012
*BAYA DA ƘURA.*
Fitattubiyar2025
©️Nana Haleema.
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11
*BOOK 1*
Page 012
Da sauri ya fito daga motar yana kallon ta da take zaune a ƙasa a da alama ya taɓa ta da motar, kallon ta yake maimaita sunan ta yaga sai waige-waige take yi a ransa yana mamakin har lokacin bata tafi ba kenan, "kina lafiya?." Ya faɗa yana kallon ta. Da sauri ta kalle shi tace, "shi na gani yana kallona, tsoro nake ji dom Allah ka taimake ni."
Kallon inda take kallo yayi yaga babu kowa yace, "waye?." Ganin a ruɗe take sai yace, "tashi." Yunƙurin tashi take amma ta kasa dan ta ɗan bugu a ƙafar ta ya riƙe hannun ta ta tashi tsaye tana ɗingishi ta shiga motar shima ya shiga motar har lokacin a tsorace take.
“Nidai na shiga uku da wannan mutum, wallahi shi na gani yana zuwa inda nake" ta faɗa tana kuka. Kallon ta yayi yace, "waye?."
"Wani ne wanda ya taimaka min ya kawo ni nan shine daga baya ya kaini wani gida na gudu, yanzu ma shi na sake gani yana zuwa inda nake."
Tunawa yayi da abinda ya faru a wancan lokacin yayi tsaki dan shi tun a lokacin laifin ta ya gani sam-sam bai san meyasa matan yanzu basa kishin kan su ba. Ƙafar yaga ya riƙe tana cize baki yace, "Kina Jin ciwo?." Kai ta girgiza kafin tace, "kaɗan ne."
"Kin tabbatar?." Ta daga kai alamun eh.
"Ina zaki je?."
"Gidan mu zanje." Unguwar ta faɗa masa ya kaita har bakin layin tace ya isa ya tsaya ta kalle shi taga titi yake kallo tace, "na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi."
Da Amin ya amsa ya kalle ta yace, "a gidan zaki kwana?." Ta girgiza kai tace, "A'a yanzu zan koma, bazan iya kwana Mama na asibiti ba."
"Okay" ya faɗa a taƙaice ta fita daga motar shi kuma ya juya motar ya tafi.
Ƙafar na mata ciwo amma haka ta taka zuwa gıda ta shiga gidan su Surayya ta karɓi makulli suka fito da Surayya suka shiga gidan. Yana nan yadda ta barshi wanka ta shiga tayi ta fito Surayya na zaune taga tana tafiya daƙyar tace, "Meya same ki?." Manal ta zauna tace, "ƙafata ciwo talemin, bige ni akayi da mota."
"Yaushe?” Ta faɗa da tashin hamkali.
"Yanzun nan, wannan likitan mai haɗe fuskar nan ne ya buge ni tsoron sa nake ji shiyasa ma bance masa ina jin ciwo ba kuma shine ya kawo ni." Surayya tayi dariya ta ce, "ke nima tsoro yake bani, da kina kwance nan fa da nayi abu sai yayi tsaki, ai wannan sam bai kamata ya zama likita ba.”
Manal tayi dariya tace, "Dr Huzaifa ya fishi kirki, bara na shirya na koma. Baba bai dawo ba ko Surayya?."
"Bai dawo ba gashi naji ana zancen ba'a samun sa waya." Manal tace, "Allah yasa lafiya" ta faɗa tana shiga ɗaki ta jiyo Surayya na cewa, "ɗazu Mubeena tazo gidan nan ai." Manal bata ce komai b dan lamarin Mubeena yanzu tsoro yake bata ba iya mamaki ba. Shiryawa tayi cikin doguwar riga kusan ko yaushe kayan ta kenan, doguwar riga musamman abaya ta ɗauki wasu a leda harda sabulun wanka ta ɗauka da humrar da turare duk ta saka a leda ta fito tace, "Surayya zan koma."
