04
by @nkds
*FAƊIME...💋🌸💕*
_(Dangin Jinnu)_
©By Nainarh KD & Zahrah Royal Star
*Dedicated to Salma Ahmad Isah (Candy)*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*A love & Laugh story that will capture your heart and soul.*
04
*FAD'IME POV*
"Inna Fatuh kiyi sauri ki ban kud'in nik'an mana, K'awaye na na jira a waje fa"
Fad'ime ta k'are maganar tana kallon k'ofar d'akin Inna Fatuh.
Da sauri Inna Fatuh ta fito tana k'irga kud'i, ta kalli Fad'ime dake dubanta ta ce.
"Y'ar albarka Fad'ime ta, dan Allah karki tsaya wasa da jan matune fad'a kinji, kar a kawo min k'ararki yau kinji, karki tsaya ko ina ki amso nik'an kawai ki dawo gida kinga yamma tayi"
Turo baki kawai Fad'ime tayi tasa hannunta ta amshi kud'in tayi waje da gudu.
Tana gaf ficewa daga zauran gidan kawai taji ta bangaje mutum, bata tsaya bada hakuri ba zata k'ara gaba, taji an jawota ta baya an d'auke ta da wani irin Mari tasssss.
"Kan uba"....
Fad'ime ta fad'a tana ware idonta akan Auta dake tsaye yana kallonta cike da jin haushinta sosai, duk da yasan tab'a Fad'ime a wajansa ba abu bane mai dad'i da zai biyo baya.
"Banza shashasha kawai mai kama da aljanun farko, komai mutum zaiyi bayayi irin na mutane, dubi ke dan Allah kamar wacce aka tonu daga kabari".
"Auta ni ka mara?".
"Na mare ki ko zaki rama ne?"
"Hmmm bazan rama ba amma ka guje abunda zai biyo ba, sanadin wannan marin da kayi min wallahi".
"Idan kin fasa yi min wani abu kin raina Allahn daya halacci ki kinji?, aikin banza kawai".
Ya k'are maganar yana k'arawa gaba ya shige cikin gidan.
"Uhmmm"
Kawai Fad'ime ke yi tana rik'e da kuncinta har yanzu, wani mugun haushin kanta ma take ji mi yasa ma bata d'aga hannu a nan take ta sauke masa marin ba, komai ta fanjama fanjam.
Juyawa tayi ta idasa ficewa daga gidan. Tana fita ta iske su Laure da Sa'ade na jiran fitowarta. K'awayenta ne tun sadda suka dawo gidan Gadonsu, a unguwar suke, tasu ta zo d'aya tsabar suma ba jin magana suke ba.
Tafiya suke buguzun-buguzun, basu aune ba suka ji wani Yaro dake d'an nesa dasu yana cewa.
"Wayyo Jama'a ga dangin Jinnu can ta biyo hanya dangin Aljanu kenan"
Ya idasa fad'ar haka yana nunama wasu Yara dake kusa dashi.
Wani mugun b'acin rai ne ya kama Fad'ime duk duniya idan akwai abunda ta tsana to ace mata dangin Jinnu.
Da gudunta ta k'arasa inda suke, kwai sai dai suka ga tsayuwarta a gabansu kamar wata walk'iya.
Zaro ido sukai a waje suna rarraba ido, wadda ya fad'i maganar ne yayi saurin juyawa zai baza da gudu, kamar walk'iya Fad'ime ta rik'o hannunsa tana kallonsa, jijjga jikinta take tana jefa masa wani mugun kallo.
Laure ce ta rik'e sauran yaran ita da Sa'ade suna cewa.
"Ubanwaye kuke kira da dangin Jinnu iyee?"
"Wallahi Allah bada ku muke ba"
Cewar wani daga cikinsu yana fad'ar maganar jikinsa na d'aukar rawa.
Wadda Fad'ime ta rik'e kuwa yana ji da rashin kunya bai san abunda zai biyo baya ba, yana ji da rashin kunyarsa, saboda wani abu bai tab'a had'asa da Fad'imen ba sai yau.
