Chapter 04
by @nanameera08
*Chapter 4*
"Nan da ƴan kwanaki zai dawo ƙasar nan kuma shigarsa Udaid na nufin abubuwa masu yawa, saboda haka na shirya komai kuma ina buƙatar taimakon ka, Rasheed!" Gyara zaman glasses ɗin fuskarsa ya yi yana kallonta ya ce"ina tare dake a kowane lokaci kawai ki sanar dani abin da kika shirya" wani cute smile tayi ta cigaba da magana.
***A hankali take taka stairs din benan dan gaba ɗaya a tsorace take, "Habibty" a dan firgice ta juyo ta saki wata ajiyar zuciya tana dafe ƙirjinta ta ce"Sabahul khair Shamma (Barka da safiya Shamma), murmushi Shamma tayi tana kama hannunta ta ce"why are you scared?" Ta marairaice fuska tana kallon Shamma bata ce komai ba, a gefenta ta zaunar da ita bayan itama ta zauna tana kallonta ta ce"kar ki saka damuwa a ranki babu abinda Dameer zai yi miki, ki cire incident din jiya a ranki kinji baby" jinjina kanta tayi hawaye na kawo idanun nata ta ce" in sha Allah Shamma" shafa kanta tayi tana murmushi ta ce"good girl" murmushin Imara ta mayar mata sannan ta tashi tsaye tana kallonta ta ce"zan tafi school" "Allah ya kiyaye" Ameen ta ce tana gyara zaman veil ɗin ta. Sound ɗin takalminsa ya sanya ta ɗago kanta tana duban inda hannayensa zube cikin aljihun trouser ɗin jikinsa ya sakko fuska babu wata walwala yana zuwa ya gaisheda Shamma ta amsa cikeda fara'a bai cewa Imara komai ba ya yi waje ta bi bayansa tana murguɗa masa baki.
Yana ƙoƙarin shiga motarsa yaga shigowar wata baƙuwar mota hakan yasa ya tsaya yana kallon motar har tayi parking, waro idanunsa waje yayi ganin wacce ta fito daga motar sanye take da wata riga irin mai kama jikin nan wacce ta tsaya iya cinyarta fararen cinyoyinta duk sun fito waje sai gyara gashin kanta wanda ya ke ƙoƙarin rufe mata fuska take tana ganinsa ta washe baki ta tawo da gudu da niyyar shigewa jikinsa saurin matsawa ya yi yana kallonta hakan yasa ta dakata tana tsuke fuska ta ce cikin wata siririyar murya
"Haba Akhii yaushe rabon dana ganka baka missing ɗina?" tabe bakinsa ya yi yana ƙoƙarin buɗe motarsa ya ce"wane ya baki shawarar ki dawo?" watsa hannayenta tayi alamar bata sani ba ya kalleta sai kuma ya shige motarsa, Imara tabi da kallo sai kuma ta juya tabar wajen. Sun yi nisa da gida ta kalleshi ganin yanda yake tuƙinsa cikeda nutsuwa ta tura baki gaba ta ce" kuma yau idan suka min magana me zan ce?" Jin bai ce komai ba yasa ta ci-gaba da faɗin"ni wlh zan ce musu ba sunana Katalina ba kuma ni ba ƴar ƙasar nan ba ce har ƙasarmu kaje ka ce aurena zaka yi ashe kai mugu n..." Cak taji ya tsayar da motar ya juyo a fusace ya shaƙe wuyanta yana kallonta da idanunsa wanda suka gama sauya kala ya ce" kina iya aikata duk abin da kikaso a sanda kikaga dama amma ki sani Maheer bazai taɓa lamuntar tunon asiri ba dole ki ɓoye sirrin sannan kiyi abin da na ce miki ki manta da cewa ke Imara ce! Ki manta da cewa ke ba ƴar ƙasar nan ba ce! Ki manta da wata rayuwa ki sanya a ranki ke Katalina ce!! Idan kuma ba haka ba..." Ya cije laɓɓansa sannan ya hankaɗata tsananin azaba ya hana Imara furta wata kalma ta riƙe wuyanta wanda takejin kamar har yanzu hannunsa yana kai wasu zafafan hawaye ne suka shiga sakkowa kan kuncinta lokaci ɗaya kuma wani irin tari na azaba ya ziyarceta, tsawon lokacin data ɗauka a haka Maheer bai kalli inda take ba har ya yi parking a compound ɗin makarantar
"Get down!"
