5
by @maidambu41
*❤️🩹SO da CIWO❤️🩹*
®©Ramlat A Manga
Mai_Dambu
05
Baffa Haruna yana da Yara uku, abin da yasa bai tara yara dayawa ba kasancewar shi yana da laluran sickle cell, a yadda naji labarin ya auri Aunty da bata da shi tayi ta haihuwar Yara suna mutuwa wasu ayi suna wasu kuma ba za ayi suna ba, wannan dalilin yasa koda aka haifi Raheemah suka dauki soyayyar duniya suka daura mata, ba iya ita ba kaf danginmu ana son Raheemah kasancewar ita ce wacce ta tsaya sai kannenta daya biyu, Umar ana kiranshi Junior, sai Mus'ab, Heemah ce babba. Heemah ta bani shekara daya a duniya domin ita tana shekara sha bakwai ce, amma na fita girma domin ka ganta zaka ɗauka yar sha biyar ce, bani manta wani lokacin da ciwonta ya tashi tayi ta suma, akan an gyara min dakina kamar na disnep princess, saboda yayuna mata idan aka jin karshen gayu na bugawa a jarida, kasancewar ni daya na tashi babu wani a gidan sai yayuna maza babu mata yasa aka ɗauki duk wani kauna da kulawa aka daura min, wanda yasa ni kaina nake jin kamar wata princess. Tun ina Yarinya na taso da farin jini da soyayyar iyaye da yan uwana, sannan kakata mace Dadah tana sona sosai. Haka kawai Addah Ma'u da take auren babban mutum suna yawan tafiye-tafiye, haka yasa idan suka dawo zata zo da tsaraba ta gyara min dakina domin ita ce ta fara cewa a ware min dakina domin a tsakaninsu Mama da Yaya nake kwana, dakinsu na yan matanci aka gyara min aka saka min gado irin na Disnep princess, an gyara min ko ina kamar wata yar tsanar Barbe, Baffanmu ma idan yayi tafiya ya dawo haka zai zo min da kayan kwalliya.
Yaya sunanta Abidah yar jahar Gombe ce, itama bafulatana ce, yar babban gida da ta fito daga familyn Doctor Hayatu, babban likitan Muslunci, sannan Sheikh a bangaren addinin Musulunci, Yaya ita ce ya ta biyu a gidansu sannan kakan Yaya da Dattijo ya'yan yan uwa ne wato Yaya itama yar uwar Baffanmu ce, koda yake ana faɗin Mahaifiyarsu Baffanmu ce Fulanin tashi ce., tana da yayu maza da mata. Sai Mama sunanta Zainab ita yar uwar Baffanmu ce, kasancewar yan uwa ne daga Mama har Yaya yasa baka gane dan waye wannan, sannan dukkansu farare ne kamar tsada amma ni nayi duhun fata kasancewar kakata Dadah itama tana da duhun fata, duk yan gidanmu farare ne sannan dogaye, ni da na tashi sai nayi dan doro kaɗan, ban yi tsawo ba kamar na sauran Yan uwana, yadda nake samun gata yasa kaf dangina ake min kallon wata shalelen dangi.
Baffa Junaid. Yana aiki da hukumar custom yar abokinsa Hamma Jamal ya aura, kasancewar shima ana da dangantaka da shi, kuma na kusa bana nesa ba danginmu bakiɗaya fa bama auren bare, duk wanda zaka ji an aura ko an auro tow Yan uwa ne da abokan arziki da aka zauna zaman amana,sannan uwa uba fulani domin Dattijo bai yarda da auren bare ba, gani yake kamar akwai matsala a auren bare don an tab'a yin auren aka samu matsala har sau biyu tun kafin su Baffanmu su yi aure.
Baffa Junaid yana da Yara amma maza uku mace daya, Umar wanda ake kiranshi Alfah, sai Haris,sai Abdullahi, sai Haseenah. Kusan ita ce sa'ata amma yadda basu shiri da Heemah yasa nima nake janye ta a jikina. Ina matukar son Raheemah, haka yasa naki ƙawance da kowa na rungume ta don duk lokacin da nayi Sabuwar kawa sai Raheemah tayi ta fushi bana son fushinta yana min ciwo, domin gaya min take don Allah ya bani lafiya kuma ana sona shi yasa nake janye-janyen kawaye. Ni kuma bana son tashin hankali, ban iya ba kuma bana son koya.