Ya ce "kaii Isah an fad'a d'in, ance K'anwar Jinnu, ai haka mukaji mutane na fad'a, muma kuma munje mun fad'a, laifi ne mukayi dan mun fad'i sunan da mutane ke fad'i akanki?".
Wata muguwar shak'a da Fad'ime tayi masa, yasa shi fasa wata gigitacciyar k'ara, bai gama dawowa dai-dai ba, tasa d'ayan hannunta ta d'aukesa da wani gigitaccan mari. Wasu taurari ne yaron yaji sun gifta masa, kunnansa ne yaji yayi wani dummmmm, gaba d'aya jinsa ne ya d'auke kwata-kwata baya jin abunda ke wakana.
Fad'ime ta kallesa tana cewa.
"Daga yau idan kunga na taho ku tsaya dan Allah ku jani kunji, idan banci kutumar uban Yaro ba".
Duk abunda take fad'a fa kwata-kwata yaron nan baya ji, jinsa da gaske ya d'auke. Ai ko yana fahimtar haka ya saki wani mugun kuka mai k'ara yana fad'uwa k'asa yana birgima yana magana da k'arfi yana cewa.
"Wayyo Allah na shiga uku na, jama'a ta dod'e min kunne bana ji kwata-kwata, jama'a ku taimaka min na shiga uku".
Abunda yake fad'a kenan yana uban kuka.
Sauran yaran kuwa wani fitsari ne ya kwace masu, sakinsu su Laure sukai suna dariyar mugunta suka kalle suna cewa.
"Abunda yasa zamu barku kuma dan baku fad'i sunan nan bane, kuma zaku iya zuwa ku gaya ma iyayensa, sai a fara nemar masa magani, dan da alama ya kunnansa ya daina aiki".
Suna fad'ar haka Fad'ime tayi gaba suka take mata baya.
Sunzo wani wajan mai tsire kawai Fad'ime ta tsaya tana had'iyar miyau, matsawa tayi kusa sosai da mai tsiren tana cewa.
"D'an juma mai tsire a yanka min na d'ari uku"
Washe baki D'an juma mai tsire yayi yana kallon kyakykyawar fuskar Fad'ime yana lashe baki ya ce.
"Ahh masoyiya Fad'ime ke ce a tahe keda K'awayenki?".
Murtuke fuska Fad'ime tayi tana jin haushin D'an juma mai tsire, wai masoyayirshi, Ubangiji ya kiyaye mata ta so wannan bawan Allahn.
Wani tsaki taja tana k'ank'ance ido ta ce.
"Kaga D'an juma idan zaka bani tsire na d'ari ukun dana ce ka yanke min, ka bani kawai bana son yawan surutu kaji Malam, ko wace ma masoyayir tashi?".
Ta k'are maganar tana harararsa.
Washe baki ya sake yi, shi dai tunda za'a masa ciniki ai ta wuce, domin son kud'i ne da shi baya jin ko yana sonta zai iya bata tsiren nan a kyauta.
Sa'ade ta matso ta kalli Fad'ime a sadda D'an juma ya mik'o mata tsire yana cewa a bashi kud'insa. Hararsa tayi ta ce "kaga na cinye na tafi ban baka kud'inka ba?".
"Ahh to ai kin san bana da mutumci akan kud'i na"
Banza dashi tayi tana jin Sa'ade na cewa.
"Amma Fad'ime karki ci masa tsire kuma al'halin baki da ko sisi fa".
Wata harara itama Fad'ime ta maka mata, ba shiri Sa'ade ta tsuke bakinta tayi shuru.
Guda d'ai-d'aiya ta basu suka amsa suka cinye suna tand'e hannu.
Sai da ta gama ci sana ta kalli D'an juma ta fiddo kud'in nik'an da Inna Fatuh ta bata naira d'ari ce ta mik'a masa.
Amsa yayi tana washe baki, can ya murtuke fuska tamau ganin naira d'ari ce, kallon Fad'ime yake, bala'i cike da cikinsa.
"Kan uba Fad'ime kinga nawa kika bani kuwa?".