Abinda ya furta kenan ba tareda ya kalleta ba, cikin sanyin jiki Imara ta sauka daga motar ta shiga tafiya toward direction ɗin class ɗin su har sannan bata daina jin zafin shaƙewar da Maheer ya yi mata ba. Koda ta shiga class ta tarar har lecturer ɗinsu ya shiga hakan yasa kawai ta zauna tana sauraran abin da yake cewa duk da rabin zaman nata tunani take har ya kammala lecturen ya fita Rania ce ta kalleta tana murmushi ta ce"yau kin makara meyasa?" kallonta Imara tayi sai kuma ta kwabe fuska ta ce"bansan lokaci ya tafi haka ba" jinjina kai Rania ta yi ta ce"yanzu ya kike jin jikin naki?" lumshe idanunta tayi nan take hawayen da yake kwance cikin idanun ya zubo kan kyakkyawar fuskarta da mamaki Rania ta ce"ya Ilahi, meke damunki? ko ciwon ne? Ina ne ke miki zafi?" hannunta ta sanya ta goge hawayen sai kuma ta kalli Rania tayi murmushi cikin sanyin murya ta ce"ba komai fa I'm fine kawai wani abu na tuna" girgiza kai Rania tayi ta ce"wannan ba halin ki bane Katalina, bamu ɓoyewa juna komai dan Allah ki sanar dani abin da yake damunki kinji" ta ƙarashe maganar cikin rauni shiru Imara tayi tana kallon Rania tabbas tana buƙatar wanda zata faɗawa damuwarta, tana buƙatar wanda zata kwanta jikinsa tayi kuka amma ba Rania ba! "Imara think idan kika ce zaki faɗa mata abin da ke zuciyarki to tabbas zaki fallasa kan ki kuma Maheer ba zai kyale ki ba dole ki danne abin da kike ji kiyi kamar yanda ya umarce ki" wani ɓangare na zuciyar Imara ta faɗa mata haka, da sauri ta dafe saitin zuciyar tata jin yanda take bugawa da ƙarfi.
"Katalina!", Rania ta kirayi sunanta a ɗan firgice ta kalleta sai kuma tayi murmushi tana kokarin ɓoye damuwarta ta ce"karki damu friend ina lafiya kinji babu komai" shiru Rania tayi badan ta gamsu da abin da Katalina ta ce ba.
****
*LONDON*
*Royal Brompton and harefield hospital specialist care*
*7:30pm*
Kwance take akan gadon marasa lafiyar, a hankali take jan cazbahar hannunta. Wata mata farar tsohuwar mata ce kana ganinta kansa ta manyanta amma kuma da gwarinta yanda take komai a nutse ne zai tabbatar da hakan, turo ƙofar ɗakin akai wanda yasa ta maida hankalinta ga ƙofar tana ganin wanda zai shigo likita ta gani hakan yasa ta ɗan tsuke fuska tana ɗauke kai murmushi kawai likitan ya yi sanin halinta ya ƙaraso gabanta cikin fara'a ya ce" how are you feeling maa?" kallonsa ta yi sai kuma ta sake ɗauke kanta tana kallon gefe, girgiza kansa ya yi ya ce cikin harshen turanci" zan miki allurar yanzu" da sauri ta kalleshi sai kuma ta galla masa harara cikin wata kamilalliyar murya ta fara magana da larabci
