013
*BAYA DA ƘURA.*
Fitattubiyar2025
©️Nana Haleema.
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11
Book one
Page 013
A fusace Rumana ta fita kalaman sa sun mata ciwo sosai ta nufi wajan Mama dan abinda ta faɗa masa so take ya tabbata taga ya zai yi. tana shiga ɗakin Mama ta wuce ta same ta a zaune da ƴan matam tace, "Mama meyasa yanzu Bebi baya sona? Meyasa yake wulaƙanta ni dan Allah ya ɗora min ƙaunar sa?. Na san nayi kuskure a baya da na auri wani bashi ba, wannan dalilin ne ya saka yake min haka? Kuma na gane nayi kuskure kuma na nemi yafiyar sa meyasa bazai sake bani dama ba?." Mama da take kallon ta tace, "me ya faru kike kuma haka? Zauna ki faɗa min ne Bebin yayi miki kuma?."
Rumana ta zauna tace, "Mama ni yake kallo yana cewa ragowar wani ce bazai aure ni ba, Mama in wani zai ce min haka bai kamata shi yace ba, amma shine yau yake cemin bazawara wai yafi ƙarfina. Kuma Mama ko babu komai ni ƙanwar sa ce tare dashi muka tashi a gidan nan, ko dan wannan alaƙa ɗin bai kamata yace min haka ba, auren nan da nayi ƙaddara ce ta kaini tunda ko shekara ban yi ba na dawo. Wallahi Mama ina son Bebi in na rasa shi zan iya mutuwa."
"Ƙaryar banza" Kausar ta faɗa tana daga gefe Mama ta harare ta ta dawo da kallon ta ga Rumana tace, "Haba uwata, na faɗa miki baki da wani miji na gaba a duniya in ba Adnan ba, meyasa kike son zubar da hawayen kina banza a wofi?."
Ta share hawaye tace, "Mama bai yana faɗa min magana kamar yau ba, har cewa yake nice na nace amma shi yanzu baya sona, ni kuma ina son sa Mama."
Mama tace, "ya isa ki daina min kuka. Duk duniya in akwai wanda Adnan yake jin maganar sa to nice, meyasa kika kasa amincewa da nace miki shine mijin ki?. Ko kina kokwanto akan umarnina ne?."
"Mama ba naƙi amincewa bane ba, Ina jin tsoron yadda ya dage kan maganar ne."
"Kar ki damu, ki kwantar da hankalin ki sai Adnan ya aure ki in sha Allah."
Ta goge idanun ta tana jan numfashi tace, "Kuma
Mama har wata na gani a motar sa ɗazu, dana tambaye shi sai yace wai wacce zai aura akwai abinda zanyi ne."
Mama da mamaki tace, "mace a motar Bebi?."
"Eh wallahi Mama na gansu."
Mama ta girgiza kai tace, "wannan ba komai bane kar ki damu, ya faɗa miki haka ne dan ya ɓata miki rai amma bashi da wata budurwa. Saboda son da yake miki tunda kuka rabu bai sake yin wata budurwar ba."
Mimi da take kallon Rumana tace, "to wai Yaya Rumana tun da kin san kina son sa kika rabu dashi kika auri wani?. Tun tashin mu tare muka san ku, ko da baya nan yana karatu kowa ya san Yaya Bebi ke yake so, amma lokaci ɗaya kika juya baya kika ce ke sam baza ki aure shi ba kuma aka ƙyale ki, dan yanzu yace baya son ki sai a takura shi?."
Mama ta harare ta tace, "ya ishe ki malama, tashi ku bani waje." Duk tashi sukayi suka fita dukkan su basa fatan ya aure ta dan lokacin da ya nuna son auren nata wulaƙanta shi tayi ta nuna bai kai wannan matsayin ba saboda ta samu wanda yake da mahaukacin kuɗin ya ɗauke ta suka koma Dubai da zama, sai gashi auren bai je ko ina ba ya mutu.
