016
*BAYA DA ƘURA.*
Fitattubiyar2025
©️Nana Haleema.
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11
*BOOK 1*
*Page 016*
A nan yayi sallar la'asar yana idawar Kamal yana zuwa, tare suka koma ciki dashi da shugaban da kuma Kamal dɗin. Kamal sai kallon Bebi yake domin ya tabbatar shine ya kawo ƙarar sa baice masa ba shima baice ba a haka suka shiga ciki suka zauna, aka gaisa da Kamal da Malam kafin yace, "Kaine Kamal?." Kamal yace, "ƙwarai ni ne."
"Kasan wannan?" Ya faɗa yana nuna masa Bebi ya kalli Bebi yace, "na san shi, ƙanin tsohuwar matata ne."
Yace, "kaima kace tsohuwar matar ka amma yace kana bibiyar ta, kana so ka mayar da ita ne?." Kamal ya sauke numfashi cikin takaici yace, "A'a babu wannan a zuciyata. Saboda saki uku ne a tsakanina da ita."
Malam yace, "to meyasa ka ke bibiyar ta?." Kamal yace, "in dai naje wajan ta saboda yaran ta ne, wani lokacin maganar makarantar su ce, wani lokacin maganar rashin lafiya ko abinda yayi kama da haka. bayan wannan babu komai."
"Yara zaka iya haɗa su da ita koda a waya ne, sannan zaka iya kai mata su ba lallai sai kun haɗu ba. Haɗuwar ma inda ba ko yaushe bace dan an haɗu an gaisa ba komai tunda akwai zuri'a a tsakani, amma ko yaushe ba daidai bane, shaiɗan zai iya shiga tsakanin ku a aikata abinda za'a yi dana sani." Kamal yayi shiru Malam yace, "Gashi da kan ka kace baka da ra'ayin mayar da ita, to meyasa kuma ka kasa rabuwa da ita?."
Kamal yace, "kamar yadda na faɗa da farko maganar yara ce take kaini wajan ta."
"In maganar yara ce kaje har cikin gidan su a gaban kowa kayi mata maganar yaran ta wannan ba wani abun bane, ko ka kira ta a waya ko ka kira wani nata kamar shi Adnan ɗin. Keɓewar ku ku biyu illa ce a gare ku, zaku dinga tuna rayuwar ku ya baya ne daga wannan lokaci kuma shaiɗan zai ratso ta tsakiya sai wani abun kuma ya afku, ga saɓon Allah ga dana sani."
Kamal yace, "za'a gyara in sha Allah." Adnan ya tari numfashi Malam da yake niyar magana yace, "Malam ayi musu tsakani da ita, tunda babu aure a tsakani to ya jira in akwai rabon zata dawo wajan sa zata koma, ya daina bibiyar ta." Malam yayi murmushi tace, "kar ka damu, duk da itama naso ace tana wajan nan dan itace babbar mai laifi, da bata bada fuskar hakan ba da bai faru ba."
"In bai je inda take ba bazata saurare shi ba" Bebi ya faɗa yana kallon Manal.
Malam yace, "A kiyaye Kamal, kodan saboda gujewa aikin dana sani." Kamal yace, "Gaskiya ne, na gode zan iya tafiya?." Ya amsa masa ya tashi ya fita shi kam Adnan godiya yayi masa sannan ya tashi ya fito.
Yana zuwa gaban motar sa yana niyar shiga yaji Kamal yace, "Wai kai me ka ɗauki kan ka ne? Mahaifin Maryam?." Bebi ya juyo yana kallon sa yace, "zaka iya kira na da hakan ba laifi bane."
"Kana ganin wai hakan da ka yi shikenan ka raba ni da Maryam?."
"Ai hukuma gaba take da kowa, in kana ganin kai kana gaba da ita ne ka sake maimaita abinda kayi. Wallahi nan gaba sojoji zan saka su yi maka dukan da zaka kasa tashi."
Kamal yayi murmushi yace, "ni ka wulaƙanta Bebi har ka kawo ƙarata wajan nan. Ka jira abinda zai faru sai na tartarsa maka zuciya wallahi, badan kai mai kishin ƴan uwan ka ba? Na tabbatar Maryam zata baka kunya wacce baka yi tunanin jin ta nan kusa ba. Kuma ina so ka sani bazan nemi wata hanyar da zan gyara auren mu da ita ba, kuma bazan rabu da ita ba kayi abinda zaka yi."
