008
*BAYA DA ƘURA.*
Fitattubiyar2025
©️Nana Haleema.
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11
***
*BOOK 1*
*Page 008*
A ɓangaren su Manal yunwa Surayya take ji gashi a zaune basu ci komai ba ta kalli Manal tace, "Milky Yunwa nake ji sosai." Manal tace, "a kuɗin da kika ɗauko kije ki siyi wani abun Kkici."
"Kefe Milky? Baki karya bafa."
"Bazan iya cin komai ba in Mama bata farka ba." Wayar Surayya tayi ƙara ganin sunan Maman ta sai tace, "bara naje na shigo da Mama." Fita tayi ba jimawa siai gasu da Mama har da abinci ta kawo musu Mama tace, "ya jikin Maman taki Manal?."
Manal tace, "tana nan dai kwance."
"Kin san wanda ya kawo ku nan ne? Surayya ta faɗa min komai."
"Wallahi Mama ban san shi ba, ni kaina gabana faɗuwa yake yi sosai. A lokacin a ruɗe nake sai yanzu na nutsu na fahimci nayi kuskure.”
"Hankalin ki baya jikin ki a lokacin ne shiyasa Manal, amma babu komai Allah yana gani dan mahaifiyar ki kika yi bazai bari ki cutu ba." Ta ɗaga kai alamun haka ne Mama tace, "Mubeena bata zo ba?." Manal ta taɓe baki kawai bata ce komai ba dan ita ta manta ma da wata Mubeena.
Ganin haka dai Mama tace, "ga abinci nan ki ci bana son musu dan nasan yunwa kike ji. Akwai salad a ciki sai ki zuba ki ci.” Jin abinda tace ya saka dole ta karɓi abincin da Surayya ta zuba mata tana ci daƙyar. Manal tace, “ni na manta, wanda ya kawo mu ya kawo mana abinci” ta faɗa tana jawo ledar ta buɗe.
Mama na wajan har akayi magriba ta kalli Manal tace, "ki kira Mubeena a waya tazo ta taya ki zama a nan." Da to kawai ta amsa dan ba yi zatayi ba dan ɓata lokacin ta zatayi indai Mubeena ce ba zuwa zatayi ba.
Ba jimawa suka tafi Manal tana ta godiya harda kuka suka tafi ta dawo ta zauna tare da yin shiru.
"Sannu Manal." Ta ɗago ganin wanda ya taimaka mata sai tayi murmushin tace, "Yauwa."
"Ya jikin Maman?."
"Da sauƙi, bacci ma take."
"Haka ake so sosai Allah ya bata Lafiya."
"Amin. Na gode sosai." Yayi murmushi yace, "ki kula da ita zuwa gobe zan zo sai muje wajan wanda ya taimaka miki." Manal ta ɗaga kai tace, "to Allah ya kaimu, na gode sosai."
Murmushi yayi ya tashi ya bar wajan ya tsaya bayan ya bar wajan tare da ɗaukar waya ya saka a kunne yace, "Ranka ya daɗe tana hannu yanzu, zuwa nan da gobe duk abinda nace tayi zatayi domin akwai target ɗina a kan ta, shiyasa na zaɓi wannan asibitin saboda yana da tsada sosai."
Shiru yayi alamun ana bashi amsa kafin yace, "zuwa gobe zan kawo ta." Shiru ya sake yi kafin yace, "Allah ya taimaki uban gıdana, wannan ai abu ne mai sauƙi, Tunda ka ganta kaji tayi maka ai an wuce wajan. Ba da ƙarfi zamu yi amfani ba da kanta zata amince saboda bata da mafita, in taƙi ta kwana a hannun yan sanda."
Dariya yayi mai sauti kafin ya kashe wayar ya juya yana hango Manal da ke zaune ya girgiza kai yace, "ba ƙarya yarinyar akwai kyau, iya wannna farin nata ko shi kaɗai ya ɗauki hankalin mai gida balle in tayi magana. Ta haɗu ba ƙarya wallahi, zata yi abinda ake so. Sorry yarinya kin zo hannu” yana gama faɗar hakan ya tafi yana dariya mai kama da dariyar mugun ta.
Manal tana nan zaune har akayi i'sha a nan tayi sallah dan wajan yana da tsafta sosai, tana idar da sallah Bebi yazo wajan ya kalle ta yana mamakin yadda bata gajiya da kuka, ta idar da sallah amma sai kuka take yi jikin ta har rawa yake yi sosai, har ya wuce ta sai ya tsaya yana kallon ta yace, "Kina ji? Ki shiga wajan maman ki zauna."
