Chapter 4
*BA DON MACE BA...*
✍️ *BY FATIMA FANTAH*
*BA DON MACE BA... LITTAFIN KUƊI NE A KAN ₦1000. GA MAI BUƘATA YA TURA KUƊINSA TA WANNAN ASUSUN 0421863702 FATIMA MUHAMMADU GT BANK. SAI A TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR ***. ALLAH YA BA DA IKON SIYA DA BIYA. AMEEN.*
*SH 4*
RUMAISA
Abaya kawai ta saka ta fita, Keke Napep ta hau zuwa kasuwar central market, tana isa ta ƙarasa layin masu siyar da gold, ciro zoben ta yi daga aljihun rigarta, tsayawa ta yi bakin shagon tana kallon zoben, shi kaɗai ya yi masu saura a abinda suka mallaka, idan suka siyar ba su da wani abun ƙaddara da za su cigaba da fuskantar rayuwarsu. Wani abu mai tauri ta hadiye cikin makoshinta, take hawaye masu ɗumi suka tsiyayo daga idanuwanta. Da sauri ta juya ta bar ƙofar shagon, da sassarfa ta fita bakin hanya inda za ta samu Napep, 'yan kuɗin da suka rage mata ta duba, "Ɗari uku," ta furta tana fitar da wani huci. Ba ta karaya ba ta tsayar da mai Napep ta ce ya kai ta Modoji, cikin sa a ya amince zai kai ta da kuɗin da suka yi mata saura.
Bakin tamfatsetsen gidan Yayanta aka sauke ta, tsaye ta yi tana kallonsa, katon gida ne da ya ji gini na tsara, ko ba a fada ba kallo ɗaya za ka yi masa ka tabbatar mamallakinsa ya tara manyan kuɗaɗe.
"Idan kuma kika je gidan AbuƊalib, ki sani kin je ba da yawuna ba, ba zan taɓa yafe miki ba..." Wasu kalaman Ummanta suka soma yawo cikin ƙwaƙwalwarta. Hawayen da suka zubo mata ta sharce, "Rayuwar Ummana na cikin haɗari, sannan kuma ga rashin amincewarta a kan zuwana nan... Wannan shi ne gaba kura baya sayaki..." Hawaye suka sake wanke fuskarta. "Ya Allah ka sa ni ba da son raina na ƙi bin umarnin mahaifiyata ba, ina son ceton rayuwarta ne, Allah ka yafe mini." Tafiya ta yi ta isa daidai ƙofar, kwankwasa wa ta yi sannan ta tsaya tana dakon jiran a buɗe mata.
Mai gadi ya leƙo, kallonta ya yi sama da ƙasa sannan ya ce, "Hajiya barka da zuwa." Ba ta amsa mishi ba saboda ba ta cikin yanayin da za ta amsa mishi.
"Ammm Hajiya Rumaisa, Hajiya ta ce kar a bari ki shiga gidan nan..." Ya faɗa cike da jin nauyin kalaman da furta mata. Wani kallo ta watsa mashi, "Salahu, ni kake faɗawa wannan zancen? To, da ni da Hajiya wa ya fi matsayi a cikin gidan nan, ina iya dawwama a cikinsa ita kuma wata rana za ta iya yin waje ta bar shi, kuma wallahi sai na shiga cikin gidan nan." "Hajiya na sani, amma ki yi hakuri, cewa ta yi idan na bari kuka shigo bakin aikina..." Cikin bacin ran da ke nuƙurƙusarta ta hankada shi har ya fadi ƙasa, da gudu ta shige ciki, harabar gidan babba ce kafin ta isa wurin da zai sada ta da ƙofar shiga falon tafiyar da 'yar tazara. Hakan ya sa har Salahu mai gadi ya iya cimma ta. Muryarsa a rikice, yake maimaita, "Hajiya don Allah kar ki mini silar aikina..." Sam ba ta sauraren shi sai ma ƙara ƙaimi da ta yi don isa bakin ƙofar.
BADIYYAH
Ta tagar bene ta hango su, ɗan guntun murmushi ta saki sannan ta mike ta bude kofa ta leƙo, cikin isa da kasaita ta ce, "Kai Salahu bar ta ta shigo." Tsayawa ya yi, ita ma cikk ta tsaya daga kai ta yi ta kalle ta, ta ɗora hannuwanta kan bagalar benen ta yi kyau sosai ta ƙara kiba da haske tamkar wata matar Gwamna. Wasu kwalla suka zubo mata, ɗan adam kenan ka yi ma shi rana ya yi maka dare, har abada ba za ta taba mance Badiyyah ba a cikin kundin tarihin rayuwarta. "Lafiya kika zuba min ido?" Ɗan firgigi ta yi, a hanzarce ta sa ƙafa ta cigaba da tafiya. Badiyya juyawa ta yi ta koma cikin dakin, ita ma cigaba da tafiya ta yi ta shiga cikin falon gidan.
