya suna jiran fitowar ogansu.
Sai da aka ɓata kusan mintina uku kafin ya ziro lafiyayyar ƙafsrsa dake sanye cikin takalman sojoji mai kyau kafin ya fito gaba ɗayansa. Kyakykyawan matashin soja ne ya bayyana mai tsananin kwarjini da cikar halitta, wandon sojoji ne sanye a jikinsa wanda da kaɗan ya wuce gwiwarsa, sai farar rigar T Shirt mai ƙaramin hannun da ta bayyana manyan damatsansa.
Fuskarsa a ɗaure take babu alamar fara'a ya nufi kofar da zata sada shi da ainahin cikin gidan, Samuel ɗaya daga cikin yaransa ne ya ɗauki jakar laptop ɗinsa ya bishi da ita.
Akan idon Hajiya Ruƙayya da ɗanta Salim da zai kaita unguwa Motocin suka tsaya hakan yasa ta kasa shiga Motar suka bishi da wani mugun kallo mai cike da tsan-tsar ƙiyayya. Sai da ya ɓace daga ganinsu kafin suka kalli juna zuciyar kowa ba daɗi "Ai fa shikenan ɗan so ya dawo mun shiga uku!." Salim ya faɗa cikin jin haushi.
Ƙwaffa Hajiya Ruƙayya tayi kafin ta shiga motar tana bawa ɗanta umarnin shiga su tafi...
# ZAYYAD DOKAJO
# ZAHEERA DO
FREE PAGE YA ƘARE, DOMIN KARANTA CI GABAN LABARIN KA BIYA NAIRA 500 A WANNAN ASUSUN
8138665117 KANSA'U BELLO OPAY
SAI KU TURO SHAIDAR BIYA TA WANNAN NO ***
OUM FATIMA