"Na sani mana"
"To miye kike nufi dani".
"Yo mifa nake nufi da kai, iya kud'in da nake da su kenan, kama gode Allah ka samu d'ari d'in".
"Ai ko yau akwai bura uba a garin nan, keeeee Fad'ime ni zaki ci ma tsire ki tsaya ido cikin ido ki ce bazaki biya ni sauran kud'i na ba?, to ai ko uwar data haife ce ta dawo duniya na rantse d........ Maganar ce ta katse jin an wasa masa k'asa har kan idonsa.
Murza idonsa yake a haukace, yana murja ido da kyar ya bud'e idon nasa muten sun zagaye shi.
Ihu ya saki ganin yadda tsirensa ya b'aci da uwar k'asa a cikinsa gaba d'ayansa ya lalace, babu wadda zai iya cinsa a haka.
Hango su Fad'ime yayi sun baza da gudu.
Wani ihu ya saki yana cewa.
"Na rantse da tsarkin mulkin Allah yau sai na ci kutumar uban wancan yarinyar Mai kama da aljanu, wallahi Mutane sunyi gaskiya da ake ce mata dangin Jinnu, ai wallahi yau ko za'ayi yak'in duniya na biyu sai an biyani duka kud'in tsire na na rantse kuwa".
Hakuri mutane suka rink'a basa amma ina sai tsine ma su Fad'ime yake daga ita har K'awayen nata, yana Allah wallahi sai an biyasa kud'in tsirensa ko za'ayi mi.
______________
Dai-dai sun iso wajan amsar nik'a, suka ja birki suna sauk'e lumfarfashi.
Dariya kawai Fad'ime keyi su Laure na tayata.
"Kee amma Fad'ime kin shammace sa fa, kawai sai dai yaji saukar k'asa akan kayan sana'arsa".
Cewar Laure tana rik'e cikinta domin ji take ya d'aure sosai, saboda gudun da suka sha da kuma uwar dariyar da suke.
Sauk'e lumfashi Kad'an Fad'ime tayi tana yin gaba taje inda ake saka layi domin amsar nik'a, ita bata sa layi ba ta shige gaba kawai.
Tana cema su Laure.
"Ai kad'an ma ya gani ya ci gaba da tab'a min iyaye sai na yi sanadiyar rugujewar sana'ar tasa walla...
Maganar Fad'ime ce ta mak'ale jin yadda aka wani bangajeta ta fita daga gaban data shiga.
Wata yarinya ce mai jiki sosai k'ibarta har tayi yawa tana kallon Fad'ime data ture tana cewa.
"Keee baki ga layi ake sawa bane?, sai ke isassa kin wani zo kin shige gaba, dama na dad'e ina jin rashin kunyarki to yau da alama zan sauk'e miki ita ne".
Tashi tsaye Fad'ime tayi tana kakkab'e jikinta saboda har sai da ta fad'i lokacin data bangajeta, domin ba k'arama bace wacce ta ture tan, bata jin wannan ko d'an bigeka tayi ba zakai taga-taga zaka zube k'asa ba, yo wannan abu kamar buhu.
Duk irin girman yarinyar hakan bai sa Fad'ime jin wani abu ba, bare azo ga tsoro.
Rik'e k'ugu tayi tana matsowa sosai inda take ido cikin ido ta kalleta ta ce
"Ni kika bangaje?".
"An bangaje ki d'in, ko akwai abunda zaki yi ne?".
Ta fad'a a tsawace tana sake matsowa sosai kusa da Fad'ime kamar zata had'iyeta da ranta.
D'an shafa kanta Fad'ime tayi tana kallon su Laure kyafta masu ido tayi, ai ko suna ganin haka suka shige wajan nik'an da gudu suka warto nik'an dake ajiye, an nik'a shi, suka fito da gudu sukai gaba, mai nik'a na faman kiransu su bashi kud'i, amma Ina sunyi gaba. Fad'ime kuma ganin hankalin mutane ya koma wajan su Laure har wacce ta tureta ma tana binsu da kallo. Batai aune ba kawai taji anyi sama da ita an fyad'a da k'asa ji kake timmmmmmmmm.
