BA DON MACE BA

Chapter 5

by @fatiimafantah

*BA DON MACE BA...*

✍️ *BY FATIMA FANTAH*




*BA DON MACE BA... LITTAFIN KUƊI NE A KAN ₦500. GA MAI BUƘATA YA TURA KUƊINSA TA WANNAN ASUSUN 0421863702 FATIMA MUHAMMADU GT BANK. SAI A TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR ***. ALLAH YA BA DA IKON SIYA DA BIYA. AMEEN.*



*SH 5*


G.R.A

MODOJI



 Sallama ta yi cikin falon gidan, a guje Badiyya ta fada jikinta, tana faɗin oyoyo Mom. Sai da ta gama murnar ganinta sannan ta sake ta. A shagwaɓe ta ce, "Mom..." 

"Na’am diyar Mom, duk kin bi kin ɗaga mani hankali." Turo baki ta yi, "Mom ba ki san yadda na gaji da jinyar nan ba, a ce mutum koyaushe yana barci, ko ya tashi fa kaman wanda ya sha kayan maye, a daddafe yake komai sai kuma ya koma ya cigaba da barcin, Wallahi ba ki ji yadda na gaji ba."

 Murmushi Mom ta yi. "Ke ki kwantar da hankalinki, aikin ne da yawa shi ya sa aka ɗauki lokaci."

"Amma yanzu komai ya kammala ko My Mom?"

"Komai ya kammala, ke dai mu je daga ciki."

"Yawwa Mommyna." Badiyyah ta ƙare maganar da murnarta. Takawa suka yi a nutse suna mai da yadda aka yi har suka isa bedroom din ta da ke saman bene. Zama ta yi kan gado ta ce, "Mom ya ake ciki? Na fa ƙagara na ji yadda aka tsaya." 

"Kwantar da hankalinki, bari ki gani." Hannu ta sa cikin haɗaɗɗiyar hand bag ɗinta ta fiddo wani magani. "Karbi wannan, yanzu da yake barcin nan kawai ki bude kwalbar ki saita daidai hancinsa, da zaran ya shaƙa zai mance da komai kuma zai tashi daidai yadda yake, wannan gane-ganen da yake yi da abubuwan da yake ji duk zai daina, haka aka tabbatar mini."

 "Yawwah Mom, ki ga fa tafiyar mu bai fi saura sati daya ba amma mutum baya hayyacinsa kamar mahaukaci, wallahi Mom ba ki ji yadda na gundura ba, kuma wallahi ba na so a ce ba mu samu damar yin tafiyar nan ba, ai ni aka fasa an tafka mini babbar asara."

 "An tafka maki, ko an tafka mana, ke mu je maza ki shaƙa mashi, ya mike ya warware a yi tafiyar nan." Karbar maganin ta yi ta ce, "Haka ne Mom, ba a bori da sanyin jiki, yanzun nan zan je na shaka mashi shi."

 "Allah sarki, mu je in gan shi." Mikewa ta yi suka isa bedroom dinsa tare da ita, kwance yake yana baccinsa a nutse,. Badiyya ta ce, "Mom kin gan shi ko ya tashi da ya sha magungunan nan sai ya koma barcin. Kwana nawa ana abu daya, kuma abun ko sauki baya yi abun har mamaki yake ba ni ma fa. Uhmm, ba na gaya maki ba aiki da 'ya'yan Malaman zaure akwai wahala an ba su sun ci sun sha, dubi fa gumurzun da muka sha kafin a zo nan."

 Wani motsi ya yi tare da juyawa, cikin ƙaraji ya furta, "Ummaaah! Lilbirrah!" Badiyya ta ruƙunƙume uwar, sake maimaita sunayen ya yi guda biyu. Badiyya ta saki Mom tana wiƙi-wiƙi da idanuwana tana kallonta. "Ke Badiyyah da ma haka yake wannan abun?" Mom ta fada a firgice. Kada kai ta yi, "Bai taba haka ba Mom, hasali ma yana dan tuna abubuwa amma bai taba ambatar sunayen su ba." Dukar da kanta ta yi kasa, "Innalillahi, Mom kwalbar ta fashe." Ta ƙare maganar a firgice. Zaro ido Mom ta yi, "Ɗauki abun ki shafa a hancinshi, dauki ki shafa mashi na ce. Kin san nawa na biya kafin a yi mini wannan aikin dubu dari biyu da hamsin na bayar, haba Badiyya ya za ki saki kwalbar?" 