Adnan yace, "zaka ga abinda zan yi kuwa, domin ba'a shiga gona ta a zauna lafiya, abinda nake so shi nake aikatawa kuma shi nake aiwatarwa akan kowa koda shi baya so. Nafi ƙarfin ka tarwatsa min zuciya Kamal, sai dai ni na tsarwata taka. Rashin ilimin addini ne yake sakawa namiji ya bibiyi wacce ba matar sa ba, ina baka shawara ka koma islamiyya domin yaƙi da jahilci domin yana damun ka sosai. Shine ya ke saka ka aikata hakan kan ganin hakan daidai ne, baka san tsabar jahilici da rashin sanin addini ne ya saka ka ke aikata hakan ba" ya faɗa yana nuna shi da key na mota kafin ya juya ya buɗe motar ya shiga yana ya fita daga cikin wajan.
Da kallo Kamal ya bishi zuciyar sa na zafin kiran sa jahili da yayi, yayi ƙwafa shima ya shiga mota lokaci yayi da zai tabbatarwa da Bebi shi zai tarwatsa masa zuciya, zai ga aikin jahilai kuwa, zai yi dana sanin kiran sa jahili da ya yi.
Mubeena ce ta fito daga banɗaki Bily ta kalle ta taga ta zauna tana cigaba da danna waya tans murmushi Bily tace, "Wai da wa kike chart da kika kasa tashi kiyi sallah?." Ta kalle ta tace, "my future husband mana." Ta faɗa tana ɗaga wayar ta yiwa kanta hoto ta kalli hoton tayi murmushi ta cigaba da danna wayar.
Bily tace, "yanzu kuma kin fara jin daɗin zancen banzan da yake miki kema kenan?."
"Na fahimci soyayya ce hakan, yanzu ma hoton sa ya tura min babu riga amma view once ne" ta faɗa tana dariya alamun abin bai dame ta ba. Bily tayi dariya tace, "Mubeena ki kiyayi wannan tashon fa, wallahi zai iya saka ki dana sani."
Mubeena ta kalle ta da mamaki tace, "na rasa yaushe kika canja Bily, Wai duk meye wannan ɗin? Bafa wani abun yake min ba kawai chart ne, kuma kin san wayewa ce ba wani abun ba."
"Sexy chart din ne wayewa?."
"Ya akayi kika san sexy chart ne?."
"Saboda naga abinda ya rubuto miki a notifications yanzu, shi ko kunya baya ji da ƴaƴan sa da jikokin sa ya tsaya yana wannan shirmen dom Allah?."
Mubeena tace, "kinga Bily don Allah ya isa haka." Bily tace, "bai isa ba Mubeena, sai na faɗa miki gaskiya. Dan ina biye miki ina cewa baki dace da haihuwar gidan ku ba hakan yana nufin na biye miki ki fara iskanci ba." Da sauri ta kalle ta tace, "ni kike ceawa ƴar iska Bily?."
"Ita kike ƙoƙarin komawa ai Mubeena." Mubeena tuna a gidan su Bily take sai tayi sanyi tace, "kinga ki ƙyale ni kawai ni yunwa ma nake ji" ta faɗa tana fita ta bar mata ɗakin, Bily ta bita da kallo tana tunanin lokaci yayi da zata raba garo da Mubeena domin tafi ƙ'arfin ta a yanzu.
Bebi yana komawa asibiti baban Yayan su yayi masa yace in ya tashi daga aiki yazo gida ya same shi ya amsa ya kashe wayar ya ajjiye ya cigaba da abinda yake yi. Huzaifa ne ya masa waya ya ɗauka ya saka a speaker yace, "ina ji."
"Nayi discharging Maman Manal suna so su ganka su yi maka godiya abubuwan da suka faru, ka dawo ne?."
"Godiyar me za'a yi min? Me nayi kuma?."
"Kaga Bebi don Allah ka nutsu, Wai kai ɓacin ranka kowa sai ya shafa? Meye haka ne wai?."
"Mtsww! To me nayi musu ne? Naga aikina ne ko? Dan na yi aikina sai an yi min godiya?. Bana son takura suj je kawai ai nasan sun gode." Huzaifa yace, "sun ce baza su tafi ba sai sun ganka, sannan akwai maganin da kace min zaka rubuta musu, meyasa kake haka ne wai?." Ya sake jin takaici a fusace yace, "indai magani ne zan turo maka yanzu kaje ka siya musu. Bana son magana ka sani in raina yana a ɓace,
domin duk abinda yazo baki na zan faɗa musu ne, don Allah ka ƙyale ni kawai bana son haɗuwa da kowa."