Ƙarema falon kallo take ya zame mata sabo kamar yau ta fara ganinsa, cike da yake da kayan alatu tamkar falon wani basarake. Kallon sashen "Yaruwarta ta yi, wasu sabbin hawayen suka zubo mata ta yi saurin gogewa. Badiyya ta ƙaraso ta zauna kan kujerar da ke kallon ta Rumaisa.
Cikin sigar rainin wayo ta ce, "Rumaisa’u sannu fa, ya gida ya su Iya?"
"Uhmmm,' kawai Rumaisa ta furta, cikin ƙyama da tsanarta ta ce, "Da ma ba wurinki na zo ba, wajen Yaya na zo, yana nan?"
"Na ce ba, na sha fada muku ku daina neman sa, saboda baya da lokacinku abubuwa ma sun masa yawa, lokacinsa nawa ne ni kaɗai. A gare ku kuma ni wakiliyarsa ce, so me ye damuwar? Rashin abinci ko? Nasan ma fi yawan matsalar talakawa ta yunwa ce." Rumaisa ba ta iya furta komai ba sai na mujiya da ta zuba mata. A wulaƙance ta ce, "Laure, Laure, Laure..." Da sauri ta ƙaraso, "A kawo mata abinci..." ta ƙarashe maganar tana kallon Rumaisa.
Muryarta na rawa ta ce, "Badiyya ke ma kin sani tun da kika san mu ba mu da yunwa, kuma har kika shiga cikin rigar arziƙinmu kina wulaƙanci ba ma nema wurin ki. Ke, ke ce dai matsiyaciya, mayunwaciya, butulu. Kuma ki sani wata rana sai kin kwashi kashinki a hannu sai kin girbi abinda kika shuka, indai rana na fitowa dare na maye gurbin haskenta da duhu."
Shuru ta yi tana mata kallon rainin wayo. "Ga abinci nan an kawo miki ki ci na san matsalarki dai duk ta yunwa ce, ita ta sa kike wannan ɗumumuwan."
Hawaye suka kara wanke fuskarta, a hankali ta ce, "Ina son in ga ɗanuwana." Harararta ta yi, "Ai fa sai ki ci gaba da yi."
Mikewa ta yi ta haye matakalar bene inda part ɗinsa yake, da sauri ta bi bayanta, "Ba inda za ki je na gaya maki."
"Wallahi sai na je tunda na tabbata ɗanuwana yana nan." Fizgo ta ta yi baya hakan ya sa ta gangaro daga kan benen, tim ta faɗa ƙasa. Dagowa ta yi jin yadda kanta da kirjinta suka bugu da ƙasa, Mikewa ta yi, daga inda Badiyya take ba ta motsa ba sai kallonta da take yadda ta dafe kanta. Juyawa ta yi ta haye benen, ba ta jima ba ta dawo, Rumaisa na tsaye inda take ta fito. "Na ga kamar kanki ya ɗan bugu, ga wannan ki sha paracetamol." Kudi ta tilla mata bandir daya na kilon Najeriya. Hannu ta sa ta dauki kudin. "Ba zan ƙi ɗauka ba saboda haƙƙinmu ne, amma Insha Allah kudin nan da kike jeho wata rana sai kin nemi daya daga cikin darinsu kin rasa, ƙarya fure take ba ta 'ya'ya."
"Yar dariya ta yi sannan ta shige part dinta har da bugo kofar da karfi don ta ji. Jinjina kai Rumaisa ta yi sannan ta juya ta nufi kofar fita. Tafiya ta cigaba da yi tana yi tana zubar da hawayen baƙin ciki, ba za ta fada ma Ummanta cewa ta karbo kudin wajen Badiyya ba, za ta yi shuru tare da fada mata wani ya taimaka mata da su.
Kai tsaye gida ta wuce, samu ta yi Umman na barci, sai Inna Uwale zaune gefe ta zuba tagumi. Ganin ta ya sa ta sauke hannun, "Nawa aka sayi zoben?"
Juyawa ta yi ta kalli Umman, tabbas bacci take yi. Durƙusawa ta yi wajen Inna Uwale, muryarta ƙasa-ƙasa ta ce, "Inna na je gidan Yaya ne, sai dai ƙudirina na ganinsa bai yiyu ba... Inna Uwale anya ko za mu sake ganin Yaya AbuƊalib? Anya zai sake dawowa cikin rayuwarmu?" Ta ƙare zancen hawayenta na ƙara yawa.
