007
*BAYA DA ƘURA.*
Fitattubiyar2025
©️ *Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11
***
*BOOK 1*
*Page 007*
Tun asuba Manal ta lura da yanayin Mama babu daɗi, bata mata magana ba amma idanun ta na kanta sai da taga yanayin ta ya canja gabaɗaya ta birkice hankalin Manal ya tashi tayi kanta a guje tana faɗinn, "Mama! Mama! Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un. Mama ki tashi don Allah." Sai ta fita a guje zuwa gidan Baba, ta samu matan sa guda biyu a tsakar gida ɗaya tana dama kunu ɗaya tana aikin wanke waken ƙosai tace, "Umma, Inna, Mama na bata numfashi, ku taimaka min don Allah na kaita asibiti.”
Wacce take amsa sunan Umma ta galla mata harara tace, "bazan taimaka ba, kaji min yarinya da sakarci, ni zan taimaki uwar taki dan bata da lafiya?. To ni ce na ɗora mata ciwon da zan taimake ta?.” Wacce take wanke waken tace, "ke kika saurare ta ma ai, wanda yake goya mata bayan baya nan sai a canja wani sarkin." Manal tana kuka tace, "don girman Allah ku taimaka min, Mama bata numfashi ban san ya zanyi ba."
Ganin sun ma ƙi sauraren sai ta miƙe ta fita a guje ta sake komawa wajan Mama ta tarar da ita yadda ta barta daƙyar take numfashi, ta saka fita a guje ta shiga gidan su ƙawar ta Surayya a guje. Maman su Surayya tana zaune ita da Surayya ɗin suna ta shirin haɗa abin karyawa Manal ta faɗo tana kuka Maman su Surayya tace, "Subahanallahi Manal Lafiya?." Manal tana kuka tace, "Mama ce bata numfashi sosai, ki taimaka min don Allah, na rasa ya zanyo.”
A firgice tace, "Subahanallahi, Surayya tashi kuje maza bara na faɗawa baban ku sai na biyo bayan ku" ta faɗa tana shiga wani ɗaki, suka fita ita da Surayya suka shiga gidan. Surayya ta tsorata da ganin yanayin Mam tace, "kina ji Manal, asibiti zamu je bara na nemo mai napep mu tafi" ta faɗa tana fita a guje ba jimawa sai ga Maman tasu ta shigo Manal na zaune kusa da Mama tana ta kuka. A guje Surayya ta dawo tace, "ga mai adaidaita sahun na samu."
Maman su Surayya tace, "to yanzu ai ɗaukar ta wahala zai mana" ta kalli Manal da take kika tace, "a gidan Baban ki babu wanda zai taimaka mana mu fita da ita?." Manal girgiza kai kawai take kafin tace, "Zamu iya Mama, mu gwada kar Mamana ta mutu." Haka suka ɗauki Mama suka fita aka saka ta a daidaita sahu Manal da Surayya suka shiga suka tafi asibitin Murtala.
A safiyar Adnan da kasala ya tashi kamar bazai je wajan aikin ba, tunawa da akwai masu jiran sa ya saka shi ya tashi dole yayi wanka ya shirya ya fito zuwa ɓangaren Mamy.
A falon Mamy ya tarar da ita da Maryam da kuma Lubna a zaune ya shiga da sallama Mamy ta amsa tana faɗin, "Har an fito Bebi?." Ya ƙarasa ciki yace, "eh wallahi Mamy, zan shiga babban asibiti ne shiyasa. Barka da safiya" ya faɗa yana kallon ta amsa fuska a sake tare da faɗin, "Allah ya taimaka ya kiyaye hanya."
"Amin ya Allah" ya kalli Maryam da take zaune fuska a haɗe ya kalli Lubna da take kallon sa sai tace, "Ina kwana Yaya."
"Lafiya lau, baki tafi school ba?."
"Bani da lecture yau." Ya kalli Maryam yace, "ina kwana." Kallon sa tayi tace, “Lafiya lau." Daga haka bai bata sake cewa komai ya tashi yace, "Mamy sai na dawo" ta masa fatan alkhairi shi kuma ya fita.
Wajan Mama ya shiga ya same ta a tsaye kitchen tana yankan albasa yace, "ina Mimi da Kausar suke da zasu barki kina aiki?" Ya faɗa yana niyar juyawa zai je ya kira su Mama tace, "ƙyale su, ba wani abun bane nice nace su huta."