Suka fito tare da Surayya tana cewa, "Milky dare yayi baza ki bari sai gobe ba?." Manal tace, "bazan iya ba wallahi, gwara na koma hankalina zai fi kwanciya, in ina na bazan iya bacci Mama na can ba, to in ta farka ma fa?" ta faɗa tana kulle gidan ta bawa Surayya makullin kafin tace, "tafi dashi ina shiga Mama han ni tafiya zata yi, bara na shiga na gaida su Umma." Surayya tace, "to nima bara na kawo miki abinci kafin ki fito." Ta amsa da to ta shiga gidan Baba da sallama jin muryar ta aka amsa a daqile tace, "Umma ina wunin ku?."
Wacce ta kira da Umma tace, "da ban wuni ba ai baza ki ganni ba, ana can ana yawon banza an fake da uwa babu lafiya, a haka dai za'a ƙare uwa yawon banza ya haka ƙanwa ma haka. To haka ne mana tunda a hanya aka tsinto uwar, waye ya sani ma ko duk a yawon banzan aka samar daku?.”
Ajiyar zuciya Manal tayi bata ce komai ba saboda darajar Baba, amma badan Baba ba wallahi sai tayi mata tas nan gaba ta kiyaye bakin ta, to ko babu komai Baba uba ne a wajan ta.
T fito ta shiga gidan su Surayya dan bata fito ba Maman su take cewa ta zauna taci abincin sai ta tafi haka kuwa akayi taci ta ƙoshi, a nan take faɗawa Mama wanda ya kawo ta Mama tace, “An gode masa, Amma Manal kar fa ganin Mama na kwance ya saka ki dinga yin abinda ba halin ki ba, wancan lokacin na san ruɗewa ce ta saka ki shiga motar wanda ya kai ku asibitin wannan lokacin fa?.”
Manal tayi shiru Mama tace, “ba halin ki bane kar ki fara yanzu, duniyar babu yarda a ciki masu zuciyar taimako kaɗan ne Manal.” Manal tace, “zan kiyaye in sha Allah Mama.”
“Allah ya tsare, sharrin mutum da aljan yasa ku fi ƙarfin su.” Suka amsa da amin sannan ta fita zuwa kan titi ita da Surayya zuwa lokaci har anyi sallar i'sha.
Bebi kuwa koda yayi gaba ja yayi ya tsaya haka nan yaji bazai iya tafiya ya bar Manal ɗin ba bayan tace masa asibiti zata koma ba, in Kausar ce ko Mimi ko Lubna bazai tafi ba, kuma shi duk wata mace a duniya indai ta riƙe mutuncin ta yana matuƙar kishin ta, baya so yaga ta wulaƙanta haka nan Allah ya halicce shi shiyasa in ba Allah ne ya kiyaye ba mace zatayi saurin cutar sa saboda raunin da yae dashi a kanta.
Tunawa yayi da abinda ya faru da wanda tace ta gani a bayyane yace, “in wani abun ya same ta kamar ina da alhakin hakan.”
Yana hango su madubi akan titin sai taɓa ƙafar ta take yi ya ƙaraso da motar ya tsaya ya sauke glass ya kalle ta itama ta kalle shi tana son yin magana amma babu wannan fuskar hakan a tare dashi, ganin tayi shiru bata ce komai yace, "shiga na mayar dake.”
Ta kalli Surayya itama ta kalle ta, da ido Surayya tayi mata alama da ta shiga hakan ya saka tace, "Sury sai kin zo, na gode."
"To Milky Allah ya ƙara lafiya" ta faɗa tana juyawa ita kuma ta shiga motar haka nan take jin gaban ta na faɗuwa. Bata taɓa shiga motar wani ba tunda take, ita adaidaita sahu ta saba hawa shiyasa take a takure ga faɗan da Mama tayi mata sai yawo yake mata. Gata ga namiji dai a mota bata taɓa yi ba sai yanzu, gabaɗaya a takure take sai addu’a take dan ɗazu a ruɗe take.
Tana shiga khamshin turare ne ta ya kai masa ziyara, ya kulle ido ya buɗe a duniya baya son khamshi mai ƙarfi yanzu sai ya ɓata masa rai ko ya saka shi ciwon kai, hakan ya saka baice komai ba ya kunna a.c sosai a motar yaja suka tafi.