A wannan duniyar Allah ya min baiwa da shiririta, tsokanar fada, shagwab'a, kukan banza domin har yau ina kukan banza wanda yasa Mama bata kaunar ta ga ina kumbure-kumbure, a yadda na tsara rayuwata shine ina son nayi karatun boko mai zurfi, amma ina family dinmu zaki yi karatun amma sai a dakin Mijinki. Wannan ma duk me sauki ne amma ni har ga Allah ina da zabin irin mijin da nake so, sannan a bangare guda bana son auren zumunta. Saboda ina yawan ganin Addah Rukayya ana musu Shari'a, Mijinta Kakanshi dan uwan Dattijo, sannan baban shi abokin Baffanmu ne, ba ita kadai ba hatta gidan Hamma Jamal kullum fada suke da Nafisa, fada kamar zasu rabu saboda kawai yana niman aure ba zaman lafiya sam.
Wannan shine labarin ahalinmu bakiɗaya, amma fa na rasa gano dalilin da yasa suka tsani Aunty. Sai dai a tafiyar gidanmu bana ce ina sane da kome ba, domin kuwa ba kome na sani ba. Kuma Yaya da Mama basu koya mana lallai sai mun ji kome ba, Aunty itama yar uwa ce, amma na nesa, don kuwa ita tace taji ta gani tana son Baffa Haruna, aka yi kome cikin kwanciyar hankali da girmamawa. Sai dai a yadda nake kallon zaman Yaya sun fi shiri da ita, Mama kuwa da Aunty Nusaiba matar Baffa Junaid, sannan daga ɓangaren Mama da Yaya ba zaka tab'a ganin wani abu na kishi ba, domin sun iya sarrafa kansu kuma sun san abinda zasu yi. Kishi ya hadu da wayewa sai ya zama babu wnada zai d'aga kai ya kalli wani abu na ki daga gare su..
----------
Buga kofar dakinmu aka yi na bude idanuna da barci me nauyi ya dauke ni. Tashi Heemah tayi ta bude kofar. "Kina nan ne?" "Eh Aunty" leka dakin tayi tana faɗin. "Maama bata farka ba ne?" "Eh bata tashi ba, wani abu kike so?" Ta fada tana rufo kofar, murmushi tayi ta ce. "A'a kawai nazo duba ku ne." Bude kofar Heemah tayi ta shigo dakin, ta kwanta. Wayata da take gefen inda take kwance yayi kara, ta dauka a hankali tana kallona barcin da ya ci karfina yasa ta ajiye wayar itama ta kwanta. Karfe daya na rana muka farka bakiɗaya. Mika nayi ina salati, "Heemah !" "Na'am Princess!" Ta fada tana me ɗaukar towel dina tana daurawa zata nufi banɗaki. "Dazun waye ya zo?" "Aunty ce tazo duba ni." "Ok!" "Yawwa an kira ki a waya." Ta faɗa tana mika min wayar, amsa nayi ina kallonta. Yadda fuskarta babu wasa nace mata. "Lafiya dai ko?" Tab'e baki tayi tana faɗin. "Hamma Sharahbil ne ya kira ki!" "Oho!" Na faɗa ina ajiye wayar don bana son ta dauka wani abu ne nasan yanzu nace zan bi kiran don na nuna mata ina da wanda zan aura ne. Asalin jin haushin Hamma Sharahbil take, haka yasa na mike ina faɗin. "Bari na dauki kayan wanka na nufi dakin Mama nayi a can." "Nan fa?" "Ke zaki yi a nan!" Wani irin kallo ta min tana faɗin. "Malama daukar wayarki zaki yi don na hanaki sakewa." "Laaa ji ki da wani batu, wayar ma a nan zan barshi!" Na shiga ban dakin na dauki kome nawa na fito, na wuce dakin Mama da take zaune akan abin sallah, a shagwab'e na kalleta. "Mamana ni ɗaya." Bude min hannu tayi tana faɗin. "Auta mowar Ya'ya, kin tashi lafiya?" Kwantar da kaina nayi a kirjinta ina faɗin. "Lafiya lau Mama, me kuka yiwa Baffanmu na karyawa?" "Chips da sauce din koda, sai kunun gyada da alkama." "Mamana Ubangiji ya bar min ku!" "Amin Autana! Maza