Rarrashin ta Mama ta dinga yi har taga ta daina fushi ta daina kukan sannan tace taje ta kwanta ta fita ita kuma ya kira Bebi a waya. Yana zaune a lokacin ya rasa wanne irin tunani ma zaiyi komai ya tsaya masa ya tsani zancen auren Rumana da ake masa wallahi, baya qaunar hakan in badan Mama bace babu wanda zai dinga yi masa zancen nan ya zauna lafiya. Wayar yaga tana haske ganin sunan Mama sai ya ɗauka sai kuma ya sauke waye ya tashi daga inda yake ya fito zuwa wajan Mama.
Falon mata babu kowa y shigo ɗakin ya same ta a zaune ya zauna shima yace, "Gani Mama." Ta kalle shi rai a ɓace tace, "Yanzu tsakani da Allah ka kyauta abinda akayi?." Da mamaki ya kalle ta yace, "Me nayi Mummy?."
"Kai yanzu na ɗauka in wani zai cewa Rumana ragowar wani kaini zaka kare ta sai inda ƙarfin ka ya ƙare saboda shaƙuwar ku da kasancewar ta ƴar uwar ka, sai gashi kaine kake faɗa da kanka Bebi, hakan daidai ne?." Numfashi ya sauke haushin ta ya ninku a zuciyar aa yace, "Mummy ƙarata ta kawo kenan?."
Mama ta fusata cikin faɗa tace, "ita ta kawo, ko kana ganin bata kawo kuka gidan magani ba?." Ya girgiza kai alamun jin abinda ta faɗa cikin faɗa yace, "A'a, ki yi haƙuri."
tace, "meye laifin yarinyar nan ne wai? Laifin ta abinda tayi kuma ta gane kuskuren ta tace ka yafe mata, kar ka manta daman Allah yayi ba kaini mijin ta na farko ba, babu wanda zai canja ƙaddarar meyasa ka ke wannan fushin bayan har yanzu kana sonta?."
"Wallahi Mama bana sonta, Soyayyar da nake mata kamar ta sauran ƴan uwa ne amma waccan soyayyar ta jima da gushewa."
Mama tayi mamakin abinda yace amma bata nuna masa ba tace, "ƙarya ne Adnan, ita ka fara so a rayuwar ka, soyayyar farko da wahalar mantawa take, domin tana da tasiri a zuciyar wanda yayi ta. tana nan a cikin zuciyar ka inda zaka bincika sosai zaka gani har yanzu kana son Bebi."
Shiru yayi baice komai ba yasan Mama baza ta taɓa fahimta ba gashi baya son mata musu tace, "ka adana kalaman ka akan ta domin matar kace wacce zaka aura, ku fara daidaita kan ku kafin maganar nan taje gaba." Nan ma baice komai ba amma mamaki abinda yake bashi, ita lokacin da ta guje shi babu wanda ya mata dole amma shi yanzu ana so ayi masa dole a kai dan babu yadda zaiyi.
"Tace min taga wata a motar ka da gaske ka ɗauki wata yau?." Lumshe ido yayi ya buɗe gabaɗaya haushin ta ya sake cika masa zuciya tunda gashi har ta fara haɗa shi da mahaifiyar sa tun kafin auren yace, "eh Mummy haka."
"Wacece ita?."
"Wacce nake so!" Ya faɗa ba tare da ya shirya ba yana kallon Mummy ɗin dan so yake yaga yanyin ta, itama tana kallon sa da mamakin abinda yace Mama tace, "har ka samu wacce kake so babu labari?." Adnan yace, "ina son sanar miki sai yanzu na samu dama."