 "Mom wallahi tsoro ya ba ni, ban san ma ya faɗi ba." Dukawa ta yi ta dauko kwalbar, abinda ke ciki mai kamar mai ya zube, sai dai ɗan abunda ba a rasa ba. Matsawa ta yi inda ya koma barcinshi bai san suna yi ba, hannu ta sa ta lakaci maganin da ke ciki a hankali ta goga mashi a hancin. Juyawa ya yi tamkar yana sane da me aka shafa mashi, ya ƙara buɗe ƙofofin hancinsa ya shaƙa. 

 "Yawwah aiki ya yi dama haka Boka Rigijim ya ce zai yi." "Wai Allah Alhmadulillah, ai Mom hankalina har ya tashi, a ce ya tashi da wadannan mutanen a bakinsa ai kashinmu ya bushe kuma. 

 "Ɗan buhun uba, yanzu kai da su Ummah kuma sai lahira kwa haɗu." Badiyya ta faɗa. Dariya suka yi gaba daya. 

"Yawwah, komai ya kammala bara na tafi."

"Yanzu Mom komai lafiya?" 

"Na ce maki garau zai tashi, ai mu dama mun san daga inda abun yake, saboda haka an ƙaras." Dariya ta kuma yi, ta ce to Mom Allah ya kiyaye, sai kin ji ni zancen tafiyarmu. Tare suka fita suna kara tattauna abubuwan da suke son cimmawa a gidan AbuƊalib.

 


ABUƊALIB

 Wuraren ƙarfe biyar na yamma ya tashi, hannu ya sa ya dafe kanshi da ya yi mashi nauyi, muryarsa a shake ya ce, "Shona… My Shona." Da sauri ta karaso cikin falon. "My Boo, ta fada tana zama gabanshi."

 "Wanka nake so na yi." Ya faɗa yana kallonta.

"Okay Bubuna bara na hada maka ruwan, ya karfin jikin naka, da sauki ko My boo, sannu ka ji," ta fada tana shafa fuskarshi. 

 "Na ji sauki sosai, ji nake kamar an cire min kaya, sam bana jin komai cikin kaina."

 "Wayyoo dadi, Alhmdlillah. My Boo ya sami lafiya, haka nake ta son ji." Shafa fuskarshi ta yi, Haka nake ta son na ji ka faɗa, Allah ya kara maka lafiya My King," bai amsa ba ya zuba mata idanu yana kallonta. Sumbatar gefen kumatunshi ta yi, sannan ta mike ta shiga toilet dinshi, ruwa masu dumi ta hada mashi cikin kayataccen jacuzzinshi, foitowa ta yi ta kalle shi tana murmushi.

 "My Boo, na hada maka ruwan." Okay. Mikewa ya yi ya buɗe wardrobe yabdauko rigar wanka. Rage kayan jikinshi ya yi sannan ya shige toilet din. Wanka ya yi zuciyarsa tana ta sake-sake da tunane-tunanen da ya rasa madafarsu.

 Sai daya gama sannan ya fito, zama ya yi kan kujerar gaban mirror. Lotion din shi ya dauko ya fara shafawa, da sauri ta isa wajen shi ta karɓa, "My king ciwon nan naka ya tayar min da hankali." Dan gajeran murmushi ya yi mata, "Ni ma ya ya daga mini hankali My, amma yanzu ji nake na yi garau don ma ciwon kai da nake ji kadan-kadan. Amma kar ki damu fa, i'm feel okay."

 "Na ji dadi My, ka warke, yanzu bara na je na hada maka Dining, ka zo ka ci abinci, ina kallon fuskarkan nan mai kyau tana mun murmushi." 

Jinjina kai kawai ya yi yana mayar mata da martanin murmushi, tana fita kai tsaye bedroom dinta ta nufa. Waya ta dauka ta kira Mom din, cikin murna ta ce mata "Mom, albishirinki, yadda kika faɗa hakan ta kasance ya tashi tangarangam, kamar ba abunda ya same shi." 

"Me na faɗa maki, ai aikin mutumin nan ƙarshe ne, sai ki mai da hankali kuɗin aiki har da la'ada za ki wawuro mana." 

"Mom ke ma kin san ba ki da matsala." Badiyya ta faɗa suna dariya. 

 Tana ajiye wayar ta fice zuwa dining area, a nutse ya fito ya zauna kan ɗaya daga kujerun dining ɗin. "My Boo, har ka fito? Ka ga ban haɗa abincin ba ko, ina fitowa na ji ina son zuwa toilet." 

 "Toilet kuma, Shona za mu ci abincin?"

"Sorry My. Kawai na yi no.1 ne fa." 

"Okay. Haɗa min abincin ina jin yunwa sosai." 

