005
*BAYA DA ƘURA*
FitattuBiyar2025
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11
©️ *Nana Haleema.*
***
*BOOK 1*
*Page 005.*
Bebi bai bar asibitin ba sai bayan azahar kai tsaye gıda ya koma ya shiga ɓangaren Mama ya samu Mimi zaune ganin sa ya saka tace, "Sannu da zuwa."
"Ina Mummy?" Ya faɗa yana kallon ta.
"Suna ɓangaren Abba har su Yaya isma'il." Baice komai ba ya juya zai koma Mimi tace, "Yaya." Ya juyo yana kallon ta yace, "ya akayi?."
"Akan zuwa get together ɗin ne kace zaka sake a kaini." Ya kalli Agogo yace, "ƙarfe nawa ne?."
"Zuwa biyar." Yayi hanyar fita yana cewa, "ki tuna min bayan la'asar." Kafin ta bashi amsa ya fice ya shiga ɓangaren mahaifin nasu da sallama aka amsa gabaɗaya yayyen sa maza suna nan da kuma iyayen nasa mata guda biyu da Yayar sa Maryam.
Zama yayi kamar yadda suke zaune baice komai ba suma basu ce ba kafin Yaya isma'il da ya kasance babba a gidan yace, "Abba kayi shiru baka ce komai ba, in ta aikin ka ne neman da muke yi ya isa mu ciyar da gidan nan gabaɗaya, kayi zaman ka ka huta siyasar ma a haƙura tunda bata karɓe ka ba. Muna cikin damuwa a duk sanda ka saka ƙafa ka bar garin nan Abba."
Abba yayi murmushi yace, "kune ku ka damu da zamana iyayen ku basu damu da hakan ba." Yaya Bilal wanda yake bin babban yace, "Abba ta ya zasu ce basa damuwa da zaman ka? Ai duk wanda zai damu da zaman ka a gidan nan a bayan su yake."
Abba ya sake yin shiru kafin yace, "Gasu nan ka tambaya, akwai wacce tace min ga abinci kaci tunda nazo jiya da daddare? Ko wacce tashi tayi ta fita ina magana ma suka mayar dani kamar shashasha kaga kenan basa buƙatar zamana a gidan nan. Yau da safe da na kira Jamila nace ina abincina cewa tayi manta ina nan, sai da na kira Hauwa itama sai cewa tayi bara ta saka Mimi ta dafa an cinye. A haka suke so na zauna?."
"Abba ko ni na manta a gidan nan ka kwana Allah y sani, bamu haɗu da asuba hakan ya saka na sake mantawa dan mun riga mun saba rayuwa babu kai a gidan nan" Bebi ya faɗa yana kallon Abba ɗin.
Abba ya kalle shi kamar zai magana sai ya fasa dan kaf yaran masa Allah ya saka masa kunyar Adnan, haka kawai in yayi magana sai ya kasa musa masa haka yake ji, kuma daman kaf gidan babu mai iya tunkarar sa da magana ko wacce iri ce sai shi ɗin.
Bebi ya sake cewa, "Abba maganar gaskiya wannan tafiye-tafiye da kake bashi da amfani bashi da fa'ida, in ya zama dole sai anyi ka dinga tafiya da matan ka ni ka bar min na gidan a hannuna zan kula dasu iyakar iyawata. Tafiyar nan da ka ke akwai ɗaukar haƙƙin su, domin ko wacce tana da hakkin a kanka, a ture mu ƴaƴan ka ne dole mu jure ko me zaka yi amma su matan ka ne kuma mata ne, barin su hakan ba ƙaramr illa bace a gare su" ya faɗa a sanyaye yana kallon mahaifin nasu da shima shi yake kallo dan yasan daman babu mai iya masa maganar in ba shi ɗin ba.
Abba yace, "tafiya tana da mahimmaci a wajana kuma dole sai nayi, iyayen ku da kake magana a kai babu wacce ta damu da zamana dani da babu duka ɗaya ne. Na dawo zanyi sati amma babu wacce ta nuna hakan ya mata daɗi sai ma zamewa da suke kamar sun haɗa baki, Tunda hakan suke so nima ai hakan nake so ba shikenan ba?."