Mama ta kalle shi kallon baka isa ba tace, "amma kasan kayi gangancin fara son wata bayan Rumana tana da rai ko?." Ya kalli Mama yace, "Mummy yanzu saboda Ruman sai a hana ni abinda nake so?." Mama ya ɗaga kai tace, "ƙwarai kuwa, ai bama za'a hana ka ba, an ma hana ka ɗin Adnan. Sannan kayi gaggawar bawa zuciyar ka haƙuri akan wacece ka gayyato soyayyar ta Rumana ta maye gurbin ta domin gida bai ƙoshi ba baza a kai wa dawa ba Adnan."
Shiru kawai yayi baice komai ba dan bai san abinda zai ce ba Mama tace, "kaje kayi abinda nace, sannan cikin satin nan ku shirya kan ku kai da ita wata mai zuwa ayi auren ku a huta. Ita kuma waccan ka faɗa mata an yi maka mata a gida." Kamar ana zuba masa ruwan zafi haka yake ji a zuciyar sa in ana zancen auren Rumana, baya so ko kusa ko alama, har mamakin Mama yake wai yace an masa mata kamar wani mace. Mama ta kalle shi tace, "zaka iya tafiya ka kwanta, ka kashe min hasken ɗakin." Da to ya amsa ya tashi ya fita itama ta kwanta.
A haka ya koma ɗaki yana mamakin wannan abu da ake son yi masa mai kama da auren dole, zama yayi yana tunani gaskiya baya son auren Rumana badan baya son yiwa Mama abinda take so bane sai dai in ya auro Rumana kamar ma maganar ta tayitasiri a kansa kenan, dolen da take cewa ta tabbata a kan sa kenan, ya bɗe ido yace, "Allah kada ka ƙaddara min auren ta, Allah ka kawo min abinda zanyi da gaggawa na gujewa auren ta" ya faɗa yana sake kulle idanun sa domin samo mafita ya zamar masa dole kafin ayi masa auren dole.
iPhone ɗin Bily take kallo tana kallon Mubeena tace, "iPhone 16 pro max, kuɗin ta ya kuwa five millions a yanzu, Sannan ga kuɗi har naira dubu ɗari bakwai just for ice cream. Wow! Mubeena you have to me very careful akan wannan tsohon. Kamar ba da aure yake son ki ba akwai wani abun a zuciyar sa."
Mubeena tace, "Bily ke kike cemin ya kamata na samu wayar da zan riƙe saboda a dinga ganina big girl, i've finallay fulfilled my dreams. Meyasa bakya murna?." Bily tace, "ban amince dashi bane Mubeena, dan nace ki samu waya ai bance kiyi komai ki samu waya ba, beside bance ki biyewa kowa ba."
"İn ba ta haka ba da wanne kuɗin zan siyi waya? Nifa na faɗa miki babu wani zance na banza da ya taɓa min, In dai ba ina kewar ki ba dama kina kusa dani, shikenan fa."
"Kissing naki da yayi fa, shima hugging ɗin ba komai bane?." Mubeena tabi Bily da kallo tace, "Bill wallahi mamaki kike bani, Meye a cikin kiss da hug dan Allah? It's normal abu da yake faruwa tun a secondary school. Maza nawa kika yi hugging da Muna school?."
Bily tace, "wannan ya wuce ak Mubeena, lokacin ba wani hankali ne damu ba ai. Muna maganar yanzu ne ba wani abun ba." Mubeena tace, "abinda kayi da dan ka yi shi yanzu ai ba komai bane Bily."
Bily tace, "okay naji, in Mama ya warke taga wayar nan a hannun ki me zaki ce mata?."
"Da wanne idon zata gani?."
"Shine ƙarfin guiwar ki? To Baba fa?.
"Shine ya haifan? Ubana ƙasa ta jima da rufe idon sa babu wani mijin mahaifiyata da yana auren uwata da zai latsa ni." Bilkisu ta girgiza kai tana kallon ta tace, "kin yi nisa bakya jin kira" ta faɗa tana shiga toilet ta barta a wajan ita kuma tan sake kallon sabuwar wayar ta.