Baice komai ba bata ce komai ba sai wayar sa da aka kira ya ɗauka yace, "Na’am Mummy." Shiru yayi alamun ana magana kafin yace, "Yanzu zan dawo, bazan wuce mintina goma ba in sha Allah.” Yanke wayar yayi ya cigaba da tafiya har bakin asibitin ya kai ta ya faka daga gefe ta kalle shi kamar ɗazu ba ita yake kallo ba tace, "na gode, Allah ya saka maka da alkhairi."
Da amin ya amsa kawai ta fita ta shiga shi kuma ya wuce gida yana tsaki bai san meyasa mata suke son saka turare ba bayan sun san haramcin da yake cikin hakan. Inda Mimi ce ko wata cikin ƙannen sa ta isa ta shigar masa mota tana wannan khamshin? Itama kawai saboda taimako ne.
Yana gab da gidan yaga an sauke Maryam a mota ya girgiza kai zuciyar sa na zafi a bayyane tace, "zanyi maganin abun" ya faɗa yana shiga da motar gida ya shiga wajan Mama.
Mama na tsaye da hijjabin tace, "au ka dawo?, shirin tafiya nake ai daman gidan Hajiya zani na jira ka shiru shine zamu tafi da Mimi."
"A daren na Mimi zata ja mota Mummy? Muje na kai ki."
"Daga dawowar ka baka ci abinci ba, baka huta ba kace zaka kaini?.”
"Bana jin yunwa naci abinci da yamma" ya faɗa yana fita Mama ta fito ita da Mimi ya buɗewa Mama baya ta shiga ya shiga shima Mimi ta shiga.
Tsaki taji yayi gaban Mimi ya faɗi dan tasan da ita yake yace, "Mummy meyasa basa jin magana ne? Meya amfanin saka wannan banzan turaren da daddaren nan?. In ma turaren yana da daɗi da sauƙi, amma wannan turare kamar na aljanu?.”
Mama tayi dariya tace, "ikon Allah, ni na jima banga mutumin da baya son turare ba sai kai, kamar mai aljanu? Baza’a yi na hayaƙi kana nan ba, baza’a saka a jiki ba. Ke Mimi koma ki canja rigar kizo mu tafi in ba haka ba kafin muje aljanun sa zasu iya tashi."
Mimi ta fice tana ƙunƙuni haka kawai ya hana su saka turaren da suke so dan kawai shi baya son yaji khamshi na tashi sosai, shi wai daga dry spary sai body mint kawai zakayi amfani dashi, ko yaya ka saka mai ƙarfi in kazo inda yake yaji yayi ta bala'i kamar a jikin sa aka saka. Kuma Mummy ce take goya masa baya shiyasa ya samu damar ham turaren wuta a falo ko su saka turare. Mimi na mita ta canja kaya ta dawo ta shiga motar suka tafi dan tasan badan Mama ba bazai jira ta ba.
A can gidan Hajiya tana tayi masa wasa yana mayar mata da amsa dan baya ƙyale ta tayi dariya tace, ka dai ki ƙi aure sai na mutu ko?." Ya ɗan murmusa yace, "kar ki damu na kusa in sha Allah." Mama tayi caraf tace, "kin san da yake takwarar taki ce dai da ita za'a yi."
Nan take fuskar da ta koma yadda take yayi shiru Hajiya tace, "da gaske? Kai amma nayi murna wallahi sosai, na jima ina burin hakan ya faru tsakanin yaran ku. ina son auren zumunci dan kar ace na takura ne yasaka nake yin shiru amma da hakan ya faru naji daɗi. Ni in tani ne yaran nan mata da maza babu wanda zai fita waje yayi aure, nafi so kowa ya zaɓa cikin ƴan uwan sa. Allah ya tabbatar mana da alkhairi."
Mama ce kawai ta amsa Hajiya ta kalle shi tace, "shugaban masu ɗaure fuska, ka dinga dariya don Allah Adnanu wannan rashin fara'ar taka yayi yawa wani lokacin.”
