BAYA DA ƘURA

014

by @nanahaleema11

*BAYA DA ƘURA.*

Fitattubiyar2025


          ©️Nana Haleema.


Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11


*BOOK 1*

Page 014




Yana barin gidan asibiti ya koma yana zama a office Hamza ya shigo yace, "Yauwa Bebi barka da zuwa." Bebi ya miƙa masa hannu suka gaisa kafin Hamza yace, Ga baban su yarinyar nan yazo yana so kayi masa bayani akan yanayin babar ta." 


Kai kawai ya ɗaga Hamza ya fita sai gashi sun shigo tare da Baba ya ƙaraso ya zauna Bebi yace, "Baba barka da rana."

"Barka dai likita, ya aiki?."

"Alhamdulillah. Ciwon sugar ta ne yayi yawa sosai, sugar ya hau sosai, da alama ta kwana biyu bata bin ƙa'idar sa kamar yadda aka saba, amma yanzu Alhamdulillah yayi yadda ake so. Sai batu akan ciwon zuciyar ta."


Baba ya gyara zama Bebi yace, "Ko zaka iya tuna lokacin da ta kamu da wannan ciwon?." Baba yace, "za'a iya kaiwa shekara biyar ko shida." Ya girgiza kai yace, "ya taɓa kwantar da ita haka?."

"A'a gaskiya, sai dai wani lokacin in ya tashi tana shan wahala matuƙa musamman in ranta ya ɓaci da yawa a cikin sati ɗaya, to kafin satin zata iya kwanciya ciwo sosai." 


Bebi yace, "ciwon idanun fa?."

"Shi bai fi shekara biyu ba, kuma a lokacin baya tan gani amma ba sosai ba. Lokaci ɗaya ya ɗauke ganin, ana shan magani amma bai dawo ba, sai dai wani lokaci tace tana gani dashi amma kaɗan."


Bebi ya girgiza kai yace, "in sha Allah ganin zai dawo ko da ba sosai ba, ko iya da rana ne zata iya dinga gani indai za'a bi dokar da zamu saka in ta warware. Rashin shan magani mai ƙarfi ne ya saka ciwon idon yazo wannan mataki, amma in sha Allah zata samu sauƙi."


Baba yace, "Alhamdulillah, Allah ya sa hakan."

Bebi yace, "Amin. Sai maganar ƙaramar, ita kuma nata bai hau ba sai dai ya ƙone, ina nufin sugar yayi ƙaranci a jinin ta sosai. Abinda mutane basa ganewa shi wannan ciwon ya fi wa masu ƙarancin shekaru kamar ta illa, yanzu Illar da zai mata ba zai yiwa Maman ta ba." 


Baba yace, "bata jin magana ne, indai akan mahaifiyar ta ne ta amince taƙi ci taƙi sha indai Maman ta zata sha. To wani lokacin in aka kawo takardar maganin in ta tabbatar babu kuɗi sosai a hannuna sai ta bada na uwar kawai sai ta hana na ta. Duk da dai daman ita ba'a ɗora ta kan magani ba gaskiya, iya kula da cima ake bata amma wani lokacin a kan bata magani."


Bebi yayi murmushi kaɗan yace, "Allah Sarki! Ayi ƙoƙarin ganin tana zuwa asibiti kamar duk sati biyu ana gwada jinin ta, tunda ita babu magani ya kamata a dinga lura ta yadda za'a fahimci a wanne mataki ciwon yake. Sannan su dinga yawaita cin cucumber, in baza su iya ci ba su dinga markaɗe ta suna shan ruwan, tana taimakawa sosai wajan daidaita sugar jikin mutum." Baba yace, "in sha Allah."

"Shikenan Baba, daman bayanin da nake so nayi maka kenan." Baba ya amsa yayi masa sallama ya tafi ya koma inda ya bar Manal a zaune ya zauna yana kallon ta yace, "kin fara bani labari aka kira ni, ina jin ki, ya akayi kika tsinci kan ki a asibitin nan? A ina kika samu kuɗin da kika kawo ta nan Manal?."


