004
*BAYA DA ƘURA*
FitattuBiyar2025
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11
©️ *Nana Haleema.*
*BOOK 1*
*Page 004*
A daren Manal suna zaune da Mama a falo cikin hasken fitilar da ya haske falon nasu Manal tace, "Mama gobe da safe zamu koma
Asibiti." Mama tace, "Manal ni ba sai mun je ba lafiya lau nake jina, in mun je goben wani maganin zasu sake bayarwa kuma ba wani kuɗi ne a hannun Baban naku ba yanzu."
Manal tayi dariya tace, "za'a samu Mama, Allah dai ya nuna mana goben. Kuma kin ga wajan Dr Huzaifa ne."
"Eh gaskiya, yana da kirki ya ɗauke ki kamar ƙanwa, sai a ɗauka ma ya jima da sanin mu."
"Auu na manta fa wajan likitan zuciya yace muje a kai masa wannan result ɗin, Allah ya kaimu goben da wuri zan fita dan ance ba wani kirki ne da likitan goben ba."
Mama tayi murmushi tace, "to Allah ya nuna mana. Yadda kike kula dani Allah ya baki mai kula dake Manal ɗin Mama." Tayi murmushi ta amsa da amin Mama tace, "Ya sayyadi bai yi waya ba?." Manal tayi dariya tace, "Mama kina bani kunya, ni nace miki Ya Sayyadi ba sauryina bane kawai muna gaisawa ne."
"Nima ai baki ji nace saurayin ki bane ba ai, Yayan ki ne." Tayi dariya kamar yadda Maman take yi Manal ta kalle ta tace, "Wallahi Mamana kina da kyau sosai."
Mama tayi murmushi sosai tace, "duk kyauna bai kai na Manalin Mama ba." Manal tayi dariya kawai Mama tace, "Allah ya kawo miki miji na gari wanda zai kula min dake ya inganta rayuwar ki ya cika miki burin ki na zama shararriyar mai dafa abinci ta duniya ma gabaɗaya." Manal tayi dake ya tace, "Mama ta duniya fa kika ce?."
"Ko baza ki iya bane?."
"Zan iya mana, amma ta duniya yayi girma."
"Kina wasa da ikon Allah?."
"A'a Mama."
"To kice amin kawai."
"Amin Mamana. Amma ni bazan yi aure ba."
Mama tayi dariya tace, "wannan kalma ta baza ki yi aure ba na faɗa miki bana son ji." Cikin sha'agwaɓa tace, "ni dake zan rayu Mamana, indai kuma zanyi aura sai dai mijin yazo nan mu zauna ko mu tafi dake." Mama tayi dariya sosai tace, "Allah ko Manal?."
"Allah Mama. In na tafi waye zai kula min dake?" Ta faɗa jikin ta nayi tunawa fa da gaske wata rana zata yi auren ta bar Maman ta. Jin yadda Manal ɗin tayi magana sai Mama tace, "ki cigaba da addu'a kawai, duk inda alkhairi yake Allah ya kawo miki shi." Ta amsa da amin bata ce komai ba.
"Ashe yau da arzuƙin nepa a unguwar" aka faɗa ana shigowa cikin falon. ko ba'a ce sun san wacce ta shigo. Manal ta kalle ta tace, "Yaya ko sallama baki yi ba fa." Hararar ta tayi tace, "bazan yi sallamar ba, bana son iyayi."
Ta kalli Mama da take zaune daga gefe tace, "Mama ki shiga tsakanin a da yarinyar nan ta daina shiga harkata." Mama bata ce komai ba Mubeena ta wuce ɗaki sai gata ta fito tace, "ke Manal wai babu abinda aka dafa a gidannan ne?."
"Inda kika je basu baki abincin ba?" Mama ta faɗa tana daga inda take zaune. Mubeena tace, "in baza'a bani ba ai sai a faɗa min kawai, daman nima karanbani na ne ya saka na tambaya, ina za'a samu irin abincin da nake so a cikin gidan nan?."
"Wallahi Yaya baki da hankali." Wara ido tayi tana kallon Manal tace, "ni ki ke cewa bani da hankali Manal?." Manal tace, "na faɗa akwai abinda zaki min ne?." Kafin Mubeena tayi magann Manal tace, "Mai hankali bazai aikata irin abinda kike aikatawa ba, ke a ganin ki wayewa ce raina iyaye, baki san hauka ne da rashin sanin ciwon kai ba. Sai girmama iyayen wasu saboda neman suna bakya girmama naki, tirrr! Kin ji kunya wallahi."