Baice komai ba akayi sallama duk suka amsa suka kalli mai shigowa sai ga Rumana ta shigo da kwano a hannun ta Hajiya tace, "ga amarya, ga kuma angon a zaune." Ganin su Adnan sai zuciyar Rumana tayi fari karr ta ƙaraso ta zauna kusa dashi tace, "Hajiya Ina wuni."
"Lafiya lau Rumana, ya Umman taki?."
"Lafiya lau. Mummy ina wuni?." Mummy ta masa tana murmushi ta kalli Adnan da yayi kamar bai ganta batace, "Beb ina wuni."
Kamar abinda yake jira tace kenan sai yayi sauri ya miƙe bayan ya amsa yace, "Mama in kin gama ina mota" ya saka hannu aljihu ya ɗauko kuɗi ya baya Hajiya yana cewa, "duk da nasan kuɗi ne dake, amma a saka mana albarka." Tayi dariya ta karɓa tana godiya tare da addu’a ya fita.
Rumana ta miƙawa Hajiya kwanon tace, "Hajiya gashi inji Ammi." Hajiya ta karɓa ta buɗe tace, "dambun kaza muka samu, kai Allah yayi albarka. Ga so yayyen nama ma Hauwa’u ta kawo." Rumana ta kalli Mama tace, "Mama ke zan bi a can zan kwana, bara na faɗawa mai kuɗi ya wuce gida kawai" ta faɗa tana ɗaukar waya ta faɗawa wanda ya kawo ta . Hajiya tace, “banda abin babar ki ma ai bai kamata ta ɗauke ki ba, ga wacce ta riƙe ki tun kina shekara biyu har kika girma, amma da tgaa kin zama mutum sai ta ƙwace ki.” Suka yi dariya suka yi sallama da Hajiya suka tafi.
Rumana ce ta shiga gaban motar Adnan yana zaune yana danna wayar sa Mama da Mimi suka shiga baya yaja motar suka tafi. Tsaki Mama taji yayi sai tayi dariya tace, "Ke Rumana ban san me yake damun ki ba, har yanzu kin kasa gane Adnan baya son turare mai ƙarfi, amma ke duk sanda zaku haɗu sai hakan ta faru, wannan tsakin da yake na turaren ki ne."
Rumana tace, "to ni Mama ban san ya yake so nayi masa ba, shi ace baya so a saka turare haka zaka zauna babu turare?" Ta faɗa tana kallon sa, bai kalle ta ba bai kuma ce komai ba tuƙa motar kawai yake yi.
Har suka je gida baice komai ba yana faka motar duk suka fita shima ya fita ya shiga ciki kai tsaye banɗaku ya wuce ya jima ciki sannan ya fito bayan yayi wanka ya saka doguwar riga ya fito ya zauna a lokacin Rumana ta shigo da abinci a hannun ta ta ajjiye masa tace, "Gashi inji Mama."
Baice komai ba ya ja abincin ya fara ci ta zauna kusa dashi ya tsayar da cin abincin yace, "in kina son zaman lafiya ki daina zuwa inda nake da irin wannan turaren, bana son oil perfume."
Rumana ta jingina da kujera tace, "nasan wannan tun a baya Beb, amma ni mamaki kake bani har yanzu meyasa baka son turare?. Da na ɗauka zaka daina zuwa yanzu sai gashi yanzu abin yafi na baya ma, kuma kai ai ana jin ƙhamshin a jikin ka.”
Bai bata amsa ba ya cigaba da cin abincin sa tace, "Ko dai yana saka ka cikin feeling ɗin mace ne?." Kallon ta yayi sai ta rufe baki tana kallon sa baice mata komai ba ya cigaba da cin abincin ta tashi zaune tace, "ni ina son turare kai ma ka sani, tun a wancan lokacin na faɗa maka amma in mun yi aure zan rage."
Ta sake cewa, "Beb wa na gani ɗazu a motar ka? Na ganka kai da mace wacece ita?." Cikin salon tura mata haushi kai tsaye yace, "Wacce zan aura ce." Tayi dariyar rainin hankali tace, "ai kasan baka da matar da ta wuce ni a duniya."
"A aya aka faɗa ko a hadisi?."
