FreeArewaPen original
AMATURRAHAMAN
- 1views
- 41chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 1
💞💞💞💞💞💞💞💞 *AMATURRAHAMAN* _*By*_ *_OUM FATIMA_* _*(Hakimar D. A. W. A)*_💞💞💞💞💞💞💞💞 _*DASHEN🌲ALLAH*_ _*WRITER'S📚ASSOCIATION*_ _*TEAM*__*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*_ BOOK 1 PAGE 1_*بسم الله الر حمن الر حيم*_ *Da ace Ɗan Adam* *shike da zaɓi akan* *yanda ƘADDARARSA zata kasance to nima* *da ban zaɓi ƙaddarmu* *tazo a haka ba. Shin* *laifinmu ne don* *ƙaddarar iyayenmu* *tazo a haka ? Ko* *kuwa laifinmu ne don mun kasance marayu? Da ace kun karɓemu kun riƙe mu kamar ko wasu ƴa'ƴa da bata saka kanta a halin da take ciki ba* *har ta zama abin* *gudu da ƙyama a* *gurin al'umma ba, da baku ƙyamacemu ba,* *kun jawomu a jiki da* *ban rasata ba kamar* *yanda na rasa Iyayena ba. Rashin Yayata a karo na biyu bayan iyayena yasa ni bushewar* *zuciyar da bana jin* *tausayin kowa a* *wannan duniyar,* *shine dalilin da yasa* *kaina kaɗai na sani* *nima kamar yanda na fuskanci haka rayuwar ta koma. Wannan* *dalilin ne yasa bana* *ragawa ko wane irin* *na Miji a wannan* *duniyar, tsakanina* *dasu gabace mai* *tsanani da ɗaukar* *fansa* . *Assalamu alaikum* *jama'a ina mai farin* *cikin sake kasancewa da ku a cikin wannan* *sabuwar tafiyar mai* *suna* *AMATURRRAHAM* . *Labarin da yake* *ɗauke da tsantsar* *tausayi da cakwakiya, kamar yanda kuka sani inji ƴan magana ba'a* *rasa *** a ruga* *haka ma labarin* *AMATURRRAHAM* *yana ɗauke da* *zazzafar soyayya mai tsayawa a zuciyar* *masoya.* *Ku dai ku kasance da alƙalamin Oum Fatima don jin abinda ke* *ƙunshi cikin wannan* *zazzafar tafiyar.* ★★★Cikin nutsuwa da matuƙar kamewa matashiyar da baza ta wuce shekara sha bakwai ba take tafiya, Uniform ɗin dake sanye a jikinta zai shaida maka cewar ɗalibace ita, yanda take ɓata fuska ne tana dafa goshinta lokaci zuwa lokaci ne ke nuna alamar bata jin daɗi ne ko kuma a gajiye take.A zahiri duka biyun ne ke damun ta domin kuwa kanta ke ciwo ga kuma gajiya kasancewar Makarantar tasu da nisa kuma a ƙafa ta taho ga zafin rana da ake ƙwalawa sakamakon yanayin da ake ciki a yanzu kenan, cincirindon mutanen da ta hango a ƙofar gidansu an zagaye motar ƴan'sanda yasa gabanta yankewa ya faɗi.A hankali ta motsa kyawawan laɓɓanta ta furta magana cikin siririyar muryarta mai daɗin gaske "Allah kasa ba Ya Nafi bace ta janyo wata rigimar ba".Sauri ta ƙara domin ta isa taga abin da ke faruwa, yanda gudun zuciyarta ke ƙara yawaita yasa tsoro ya fara kamata, isowarta wurin ta fara kutsawa cikin mutanen sabo da jin muryar kawu Isa yana masifa, a cikin faɗan nashi ne taki jin yana faɗin. "Yallaɓai gaskiya ni dai ba zan iya taɓa ta ba tun da ban ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.