"Salamu alaikum wai Nusaiba tazo!." Wani yaro ya faɗa yana shigowa, abinda ya dakatar da Mubeena ga yiwa Manal masifa ta juya kan yaron tace, "sai naci kaza kazan wanda ya sake kira na da Nusaiba, sai na zage shi duk girman sa na rantse da Allah. Kar a kuma kira na da Nusaiba ba sunana bane, in baza'a ce Mubeena na ba a kira ni da baiwar Allah. Meye wani Nusaiba ana zaune Lafiya? Ni an cuce ni ma da aka samin Nusaiba wallahi."
Yaron da take yiwa masifa tace, "Baba ne yace kizo in baza ki zo ba sai naje na faɗa masa" ya faɗa yana fita daman dan ya tunzura ta yace Nusaiba. Mubeena tace, "ko ne zan masa da zai aiko nazo oho, ni bana son takura da saka ido wallahi. Tunda ba shi ya haife ni ba meye nasa na takura min?" ta faɗa tan figaat mayafi ta fita daga gidan.
Manal ta kalli Mama dan tasan bata so taji Mubeena tana ambatar sunan mahaifiyar ta tana cewa bata so, ranta yana ɓaci sosai har hakan sai ya nuna a fuskar ta. Manal tace, "Kiyi haƙuri Mama, ki cigaba da yiwa Yaya addu'a wata ran zata daina duk abinda yake yi." Mama bata ce komai ba tayi shiru kawai Manal sai ta tashi ta ɗauke kwanon da suka gama cin abinci ta fita dashi ta dawo ta ɗauko kayan shimfiɗa Mama ta shimfiɗa musu tace, "Mama nayi shimfiɗa in zaki kwanta."
Kafin Mama tayi magana Mubeena ta shigo tana cewa, "ni wallahi babu wanda zai takura min, sai nayi abinda nake so bazan kuma auri talaka ba wallahi. Ni Mubeena nafi ƙarfin ɗan mai kuɗi, sai dai mai kuɗin kan sa ba ɗan sa ba. Bazai yu ace sai uban miji ya bawa mijina sannan shima ya bani ba, na fi so daga hannun mijina sai wajena. Babu wanda zan aure gwara ma Baban ya sani, dan yana ƙanin mahaifin mu kuma yana auren Mama ai mahaifin mu bane. Bana son takura a bar ni na sake" ta faɗa tana shigewa ɗaki Manal zata bita Mama tace, "kar ki bita Manali, zo ki bani ruwa na sha." Manal ta canja hanya ta kawowa Mama ruwa ta sha tace, "kashe min hasken falon ki kwanta, in kuma kin kashe shikenan."
Kamar yadda tace haka tayi ta kashe hasken Mama ta kwanta ita kuma ta ɗauki alqur'ani ta koma tsakar gida ta zauna tana karantawa zuciyar ta babu daɗi. Bata son halin da Mubeena take nunawa Maman su ko kusa ko alama, tana jin haushin hakan domin yana daga cikin dalilin da ya saka ciwon zuciyar Mama yaƙi sauƙi saboda damuwar Mubeena.
Da sassafe Manal ta tashi tayi abubuwan da ta saba dan zasu je asibiti da Mama kuma bata so su makara, dan sau biyu suna son ganin likitan makara take hana su ganin sa. Ɗorawa Mama ruwan wanka bayan ta fito ta juye mata a bokiti ta kai mata banɗaki sannan taje ta tarar da maman a zaune ta dafe kanta tace, "Sannu Mama, har yanzu ciwon kan ne?." Mama tace, "kece da sannu Manal, har yanzu bai sake ni ba ciwon nan kaina yayi nauyi sosai."
Manal tace, "har na juye miki ruwa saboda zuwa asibitin, Anya zaki iya zuwa ma kuwa?." Mana tace, "gaskiya bana tunanin zan iya fita, kaina ciwo yake min sosai ba kaɗan ba Manal." Manal tayi shiru ta kalli ƙaramin agogo falon su tace, "gashi har bakwai ta kusa, ance likitan tun shida yake zuwa. Bara na shirya naje kawai na kai result ɗin zuciyar sai ya bani maganin na ki." Mana tace, "Anya zai saurare ki?."
"Zan gwada Mama, tun yaushe ake saka mana ran zamu ganshi bamu ganshi ba, ga dama mun samu baza mu yi wasa da ita ba. Bara na saka kayana nayi sauri naje na dawo" ta faɗa tana shiga ɗaki a lokacin Mubeena bacci take sosai ko alamun tashi bata yi ba, ta shirya ta saka hijjabi ta ɗauki katin Mama da kuɗin mota ta fito ta samu Maman ta koma ta kwanta tace, "Mama zan tafi babu abinda kike so?."