"Okay. Let me do it quickly. Ba za ka jira ba." Kitchen ta shige ta fara harhaɗa kayan tana ajiyewa. Bayan ta gama tsaf ta fara zuzzuba mashi, ci yake a hankali. Jefi-jefi take jifar shi da hira, amsawa yake yi kamar baya son magana har ya gama cin abincin gaba ɗaya. 

 

★★★★★


 Tun bayan komawar su asibiti jikin Umma ya dan yi sauki, har tana iya cin abinci sannan tana iya zama da zuwa toilet. Rumaisa ta kalle ta cikin tausayawa, tabbas Ummah ta hadu da jarabawa da kaddarar rayuwa, wacce ko a mafarki ba ta taɓa tunano ta ba.

 Abu kamar wasa har an kwashi tsayin watanni shida ciff ba tare da sun kara saka Yayansu AbuDalib a idanuwansu ba, haka sunan 'yaruwarsu Lilbirrah ya zama tarihi daga zuri'arsu, wannan abun takaici ne da baƙin cikinsa ya wuce a kwatanta.

 Ummah ta fito daga daki ta nufi toiet a hankali. Kallon Inna Uwale Rumaisa ta yi, cikin sanyin murya ta ce, "Inna ranar nan kika ce za a shiga cikin lamarin nan na Yaya Abudalib, Umma kowa ya yi shuru ya rabu da mu, tamkar ba wanda ya san abinda ya faru, haka za a zuba idanuwa Badiyyah su cigaba da juya Yaya su kaɗai?" Numfashi Inna Uwale ta sauke a hankali ta ce, "Ban mance ba Rumaisa, abun yana raina kamar kuɗin haya, kuma tabbas zan ɗauki mataki ba za mu zauna bisa hukuncin Umma ba, don ba mu san abinda su Badiyya za su yi a gaba ba. Alhamdulillah jikin Umma ya yi sauki, don haka da yamman nan zan shirya in fita idan na fita zan je can Yammawa wurin Malam Saleh, idan an gama abinda ake yi, an ɗauki mataki Umma ta san komai."

 "Shi ke nan Inna Uwale, amma idan Umma ta sani yanzu akwi matsala."

"Ki kwantar da hankalinki ba wanda zai sani, ba kuma abinda zai faru."

 Jin takun Umma ya sa suka yi shuru suka daina zancen da suke yi. Wuce su ta yi ta koma kan gado ta kwanta, kallon Inna Uwale suka yi da Rumaisa, shuru ta yi alamun ba ta ji zancen da suke ba. 


 ★

 Inna Uwale tana fita kai tsaye Yammawa ta yi ma tsinke. A kofar gida ta samu Malam Saleh, kasantuwar yana cikin daliabai gaisawa kawai suka yi ta wuce cikin gida.

 Inna Uwale suna cikin gaisawa da Sa'adatu matar Malam Saleh ya shigo. Cikin girmama juna suka sake gaisawa.

 A hankali ta ce, "Malam na zo ne kan maganar AbuƊalib, duk kun yi shiru tamkar AbuƊalib ba jininmu ba ne, kun zuba ida kun bar waccen yarinyar ita da mahaifiyarta suna cin karensu babu babbaka."

 Ɗan gajeran murmushi ya yi irin nasu na manya, "Uwale, kin faɗi jini ga Uba da ya haifi ɗansa da kansa? AbuƊalib fa ɗana ne, ɗan da na haifa. Kamar yadda bana mance karatun da ke kaina, sau ɗaya ba na mancewa da AbuƊalib. Kamar yadda kika ce, na bar su ne su ci karensu babu babbaka, na bar su kuma na ga iya gudun ruwansu. Amma na lura ba su san me suke yi ba, kuma ba su san kawaici da kauda kai ba. Saboda haka sun yi nasu, muma za mu yi namu."




*KI MALLAKI NAKI A KAN ₦500 KACAL.*

*CONTACT ME @*** IF YOU'RE INTERESTED*


*TAKU MAI ƘAUNAR GANIN FARIN CIKINKU A KOYAUSHE, FATIMA MUHAMMAD SANI AKA FANTAH. NAKE MUKU FATAN ALKHAIRI KU KASANCE CIKIN ƘOSHIN LAFIYA.* 

 

*KU DANNA BLUE LINK DA KE ƘASA KU YI FOLLOWING WHAT'S APP CHANNEL ƊINA DOMIN SAMUN DUKKAN SHAFUKAN ƊANƊANO.*


***


*DON'T FORGET TO LIKE👍 COMMENT💬 SHARE🔀*