Manal ido ya ciko da ruwa ta kalle shi tace, "wallahi Baba banyi komai ba, ka tambayi Surayya da ita muka zo babu abinda nayi." 


Baba yace, "ai bance nima kin yi wani abun ba Manal, faɗa min abinda yake faruwa." Manal ta bashi labarin abinda ya faru kafin tace, "ban san hakan zata faru ba Baba, na ɗauka tsakano da Allah ya taimaka mana ganin yana ta taimakawa mutane a wajan, ban yi tunanin hakan ne zai faru ba Baba."


Baba y sauke numfashi yace, "kin yi kurkure Manal, abinda kika yi ba ƙaramin shirme da rashin hankali bane, yanzu da ya cutar dake fa ki cewa Maman ki meye in ta farka?." 


Manal tana kuka tace, "bazan sake ne, na ruɗe ne sosai Baba, a lokcin ina tsoron kar na rasa Mama." Baba yace, "Dan kin ruɗe bai kamata hankalin ki ya gushe ba, ina ke ina bin wanda baki sani ba? Babban abin haushin ma da ya sake ɗaukar ki kuka fita kuma kika bishi, da mai satar mutane ne fa Manal?."


Manal ta goge hawaye tayi shiru Baba yace, "da wasa kar ki sake wannna kuskuren, daga haka wata ran zaki tsinci kan ki a inda baki tunani ba, ba ko wanne mutum ne mai kyakykyawar zuciya ba, na banza sun danne na kirin, ki kula kar rashin lafiyar Babar ki y saka ki fara abinda ba halin ki ba."


Manal ta ɗaga kai tace, "bazan kuma ba, ka yi haƙuri."

"Shikenan, Yanzu nawa ne bill ɗin asibitin? Sun faɗa miki?." Manal ta girgiza kia tace, "tun lokacin nace zamu tafi sai likitan da muke ganin a babban asibiti yace kar na damu shine aka cigaba da yin komai."


Baba yace, "Kar ki damu kamar ya?."

"Ban sani ba Baba, haka yace."

"Bara naje na same shi naji abinda ake nufi." Har ya tashi sai ya kalle ta yace, "Mubeena bata zo ba?." Manal ta sauke numfashi tace, "Tunda tazo da daddare nayi nayi ta zauna taƙi, koMaman bata san tazo ba tayi tafiyar ta, ko waya bata min." 


Baba ya girgiza kai yace, "kar ki sanar da mahaifiyar ki in ta nemi sani, kice mata Mubeena kullum tana zuwa tana barin wajan ne saboda makaranta." Ta ɗaga kai alamun to Baba yace, "zan je na dawo yanzu" ta amsa Baba ya fita ta zauna tayi shiru alamun tunani take yi.


     Washe gari Mama ta farfaɗo jikin ta yayi kyau sosai har abinci taci tana kwance Manal na kusa da ita ta riƙe hannun ta, Maman kallon ta take yi tace, "Manali Yayar ki bata zo ba ko?." Manal tace, "tazo Mama, tana ma zuwa makaranta ce ta saka baki ganta ba." Mama tayi dariya tace, "ƙarha kike" ta faɗa tnaa kallon ta kafin tace, "Allah yayi miki albarka Manal, yadda kike kula dani Allah ya kula dake kema." 


Manal ta amsa da amin Mama tayi shiru tana jin zafin halayen Mubeena a zuciyar ta ko ba'a faɗa ba tasan yana daga cikin abinda ya saka ciwon zuciyar ta yaƙi warkewa kenan.


   *****Kamal ne a zaune a mota shida Maryam tana kallon ta cikin ɓacin rai shima kallon ta yake yi kafin yace, "Wai Adnan ba ƙanin ki bane ba?." Maryam tace, "tunda naji kace kana so mu haɗu nasan bazai wuce zancen Baebi ba, ƙanina ne me ya faru?."