Washe gari ma da wuri Bebi ya fita koda yaje asibiti theater sukayi bai samu yaje inda su Manal suke bama sai kusan sha ɗaya na safe sannan ya shiga inda Maman take ya samu zuciyar ta t dawo bugawa normal sai jiran tashin ta. Yana fitowa daga ɗakin suka haɗa ido da Manal ta saka black ɗin hijjab yayi mata wani mahaukacin kyau, ganin sa sai tayi murmushi ta ƙaraso tana jan ƙafa tace, "ina kwana, tun ɗazu nake jira kazo ka faɗa min ya jikin Mamana, Yaya Dr Huzaifa bai zo ba balle ya faɗa min a madadin ka."
Kallon ta kawai yake yi, na farko tayi amsa kyau sosai bazai ƙaryata zuciyar sa ba, na biyu ya fuskanci yarinyar akwai surutun kafin ya amsa gaisuwa ta faɗi ma abinda yake ranta.
Ɗauke kai yayi daga kallon ta yace, "tana lafiya kar ki damu."
"Ko yaushe haka ka ke cemin, dan Allah ina son na ganta." Hanyar ya bata alamun ta shiga tayi hanzari zata wuce sai ta taya tace, "Wayyo." sai kuka ta cigaba da jan ƙaafar ta shiga ɗakin.
Bata jima sosai ba ta fito tan darıya da kuka tace, "naji daɗin ganin Mama da aka cire mata oxygen, na gode da kulawar da kake bawa Mama. Duk da baka darıya amma kana da mutunci." Dariya yayi a zuciyar sa ya kalli ƙafar ta yace, "Jiya kika ce ƙafar ki bata ciwo."
"Yau ta fara."
"Ki biyo ni" ya faɗa yana yin gaba tabi bayan sa har office ɗin sa ya nuna mata kujeara babba a gefen office ɗin alamun ta zauna, ta zauna ya tsuguna yana kallon ƙafar daga wajan idn sahun ta ga wajan nan har ya kumbara sosai.
Hannu ya saka ya shafa wajan a hankali tayi shiru dan taji ba da ƙarfi ya riƙe ba, sai da ya shammace ta ya tashi ya ɗauko wani cream ya saka safa ya dawo ya shafa a wajan ya fara matsa ƙafar da ƙarfi.
Da hanzari ta riƙe hannun sa tana kuka tace, "don Allah ka bari ƙafata zata cire da zafi sosai, don girman Allah ka dakata na haƙura na cigaba da zama a haka." Ido cikin ido ya kalle ta sai ta janye hannun ta tayi shiru ya janye idon sa daga kanta ya cigaba da abinda yake yi sai kuka take.
Bai jima ba ya tashi ya zare safar da ya saka ya kalle ta sai kuka take yi sosai yayi tsaki a bayyane yace, "kamar wacce aka karya." Sai da taci kukan ta sosai ta kalli inda yake yana zaune kamar bai ma san da zaman ta ba tace, "ina ganin yana da kirki ashe ba haka bane ba" ta faɗa a bayyane ba tare da ta sani ba, ya jita amma bashi da lokacin kallon ta.
Yatsun sa biyu ya murza suka bada sauti ta kalle shi ya nuna mata ƙofa. Daƙyar ta tashi amma taji daɗi babu laifi, ta fita tana waigen sa. tana fita ya ajjiye pen ɗin hannun sa yayi murmushi ya cigaba da abinda yake yi ba tare da ya san murmushin na meye ba. Bai jima ba ya tashi ya nufi office ɗin Huzaifa ya same shi a zaune shida Hamza suna magana shima ya zauna yace, "me ake cewa da baza'a kira ni ba?."
Huzaifa yace, "yanzu nake niyar yi maka waya, zance ne akan meeting ɗin da za'ayi."