"Babu ɗaya, amma dole ya tabbata." Ta sake yin dariya tace, "gwara ka faɗa mata tun wuri ta nemi mijin aure wannan mijin na Rumana ne kawai."
Ya ajjiye abincin ya sha ruwa ya kalle ta sosai yace, "kina ji, ni banza auri ragowar wani namijin ba, komai nawa sabo nake amfani dashi ko meye kuwa. You have to know that, I'm not your type. Banyi kama da wanda zai auri ragowar wani banza ba kin gane?. Ya kamata ki daina hauka a kaina Ruman, na riga na rufe shafin rayuwar ki bazan sake buɗe shi ba har abada. Mummy baza tayi min dole ba dan nasan duk wani hope din ki akan Mummy yake, nobody can force into married you, ki daina wannan rawar kanAdnan na sabuwar mace ne ba na wacce aka rage ba" ya faɗa yan kallon ta ido cikin ido, ya lura maganar ta kashe ta dan tunda auren ta ya mutu ta dawo tana wannan rawar kan bai taɓa faɗa mata magana kamar haka ba.
Murya a sanyaye tace, "Adnan ni ka ke cewa ragowar wani?." Ya jingina da kujera yace, "to meye in ba ragowar wani ba? Ke ba ragowar bace?. Kuma wacce ke da bazan faɗa miki haka ba Ruman?." Ta girgiza kai tace, "ni Ruman wacce ka ke so."
"Point of correction! Ruman wacce Adnan yaso a duniyar yarinta ba wacce Adnan yake so ba. Adnan mace ɗaya yake so yanzu tak a duniya itace wacce kika gan mu tare, ya kamata ki ƙyale mata mijin ta ki daina wahalar da kanki akan abinda baza ki samu ba.”
“Adnan har yanzu kana sona." Yayi Murmushin da yake masa kyau a duk sanda ya bayyana a tare dashi yace, "this is your failure Ruman, kina tunanin har yanzu Adnan yana son ki wannan shine abinda yake cutar dake, Baki san Adnan ya manta da wata mace mai suna Ruman a duniyar soyayya ba. Yana mata kallon ƴar uwa ne kawai kuma wacce suka tashi tare bayan nan babu wani abu. Inda zaki kwantar da hankalin ki ke ƴar uwata ce, kina da wannan matsayin a wajena amma batun soyayya babu” ya faɗa yana wara idanun sa yana girgiza mata kai.
Ta kasa magana sai kallon sa da take yi, ya lura da ya kulle mata baki shi kuma yana sane ya mata haka dan ta san bata isa ta barshi taje tayi aure ba bayan ta fito kuma tace sai ya aure ta ba, beside shi babu soyayyar ta a zuciyar sa Allah ya sani. Ana cewa ba’a mantawa da first love shi kam ya mata da ita.
Ya sake kallon ta yace, "Kina ji, na farko turaren ki ya dame ni, na biyu bana son magana dake ki tashi ki bani waje."
Kai take girgizawa cikin ɓacin rai tace, "wallahi sai ka aure ni Bebi, ko sama da ƙasa zata haɗe sai na zama matar ka." Ya taɓe baki ya tashi yace, "babu abinda zai saka sama da ƙasa ta haɗe a kan ki Ruman, aure ne bazan yi dake ba tunda ba’a dole you have to give me some space please, kina ta insisting akan abinda bazai faru ba."
Tashi tayi tsaye tana kallon sa tace, "dole ya faru ko bak so. Ko dan wannan cika bakin naka sai na tabbatar da ka zama mallakina, wallahi sai ka aure ni, a ranar zan mayar maka da martanin ba ko yaushe ake samun abu sabo ba, ni da ka ke kira ragowar wani sai an kira ni da suna matar Bebi.”
"Okay! we shall see" ya faɗa yana kallon ta ta fita ya bita da kallo sannan yayi tsaki. A bayyane yace, "na gode Allah da ya cire min son wannan yarinyar da ban san ya zanyi ba, ina ni ina auren ta? Ga rashin kunya sannan gata bazawara?. A baya ma tsautsayi ne da ƙuruciya ya kai ni” ya faɗa yana tashi ya shiga ɗaki.