"Yaron nan da tsabar wulaƙanci har gida ya bini ya shiga har cikin gıdana ya zauna yana cemin wai in ban fita harkar ki ba sai ya bani mamaki, ke kin ji wulaƙanci da cin fuskar da yaron nan yayi min akan ki?." Maryam ranta ya ɓaci tace, "na rasa abinda yake damun wannan yaron wallahi, ya takura min kamar shine ya haife ni ko kuma shine babban yaya a gidan gabaɗaya. Nima fa yanzu cewa yayi wai kar a barni na fito."


Kamal yace, "kar a barki ki fito?."

"Wallahi haka yace."

"Lallai ma yaron nan ya fara wuce gona da iri. Dan ina son ki hakan ba yana nufin zan ɗauki wulaƙanci daga wajan ƙanin ki ba Maryam, bazai yu yazo har gida yaci min fuska ba, darajar ki akwai yaci matsayin sa na jinin ki amma wallahi da yanzu ba wannan magana ake ba ke kin san waye ni."


Maryam tace, "ka barni dashi zan yiwa tufkar hanci, bazai sake aikata abinda ya aikata ba in sha Allah." Kamal yayi shiru baice komai ba tace, "kayi haƙuri, bazai sake faruwa ba in sha Allah." Ya kalle ta yace, "soyayyar da nake miki shine ya saka nake bibiyar ki bayan wannan kin san babu komai, amma yaron nan yazo har cikin gida ya ci min mutunci. Da farko da yaje nayi tunanin wajan su Nabil yaje ashe ba haka bane."


Maryam tace, "kayi haƙuri don Allah."

"Ya zanyi, ai dole nayi haƙurim."

"To kayi dariya mana." Ya kalle ta ya kawar da kai bai yi murmushi ba sai ta tuna lokacin da take gidan sa in yayi irin haka, ta kalle shi suka haɗa ido sai tayi murmushi yasan abinda ta tuna shima kuma shi ya tuna a lokacin amma shi baiyi Murmushin ba so yake sai ta aikata abinda ta tuna ɗin dan yasan zatayi bata jurewa fushin sa ko kaɗan.


Hannun ta ya riƙe sai ta kalle shi ya ɗaga mata gira yace, "ina kewar ki." Murmushi tayi tace, "har nayi farin ciki da ka wuce." 

"Na mayar dake gida ko akwai inda zaki je?."

"Eh, Mamy ta aike ni kasuwa akwai atamfar da zan siyo mata." 


Bai ce komai ba ya kunna motar har lokacin yana riƙe da hannun ya fara tafiya sannan ya kalle ta yace, "ina tuna yanayin da muke kasancewa dake, yanayi mai daɗi da yake gusar mana da hankali ni dake, haƙiƙa kin yi matuƙat iya sarrafa...." Sai yayi shiru ya kalle ta sai ta kawar da kai tana darıya amma bata ce komai ba.


Shima dariyar yayi suka cigaba da tafiya ya kai ta kasuwar ya jira ta shiga ta fito ya dawo da ita gida sannan ya wuce inda zai je. 


Tana shiga gida wajan Mamy ta ajjiye ledar tace, "Yanzu Mamy abinda Bebi yake a gidan nan ya kyauta? Ya dinga yin abu kamar shine Yaya komai cikin gadara. Kamal fa yaje ya samu har gida yaci masa mutunci kawai dan yana kawo min yarana ina ganin su, yanzu me ya aikata don Allah?."


Lubna da ke gefe tace, "haka kawai ya hana ni kula Mujahid, ina son shi yana sona yana son rabu mu kawai dan baya son sa, shine nima bazan so shi ba. Wallahi Yaya zanje na samu da maganar nan na gaji, a gida yake so nai ta zama duk wanda yazo yace ya tafi."