"Amma Mummy kina aiki su suna kwance suna bacci meye amfanin su?."
"Ƙyale su kawai. Baka fita ba kenan?."
"Yanzu zan tafi. Ina kwana" ya faɗa yana durƙusawa har ƙasa ya gaishe ta amsa tare da faɗin, "Lafiya lau. Yau me ya hana ka fitowa da wuri?."
Ya tashi tsaye yace, "gabaɗaya da bazan ma fita ba bana son jin daɗi ne" ya faɗa yana shiga kitchen ɗim ka karɓi albasar hannun ta wacce ta gama yankawa yaga kwai guda uku a ajjiye da alama shi zata soya, ya ɗaulp bowl ƙamari ya fasa kwan ya zuba albasar ya kunna gas cooker ɗin dan ta ɗota fan a kai, da kallo take bishi tana murmushi kafin tayi magana yace, "Abba bai kwana a gida ba kenan?."
"Hmmm kai ka damu wannnan ai an saba, ƙiris nake jira da mahaifin ku wallahi." Jin abinda tace sai yayi shiru baice komai ba kafin ta kawar da maganar tace, "yaushe zaka yi aure ne Bebi?."
Baice komai ba ya zuba mai a kaskon ya juye ƙwan a kai tayi dariya tace, "haka zanci ba gishiri ba maggi?." Ya dan dafe kai yace, "na manta" ya faɗa yan ɗaukar abinda yasan tana ajjiye gishiri ya zuba mata ta sake cewa, "yaushe zaka yi aure ina tambayar ka."
"Mummy sai ranar da Allah yayi."
"Komai akwai niya ai Bebi, ya kamata zuwa yanzu kana da iyali kaima."
"To Mummy zan fara neman matar aure in sha Allah" ya faɗa a lokacin yana juya ƙwan sama ya dawo ƙasa.
Mummy tace, "Rumana ai a shirye take ko yau kace zaka aure ta zata shirya." Ya ɗan sauke numfashi ya kashe gas ɗin baice komai ba tace, "kayi shiru." Ya kalli Mummy yace, "Wallahi Mummy babu Ruman a raina a ya kamata ku fahimci hakan, Tunda daga lokacin da tace na barta shikenan na barta har raina, bana tunanin zan sake dawo da ita yanzu ko nan gaba."
Mummy ta ta kalle shi shi kuma ya ɗauke ƙwan daga cikin fan ɗin ya saka a plate ya fito mata dashi ta zauna tace, "ya kamata ace ka mayar da ita kam Adnan, tana sonka kaima kana sonta, kawai abinda tayi maka ne ya saka ka kasa mantawa, amma da ka kawar da komai shikenan. Ai soyayya bata fita duka, tana nan a zuciyar ka na tabbatar da hakan.”
Shiru yayi baice komai ba kafin ya kalli agogo yace, "zan tafi."
"Allah ya kiyaye in ka dawo zamu tattauna akan maganar dan baka da matar da ta wuce ta indai ina da rai, Rumana itace matar ka in sha Allah.” Baice komai ba ya fita hau mota ya fita daga gidan gabaɗaya baya jin daɗin maganar Rumana da ake masa ko kusa, dan shi kam ko meye zai faru bazai aure ta ba, yadda ta barshi tayi aure shima haka zai barta yayi auren sa.
Ɓangaren Manal suna yashe a ƙofar shiga A&E an hana shiga da Mama ance babu gado, hankalin Manal ya tashi ta fita daga hankalin ta saboda gigicewa musamman in taga idanun Mama suna yin harrrr kamar zasu kulle sai hankalin ta ya saka tashi matuƙa. Babu irin magiyar da bata yi musu ba amma sun ƙi sun ce babu gadon da za'a ɗora Mama, sai kuka take tana zaune kusa da Mama Bata da tsuntsu bata da tarko.