je kiyi wanka sai ki zo jiya an kawo miki kayanki na bikin Bakir!" "Yawwa Mamana!" Na wuce banɗakinta na kwanta a ruwa sai da na jima kafin nayi wanka, na fito na samu ta dauko min kayana a dakina ga wayata a gefe. "Mama Heemah ta tafi ne?" Murmushi tayi ta ce min. "Eh!" Ta fada min a takaice, "Bata karya ba fa." Ina son fita, "dawo nan ko ki saka kaya." "Tow!" Na fada ina kallon yadda ta haɗe rai, shafa mai na nayi ina kallonta, ta fita sai gata da kit din kayan makeup dina, na kalleta ajiye min tayi ta zauna a bakin gadon ta kalle ni da kyau. "Bayan ke waye ya san password din wayarki?" Yadda tayi maganar a dake nace mata. "Heemah!" "Bayan haka sunan mijin da zaki aura me kika saka?" "Hamma Sharahbil!" Gyada kai tayi tana faɗin. "A wannan rayuwar da kome ya zama abin tsoro, ki kula da wanda zaki yi mu'amala da shi kin ji Princess." Gyada kai nayi ina mai da mata da murmushi, Hadiza mai aikinmu ta shigo min da abin karyawa ta kalle ni ta ce min. "Hajiya yarinyar nan anya bata fi karfin sharahbil ba? Ku ga yarinya sai kace yar tsana roba, Hajiya dai da yadda za ayi wallahi bana hango auren Uwar dakina nan kusa, ku ga mace kamar wacce aka sassakata da zinari da madara." Kurawa Hadiza idanun nayi kafin na tura baki nace mata. "Ni wallahi Aunty Hadiza ko daina fisabiilillahi ji yadda kike zagina." "Wayyo, ni ban ga abin zagi ba ko Hajiya? Kawai na fadi abin da na sani ne." Murmushi Mama tayi tana faɗin. "Dijah je ki aikinki, naki wayon yau Autana bata da kudi nima zan tambayo mata Alhaji ne." "Kai Hajiya ni ba roko nake ba, Hajiya da gaske nake gaya miki." Ta fada tana dariya barin dakin tayi tana faɗin. "Koda yake Hajiya Uwar dakina fa bata iya girki ba!" "Eh ai na tausayawa gayen nan da yake mayye ne ya makalewa yarinyar nan da kana ganinta ka ga bera!" Kwal-kwal nayi da idanuna ina kallon Mama, Hamma Umar ne tare da Hamma Salim. "Ke yanzu fisabiilillahi babu me gaya miki gaskiya ne? Wallahi sam baki hadu ba, ga muni kamar kashin dare." "Mama!" "Baffa tashi ka bar min dakina." "Mama maganar kudin nan ya kawo mu!" "Baffa ya jaza muku ba zan bayar ba kuma ba zan gayawa Alhaji ba." "Don Allah Mama ki rufa mana asiri ki bamu wallahi ba zamu kara tsokanar goshi ba!" Tashi nayi ma fita a dakin da kofin kunnuna da plat din dankalin, bangaren Baffanmu na nufa da sallama na shiga, ina ganin shi na fashe da kuka. "Autana" ya kira sunana yana ajiye magazine din hannunshi. "Me ya faru?" "Baffa'am har yau Hamma Umar bai daina ba ce min yayi goshi." Kallona yayi yana faɗin. "Yaron nan sam bai jin magana, ya ga tsaleliyar budurwa ya kira da goshi? Maza kira min" Hassanah wato Mama, fita nayi har lokacin ina rike da kofina da plat din. Na nufi bangaren Mama, a baranda muka hade da Yaya. "Baure Sarkin kuka, ke da waye?" "Hamma Umar mana!" Na fada ina nufar parlour Mama da suka fito daga uwar daki ake ta zuba rokonta. "Mamana wai kizo inji Baffanmu!" "Kai kararsu kika yi?" Tura baki nayi nace mata. "Ke zasu lallabaki, ki basu amma idan na samu Baffanmu zai hana su." "Amma yarinyar nan ke muguwar ina ce?" Murguda mishi baki nayi nace mishi. "Sai dai ka nima aro amma yau ka janyowa kanka an cire subsidy din yau." Na fada ina murmushin