Mamy da take jin su tace, "to meye na zuwa wajan Kamal kuma?." Maryam ta zauna tace, "wulaƙanci mana." Mamy tace, "gaskiya bai kyauta ba, ko babu komai akwai yara tsakanin ku da Kamal dan an gaisa ai ba wani abun bane. Maganar Mujahid nima yana bani mamaki ya hana Lubna kula shi a gidan nan gabaɗaya, kuma in kika tambayi dalili babu, akan ra'ayin sa kawai yake son danne mata haƙƙi."


Maryam tace, "to kuwa wallahi bai isa ba, sai ta aure shi dan ni ban ga aibun da yake dashi ba." Mamy ta girgiza kai tace, "abin da mamaki." Maryam ta girgiza kai domin kuwa ta ɗaura ɗamarar cigaba da kula Kamal ko dan taga abinda zai yi.


     

   Kamar yadda ya saba bai dawo ba sai dare ya faka motar sa a gidan ya shiga wajan Mama dan da yunwa ya dawo sosai, yana shiga ya tarar da ita a zaune ita da Rumana ne kawai dan su Mimi basa wajan. Zama yayi yace, "Sannu da hutawa, Mummy yunwa nake ji."


Mama ta kalli Rumana tace, "kawo masa abinci." Ta tashi ta wuce kitchen ba jimawa ta kawo abincin ta bashi ya karɓa ya fara ci yana zaune kafin yace, "Ina Mimi take?." Mimi da yake fitowa daga daki tace, "Gani Yaya, Sannu da zuwa."


Zama tayi sannan yace, "Yauwa. Wannan saurayin naki" sai yayi shiru yana shan ruwa kafin yace, "mun gama magana dashi zai zo gobe, da yau ne ma zai zo sai da ya kira ni nake sanar dashi na manta ban sanar dake ba amma gobe yana nan zuwa" ya faɗa yana kallon ta. 


Da to ta amsa Mama ta kalle shi tace, "ka gama yi masa interview ɗin kenan ko?." Yayi murmushi baice komai Mama tace, "wataƙila a haɗa auren naku kai da ita ai, in Allah yayi shine mijin ta shikenan faɗuwa tazo daidai da zama sai ayi auren naku a wuce wajan."


Shi dai baice komai ba yana cin abinci Mama tace, "ko ba haka ba Rumana?." Rumana tayi ƴar dariya tace, "Haka ne Mama." Sai da yaci abincin sosai sannan ya tashi yace, "yau ban shiga wajan Mamy ba, zanje mu gaisa daga nan bazan fito ba sai gobe." 


Mama tace, "Allah ya tashe mu Lafiya" ya amsa da amin ya juya zai fita Rumana tace, "Gud night Beb." Bai amsa ba bai kuma juyo ba ya fice daga falon haushin ta yake ji sosai a zuciyar sa, ita ko kunyar Mummy bata ji ta dinga abu kamar mara hankali.


    Wajan Mamy y shiga da sallama ta amsa a ciki bai ma lura da yanayin ta ba ya zauna yace, "Mamy barka da dare, yau ban shigo mun gaisa ba gabaɗaya." 

"Barka, ya aikin?." Sai da ya kalle ta jin a yadda ta amsa kamar bata so, amma sai bai nuna ba yace, "Alhamdulillah." 


Maryam da take gefe tace, "wai Bebi meye damuwar ka da Kamal ne? Dan rashin kunya da rashin mutunci har cikin gidan sa kije ka ci masa mutunci? Meya tare mata wai? In ma bibiyar tawa yake ina ruwan ka ba rayuwa ta bace ba?." Kafin yayi magana ta sake cewa, "dan tsabar wulaƙanci da raini shine ɗazu kace wai kar a barni na fita da yake ga wacce ka haifa ko?, ko kuma ga gidan da ka gina ubana?."