Wani mutum ta gani ya fito daga cikin A&E din ta tashi a guje taje wajan sa tace, “Don Allah ka taimaka min Mamana bata da lafiya, don Allah ka taimaka min sunce babu gado ban san ha zanyi ba. Mamana zata mutu anki karbar ta ance Wai babu gado. Na rasa abinda zanyi dan Allah ka taimaka min." Kallon ta yayi ya murmusa a zuciyar sa dan ya tabbatar itace yace, “Subahanallahi! Maman ce babu lafiya tana ina?." Da sauri ta nuna masa inda Mama take ya wuce ta zuwa wajan ya kalli Mama ganin da gaske fa Mama babu lafiya ya bar wajan zuwa wajan mai gadin shiga ciki ya tabbatar masa da babu gado a ciki ko ina ya cika, ya kalli ciki yaga mata da maza nan a ajjiye a kasa..
Da baya ya dawo ya kalli su Manal da Surayya da dukkan su kuka suke ya kalli Manal yace, "tana buƙatar taimakon gaggawa ina zuwa" ya faɗa yana shiga ciki bai jima ba ya dawo tare da wani nurse ya tsuguna kusa da Mama, ya kalli Manal yace, “me yake damun ta?.” Manal tana kuka sosai tace, “ban sani ba.” Surayya tace, “amma dai tana da ciwon sugar.”
Kai ya girgiza ya tashi ya shiga ciki ba jimawa ya dawo ya sake tsugunawa yana auna sugar ta kafin ya ya buɗe bakin ta ya saka wani tablet a ƙasan harshen ta ya kalli mutumin yace, "ku canja asibiti kawai zai fi." Surayya tace, "bamu san inda zamu je ba, ko kuɗin mota babu a hannun mu." Mutumin Ya sauke numfashi ya kalli Manal yace, “kar ki damu zan taimaka miki in sha Allah.” Kuka take kamar zai sake magana sai ya fasa ya kalli wani namiji da yake tsaye ya taimaka masa suka fita da Mama su kuma suka bi bayan sa da gudu aka saka mama A mota suma yace su shiga suka tafi.
Sai da suka tafi ya kalli Manal da take baya tana kuka yace, "kar ki damu zata samu sauki in sha Allah. Akwai asibitin da zamu je yanzu za’a kula da iya sosai.” Duk da yanayin garin a cike yake amma haka yake gudu dan ya isa asibitin, nan da nan suka isa ya faka motar ya budɗe ya fito da sauri ya shiga ciki sai gashi an fito da gado aka ɗora mana a kai suka shiga su kuka suka bi bayan sa.
Wani ɗaki aka shiga da Maman tsabar ruɗewa zasu shi shiga aka dakatar dasu suka tsaya bai jima sosai ba ya dawo yana nan tsaye wani nurse ya fito ya kalle su yace, "Ya akayi aka bari sugar ɗin ta ya hau da yawa haka? Magani ta daina sha ko me?." Manal hawaye ya zubo mata tace, "Tunda maganin ya ƙare ta daina sha, kuma kwana biyu tana yawan sham shayi da sugar." Ya girgiza kai yace, "sugar tane ya hau sosai, sai kuma zuciyar ta da bata bugawa yadda ya kamata.”
Mutumin ya kalli nurse din yace, “yanzu ya ake ciki likita? Ya jikin Maman?.” Ya sauke numfashi yace, “yanzu dai mun samu komai ya daidaita, Amma akwai likitan da zai zo anjima zai duba yanayin zuciyar ta ta in sha Allah komai zai zo da sauƙi. Tayi wani gwaji ne na zuciya cikin kwanakin nan?.” Manal ta daga kai tace, “eh tayi.”
Nurse din tace, “yana ina?.”
“Wallahi Mun bar shi a gida.”
“To a kawo kafin zuwan likitan.” Manal ta girgiza kai tana kallon Surayya da wanda ya taimake su.
Ta kalli Surayya tace, "ƙawata ko zaki je ki ɗauko? Wallahi hankalina bazai kwanta na bar Mama a nan bana wajan ba." Surayya tace, "kar ki damu Milky, zanje na ɗauko, a ina suke?."
"Suna nan cikin jakata ta islamiyya."
"Shikenan zan je, kinga ko kulle gidan ma bamu yi ba Allah yasa Mama ta kulle. Amma bani da ƙudim motar tafiya Manal."