"Ya Ilahy, wane ya ce maka bani da lafiya? A'a ni nasamu sauƙi Ana-bikhair Shukran laak" ta haɗe hannayenta alamar godiya. Daman ya rigada yasan haka zata yi yasa ya yi murmushi kawai ya ce"I'm sorry maa dole a miki kodan lafiyarki" wangale baki tayi tana kallonsa sai kuma ta ce" yau naga abin da ya isheni to na ce na warke ai sai a barni haka ko kuma..." Shiru ta yi da maganar ganin ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo jin takun tafiyarsa ya sanya doctorn yin murmushi ya juya ya kalleshi, sanye yake da wata riga t-shirt fara jikinta da stickern hoton Damisa sai wani cargon 3-quater black colour sai canvas fari a ƙafarsa yanada tsayi sosai haka kuma yanada faɗi yanayin jikinsa zaka kalla kasan ma'abocin gym ne saboda yanda duk wani ƙashi na jikinsa yake a murɗe kallo ɗaya ya yi musu ta tsakanin gashin da ya rufe fuskarsa sai kuma ya ɗauke kai yana gyara zaman Bluetooth ɗin kunnensa ya shiga takawa har wajen window ɗin ɗakin da alama waya yake da wani. Ganin ya juya musu baya yasa ta yafito likitan da hannu cikin ƙasa da murya ta ce"kaga wannan azababben ya zo dan Allah ka tafi idan ya fita zan nemeka da kaina kaji"
"Min Fadlhik(Excuse me)"
Tsit tayi shiru da bakinta tana kallonsa ganin har sannan wayarsa yake yasa ta sake kallon likitan ta ce"ka ji yaro" jinjina mata kai ya yi sannan ya juya zai fita, "wait" ya faɗa yana juyowa murmushi doctorn ya yi yana kallonsa ya ce"sir You need something?" bai ce masa komai ba ya zauna gefen gadon yana ƙarewa hannunta kallo above 2mins kafin ya buɗe bakinsa cikin cool voice ɗinsa ya ce" zo ka mata injection ɗin" da sauri ta kalleshi sai kuma ta hade ranta tana huci ganin haka yasa likitan ya dawo har ya yi mata allurar ba ta ce komai ba sai kallo da ido tana ganin ya fita ta bisa da harara.
"Da kin daina harararsa Jadda tunda bashi ya sa kansa ba" a fusace ta ce"koma wane ya saka shi ya je shi da Allah babu wanda zai dinga cutata yana azabtar dani wlh" jin ya yi mata shiru yasa ta yi kwafa ta ce"tunda ga mahaukaciya na magana dole ayi min shiru to uwarka Fateymarh ita ka yiwa shiru ba ni ba" tamkar tana magana da gadon da take kai haka ya yi mata daga ƙarshe ma ya tashi ya fice daga ɗakin, girgiza kanta ta yi cikin faɗa ta cigaba da magana " yaro sai shegen miskilanci da jin kai wai shi wani wannan matarsa ta shiga uku a wajensa wai KA SAUYA HALI!" Jadda ta faɗa tana cigaba da jan cazbahar hannunta.
Kai tsaye office ɗin likitan ya shiga bayan ya zauna doctorn ya kalleshi fuskarsa ɗauke da fara'a ya ce cikin harshen turanci" she's getting better yanayin jikinta ya nuna tana samun sauki sosai" shiru ya yi for some second sai kuma ya numfasa "zuwa yaushe za'a iya discharging nata?" Ya faɗa yana miƙewa tsaye, "maybe by next week" jinjina kai ya yi ya juya ya fice daga office ɗin yana wata irin tafiya mai nuni da isa.
