BAHIYYA

Chapter 9

by @oumameer2671

💝 *BAHIYYA*💝





*ADABI WRITERS ASSOCIATION*






        *BY*

*AMINA IBRAHIM*

 *(OUM-AMIR)*




*BAHIYYA NOVEL ƊIN KUƊI NE KIBIYA 500 TA WANNAN ASUSUN 3132703269 FIRST BANK AMINA IBRAHIM SAI KI TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAYIN ****





*FREE PAGE*

     *BABI NA TARA*






BAHIYYA 



..................... Tunda Maman Khadijat ta fito ni ke kallon ta. Kallo ne mai cike da abubuwa masu yawa waɗanda suka tsaya min a rai na masu wuyar fassarawa, ban san ma wacen irin kalar ƙauna zance ina yiwa wannan baiwar Allah ba, domin ta yi min abinda har in koma ga Mahalicci na bazan daina gode mata ba. Jin nike bayan Uwar da ta haife ni da Nuhaira babu kuma wani makusanci na kusa da zuciya ta wanda yafi ta. Allahu ya sani daman can ina ƙaunar ta sai gashi kuma yau ta yi min abin alherin da baki ma ba zai iya magantuwa ba wurin gode mata, sai dai in yi ta yi mata addu'ar gamawa da duniya lafiya don bani da wani abinda zan bata wanda yafi wannan. 


“Bahiyya let's go mana, Wai mi kike tunani haka?”


Cewar maman Khadijat ganin na shagala da kallon ta duk inda ta wulga tamkar naga farin wata ɗan goma sha bakwai.


Miƙewa nayi ina mai share guntun hawaye na nace.


“Ba komai maman Khadijaht na gode sosai”


Murmushi kawai tayi ta girgiza kai tare da yin hanyar waje nima na rufa mata baya.

Motar ta muka shiga mai sanyin daɗi, dani da ita duk baya muka shiga yayin da driver ya shiga gidan gaba.


Yana cikin warming ɗin motar sai ga wata rantsatstsiyar motar ta kunno kai cikin gidan a raina ina mamarin ganin wanene wannan da zai fito a cikinta.


Da sauri naji maman Khadijat tace.

“Wait.. Wait Ishaq”


Daga haka ya kashe motar ita kuma ta sauka tana cewa. 


“Bahiyya fito ku gaisa da baban Amed shine ya dawo” 


 Kallo ɗaya na yi masa na gasgata zancen ta domin ba ƙaramin kama suke yi da Ahmad ɗin ba, mutumin ya haɗu ba ƙarya. 


Har wurin motar naje bayan ya fito na duƙa har ƙasa na shiga gaishe sa.

 Cikin ɗaure fuska ya tanka min tamkar wadda akace ta yi masa wani laifin. A raina nace shi kuma kalar tasa fuskar kenan. 


 Komawa na yi daga nesa da su na juya fuska ta su kuma suka ci gaba da magana ƙasa ƙasa. Bayan kusan mintuna goma na ji muryar maman Khadijat tana faɗin. 


“Bahiyya shigo ki jirani ina fitowa yanzu” 


Ba tare da wani tunani ba na bi bayan su na shige farlourn da muke zama zaman yin kitso ina jiranta ita kuma suka shige ciki. 



Ruwa taje ta kawo masa da lemu as usual tace. 


“Ka fara shan ruwa tukun Baban Amed, sai muyi maganar.....” 


Wayar shi ya ajiye a gefensa in da yake zaune ya kalle ta yace. 


“Sweetheart ba wani ruwan da zan sha, ko na sha ruwa ba wata maganar kawai ba zaki biya wannan kuɗin ba fa gaskiya” 


Cike da mamaki ta kalle shi tace. 


“But baban Amed why? This poor girl need help badly, why won't I help her since Ina da yanda zanyi?” 


Girgiza kansa yayi yace

“Rasi, to tell you the truth the money is too much....”


Cikin nuna ɓacin rai tace. 

“But it's my money not yours, I have every right over my wealth...” 


Cikin mamaki yace


“Oh! Is that So? You are telling me that is your money not mine...” 


Sai yanzu ta fahimci katoɓarar da ta aika ta, cikin sigar rarrashi ta zauna a ƙasa tare da dafa ƙafar sa tace. 


“Abdulfatah, na sani cewa ni da abinda duk na mallaka mallakin ka ne, I beg you in the name of God, ka barni in taimakawa mutanen nan dan Allah...” 


Ajiyar zuciya ya sauke ya kalle ta yace. 


“Rasi'atu, ban hana ki taimaka mata ba, but kuɗin ne sunyi yawa Rasi, 10 million fa, Haba! Da Allah bai sa naga text ɗin na yi saurin garzayowa na zo gidan ba da shikenan sai kije ki narka wannan uwar dukiyar ga wasu mutane waɗanda ma ni ban san su ba..”