Mana tace, "babu komai Manal, sai kin dawo Allah ya kiyaye yayi miki albarka." Ta amsa da amin ta fita daga cikin gidan. Napep ta hau zuwa asibitin murtala ta sauka ta shiga ciki inda aka yi mata kwancen likitan yana zuwa nan ta hango dandazon mutane mata da maza a zaune a cikin wata rumfa da alama duk likitan zasu gani.
Ƙarasowa tayi wajen wanda yake tsaye da katina a hannun sa tace, "sannu da aiki." Ya kalle ta yace, "Yauwa."
"Dan Allah nan ne wajan likitan zuciya?."
"Eh nan ne, kawo katin naki." Miƙa masa katin tayi ta koma ta zauna akan abinda ake zama tana jiran azo kanta.
Ta jima sosai sama da awa ɗaya tana zaune kafin a kira sunan Mama jin hakan ya saka ta tashi da sauri ta karɓi katin ta shiga office ɗin. Bebi yana zaune a kan kujera cikin manyan kaya ya sunkuyar da kai yana rubutu ta zauna ya miƙa mata hannu yace, "bani katin." Ba musu ta bashi katin ya karɓa tace, "ga sakamakon gwajin zuciyar da akayi." Karɓa shima yayi ya buɗe takardar yana kallon ta sai ya ɗago suka haɗa ido da Manal ya sake kallon age din jikin katin ya sake kallon ta yace, "Zahra'u Muhammad, are you?."
Manal tana kallon sa tace, "Mamana ce, bata da lafiya baza ta iya zuwa ba shine nazo na kawo da kaina. Bana son rasa damar ganin ka ne, sau uku ana saka ran zamu ganka bamu ganka ba shiyasa na karɓo nazo a madadin ta." Kallon fuskar ta yake yi jin yadda take magana da sanyi ya jingina da kujera yace, "Maman kice babu lafiya kuma kece kika zo ganin Dr?." Manal ido ya ciko da ƙwalla tana kallon sa tace, "eh." Wani irin kallo na ta raina masa hankali ma yake mata, yanzu banda ma raini shi zata zo ta cewa wai katin babar ta ne amma itace tazo ganin likitan?.
Tsaki yaja ya ajjiye mata katin zaiyi magana tace, "don girman Allah ka bani maganin kwana biyu har bacci kasawa take saboda ciwon ƙirji, yanzu haka bata da lafiya na fito na barta dan Allah ka taimaka ka rubuta maganin dan Allah." Sai hawaye ya sakko daga idanun ta yayi shiru yana kallon ta, yana girmama mace a rayuwar sa duk ƙarancin shekarun ta amma baya so azo masa da rainin hankali, in ba rainin hankali ba tazo tace ya bada magani bayan bai ga mata lafiya ba sannan ba'a faɗa masa ya ake jin ciwon ba kawai sai ya ɗauka ya bayar, wani abun na faruwa kuma sai dai yaji sunan sa a gidan radio ana cewa bai san aikin sa ba. Ta saka shi a gaba tana masa kuka kamar wacce ya daka, baya son shagwaɓa ta banza da wofi, in zaka yi ma kayi akan hujja.
"Zaki iya fita daga nan?. Ta ɗago idanun ta da suka koma ja tace, "ka taimaka dan Allah."
"ki je, duk sanda Maman naki ta samu lafiya sai kuzo." Ta girgiza kai tace, "wahala ake sha kafin a sake samun ka, dan Allah ka amince ka bani maganin." Shiru yayi yana kallon ta ya lura baza ta fahimta ba.
"Out!" Ya faɗa yana nuna mata ƙofa. Jikin ta a sanyaye ta tashi ta ɗauki katin da takardar ta fita bata sake cewa komai ba a lokacin wata mara lafiyar ta shigo. Tsaki yayi bai sani ba ya kalli sabuwar da ta shigo ya karɓi katin ta ya fara rubutu a kai.
Manal tana tafe tana kuka, wannan shine taga samu taga rashi, ga likitan da suke son gani kwana da kwanaki amma ta ganshi ganin nasa babu amfanin da yayi mata. A haka ta shiga gida tun daga soro take jin muryar Mubeena tana mita kamar yadda ta saba. Kai ta girgiza kawai ta shiga a lokacin Mubeena yake cewa, "Yauwa gwara da kika dawo, sai ki ɗauki hanya ki fita bayan kin kulle kitchen da kika bar mu uban me zamu ci?." Manal da fuskar ta tayi ja sosai tace, "kin san inda nake ajjiyewa" tana faɗar hakan ta ƙarasa falon ta tarar da Mama a zaune har tayi wanka amma kayan shimfiɗat suna nan ba'a kwashe ba.