Bebi yace, "Duk abinda nake yi ina yi ne saboda rayuwar ki, badan son raina ba ko kuma dan ra'ayina ba....." a fusace ta katse shi tace, "Ina ruwan ka da rayuwar tawa? Ka cire hannun ka daga cikin rayuwar tawa mana sai me?." 


Ya kalli Mamy tace, "Mamy nasan ke kin fahimci abinda nake nufi, ya kamata ki mata faɗa abinda take yi ba daidai bane nan gaba zai jawo mata dana sanin da har ta mutu baza ta daina ba. Meye amfanin kula mijin da ya rabu da kai har da zama dashi a mota ko ina a kulle da sunan gaisawa?. Ko ɗazu shine ya ajjiye ta a ƙofar gidan nan, meye amfanin aikata hakan a wajan ta don Allah?."


Mamy tace, "A'a Bebi, ɗazu nice na aike ta kasuwa, kuma dan sun gaisa da tsohon mijin ta kamar ba laifi bane ba ai ko?." Jin abinda Mamy tace sai ya kalle ta da mamaki sosai yace, "Mamy kina goyan bayan hakan kenan?."

"Ai babu wanda zai ƙi hakan sai kai, ka hana Lubna sauraren Mujahid kawai dan bai maka ba, ko kuma dan ta samu miji su Mimi basu samu ba shine damuwar ka?."


Maryam tace, "ba dole ba, kishin ƴan ubancin ne ya tashi shiyasa yake so ya korar mata shi, yadda nasa basu samu ba itama ta zauna haka."


A fusace ya kalle ta yace, "Kul kar ki sake faɗar haka in ba haka ba zaki nadama. Mimi, Lubna, Kausar, Maryam da Farida duka ɗaya ne a wajena basu da wani banbanci sai na halitta. Kuma bara kiji, ko me zai faru sai na tabbatar na raba alaƙar ki da Kamal wallahi, haka itama Lubna indai ina da rai bata isa ta auri Mujahid ba, duk abinda zaku ce kuce wannan kamar umarnina ne babu wanda ya isa ya canja shi koda Abba ne, dan ni kaɗai nasan hatsarin da yake cikin abinda kuke son yi. Sam baki San abinda kike yi ba, miji ya sake ki saki uku amma kice kike biye masa har ake zama a mota ana tuna rayuwar da ta wuce ana dariya, hakan a wajan ki daidai ne ko kuma wayewa. Rashin sanin darajar kai ne, da kuma rashin sanin ciwon kan ki da bakya yi, ki gyara rayuwar ki ko dan yaran ki" ya faɗa cikin faɗa dan tasan daman dole zaiyi haka baya jurewa tension, kuma in ransa ya ɓacı kome yazo bakin sa faɗa yake kuma a gaban kowa.


Maryam ta kalli Mamy tace, "Mamy kina jin abinda yake cewa ko?" Ta sake kallon shi tace, "ni kuma wallahi sai Lubna ta auri Mujahid sai dai duk abinda akayi kayi" ta faɗa shi lokacin ma yayi nisa da barin falon. ta sake kalli Mamy tace, "Daman Mamy ke kike goya masa baya, gashi yanzu a gaban ki yake zazzaga min rashin kunya kamar ba gaba nake dashi ba, ko da yake har ke ya yiwa bama ni kaɗai ba." Mamy na zaune dai kawai bata ce komai ba amma ya bata mamaki kam sosai.


Rai a ɓace Bebi ya shiga ɗakin sa ya rasa abinda yake damun Maryam gabaɗaya bata da girma sai na jikin ta, in badan haka ba da hankalin ka da tunanin ka ka dinga sauraren tsohon mijin da ya sake ka har ka dinga yi masa darıya kuna zama waje daya?. Yayi tsaki ya zauna, dole ya yiwa tufkar hanci kar abinda yake gudu yazo ya faru.




Nana Haleema❤️🥂