"Oh!" Shine abinda yace kawai yayi shiru kafin yace, "ba wannan ba, ya zanyi da damuwar Ruman ne? Abin har ya kai Mummy tana cewa Hajiyar ta wai mun daidaita da Ruman yanzu aure zamu yi, jiya haka tazo har ɗakina tana cewa sai na aure ta ko bana so, bayan ta fita taje ta samu Mummy duk abinda na faɗa mata sai da ta faɗawa Mummy. Babban tashin hankalina da na cewa Mummy ina da wacce nake so amma Mummy ta nuna na ajjiye soyayyar ta na dawo da ta Ruman."
Huzaifa yace, "İkon Allah, Mummy ta riƙe wuta akan Rumana gaskiya. Amma kai meyasa baza ka amince ba ko dan Mummy ɗin?."
"Wallahi Huzaifa bazan iya ba, ina so ayi kodan Ita amma zuciyata ta kasa amincewa da ita a karo na biyu, haushin kaina nake ji in na tuna cewa na sota a lokacin baya. In na amince da auren ta gaskiya zan cuci kaina ne kuma zan cuce ta." Hamza yace, "amma a baya ka sota, ya kamata ka jure saboda Mama ba bawai dan ita ba."
Bebi yace, "baza ku gane abinda nake ji bane akan ta shiyasa." Huzaifa yace, "to kai wa kake so ɗin? Da gaske kuma ta ganku a motar?." Bebi yace, "wannan yarinyar ce da Manal take kowa oho, na ganta akan titi kun san I can't leave her alone, because I took every woman as my sister. In na barta a akan titi a tsaye nima wani bazai taimaki su Mimi ba in matsala ta same su, that's why na ɗauuke ta na kaita har gıda, har buge ta nayi da motar ma ban sani ba."
Huzaifa yace, "ita Rumana ya akayi ta ga Manal a motar ka?."
"Oho mata, shegen munafurci a cikin ta mana. Ni kuma nayi amfani da damar ne nace ai itace wacce nake so ɗin dan Mummy tayi sanyi ta ta janye maganar ta amma sai ta sake yin zafi."
Hamza yace, "shawara ɗaya a nan Bebi, ko ka amince da auren Rumana ko kuma duk yadda za'ayi ka samo wacce kake sona cikin kwanakin nan. İn Mama ta tabbatar da gaske akwai wacce ka ke so zata iya baka dama guda biyu, na farko ko tace ka aure su dukkan su, na biyu ko tace ka fara auren wacce ka ke so ɗin kamar yadda aka bawa Rumana dama sannan ka aure ta daga baya."
Ya dafe kai yace, "kun kasa fahimtar bazan iya zaman aure da Rumana ba kwata kwata." Huzaifa yace, "ajjiye wannan maganar zakayi, zancen Hamza shine abinda ya kamata ayi."
Ya kalle su ta cikin glasses ɗin idon yace, "a ina zan samu wata mace a yanzu?, ban shiryawa hakan ba wallahi."
Hamza yace, "ga mata nan da yawa, ko yanzu kaso zaka iya haɗuwa guda ɗari na tabbatar a cikin ɗarin nan casa'in zasu karɓe ka hannu biyu ma kuwa."
"Nema matar babu wahala samun wacce zance zan so shine shine mai wahala."
"Ba lallai sai kana son ta ba ai, in ka aure ta nan gaba zaka so ta." Ya girgiza kai yace, "har abada bazan auri wacce bana so ba, in kunga nayi aure to auren soyayya ne, bazan auri wacce bana qaunar ta ba,"
Hamza yace, "ka mayar da hankali akan neman matar, ka saurari zuciyar ka a duk lokacin da idanun ka suka shiga cikin na wata mace, kasan meye so kasan yadda bugawar zuciya take canjawa a duk lokacin da idanu ya kalli abinda yake so ko yake maradin fara so." Bebi yace, "nifa soyayyar ƙurucuya nayi bazan wani gane sosai," Huzaifa yayi dariya yace, "zaka gane, so sunan sa so, balle kai da kayi shi a matsayin na farko. Zaka tabbatar kamar yadda ya faɗa maka hakan shine mafita a wajan ka."