*UDAID*
Murmushi Shamma tayi tana kallonta ta ce"shine kika dawo?" kwaɓe fuska tayi ta ce"wlh Shamma na gaji akwai wahala sosai acan shiyasa na dawo kuma wai ina Ameer?" bata rufe bakinta ba ya shigo gidan bakinsa ɗauke da sallama, da gudu ta tashi tana zuwa ta shige jikinsa tana dariya shafa kanta ya yi da murmushi a fuskarsa ya ce"kaifa-al-hal?(ya ya kike?)" tana sake riƙe shi ta ce" Ana-bikhair Ameer" jinjina kansa ya yi sannan ya janye ta daga jikinsa, akan royal cushion ɗin dake parlon ya zauna ya lumshe idanunsa, kallon Shamma tayi sai kuma ta sake kallonsa ta zauna gefensa da mamaki ta ce"Shamma Ameer bashida lafiya ne?" numfasawa Shamma tayi tana kallonta ta ce"nima bana ce ba Maha haka kullum yake yanzu kamar akwai abin da yake damunsa" hannunta na dama ta ɗora akan fuskarsa ya yi saurin sakin ajiyar zuciya yana buɗe idanu, sosai ta ji zafi a jikinsa hakan yasa ta kwaɓe fuska tana kallonsa ta ce"Ameer ka je asibiti kuwa?" jin ya yi shiru yana kallonta yasa ta cigaba"ka ji jikinka akwai zazzaɓi please ka je asibiti ko a kira doctor ya duba ka?" tayi maganar tana sake kallonsa. Ɗan murmushi ya yi yana jan kumatunta ya ce" ina lafiya fa" turo baki tayi tana kallonsa ta ce"a'a ni dai ka shirya gobe muje asibiti" jinjina mata kai ya yi bai sake cewa komai ba ya tashi ya bar parlon. Da kallo ta bishi har ya shige apartment ɗinsa sannan ta kalli Shamma dake zaune har sannan ta ce"Shamma wai ina Akhii?" murmushi ta yi ta ce" bai shigo ba har yanzu" taɓe baki tayi ta ce"wacce na gansu tare ita ce matar tasa?" gyaɗa mata kai Shamma ta yi, tayi murmushi ta ce"she's beautiful" girgiza kai Shamma ta yi saboda sanin surutun Maha kawai ta tashi ta bar wajen. Tana tashi Joda ta fito hannunta riƙe da system ɗin ta as usual kallo ɗaya Maha ta yi mata ta ɗauke kai dan ko kaɗan basa shiri itama Jodan zamanta tayi wajen kamar batasan da mutum a gurin ba, above 5mins kafin Maha ta tashi zata bar wajen har tayi gaba sai kuma ta dawo tana kallon Joda ta ce cikin harshen larabci
"Ina mai baki shawara ki gyara ɗabi'unki tun kafin lokaci ya ƙure miki, akwai lokuta da dama da bamu gane masoyanmu da kuma maƙiyanmu musamman idan mutum ya kasance yana rangwamin sanin ya kamata kamar dai ke ɗin nan. Ki sani lokaci na nan da za kiyi danasanin abubuwan da kika aikata kuma danasani mara amfani, it's better for you to change your attitude or else..." Ta juya fuu ta haye sama. Sai a sannan Joda ta ɗago idanunta wanda suka kaɗa sukayi jajur tabi bayanta da kallo wani irin tafarfasa zuciyarta ke yi tashi tsaye tana sake duban inda Maha ta yi sai kuma ta daki glass table ɗin dake gabanta nan take ya tawarwatse hannunta ya fashe kallon fararen hannunta wanda suka jiƙe da jini tayi sai kuma ta fasa wata irin ƙara ta zube a wajen sumammiya.
***Zaune ta sameshi a gefen gado ya jingina da jikin fuskar gadon idanunsa a rufe amma ba bacci yake ba, zama tayi gefensa ta kama hannunsa ta riƙe, buɗe runannun idanun nasa ya yi yana kallonta sosai abun ya bata mamaki dan ta daɗe bata ga Ameer cikin irin wannan yanayin ba, cikin sanyin murya ta ce"yallaɓai idan da abin da ke damunka ka sanar damu ko zamu iya maka maganinsa, idan kuma ba zamu iya ba mu tayaka da addu'a amma wannan damuwar bata dace da mai irin Shekarunka ba" da idanu kawai Ameer ya bita ganin hawaye na zuba a idanunta, hannunsa ɗaya ya sanya ya jawota gefensa ya riƙe haɓarta yana kallonta sai kuma ya yi murmushi yana girgiza mata kai da sauri ta shige jikinsa tana fashewa da kuka, shiru Ameer ya yi mata yana jin yanda take kukan. Saida tayi shiru dan kanta sannan ya ɗago fuskarta ya goge mata hawayen cikin kamilalliyar muryarsa ya fara magana
"Zan so a ce kunada damar warwaren matsalata da nafi kowa son na sanar daku, saidai abin da ke cikin raina ya shige tunanin mai tunani. Saboda haka ku tayani da addu'a kawai" kallonsa Shamma tayi sai kuma ta girgiza kanta tana kallonsa ta ce".
# *Imara*
# *Lolo*
# *Joda*
# *Nanameera*
# *Fashion gurl*