Yadda kasan an kada gini.
Kamin ta gama dawowa dai-dai taga Fad'ime ta haye ruwan cikinta ta kama fuskarta sai yakushi take tana kai mata naushi a ciki, sai k'ok'arin k'are kanta take amma ina, taji uwar bari sai kuka take tana kiran azo a ceceta zata kasheta.
Duk irin taruwar da jama'a sukai wajan suna k'ok'arin b'anb'are Fad'ime a jikin yarinyar nan amma Ina abun ya gagara. Shi kansa Mai Nik'an dole tasa ya fito daga Shagon nik'an aka taru dashi ana sun kwace Fad'ime daga jikin baiwar Allahn.
Da kyar da sub'in goshi aka samu Fad'ime ta saki Y'ar mutane, tana uban nishi, tana tashi kuma bata tsaya ba ta k'ara gaba da uban gudu kamar wata zakanya.
Tashi tayi da kyar yarinyar tayi tana kuka. Wata ce ta rik'eta tana cewa.
"Binta mi yasa kika ja Fad'ime, wadda kowa yasan Fad'ime duk garin nan shaid'aniya ce, duk bala'inka waccar yarinyar ta fika".
Kuka Binta ta k'are fashewa dashi tana cewa.
"Na rantse da Allah bazan yarda ba, idan na yarda Allah ya tsine min, wallahi saina gaya ma Innata, wallahi yau sai an d'akko masu Y'an Sadda ko waye ya tsaya mata a garin nan wallahi".
Buguzun-buguzun ta wuce gidansu tana k'ara b'are baki.
__________________
Dandazon jama'a ne a k'ofar gidan su Fad'ime sun taro kowa na tofa albarkacin bakinsa, hayaniya ta kaure sosai a k'ofar gidan mutane na cewa.
"Ai wallahi a fiddo mana ita nan muci uwar shegiya tunda ta addabi kowa a cikin gari".
Inna Fatuh dake tafe har sauran kad'an ta kife a k'asa, ta fito k'ofar gidan tare da su Inna Lami da Malam dake biye dasu, da duk mutanan gidan.
"Wai miye ne da naji anata kiran sunan Jikata ne?"
D'an juma mai tsire ne yayi saurin cewa.
"Ai na rantse da Allah yau sai an biyani kud'in tsire na, Jikarki Fad'ime taje ita da K'awayenta suka watsa min k'asa a cikin tsire na, dan haka tsire na, na kusan dubu talatin ne, kuma wallahi ko za'a sake yak'in duniya na biyu sai an biya ni kud'i na, ko mu had'u a Ofishin Y'an Sadda".
"Ai ba kai kad'an bama Malama D'an juma, ni Yaro na ta kama ta kantsama ma Mari har jinsa ya d'auke, dan haka wallahi ko za'ayi mi yau sai tazo ta maido masa da jinsa yadda yake wallahi, ina nan ina jiran Jikar taki".
Cewar wata mata dake rik'e da Yaron har yanzu baya jin abunda ake cewa sai kuka yake.
Inna Fatuh ta wani k'ank'ance ido tana kallonsu d'aya bayan d'aya ta ce.
"da'aAllah Malamai ku tsaya min na ce, nasan dai Jikata bata jan fad'a sai an tab'a ta, su yaran naku baku tabbaye su miye sukai mata bane?, Kai kuma D'an juma akwai abunda kayi mata kaima wallahi. Kuma bamai tab'a min Jika wallahi ehee".
Inna Fatuh ta k'are maganar tana turo kallabi gaban goshinta, dan ko hijab bata sa ba, wani gyale na yafo saman kafad'arta.
Zasu sake magana wata mata ta shayo kwana ita da d'iyarta rik'e a hannunta had'e da Y'an Sadda guda biyu biye da ita fuska murtuke.
"Mun shiga uku, ku kuma fa, daga Ina?".
Cewar Inna Lami tana rik'e k'ugunta.