Knocking ake yi hakan ya saka shi datse kiran yace, "yes." Aka buɗe ƙofar aka shiga ya hango Manal ta shigo ya dauke kai daga kallon dan ji yayi kan sa ya sara haka kawai bai san dalili ba, ta kalle shi a nutse tace, "Dr zamu tafi, Allah ya saka da alkhairi Mun gode."
"Amin" ya amsa a taƙaice ya cigaba da abinda yake yi. A tsorace take itama tace, "Dr Huzaifa yace zaka bani takardar magani...." A fusace ya katse ta yace, "kije ki same shi zai naki, bana son magana bana son takura kije kawai!" Ya faɗa yana nuna mata hanyar fita.
Sai da ta tsorata jin irin tsawar da yayi mata tayi baya tana kallon sa tace, "Allah ya baka haƙuri, baza mu iya tafiya bane ban maka godiya ba ka ceci ran mahaifiyarta wacce bani da kamar ta, koda dukana zaka yi bazan tafi ba sai na tabbatar na gode maka."
Shiru yayi baice mata komai ba, amma ji yake kamar ya tashi ya tsinke ta da marin da zata daina gani, ya lura shegiyar maganar ta inda waje ɗaya suke zai iya sakawa ya mata dukan tsiya, ta juya tana tafiya ido ya ciko da hawaye. Da wata likita mace suka haɗu tana fitowa tana shiga ita kuma ta wuce wajan Dr Huzaifa ta shiga da sallama ya amsa yana murmushi domin nutsuwar ta na burge shi sosai yace, "Manal zaku tafi ko?." Ta goge idon ta zata yi magana yace, "ya dai? Ko jikin Maman ne?."
"A'a babu komai."
"Faɗa min mana, me ya faru kike goge hawaye?."
"naje wajan Dr nan abokin ka mai glasses na yi masa godiya shine yake ya faɗa kamar zai dake ni." Yayi murmushi yace, "Kar ki damu ransa ne a ɓace na faɗa miki, haka yake in ransa ya ɓaci baya son magana. Ga maganin ya bani duk zan baki in har tana sha komai bata zai dawo daidai hatta idanun ta zasu iya gani wani lokacin. Kema kuma zan baki naki ki tabbatar kina sha saboda ya daidai miki sugar jikin ki."
Ido ta goge ta amsa yayi murmushi sai ya kalli maganin ya kalle ta yace, "ki jira ni a inda kuke zama zan je na kawo miki kafin ku tafi." Kafin tayi magana aka shigo taga likitan da suka haɗu da ita a wancan office ɗin tace, "Huzaifa meyake damun Adnan yau?."
"Kema ya koro ki ɗin ko?" Ya faɗa yana dariya.
"Inda kaga zai min duka ma kuwa" ta faɗa tana dariya itama yace, "ran sane a ɓace kawai shiyasa." Ta girgiza kai tace, "lallai kam naga alama" ta faɗa tana fita shi kuma yacewa Manal su je suka fito ta koma ɗakin su shi kuma ya fita.
Da maganin ya dawo ya shiga har ciki ya basu suka dinga masa godiya har Baba yace babu komai ai yiwa kaine. Bayan ya fita suma suka fita Manal na riƙe da hannun Mama Baba ya riƙe kayan suka fita harabar asibitin. Bebi yana tsaye yana kallon su ta window sai a lokacin ya tuna abinda ma yayi mata. Yayi tsaki yana kallon su har suka fita daga harabar asibitin daga nan ya daina ganin su.
Yana nan tsaye Huzaifa ya shigo ganin ya juya baya yana kallon taga yace, "abinda kake yi ba daidai bane ba Bebi, bai kamata ɓacin ranka ya dinga shafar wanda bashi ne ya maka ba. Meye laifin yarinyar nan da tazo maka godiya? Don Allah?."
Bebi ya juyo yana kallon sa da mamaki yace, "wai na tambaye ka, Yarinyar nan aure ta zakayi ne?."
"In ma auren nata zanyi ai ba laifi bane ba ko?, bata isa na aure ta ɗin ba ko kuma ni ban kai matsayin auren ba?."
Kallon sa yake yi kafin ya taɓe baki yace, "Ba laifi kam" ya faɗa yana sake juya masa baya.