"Za mu sake ganin shi, kuma zai dawo gare mu, saboda ƙarya fure take ba ta 'ya'ya, ki bar ta ta sha sharafinta, wannan na ɗan lokaci ne kamar ƙiftawar ido da bismillah za ki ga komai ya warware gaskiya ta ɗauki kambunta." Numfashi mai ɗumi Rumaisata furzar. Kuɗin ta fiddo daga cikin abaya ta miƙa ma Inna Uwalen, "Dubu ɗari ne Inna, abun baƙin ciki da takaici jifa ta ta yi da su." Kaɗa kai kawai Inna Uwale kawai ta yi. "Yanzu tunda an samu waɗannan 'yan kuɗin asibiti za mu koma, a yi mata awon nan da suka ba da."
"To Inna, ni ma shi nake ta so a yi, saboda jikin Ummana ƙara nisa yake yi, kullum jinina kan akaifa yake Inna..."
"Insha Allahu ba abinda zai same ta, ai cuta ba mutuwa ba ce za ta ji sauƙi Insha Allah. Kuma zan yi duk yadda zan yi a shiga lamarin nan."
"To Inna Allah ya ba da sa a."
"Ameen." Ta faɗa.
★★★★★
Kuɗin da Yunus ya ba ni kamar yadda ya faɗa mini sunanshi suna da dama, a dunƙule naira dubu ɗari uku ne domin daurin Kilon Najeriya ne uku a haɗe. Na ɗauki kwanaki masu tsayi ban fita don bara ba, sai dai kamar yadda nake zuwa barar ina fita ina bayar da sadaka a cikin kuɗin da Yunus ya ba ni. Tun daga ranar ban sake saka shi a idona ba, domin bai sake zuwa inda nake ba, duk da na ta'allaƙa rashin ganinsa da nake yi a kan rashin zuwana Ipaja bara da safe lokutan da ya fi zuwa yana bayar da taimako. Na fi zuwa da rana bayan na gama 'yan abubuwan da nake, gami kuma da cikin jikina da ya ƙara mini nauyi.
Juyin da abun ƙaunata ya yi ya dawo hayyacina, hannu na ɗora kan cikina, zancen da muka saba daga zuciya zuwa zuciya muka fara, "Abun ƙauna... Yau ba mu gaisa ba ko? Amminka tana gaishe ka, ya ka wayi gari?" Shuru na yi ina sauraren shi, ina ji kamar yana amsa mini. "Yawwah kana lafiya ko abun ƙauna. Ni ma ina lafiya, kuma na daina shan wahala sosai, ai ka gani ko abun ƙauna."
Na daɗe zaune ina hira da halittar da na fi ƙauna a cikin duniyata, wacce ba ni da masaniya game da jinsinta, ina dai tsananin ƙaunarta sama da son da nake yi wa ruhin da ke manne da gangar jikina. Sai da na yi mai isata sannan na miƙe. Bokiti na ɗauka da kwandon wankana, wanda na samu damar siyen su bayan na samu kuɗin da Yunus ya ba ni. Ruwan da Ayuba ya tara mani na ɗiba na fita domin yin wanka.
Zaune na iske Saratu bakin toilet ɗin tana ta busar da hayaƙin taba, ɗago jajayen idanuwanta ta yi ta kalle ni, gabana ya faɗi rass na ja baya domin ban san me ta shirya ba, domin ina jinta, shi kan shi Ayuba da Mahaifinta fama suke da ita, amma sam ba ta shiga shirgina, ko gaisuwa ba ta haɗa mu. Kallona ta yi sama da ƙasa, "Wai ke a Alaba kika kwaso wannan cikin kika zo nan ki haife mana shi? Ubansa ya gudu ya bar miki shege, shi ne kika zo nan ki haife ki gudu ki bar mana ko..."
Har tsakiyar raina na ji saukar kalamanta tamkar ta watsa mini ruwan zafi, karo na farko da na ji baƙin cikin rashin yin maganata tabbas da na sauke mata kalamai daidai da wawan zancen da ta yi mini. Kaɗa mata kai kawai na yi, alamun ba haka ba ne.
Taɓe baki ta yi, "To bara ki ji, na farko daga ƙarshen watan nan za ki fara biyan kuɗin haya domin zaman cin banzar ya isa haka. Na biyu kuma... Ki tabbata ba ki haife mana shege a gidan nan ba, na ga alamu nan da ɗan lokaci kin haihu ba wani da nisa ba, so ki koma inda kika baro ki haifi abinki, domin mu nan namu sun ishe mu."
Kallonta nake yi, baƙa ce wuluk kamar an mata fenti da kwalta, gefen kumatunta na hagu an yi mata ƙaton hetali 'bille'. Juyawa na yi na kalli gidan, bayan ƙazni da warin naman da Ayuba yake siyarwa da yake damunmu wasu lokutan, ga rashin gyara a haka take so na riƙa biyan ta kudin haya, shi ko Ayuba ɗan uwanta cikin tausayawa ya ce, "Na zauna iya lokacin da na ga dama, me ya sa ita 'yar uwata mace ba za ta tausayawa matantakata ba? Me ya sa ita ba za ta rufa min asirina ba ko da kuwa cikin jikina shege ne kamar yadda take iƙrari?"