Bebi ya sake cewa, "Abba an saba da zama babu kai ɗin ne ya saka ka ke ganin kamar ba'a damu da kai ba, an damu wallahi kawai ana nuna hakan ne saboda kwanakin da aka ɗauka baka nan, kuma mun san ba jimawa zaka yi ba zaka sake cewa zaka tafi. Abba koda suna fushi ne akan rashin zaman da baka yi ba akan komai ba."
Abba yace, "Adnan ban yiwa ko wacce dole a cikin su sai ta saurare ni ba, sannan babu ta yadda za'ayi a hana ni yin abubuwan da suke gabana ka gane ko?."
Bebi yayi shiru baice komai ba Abba ya kalli su Mama yace, "in fushi ma kuke ya kamata ku sauke dan bani zai yiwa amfani ba." Shiru falon yayi babu mai magana kafin Abba ya tashi tsaye yace, "in ba ku da magana ni zan fita naje na samu abinci tunda a nan an hana ni" yana faɗa ya fita ya barsu a zaune kowa ya kasa magana a cikin su.
Mama ce ta fara tashi ta fita Bebi ma ya tashi yabi bayan ta aka bar Mamy da nata yaran a falon Abba kafin suma su fito.
Mama na shiga ɗaki ta Bebi ya biyo bayan ta yace, "Mummy wannan fushin da ku ke yi bashi da amfani ƙara cutar daku zaiyi, Abba ko a jikin sa ya kamata kiyi haƙuri komai ya wuce." Mama ta taɓe baki yace, "ba'a haifo shi ba wallahi, daman ai mun saba zama babu shi kuma babu abinda ya dame mu, zamu cigaba da zama babu shi ɗin babu abinda zai dame mu kuma."
Zaiyi magana tace, "Kaga Bebi wannan ba maganar ka bace, ka ƙyale mu kawai kaje kayi abinda yake gaban ka, indai mahaifin kane takaicin sa kuka zai saka ka." Baice komai ba ya fito ya shiga ɗakin sa ya zauna yana tunanin mafita. Ƙarar wayar sace ta katse shi ganin sunan Hamza ya saka ya ɗauka baice komai ba sai daga baya yace, "to zan zo" yana faɗa ya yanke wayar ya fesar da numfashi mai zafi.
Matsalar Abba, da maryam da kuma Lubna suna neman tarwatsa masa zuciya, ko yaushe cikin tunani su yake baya barin zuciyar sa ko kaɗan. Tashi yayi ya shiga ɗaki yayi wanka ya canja kaya ya ɗauke key na mota ya fita daga gidan gabaɗaya
Lafiyayyen gidan abinci ya nufa ya faka motar ya ɗauki waya yace, "gani kuna ina?." Kashe wayar yayi alamun an bashi amsa sannan ya fito ya shiga ciki. A zaune ya hango su su biyu Hamza yana shan lemo shi kuma Huzaifa yana shan ruwa, ƙarasawa yayi ya zauna yace, "Yanzu ya ake ciki akan maganar shigo da machines ɗin?." Hamza yace, "Bebi kalli wata yarinya kamar dan kai aka ajjiye ta. Kyakykyawa irin wacce ka ke so, gata fara har tafi Ruman kyau." Juyawa Bebi yayi ga inda aka nuna masa yayi karo da kyakykyawar budurwa a zaune ita da wata suna cin shawarma suna ta hira. Kyakykyawa ce sossi kam gaskiya bazai ƙaryata kan sa ba tana da kyau.
Ɗauke kai Bebi yayi yace, "muyi abinda ya tara mu a nan bana son ɓata lokaci kun sani." Huzaifa yace, "to mun ji wanda yasan mahimmacin lokaci, ka dinga sakin fuska don Allah wannan ɗaurewar ba kyau yake maka ba wallahi."
"Haka Allah ya yi ni, zaka canja ni ne?."
"Ka dinga dai sassauta fuskar, haba kullum fuska a ɗaure shiyasa ake cewa baka da kirki saboda fuskar ka."