"Kai kasan ina da wacce zan aura bikina bai wuce kwanaki kaɗan ba, ina mata kallon ƙanwata ne har a jikina haka nake ji saboda yarinyar ta san abinda take yi, ina son naga wanda ya san mahimmacin mahaifiyar sa." Bebi ya sauke numfashi baice komai ba ya juyo ya kalli Huzaifa yace, "to naji mai tausayi, zaka iya bani waje?." Nan da nan ya hasala Huzaifa yace, "bazan fita ba ka fitar dani."
Murmushi yayi ganin ya fusata baice komai ba ya zauna, lokaci ya tafi har magriba ta kusa sanin babu abinda zaiyi kawai ya tashi ya ya kalli Huzaifa yace, "in ka gama ka bada key ɗin a ajjiye min" ya faɗa ya fita ya barshi a tsaye cike da jin haushin sa.
Mota ya hau ya fita abin mamaki sai ya hango su Manal a tsaye Maman su kuma tana zaune da alama babu abin hawa, har zai canja hanya sai ya fasa, ya ƙarasowa inda suke ya tsayar da motar ya sauke glass daidai inda Baba yake yace, "Baba ku shigo na kai ku gida, wajan nan ba'a samun motar haya sosai daman."
Baba ganin sa sai yayi murmushi yace, "ai kam ka kyauta likita, mun gode Allah yyi albarka. Manal riƙe Maman ki mu shiga?." Manal ta buɗe baya Mama ta shiga itama ta shiga Baba ya shiga gaba suka tafi.
Jan motar yayi suka tafi Bebi yace, "hanyar babu jama'a sosai." Mama da take baya tace, "Likita Allah ya saka da alkhairi, Mun gode da taimakon da ku ka yi mana Allah ya biya ku." Ya amsa da amin Manal dai tayi shiru bata ce komai ba kafin Bebi yace, "Ku dinga zuwa asibiti duk bayan sati biyu ana gwada jinin ku sannan ana duba ki saboda matsalar zuciyar ki, sannan Mama sai kin daina ajjiye damuwa in ba haka ba ciwon ki bazai yi sauƙi ba." Mama tayi murmushi tace, "to likita na gode. Manali kina ji a dinga shan magani, likita itace bata son magani ko kaɗan, dana matsa mata sai ta fara min kuka dole na ƙyale ta."
Baba yace, "da yake bakya son kukan ta ba." Mama ta sake murmusawa ta riƙe hannun Manal tace, "To nima ai bata son nawa kukan ne shiyasa bana son nata."
Ɗago ido Bebi yayi ya kalle ta ta mirror sai yaga tana sake goge ido alamun kukan sannan gashi face ɗinta yayi ja alamun tayi kuka. Ɗago ido itama tayi sai suka haɗa ido ya janye idanun sa daga kanta dan yaga alama ta cika sangarta da yawa.
Da yake Manal ta basu labarin har gıda ya kai ta basu yi mamakin ganin ya tsaya a bakin layin ba sai kuma ya kalli layin yace, "mota tana shiga?."
"Ƙyale mu nan ma, Mun gode sosai" Baba ya faɗa yana kallon sa.
"A'a muje ciki" ya faɗa yana shiga da motar daidai gidan Baba yace, "nan ma yayi likita, Allah ya saka da alkhairi yayi albarka ya raya zur'ia." Bebi yace, "Amin. Babu komai."
Mama tace, "Gashi zamu fita ban san sunan ka ba, muryar ka kawai na sani." Bebi yayi murmushi yace, "Adnan."
Mama tace, "mun gode sosai Allah biya" ya sake amsawa da Amin har lokacin Manal bata ce komai ba domin tsawar da yayi mata tana cikin kanta sosai, bata son sake masa magana ya wulaƙanta ta dan ba jurewa zata yi ba.
Suka fita daga motar bayan juya motar yaga Manal ta shiga wani gida su kuma sun isa ƙofar gidan da yake a kulle da alama nan ne gidan, gama juya motar yayi amma ya kasa tafiya kawai so yake ta fito ya sake ganin ta dan yaga kukan take yi. Sai gata kuwa ta fito tana murmushi tana kuma magana ta isa ƙofar gidan ta buɗe suka shiga, ita kuma ta kwashe kayan ta shiga dasu. Kallon ta yake a bayyane yace, "shegen surutun tsiya ne da ita, ga shagwaɓa kamar wata auta." sai yaji babu daɗi akan abinda ya mata ɗazu, duk da ba laifin sa bane laifin tane, yayi ƙaramin tsaki yaja motar ya tafi.