Ajjiye katin tayi tace, "Mama na dawo" ta faɗa tana kwashe kayan ta kai ɗaki ta dawo Mama tace, "sannu, ya bada maganin?."
"Bai bayar ba Mama, wani fusatacce ne ba irin roƙon da ban masa ba amma mutumin nan da yake bashi da mutunci ko ya kalle ni ma, wai tunda babu ke babu amfanin bada magani ba. Amma a haka Dr Huzaifa yake cewa yana da kirki."
"Sai bayan kin tafi nayi tunanin hakan Manal, zuwan babu ni a kamar gwara ba'a je bane dan kin San likitoci basa son ka saka musu baki ko tambaya suka yi balle kuma ace kinje babu ni. Kin ga ai bai san ya nake jin ciwon ba balle ya bani magani."
"Amma Mama tunda na faɗa masa uzurin rashin lafiya ne ai yaci ya saurare ni." Mama tayi dariya tace, "shine ki ka sha kuka kenan?." Manal tace, "Mama ya akayi kika san nayi kuka?."
"Manali kenan, ni nasan abun kuka baya miki wahala, sannan ga muryar ki nan ta canja."
"Wallahi Mama ina tafiya ina kuka." Mana tace, "Kiyi haƙuri, Allah ya kaimu wani lokacin sai mu koma nida ke din."
"Amma Mama ciwon nan yana damun ki sosai, bana so abin yazo yayi miki yawa ne."
"Babu abinda zai yi yawa, kar ki damu."
Manal ta tashi tace, "ya bani haushi sosai wallahi, daman fuskar sa a tamke kamar mala'ikan mutuwa ko annuri babu, da gani bazai yi kirki ba." Mama tayi dariya tace, "ke kin taɓa ganin mala'ikan mutuwan ne?." Manal tayi dariya tace, "bara na kawo miki kunun ki" ta faɗa tana fita a nan ta tarar da Mubeena ta fito daga wanka bata tanka mata ba ita ma haka ta wuce zuwa ɗaki.
Da kofin kunun ta dawo a hannun ta tace, "Mama gashi." Mama ta karɓa tace, "gaskiya yau ma sai na saka sikari Manali." Manal tace, "kai Mama! Jiya ma kin sha sugar shekaran jiya ma fa haka."
"Zuciyata tana so Manal, mutuwa dai ake gudu kuma dole mu mutu. Bani sikarin na zuba."
"Dan Allah Mama kar ki sha."
"Allah sai na sha Manal, Haba kai kenan cikin hana ni abinda zuciyar ka take so, bani ki gani."
Manal ta kwance ledar ta zuba mata kaɗan jin tace Allah tace, "gashi nan na zuba miki." Mama ta juya tace, "bai ji ba, ƙara min."
"Haba Mama dan Allah, ki daina sha sugar kwana biyu kina sha sosai kar yayi miki illa."
"Ke ƙara min daga yau bazan sake ba." Manal ta ƙara mata kaɗan Mama ta juya tace, "shiyasa naso bakya nan zan sha sikari son raina, da bakya nan ai gashi har biredin da Baban ku ya rage jiya na cinye ba wanda ya sani,"
Manal kamar zatayi kuka tace, "amma Mama kin san hakan zai cutar dake sosai ko?." Mama bata ce komai ba ta shanye kunun ta tsaf Manal na zaune a gefen ta tana kallon kafin Mubeena ta fito cikin hijjabi mai kyau baƙi dogo wanda ya amshi fuskar ta tace, "ke Manal zan tafi makaranta, ina kud'in mota?."
"Bani dasu kuma Baba bai bani ba, in zaki je ki tambayi Baba kije, in baza ki ba sai ki tafi a ƙafa." Mubeena tace, "nice zan tafi a ƙafa?." Mama tace, "kin wuce kije da ƙafar ne?."
Jin mama tayi magana sai tayi shiru kawai ta wuce ta fita Mama ta girgiza kai tace, "Mubeena na da rai ba dole zuciya ta dinga min ciwo ba." Manal bata ce komai ba ta tashi ta fita ta sha mata kunun babu sikari ta fara gyara gidan kamar yadda ta saba.