Zaiyi magana aka yi masa waya ganin Mimi ce ke waya sai ya ɗauk yace, "kije Saminu ya kai ki amma kar kiyi dare na faɗa miki, wallahi kika kai dare ranki ne zai ɓaci kuma kin kori gaba" abinda yace kenan ya yanke wayar baice komai ba.
Hamza yace, "ƙanwa fa kenan ake yiwa wannan kashedin, Anya zaka bar matar ka zaka dinga barin ta fita kuwa?." Baice komai ba ganin hakan sai suka fara tattaunawa akan abinda ya ajjiye su.
Ɓangaren Mubeena a kan idanun ta Bebi ya wuce Bily tace, "Kai Mubeena kin gani handsome ya wuce ko kallo ma bamu ishe shi ba?." Mubeena ta kalli Bebi a lokacin yana zama tace, "wannan ne wani handsome? Ki duba abu baƙi dashi kice masa handsome?."
"Kee Mubeena bana son sharri, wannan ne baƙi dan kina ganin kanki kamar kina wanka da madara shine zaki kira wannan baƙi? Ina laifin kice chocolate."
"In fari ne kawai fari ne, in baƙi ne kawai baƙi ne. Ba wani chocolate duk ƙarya ce."
"Amma yana da kyau sosai, kuma akwai naira daga ganin sa ai."
Mubeena tayi dariya tace, "ni ai nafi ƙarfin ɗan mai kuɗi sai dai mai kuɗin da kansa. Ke ni yanzu samari ma ba burge ni suke ba, na fi son manya wanda suka san daraja ta."
Bily ta bata hannu suka tafa suka dariya da hira kafin su tashi su bar wajan. A inda Bily ta ajjiye mota suke a tsaye sai suka ga an sauke glass ɗin wata mota mai kyau ance, "ƴan mata adon gari, tsayuwar nan baza ku gaji ba?." Dukkan ya suka kalli wajan suka ga mutum babba a cikin mota yana jifan Mubeena da murmushi mai kyau.
Ganin kalar sa irin wanda take nema ne sai tayi murmushi itama tace, "wayar sister na ta faɗi shine ta ɗauko."
"In babu damuwa kizo muje na kai ki a ragewa sister tamu nauyi." Mubeena ta kalli Bily suka yi murmushi Mubeena tace, "da ka barshi ma."
"Bazan barshi ba, ki taimaka kizo muje." Mubeena ta kalli Bily tace,"Sis min haɗu" ta faɗa tana shiga motar Alhaji Mu'azzam Alhassan.
Tafiya suke yi ko ina na motar a kulle da baƙin glass sanyi ya gama gauraye motar ya kalle ta yana murmushi yace, "ya sunan ki?." Mubeena ta sauke numfashi tana murmushi tace, "Mubeena." Ta faɗa can ƙasan maƙoshi tana kallon sa yayi murmushi yana kallon titi yace, "suna mai daɗi. Ina zaki je Muna ta tafiya ban tambaye ki ba?." Murmushi tayi tace, "Zoo road nake."
Ya sake kallon ta yace, "an taɓa ce miki kina da kyau Mubeena?." Mubeena tayi Farr da ido tace, "har na gaji dajin hakan." Yayi murmushi yace, "yau na sake maimaita miki, bai kamata ki gaji ba kina da kyau sosai."
"Thanks you."
"You deserve it." Murmushi ta sake yi ya kalle ta yace, "duk da ba'a tambayi sunana ba zan faɗa miki, sunana Alhaji Isah shugaban kamfanin golden noodles" ya faɗa yana ɓoye asalin sunan sa kamar yadda ya saba yi in dai a Kano ne.
Mubeena farin ciki ya mamaye mata zuciya bata ce komai ba yace, "naji daɗin haɗuwa dake." Itama tayi murmushi tace, "nima haka."
"Gamu a zoo road." Mubeena ta kalli titn ta nuna masa inda zai bi ya shiga da motar har ƙofar gidan su Bily tace, "nazo gida." Ya kalli gidan ya kalle ta tace, "har sauri kike ki tafi ko?." Tayi murmushi tace, "A'a."
"Ki bani number ki mu dinga gaisawa ko baby?." Mubeena tace, "to Baby."
Yayi dariya sosai yace, "Ni ne Baby?."