Jin magana a kanta sai ta ɗagp suka haɗa ido yace, "tashi kije ciki." Jikin ta a sanyaye ta tashi fuskar ta jiƙe da hawaye ta shiga ciki yabi bayan ta har lokacin Mmaa bacci take.
Bugun zuciyar ta ya sake dubawa ya rage gudun ruwan da yake shiga jikin ta ya sake yi mata allura sannan yace, "anytime zata iya farkawa, in ta farka zaki iya zuwa reception ki sanar da nurse." Ta ɗaga kai alamun to har lokacin kuka yake yi ya bita da kallo yana tunanim ita wannan yarinyar kuka baya mata wahala ne ko kuwa me?. Huzaifa ne ya shigo ɗakin yana cewa, "kai nake ta nema ashe ka shigo nan" ya kalle ta yace, "Manal kar ki damu zata ki sauƙi, ki daina wannan kukan kar ya cutar da ke.”
Ta ɗaga kai alamun to yace, "ina Yayyen ki suke?." Ta kalle shi tace, "Bana da yayye, Yayata guda ɗaya ce kuma tana makaranta."
"Ke kaɗai zaki kwana a nan?."
"Eh" ta faɗa a sanyaye tana kallon sa. Yace, "shikenan to zuwa da safe duk zamu dawo, in akwai abinda kika ga Mama nayi in ta farka kije ki sanar a reception."
"To" ta fadɗa muryar ta na rawaHuzaifa yana kallon ta Allah ya sani yana jin tausayin Manal sosai har zuciyar sa bai san dalilin hakn ba. Shi kansa Bebi kallon ta yake yi kafin ya kalli Huzaifa ya wuce ya fita shima ya biyo bayan sa.
A wajan ajjiye mota ya samu Bebi yana niyar shiga mota Huzaifa yace, "yarinyar nan tana bani tausayi Bebi, har zuciyata nake jin tausayin ta wallahi ban san meyasa hakan ba." Bebi yace, "Akwai tausayi kam, sai da safe" ya faɗa yana shiga mota ya fita daga asibitin. Shima Huzaifa shiga motar yayi ya tafi.
Yana komawa gida ya tarar da ɓacin rai a harabar gidan nasu domin kuwa Lubna ce tana zaune da saurayin da ya hana ta kulawa suna hira. Ransa yayi mugun ɓaci ya rasa ya zaiyi da yarinyar nan duk abinda yace sai ta tsallake, in yace kar tayi sai tayi bata san abinda yake ji a zuciyar ba in hakan ta kasance.
Lubna tana ganin sa ta tashi ta shiga gida da sauri shi kuka saurayin nata sai ya tashi ya nufo inda Bebi yake a lokacin ya fito daga mota ya miƙa masa hannu yace, "Barka da dare Yaya Adnan." Kallon hannun nasa yake yana kallon fuskar sa kafin yace, "Mujahid wannan abinda kake yi bai kamata ba, dani kake faɗa banga dalilin da zai saka ka sako ƙanwata a ciki ba."
Wanda aka kira da Mujahid yayi dariya yana kallon sa yace, "Neman aure nake fa Yaya Adnan, ba da wani abun nazo gidan nan ba auren ta nake so nayi in an bani dama." Adnan ya gyara tsayawa yace, "zan maka last warning akan Lubna, babu kai babu ita ka fita daga cikin rayuwar ta in ba haka ba.." kafin ya kai ƙarshe Mujahid yace, "in ba haka ba zaka saka a ɗauki raina?" Sai yayi dariya ya ce, "naga Lubna ina so kuma auren ta zanyi, baka isa ka hana ni neman auren ta ba, domin kuwa ba kaine mai gidan ba kuma ba kaine riƙe da gidan ba. dan haka zan nemi auren Lubna sai kuma na aure ta sai naga iya abinda zaka iya yi."
Juyowa yayi zai tafi sai kuma ya dawo ya saka kallon sa yace, "in ma ban aure ta ba zata faɗa cikin soyayya ta wacce zata kasa sarrafa ta, daga nan duk abinda nake so zanyi da ita baka isa ka hana ni ba, sai dai kaji ance likitan zuciya Dr Adnan Mu'azzam yana kwance yana jinyar zuciya saboda saurayin ƙanwar sa. Wannan fagen nawa ne Adnan, ba wajan ƙwace leinses bane” ya faɗa yana murmushi tare da barin wajan ya fita daga gate ɗin gidan dan motar sa ma a waje ya barta.