mugunta, da gudu ya taso nayi watsi da abin karyawa na fita da gudu. Ina kiran."Wayyo Allah! Yayana, Wayyo Baffanmu." Tare shi Yaya yayi jin yadda nake ihu, ta fito da sauri. "Kai kai Faruq baka da hankali ne?" Yana huci ya ya tsaya yana kallona. "Na rantse kika sake na kama ki sai na karya kafarki, Yaya ki gaya mata shekaru goma sha biyu na bata ta sake min." "Bana son fadar rashin gaskiya Faruq, kai ne ka janyo ta maka haka mu da muke nima kamata yayi mu kiyayye!" "Kyale dan kaniya, muje Rahmatullah na!" Baffa'am ya saka ni a gaba yana faɗin. "Dukiyata ce idan aka batawa Maama rai ba zan bayar ba, ai na fada muku ba yau ba ba jiya ba, tunda ka dauki zuciyar Datti sai ka kiyaye amma kato basamude ka dauko zuciyar da baka da abin da zaka amfanuwa kanka." Zuba musu idanu Mama da Yaya suka yi kafin suka rufe su da fada. "Nawa ne kudin?" "Dubu dari uku ne!" Ware idanun Mama suka yi. "Me zaku yi da kudin haka?" "Kawai zo muje!" Hamma Umar yayi zuciya. "Sai kaje ai nace sai ka je mara kirki, oya Salim wuce ka duba min Ac dakina." Inji Yaya tana hade rai. "Tow Yaya!" Ya kyale Umar a wurin, "baffanajina muje na baka hakuri." Tashi yayi har da samarin kwallarshi. Yana kunkuni. "Kuma wallahi na kama yarinyar can sai na karyata!" Zuba mishi dundu Mama tayi tana mishi dakuwa. "Kai dai zan ga ranar da zaka girma!" Suka wuce wardrobe dinta, ta wuce ta dauko dubu dari biyu ta mika mishi. "Mama!" "Jeka da shi kudinku ne rashin hakurinka yasa Rahama ta lalata maka shiri!" "Na gode sosai Mama, Allah ya jikan magabata!" Ya fita a hanya suka hade da Salim, nuna mishi bunch din dubu dari biyu yayi yana faɗin. "Ta kara min da kyautar dubu hamsin ne!" "Eh nima haka!" Ya fada yana gatsine, "kana da matsala." Lokacin da suka fito nima rike nake da kudina. "Sai ni yar Autar Mama da Yaya da Baffana ni daya."
"Sai ke fa, an hada ta da dubu hamsin tana ihu tow dari hudu aka bani!" "Sannu munafiki!" Aka fada daga kofar shigowa gidan Hamma Abdulhameed, ya fada yana kallonmu. "Maama!" Ya riko hannuna ya ciro yan dari biyar biyar ya kara min. Ya samu kanshi ya make shi. "Hamma Abdulhameed!" "Kaniyarka, kai baka ji kunya ba kana saka princess kuka ba!" Daura kaina nayi a kafadarshi. "Hamma Abdulhameed da kai shi Almajiranci aka yi maybe da ya nutsu!" Dariya Hamma Salim yayi yana faɗin. "Da yake kin ji labarin yadda aka yi ta fama da shi. " "Muje Auta!" Hamma Abdulhameed ya saka ni gaba har parlour Mama. "Mamanmu!" "Na'am! Abdul!" Ajiyar zuciya ya sauke yana faɗin. "Maama ki kawo min abin karyawa don Allah." "Tow!" Na fita, zama tayi ta zuba mishi idanu. "Lafiya kuwa?" "Lafiyar kenan Mama, kin san yadda nake fama da Shamshiya, Mama hakurina ya fara karewa." "Dama can ba hakurin ka yi ba, idan kayi hakuri zaka ci ribarshi, kasan kome." "Shi yasa bana fatan Auta ta yi auron zumuncin. Mama a cikin gidan nan babu wanda bai da matsala, idan aka samu matsala su ke fara gaya mana su bamu suke so ba, suna da zabinsu Mama taya zamu bar Little Princess ta shiga wannan rayuwar? Mama don Allah ku tayata da Addu'a Allah ya bata na gari." Da sallama na shigo na ajiye mishi tiren. "Mamana bari na kaiwa Heemah nata kason!" "Ok bani kudin." Mika mata nayi, na tsaya ina