Manal tace, "kuma akwai kuɗi a jakar Baba ya bani jiya suna ki ɗauko su.” Wanda ya taimake su yana jin ta sai yayi murmushi yadda take kuka saboda mahaifiyar ta abin burge shi, da alama duk abinda ya nema saboda babar ta zata yi. yace, "ga dubu biyu kije ki dawo da sauri, kin ga lokacin sallar juma’a ya kusa.” Surayya ta kalli kuɗin da yake miƙa mata ta kalli Manal sai Manal ta girgiza mata kai yayi murmushi yace, "karɓi kar ki damu." Hannun a rawa ta karɓa tace, “mun gode, Milky sai na dawo” ta faɗa tana yim gaba.
Manal ta kalli mutumin da bata san shi ba, bata taɓa ganin sa ba balle sunan sa tace, "bawan Allah na gode Allah yasa maka da alkhairi ya baka abinda ka ke so.” yayi murmushi yace, "bani zaki godewa ba, akwai wanda ya saka nayi miki shi zaki yiwa godiya. Shine yace duk abinda ake buƙata nayi miki, yana tausayin ki sosai.” Manal tace, "yana ina?." Yayi murmushi yace, "anjima zan zo na kai ki wajan sa, yanzu ya tafi saboda sallar juma’a, amma zuwa yamma zai dawo sai ki masa godia har gida.” Kai ta girgiza tace, “to sai kazo ɗin.” Yayi murmushi ya tafi ta samu waje ta zauna.
Ba jimawa ya dawo da ledar abinci ya bata ta sake yin godiya ya tafi. Sai kuma gaban ta ya faɗi sosai tsoro ya mamaye mata zuciya, a zabure ta miƙe ta leƙa ɗakin da Mama take ta tagar dake wajan ta hango Mama a kwance tana bacci cikin ɗakin mai a.c.
"Mai na aikata ne ni Manal? Waye wannan? Meyasa ma na amince dashi har aka kawo ni nan?. Waye shi? In Mama ta tambaye ni nace mata meye?.” Ta wara ido waje tace, "in aka cutar dani ko Mama fa?."
"Manal!." A firgoce ta juya jin an kira sunan ta kuma muryar namiji sai hakan ya bata mamaki ta kalli wajan, Dr Huzaifa ta gani a tsaye yana mata murmushi yace, “me kike yi a nan?." Manal ta juya tana kallon sa tace, "ina kwana?."
"Lafiya lau, ohhh! Mana ce aka kawo yanzu ko?. Haba nidai ina ta tunanin nasan fuskar ashe Maman ki ce. Ya akayi kika bari sugar ta ya hau sosai haka?."
"Bata Shan magani kuma kwana biyu har sugar take sha."
"Zata samu sauƙi in sha Allah, ki daina kuka."
Ta goge idanun ta yace, "waye ya kawo ku nan asibitin?." Manal ta kalle shi tace, "wani ne ya taimaka mana wallahi, ban san ma nan zai kawo mu ba a can Emergency ance babu gado aka ƙi kula Mama" ta faɗa tana kuka sosai. Dr Huzaifa yace, "kar ki damu zata samu lafiya in sha Allah. Ki zauna nace aje a kawo gwajin zuciyar zuwa anjima likitan da zai ga sakamakon zai zo."
Kafin tayi magana ya kuma cewa, "Jiya da nace kije wajan sa baku je ba kenan?."
"Naje, tun jiyan Mama babu lafiya sai naje na kai masa dan ya rubuta magani shine ya kore ni." Yayi murmushi yace, "dole ya kore ki ai, kin taɓa ganin anje ganin likita babu mai jin ciwon?."
Tayi shiru bata ce komai ya sake cewa, "zata samu lafiya in sha Allah." Yana faɗa ya bar wajan ta koma ta zauna, sai a lokacin taji sanyi a ranta ganin likitan da ta sani wanda suke wasa da dariya kamar ba likita ba in suka je wajan sa. Ba jimawa sosai Surayya ta dawo amma tayi wanka ta canja kaya a nan suka yi sallar azahar suna zaune suna jiran tsammani.
Ba jimawa Dr Adnan yazo asibitin kai tsaye office ya wuce yana zama Huzaifa ya shiga yace masa, "daman kai nake jira wallahi, duba min wannan result ɗin" ya faɗa yana bashi takardar, bai musu ba ya karɓa yana dubawa ya kalle shi yace, "ina patient ɗin?."
"Anyi admitting ɗin ta, tana nan emergency." Adnan yace, "ciwon ya ɗan yi ƙarfi kaɗan gaskiya, tana buƙatar magani masu kyau sosai. Wanne magani take sha?.”