"Zuwa mukai a kama Fad'ime ta kama Y'ata Binta ta haye ruwan cikinta ta kama bugunta kamar ta sami Jaka, yo ko ni dana haifeta ban tab'a mata irin wannan uban dukan ba, dan haka banga ubanda ya isa ya bigeta haka na kyale shi ba wallahi".
"Wayyo Allah na shige su ni Inna Fatuh, ace duk garin nan duk an tsani Jikata, kamar ita ce kad'ai yarinya a cikin garin nan. Shine ke baiwar Allah harda zuwa ki kwasu Y'an Sadda domin kawai su kama Jikata?, ai ko wallahi banga wadda ya isa ya kama Jikata ba ehee kiji da kyau".
"Haba haba haba Inna Fatuh, Fisbilillahi sai tare ma Fad'ime fad'a kike al'halin kinsan ita ce wacce keda laifi. Ki bari kawai ma ta dawo daga yawon ta zubar d'inta su kamata su wuce da ita can Ofishin Y'an Saddan, su lallasa mana ita ma ko ta d'anyi halkali ma"
Cewar Auta yana duban Inna Fatuh.
Wata dak'uwa Inna Fatuh ta makama Auta tana cewa.
"Ungo nan Auta, kaci gidanku na ce kaji, idan kaga an tafi da Fad'ime to sai dai a had'a da ni da Ubanka duka a tafi damu wallahi".
"A'afa wannan d'aya, sai dai keda Fad'imen za'a tafi da ku amma dai banda Malam wallahi"
Malam ne ya kalli Auta ya ce .
"Karka sake magana a nan wajan, wuce ka shige gida na ce".
Malam ya fad'a yana nuna Auta dake kallon Inna Fatuh fuska ba Rahma.
"Yo ka barsa mana tunda ai uwarsa ce take d'aure masa gindi yayi ma mutane rashin kunya ai".
Inna Lami ta katse Inna Fatuh tana d'aga mata hannu ta ce.
"Kinga Inna Fatuh tunda aka fara wannan kicimulin baki ji baki na ba, dan haka kar a sake saka ni a ciki a'ato".
"Ai kawai ki fito fili ki ce zaki zage ni Lami, dama ai kema ba k'aunar Fad'ime kikeyi ba wallahi, bakik'i ma Fad'ime zuwa yanzu ta mutu ba ai, to Fad'ime dai nan gani nan bari ajiyar Allah ce wallahi".
Lami zata sake magana ranta a b'ace Malam ya d'aga masu hannu zuciyarsa babu dad'i ya kalli dandazon jama'ar dake wajan ya ce.
"Kowa ya fad'i kud'in da tayi masa asara da wadda zasu je asibiti sukai Y'ay'ansu. Dan Allah kuyi hakuri kuma, Yaro ne ka haifesa baka haifi halinsa ba".
Jama'ar wajan tausayin Malam ne ya kamasu dan haka da kyar wasu suka hakura nan take yasa aka kamo Akuya har biyu aka saida, aka biya kowa kud'in da ya kamata, sai mutum d'aya ce bata karb'a ba, wacce Yaronta jinsa ya d'auke ita ce tsaya a wajan yanzu tana cewa.
"Babufa kud'in da zan amsa naku, iyakaci a fito min da Fad'ime ta bud'e ma Yaro na kunnansa, idan ba haka ba kuma nima wallahi wajan Y'an Saddan zan kai k'ara, domin ni kud'inku babu uwar da zasu min".
Inna Fatuh zatai magana ta hango Fad'ime dake tafe ita da zugar K'awayenta.
Ganin Ibrahim zai nufi wajanta Babban Yayansu ta d'aga masa tsawa tana cewa.
"Na rantse da Allah karka sake ta tab'a min Jika, karka sake na ce".
Duk maganar da take yi hakan baisa Ibrahim tsayawa ba, sai da ya kamo hannun Fad'ime dake zare ido waje y'an cikinta na k'ara, domin tasan an kawo k'ararta tun kan ta iso gida, tana jin tsoron Ibrahim shine kad'ai duk cikin familynsu take d'an shakka shima kad'an.