Ya sauke numfashi ya kulle ido ya buɗe yace, "Yanzu Ina zan fara nemo wacce zan so ni Adnan?. Wannan yarinyar Ruman sai Allah ya saka min wahalar da ta saka ni." Dariya sukayi ya kalle su ya sauke numfashi yace, "baza ku gane abinda nake ji bane shiyasa kuke dariya" yana faɗa sai ya miƙe dan ya tuna da abinda zai yi a wannan lokacin hakan ya saka ahi ya fita daga office din.
Sai da yayi sallah a masallaci sannan ya hau mota ya bar cikin asibitin. A ƙofar wani gida ya faka ya tsallaka ya ƙwanƙwasa ƙofar gidan aka buɗe mai gadi ya kalle shi suka gaisa yace, "mai gidan yana nan?." Mai gadin yace, "eh yana nan."
"Dan Allah ka sanar dashi Adnan yana son ganin sa, in yace wanne Adnan kace masa Adnan ƙanin Maryam." Ya amsa da to ya kulle ƙofar ya juya shi kuma ya koma mota zauna.
Ba jimawa sai gaahi ya fito ganin sai ya fito daga motar ya tsallako yace, "yace ace ka shiga ciki."
"Na gode, ga wannan ka sha ruwa" ya faɗa yaana bashi kuɗiya karɓa yana godiya shi kuma ya shiga gidan.
A wata ƙaramar rumfa ya hango shida yaran sa a zaune, yara biyu mace da namiji su naganin Adnan suka taso a tuje suka rungume shi ya kalle su yace, "ba wani Uncle baya bakwa ma zuwa inda nake?" Ya faɗa yana zama a kan kujera kamar yadda yake shima.
"Uncle muna zuwa sai ace kaje aiki." Ya basu chocolate da kuɗi yace da Nabila ta raba musu yaran suka wuce ciki ana murya.
Kallon Kamal yayi mijin Yayar tasa yace, "nasan kayi mamakin gani na." Kamal yace, "sosai ma kuwa, da farko na ɗauka kazo ganin yaran yayar kane sai naga ba haka abin yake ba." Ya ɗan murmusa ta gefen baki kafin yace, "warning nazo maka na ƙarshe akan Maryam, babu aure tsakanin ku ya kamata ka daina bibiyar ta, ina so na tuna maka saki uku ne a tsakanin ku, babu maganar dawowa gidan nan sai tayi wani auren ta fito. Na faɗa ka ƙi, shiyasa nazo da kaina nayi maka warning da babbar murya."
Kamal yayi dariya yace, "Allah sarki yaro man kaza in ji hausawa, yo kai baka san ita yayar taka ya kamata ka jawa kunne ba ni ba? Ita take nema na bani nake neman ta ba."
"Wannan kuma kai ne ka sani Kamal bai dame ni ba, abinda nake so ka sani ka ja mutuncin ka ko dan yaran ka, in ba haka ba zan jawo mutuncin ka kan titi nayi wasa dashi son raina har sai naga ya gushe daga gare ka,"
Kamal yayi dariya yace, "ni ne nake da wannan makamin ba kai ba." Bebi ya girgiza kai yace, "in kana ganin bazai yu ba na sake ganin ka da maryam don Allah."
Kamal ya kalle shi yace, "Ko gobe ma zamu haɗu da ita zan so naga abinda zakayi." Bebi ya miƙe ya kalle shi ya girgiza kai yace, "Allah ya kai mu goben" yana faɗa ya fice ya bishi da kallo yana darıya domin kuwa Bebi bai isa ya hana shi bibiyar tsohuwar matar sa ba duk da babu kome a tsakanin su.