kallon ikon Allah, raba wanda Baffanmu ya bani tayi kashi biyu, ta kara raba shi kashi biyu ta mika min rabi ta ajiye min sauran a hannunta. "Wannan nata wannan naki, sauran sai ki zo a kai a tura miki account dinki." "Tow Mama!" Na fada tare da fita ina murna, bina da idanu suka yi ajiyar zuciya ta sauke tana faɗin. "Zuciyar zinari ce a kirjinta, bata ki duk abinda ta samu ta mallaka mata ba. Da ina jin haushinsu Ma'u amma yau naga wani abin da ya bani mamaki, mu tsaya mata da addu'a domin zuciyarta wankakke ne, sannan batun baku son auren zumunta akanta. So kake mahaifinku ya fuskanci matsala ne da Kakanku?" "Gyara zama yayi ya ce mata. "Wato Mama nayi kokarin ko adda Mairoh ce ta shiga maganar amma ban samu yadda nake so ba, yanxu ta kai ta kawo Shamshiya a gaban jama'a cin mutuncina take, da na gayawa Adda Mairo sai cewa tayi nima na daina b'ata mata rai, na gaji na gayawa Dadah amma babu matakin da aka ɗauka ko Baffanmu na gaya mishi amma bai damu ba, wai saboda Datti yake gudun magana fisabiilillahi haka zamu tabbata bamu da yadda zamu yi sai akan wasu zamu na kashe kanku, har ga Allah zan yi aure." Ya fada kamar zai yi kuka.
Bangarensu Raheemah na nufa, na same ta a parlournsu, taci Uban kwalliya da kayana da Adda Salaha ta dinka min, ko sakawa ban yi ba amma bai dame ni ba. "Ga naki!" Amsa tayi tana kallon kudin kafin ce min. "Ina naki?" Mika mata nayi ta amsa ta kirga ta ga daidai ne. "Waye ya raba mana?" "Mama ta raba ba mana!" Hade rai tayi tana faɗin. "Ina sauran kudin? Ai naji shigowar Hamma Abdulhameed!" "Yana wurinta." "Je ki da shi bana so." "Me yasa tow?" Na tambaye ta kamar zan yi kuka. "Ni bana so nace ki tafi! Kada na kara ganinki a gidanmu!" Hawayen da nake dannewa ne ya zubo min. "Kiyi hakuri zan baku bari na amso!" "Bana so kada na kara ganin kafarki anan gidan!" Kin tashi nayi, ai kuwa ta tashi ta bar min parlourn, na fashe da kuka me cin rai. Wanda yayi sanadin fitowar Baffa Haruna. "Ikon Allah rahama me aka miki?" "Tace kada na kara zuwa!" "Akan me?" Sai ga Aunty ta fito, cikin d'aga murya ya ce mata."Akan me? Akan me zata ce kada ta kara ganin Rahama a gidan nan? Akan me nace!" "Kayi hakuri Baffa ba haka nake nufi ba, wasa nake mata!" "Karya kike!" "Alhaji bafa wani abu bane kasan Rahama da shagwab'a, Maybe." Yadda Aunty ta mai da laifin kaina ya bani mamaki, amma da yake burina Heemah ta hakura yasa ban damu ba tana cewa ya wuce na mika mata kudin dukka na ce mata.."zan kawo miki sauran." Shiru suka yi, anan Baffa Haruna ya d'ago dalilin fadarmu. "Je ki gida Maama!" Fita nayi ina kallonta nace mata. "Ki yi hakuri zan kawo miki sauran!" Na fita, da sauri. Shiru yayi kafin ya kalli Aunty ya ce mata. "Ke kike sakawa ta amshi kudin Rahmah?" "Ni kuma Alhaji? Akan me? Ba kawarta ba ne?" "Ba kawarta ba ce cutarta kuke? Saratu idan kika sake kika lalata min tarbiyyar Yarinya za a ji mu dake, wato don kun ganta Wawuya kuke juyata son ranku? Don tana son Raheemah sai ta yi zunubi? Ina ga Yaran a gidan da na yan uwa waye yake hidima da ita kamar Rahmah? ba zan yi kaffara ba wannan kayan jikinta ba nata bane na Rahmah ce me yasa.....?
(Allah ka raba mu da hassada, kishi, kyashi, munafunci, da gulma😁)
***