Sai da ya d'auketa da Mari har sau biyu, yana zare mata ido yana cewa.
"Dan Ubanki abunda aka ce kije kiyo kenan?, kin san iyayen mutanan da suka zo kawo k'ararki? Ke wai wacce irin y'ar banzar yarinya ce ne?, shegiya kamar shaid'aniya, ke kullum kece y'ar kawo k'ararki wajan mutane, dalla wuce min a nan karna karya miki k'afafu yanzu nan wallahi".
"Karyata mana, ai kawai ka idasa min ita na ce kaji Ibrahim?"
Cewar Inna Fatuh data warce Fad'ime daga hannunsa yanzu tana b'alla masa uwar harara.
Banza yayi da ita ya kalli sauran K'awayen yana zare masu ido ya ce.
"da'aAllah can kuma kubar wajan nan".
Aje nik'an sukai da sauri suka juya da gudu suka bar wajan.
Sake fisgo Fad'ime yayi a hannun Inna Fatuh ya matso da ita inda Matar nan take da Yaronta yana cewa.
"Kiyi Maza-maza ki bud'e ma Yaron nan kunne idan ba haka ba kuma na rantse miki na lahira sai fiki jin dad'i".
Matsowa Inna Fatuh tayi wajan tana cewa.
"Wai kai Ibrahim wane irin abu ne wannan kake haka, kana ma yarinya tsawa sai ka ce ba ubanku d'aya ba, ai ku duka ba k'aunarta kuke ba, shikenan kullum ace cikin hantarar kuke, to wallahi ranka zaiyi mummunan b'aci ne".
Nan d'in ma ba tanka mata yayi ba.
Sai k'ok'arin bugu da yake son kaima Fad'ime domin yaga yadda ta wani tsaya bata niyar yin abunda ya ce.
Yasa Inna Fatuh kallon Malam dake tsaye cike da jin haushinsa shima ta ce.
"Idan har ni ce na haifeka to kaba Yaronka umarnin cewa karya sake ya sake tab'a min Jika, idan ban isa dashi ba, ai kai na isa da Kai".
Ba dan Malam yaso ba ya dakatar da Ibrahim daga dukan da yake son kaima Fad'ime.
Malam ya matso a hankali cikin kwantar da murya ya ce.
"Fad'ime y'ar albarka ki bud'e ma yaron nan kunnansa kinji".
D'an sakin fuskarta tayi domin da tun farko da lallami aka bi da ita da tuni tayi abunda suke so. Dan a duniya Fad'ime ta tsani a d'aga mata murya.
A hankali ta juya wajan Inna Fatuh tana cewa.
"Suje gida Kunnan nasa zai bud'e".
Tana fad'ar haka ta shige cikin gidan.
"Kutumar uban can, ni Lami naga takaina, ace yarinya tayi laifi amma ko a jikinta, ko da yake d'aurin gindi ta samu ai, dole tayi abunda take so ai, ta taka wadda take so ".
Inna Lami ta fad'a cike da bak'in cikin Fad'ime, yau so tayi a tafi Police teshin d'in da ita ace ubanta sosai.
"Ohhh dai ba kuma yadda za'ayi da ita kuma ba".
Cewar Inna Fatuh.
Lami ta shige gida tana jin bak'in cikin dawowarsu wannan gidan, da ace suna can gidansu ai da sai yadda tayi da wannan aljanar yarinyar.
Kamin su wuce ga mamakin Matar nan uwar yaron nan sai ji tayi Yaronta na cewa yanzu yana jin komai cike da murna yake fad'ar haka.
Inna Fatuh ta kallesu tana cewa.
"To daga yau sai kiyi ma D'anki gargad'in cewa karya sake Jan Jikata, dan k'ila a gaba zai iya rasa idanuwansa ma".
Itama ta k'are maganar tana d'aukar nik'anta dasu Laure suka aje, ta shige cikin gidan.
Malam ne ya tsaya ya sake ba Matar hakuri sosai...........