"Uhum!" Ta faɗa tana kallon sa. Murmushi yayi ta karanto masa lambar ya rubuta ya kira sai tace, "wayar na jakar bily in na sauka zan duba."
"Nasan ƴan mata ba'a raba ku da wannan OPay ɗin, let me check a saka miki na siyan data." Mubeena tace, "thanks you."
Baiyi magana ba yana danna waya ya tura mata kuɗi kafin ya kalle ta yace, "zuwa anjima zan kira ki." Mubeena tace, "okay Baby, thanks you." Yayi murmushi yana mata wani irin kallon ƙulla yace, "you deserve anything's from me baby." Buɗe motar tayi ta fita ya bita da kallo yana murmushi har ta shiga gidan kafin ya ja motar ya bar wajan yana jin farin ciki a zuciyar sa dan ya samu irin ƴan matan da yake nema. Gashi da alama sabuwa ce dan yanayin yadda bata sake ba ya nuna masa ba ƴar hannu bace, hakan ya saka shi farın ciki sosai domin irin ta yake nema ya koya mata komai sannu a hankali ta zama yadda ya ga dama, yayi kiɗan sa ya taka rawar sa.
Itama Mubeena da wannan farin cikin ta fita, ta samu abinda take nema, Wato ta samu mai kuɗi ba ɗan mai kuɗi ba, kuma babba ba yaro irin wanda take so gashi har ya fara bata kuɗi daga haɗuwar farko, a haka ta shiga gidan su Billy a guje.
Mubeena na shiga gidan ta samu Mummy bata falo ta shiga ɗakin Billy a guje ta same ta tana sallar magriba itama sai ta ajjiye mayafi ta shiga banɗaki tayi alwala ta fito ta yayar da sallah. Tana idarwa ko salati batayi ba ta kalli Bily tace, "nayi mugun kamu Bily, shugaban kamfanin golden noodles, ke kin san ko ina akwai wannan noodles ɗin, har a ƙasar waje." Bily tayi dariya kaɗan tace, "kin ji daɗi, kin samu kalar wanda kike so, sai ki yi sadaƙa."
Mubeena duk ta ruɗe saboda farin ciki, ta rasa abinda yake mata daɗi, wanda take burin haɗuwa da irin su dasu ta haɗu.
"Innalillahi! Bily burina ya cika Alhamdulillah." Bily tayi dariya tace, "ga wayar ki nan Ana kira tun ɗazu." Hannu na rawa ta ɗauki wayar taga lambar sa da sauri tayi saving tana duba abinda ya saka mata.
Ihuuu tayi tace, "bily two hundred thousand ya saks min, dubu ɗari biyu daga haɗuwa kawai." Bily ta taɓe naki yace, "duk ba wannan ba, ya kamata ki canja wannan banzar wayar hannun taki sai anfi ganin girman ki walalhi."
"Yanzu wacce zan siya?."
"iPhoton 13 zuwa sama ya kamata kiyi, shine zaki fito a big girl ɗin ki, ko talaka ne ya ganki da yaga wayar hannun ki yasan kin fi ƙarfin sa, wannan waya in kina fito da ita kunya kike bani."
Mubeena tace, "Yanzu ina zan samu kuɗin iPhone 13?." Bily tace, "ki dai san abinda zaki yi kawai, Allah yasa Alhajin ba ɗan iska bane, dan yawancin manyan nan wani lokacin ba na gari bane, sai kiga mutum da farin gemu amma ɗan iska ne." Mubeena tace, "in ma shine shi ya sani, nidai na tara kuɗi kawai." Bily tace, "Yanzu a nan zaki kwana ne?."
"A nan zan kwana bazan koma wancan gidan naje an ɗauke wuta ba." Bily ta tashi tace, "to nidai yunwa nake ji, bara na dafo mana indomie."
Jin hakan sai Mubeena tace, "Kee kuma shine mai kamfanin golden noodles fa." Bily tace, "kin faɗa min ai, duk kin ruɗe walalhi, ki nutsu kar ya gano baki taɓa kamar sa ba" tana faɗa ta fita Mubeena ta baje a akan gadon tana jin farin ciki na ratsa zuciyar ta.