Huzaifa yace, “bani dasu a yanzu.”
“Okay, tana da buƙatar kula dai sosai, in aka cigaba da haka ciwon wuce yanzu.”
Huzaifa yace, "patient ɗina ce duk two weeks suke zuwa wajena itace ƴarta, itama ƴat ciwon ne da ita amma na uwar yafi yin worst tunda kaga ya taɓa mata ido yanzu ko gani bata yi sosai, ga zuciya ma."
"Subahanallahi, haka ciwon naku yake ɓarna?."
"Yanzu kazo muje ka ganta don Allah, ni kaina ya kulle wallahi na rasa ma abinda zan mata.."
"To kai da kake endologisy baka iya komai ba ina ga ni cardiologist? Me zan iya?."
"Experience ɗinka akan zuciya ne kana da abinda zaka iya."
"To kai kuma akan ciwon ne gabaɗaya, kamar ka fini sanin aikin ka."
Huzaifa yace, "Nidai kazo muje ka ganta kawai don Allah." Ba musu ya tashi suka fita bai ma kula da Manal ba ya wuce zuwa ɗakin ba jimawa suka fito Huzaifa ya tsaya ya kalli Manal tace, "kar ki damu Manal, ga wanda zai kula da lamarin zuciyar Mama nan, kar ki damu." Kallon Adnan tayi suka haɗa ido ta glasses ɗin Idon sa, ita ta gane shi amma shi bai gane ta ba sai ta sauke kai ƙasa bata ce komai ba, shi kuma a zuciyar sa yana ayyana ita kuma ko gaisuwa bata iya ba.
Ya wuce ya shiga office ya samu Hamza a zaune a ciki bai kula shi ba ya kalli Huzaifa Adnan yace, "Huzaifa meye alaƙar ka dasu?." Huzaifa da yake bayan sa yace, "babu komai wallahi, patients ɗina ne kawai kamar yadda nace maka."
"To yayi, tana buƙatar hutu a ƙalla one week to ten days a nan, sannan akwai abinda yake damun ta wanda yake jawo mata ciwon, in aka yi bincike sosai babu lallai diabetes ya kawo shi.”
Hamza cikin tsokana yace, "taya ka gane?." Ya Harare shi yace, "iya pulse ɗin ka zan riƙe zan fahimci yanayin heart beat ɗin ka, in stress ne ya saka ta bugawar zan gane, in gudu kayi zan gane, in damuwa ce zan gane ka fahimta?. Nan ba office ɗin kallon matan mutane bane, i am cardiologist.”
Hamza yayi dake shi yace, "wallahi zan baka amsa a lokacin da matar ka zata haihu a hannuna." Bebi ya taɓe baki yace, "Allah ya kiyaye, ni matata ta haihu a wajan ka…? ai har abada wallahi." Suka yi dariya a tare banda Bebi da yake sake kallon sakamakon gwajin Maman Manal.
Sai ya ajjiye takardar ya furzar da iska yace, "wa kuka sani a police station? Akwai wanda na ke so a kama min." Huzaifa ya ce, "to me yayi maka kuma?."
"Mijin Maryam nake so a kama, in ba kama shi nayi ba bazai daina bibiyar ta ba."
Hamza yace, "wannan matsalar fa daga Maryam take ba daga shi ba Bebi, da bata bashi dama da fuskar zuwa wajan ta bayan ya sake ta ba wallahi da bazai zo ba." Huzaifa yace, "wannan gaskiya ne abinda kake faɗa, itace ta bayar da dama tun farkon rabuwar su da bata bada dama ba da hakan bata kasance ba.”
"Shiyasa nake so ayi mana iyaka dashi, tunda babu ragowar igiyar auren sa a kanta a kan me zai dinga bibiyar ta? Tunda dai babu damar mayar da ita wallahi kar ya sake sauraron ta. Jiya da daddare bayan na koma na ganshi da ita mota, me ake a motar? Meye alaƙar su da har zata dinga shiga motar sa?." Hamza yace, "wannan ita zaka tambaya, kuma ira zaka jawa kunne ba wani ba." Ya girgiza kai kawai baice komai ba suma basu sake ce masa komai ba suka fita shima ya fita.