Ransa ya ɓace sosai ya nufi cikin gidan ko wajan Mama bai shiga ba ya shiga ɗaki ya zauna a kan kujera yana tunani. Shi yasan da biyu Mujahid yake zuwa wajan Lubna, yasan saboda wani nufin da yake zuciyar sa ne yake zuwa ba don Allah da annabi ba. Waya ya ɗauka hannu na rawa ya kira Lubna tana ɗauka yace ta zo ta same shi ya yanke wayar ya ajjiye.
Ba jimawa ta shigo jiki a sanyaye ta zauna tace, "gani."
"Ban miki warning akan kula Mujahid ba?, bance kar n saka ganin ki dashi bane yasa kike haka ne Lubna?." Tayi shiru bata ce komai ba amma a zuciyar ta mamaki yake bata, to wai shi ina ruwan sa da samarin tane?. Katse mata tunani yayi ta hanyar cewa, "magana nake miki fa, in baki amsa ba sai na taso na fasa miki baki." Jin yadda yayi magana sai tace, "To ni ina son sa."
Wani iri yaji a zuciyar sa ya kulle ido ya buɗe cikin takaicin abinda tace ya fuzar da iska yayi shiru baice komai ba. "Allah Yaua ina son sa, kuma daman kace na zaɓa aure ko karatu ko?, to ni aure nake son yi kuma shi zan aura." A fusace yace, "ba sonki yake ba shi, yana amfani dake ne saboda wani nufi masa amma ba dan yana son ki ba. Ki dawo hankalin ki malama, wannan tunanin da kike bashi da amfani domin kuwa baza ki aure shi ba.” Tayi shiru ganin yana zare mata idanu, ido ya cika da hawaye sai ya dafe kai yace, "look Lubna! Mujahid ba irin mazan da zaki saurara bane a matsayin wanda zaki aure kin gane?."
Magana take so tayi amma ta kasa yace, "faɗi abinda yake bakin ki ina jin ki." Tace, "Yaya naga abokin kane fa, meyasa baka so yake zuwa wajena? kuma ni nace auren sa zanyi ina son ..."'yadda ya taso kamar zai mare ta shine ya hana ta k'arasa maganar yace, "shut up your mouth, stupid girl ina miki magana kina sake maimaita min kina son sa? Ni zaki faɗawa kina son sa don kin raina min hankali..? Ina magaa kina maganq? baza ki aure shi ba ki rubuta wannan ki ajjiye. Indai Adnan yana da rai baza ki auri Mujahid ba, ya kamata ki san da wannan. Kuma na sake ganin ki dashi sai nayi miki dukan da ba'a taɓa yi miki irin sa ba tunda kika zo duniya, sai na miki dukan da shi Mujahid ɗin bazai gane ki ba, daga ranar zaki shaida waye Adnan.”
Cikin tsawa yake magana hakan ya saka ta shiga hankalin ta sosai, ya sake cewa, “Tashi ki bani waje." Da sauri ta zabura ta miƙe ta fita da sauri ya daki kujera cikin takaici da baƙin ciki.
Mujahid yayi nasara a kansa tunda har Lubna ta fara son sa shikenan ya gama karya masa lagon Lubna, amma yasan abinda zai masa bazai sake waiwayon Lubna ba itama dole ta haƙura dashi domin bai dace da ita ba, ba irin sane ake kira da mijin aure ba.
Mujahid da murmushi ya bar gidan ya shiga mota ya zauna ya samu abokin sa a zaune yana jiran sa yace, "tunda naga kana murmushi nasan akwai abinda ka shirya wanda kake gab da samun nasara." Yayi dariya kaɗan yace, "burina na baƙantawa Adnan kamar yadda ya baƙanta min, badai ƙannen nasa yake tattali kamar ƙwai ba? To ni kuma sai na saka ƙafa na take wannan riritawar da yake musu dan wallahi sai na saka masa baƙim ciki a zuciyar sa."
Wanda yake sanarwa ya shigo a kai yace, "kar ka manta Adnan abokin nake fa Mujahid, da sunan ka aka buɗe asibitin getting better kana daga cikin ma'aikatan sa kafin ka daina aiki."
"Kafin yayi silar daina aiki na dai, har abada bazan manta da abinda Adnan yayi min ba, kuma wallahi sai na rama akan ƙanwar sa Lubna. Bashi da weakness point a duniya kamar familyn sa, musamman ƙannen sa mata guda uku, tabbas zan yi amfani da Lubna na saka masa baƙin cikin da na ɗanɗana a zuciyata nima."
"Kenan baka son Lubna?." Yayi tsaki yace, "bana ce ba" ya faɗa yana jan motar suka bar wajan yana aiyana irin abinda zai yiwa Lubna, dan walalhi sai ya saka Adnan kuka in ba haka ba bazai daina jin da daɗin abinda yayi masa a zuciyar sa ba