"Kin zuba mini idanuwa kaman na mage. Ay kin ji abinda na ce ko? Idan kika ƙi yin abinda na ce za ki sha mamakina..." Miƙewa ta yi ta bar ni tsaye kamar dasasshen icce.
"Wataƙil ta ga sauyin da kika samu, domin kwana biyu ay ba ta fita tana nan tana masifa. Shi ne take son sai ta samu a jikinki," Wata zuciyar ta faɗa mini. Kada kai kawai na yi, domin tuni halayen 'yanuwana a jinsi ya daina ba ni mamaki, kuma tabbas zan yi duk abinda ta ce, har zuwa lokacin da abun ƙaunata zai diro duniya, wanda za mu samu a nutse mu nemi mafitar rayuwarmu.
Toilet ɗin na shige na yi wankana, ina fitowa na wuce ɗakina. Mai na soma shafawa, gani na yi gaba ɗaya jikina ya yi ɗan kumburi ba da yawa ba, a kintacena cikina ya shiga wata na bakwai, shuru na yi ina bitar abubuwan da ke kawo kumburi ga mai juna biyu. Numfashi na sauke, domin ban san ta ina zan je asibiti ba, yadda na saba addu'a nake Allah ya raya min abun ƙaunata ya kawo mini shi lafiya cikin wannan duniyar tamu mai cike da rikici.
Bayan na gama shiryawa kai tsaye Ipaja na nufa. Kuɗi ne dubu biyu na riƙo a hannuna domin yin sadaka kamar yadda na saba yi tun da na samu kuɗaɗen da Yunus ya ba ni.
Inda Maman Nana take zaune na nufa, duk da ba na magana, Maman Nana ta zayyana mani irin halin ƙuncin rayuwa da take ciki a lokutan da nake zuwa bara. Na tausaya mata matuƙa, hakan ya sa duk lokacin da na zo da 'yan kuɗina ita nake ba wa. Kamar koyaushe zuwa na yi na ba ta kuɗin. "Ban san sunanki ba har yau, amma yadda kike taimaka mani ni ma ba zan gajiya da yi maki addu'a ba kamar yadda kika buƙata. Allah ya ba ki mafitar rayuwarki. Hannuwa biyu na haɗa alamun yi mata godiya.
Ban jima ba na tashi domin komawa gida, tafiya nake yi a hankali. "Baiwar Allah... Baiwar Allah..." Na ji muryar da na tabbatar mammallakiyarta mace ce na faɗa daga bayana. Juyawa na yi domin ganinta, muna haɗa na ji gabana ya faɗi, zuciyata ta buga da ƙarfi. Da ƙyar na fizgo numfashina da na ji yana kaiwa da komawa, "Sannu baiwar Allah..." Ta faɗa mini cikin tsananin tausayi. "Ai na san ba ki magana, sannu kin ji. Wallahi kullum na zo gurin nan ina tausaya maki matuƙa." Ta ƙare zancen cikin gurɓatacciyyar hausarta da ba ta fita.
Kuɗi ta miƙa mani, "Ga wannan kin sayi wani abun kin ji." Karɓa na yi, na haɗa hannuwana biyu ina mata godiya.
"Sai an jima." Ta faɗa tare da juyawa ta yi tafiyarta. Ni ma juyawa na yi na tafi. Kuɗi ne dubu uku ta ba ni. Kai tsaye gida na koma, zaune na iske Saratu a ƙofar ɗakinsu tana waya, sam bana jin yaren da take magana da shi wanda nake tsammanin yarbanci ne. Shigewa na yi ɗaki na ɗora girki da nake yi kan murhun gawayi, bayan na ɗora na yi alwala domin gabatar da sallar azahar.
*KI MALLAKI NAKI A KAN ₦1000 KACAL.*
*CONTACT ME @*** IF YOU'RE INTERESTED*
*TAKU MAI ƘAUNAR GANIN FARIN CIKINKU A KOYAUSHE, FATIMA MUHAMMAD SANI AKA FANTAH. NAKE MUKU FATAN ALKHAIRI KU KASANCE CIKIN ƘOSHIN LAFIYA.*
*KU DANNA BLUE LINK DA KE ƘASA KU YI FOLLOWING WHAT'S APP CHANNEL ƊINA DOMIN SAMUN DUKKAN SHAFUKAN ƊANƊANO.*
***
*DON'T FORGET TO LIKE👍 COMMENT💬 SHARE🔀*