“Baban Amed idan kai baka san su ba ai ni na san su, kuma manzon Allah (S. A. W) ya faɗamana a cikin hadith ɗinsa mai girma cewa duk wanda ya korewa ɗan uwansa wani baƙin cikin duniya Allah zai kore masa nasa baƙin cikin ranar gobe alƙiyama. So miye a cikin ten million Baban Amed, ni kaina nafi ƙarfin ta balle kai..” 


“Sadaƙallahul Azim! Malama Rasi, ki fahimta, ni fa bance kada ki taimake ta ba, cewa kawai nayi kuɗin yayi yawa and I'm serious about it, zaki iya bata tunda ga 100k har 500k idan kuma ya fi haka to ban amince ba.”


Cikin karyewar zuciya tace. 


“Abdulfatah kasan mi manzon Allah (S. A.W) yace ? ;cewa yayi ko wace irin al'umma tana da kalar ta ta fitinar, amma ni fitinar al'umma ta, itace dukiya. Idan ba fitinar dukiya ba miye a ciki don na biya musu kuɗi? Kafi ƙarfinsu na fi ƙarfinsu, Don mun bayar da 10 million miye a ciki Baban Amed??” 


Miƙewa yayi yace. 


“Mun gama magana Rasi, ban amince ba idan har ni kin yarda mijin ki ne shugaban ki ne” 


Wani irin kuka ne ya kubce mata mai ban takaici da baƙin ciki, wai maza miye suka dauki kan su ne? Shi da yake yin duk abinda ya ga dama da kuɗin sa ta taɓa yi masa shamaki a kai ne? 


Har ya kai ƙofa da sauri ta waiga tace. 


“Baban Amed Kaji tsoron Allah, wannan yarinyar suna da buƙatar taimako, ba wani abin saɓa shari'a ne zan yi ba, ceton rai ne zanyi, Allah ya ga zuciya na da niyyana. Matuƙar muna da rai to jarabawa ba zai taɓa ƙare mana ba kar kayi mamakin hukuncin ubangiji kaima ya zama na ya jarabce ka ta wani hanyar da kake neman wani taimako wanda kai kuma kuɗi basu iya yi maka magani to sai ka yi yaya kenan..?” ko kuma ace Ɗanka Amed ko 'ƴarka Khadijat suna neman wani taimak....” 


Cikin ƙaraji yace. 


“Stop it! Stop it Rasi'at, kada ki tsaya ki nemawa kan ki zunubi akan wani dalilin ki na banza da wofi har yasa ki kai ga ɓatamin raina in yi abinda bai kamata ba. Na ce ban amince ba, ban amince ba! That's final. And pack all your things we are leaving this country tomorrow morning as early as possible” 


Daga haka ya juya ya wuce abin sa ba tare da ya sake bata damar furta ko da kalma ɗaya ba. 


Kuka ta ke sosai tamkar ranta zai fita. Wannan abun sam bai yi mata daɗi ba,Abdulfatah bai kyau ta mata ba, to ta ya ya ma zata iya fuskantar yarinyar nan da wannan mummunar magana? Tace mata mijinta ya hana ta ko ya ya? 

 Bayan ta gama darzar kukan ta mai isar ta ta gama duk wani saƙe saƙen ta taga cewa babu wata mafita dole ta miƙe jiki a saɓule ta fito zuciyarta na wani irin tuƙuƙi tamkar an ɗora ta akan tuƙubar tsire. 


Tana shiga farlourn ta suka yi ido biyu da Hanifah. Take taji wani sabon kuka ya ƙwace mata, da gudu taje ta yi hugging ɗinta murya a raunane tace. 


“Hanifah why is men like this? Su Idan suna son abu babu mai hanasu sai amma idan kai ne ka ke son abu kai da abun ka su nuna maka fin ƙarfi” 


Cikin rashin Fahimta Hanifah tace. 


“Me I don't understand you, can you made your self clear please?” 


Zaunawa tayi ta gaya mata komai da ya wakana tsakanin ta da Bahiyya da kuma irin rashin mutuncin da Baban Amed ya gurza mata. Ƙarshe tace. 


“Kin ma san wani abun takaici Hanifah? I'm 6weeks pregnant, cikin ɗoki yace min dole zai zaɓi wata ƙasar mai daɗi muje muyi renon cikin a can har na haife sai mu dawo na ce masa ban amince ba ya bari dai idan cikin ya kai term sai mu tafi,shine yace ya amince amma idan muka tafi sai babyn ya kai 2years zamu dawo nace na amince nima, a haka muka tsaya amma wai shine don yayimin baƙin ciki wai yanzu yake faɗamin in shirya gobe zamu bar ƙasar.” 


Cikin Mamaki Hanifah tace. 


“Ke ma dai Rasi kina bani mamaki wallahi yadda kike iya tolerating nonsense ɗin namiji, kuɗin sa ne? In da ace kuɗin sa ne don ya hana ba matsala ba ne...” 


Wani murmushin takaici Rasi ta saki wanda yafi kuka ciwo tana girgiza kai tace. 


“Hmm! Up to now you don't know men Hanifah, but bet me, one day one time sai namiji ya gurza miki watarana I promise you this, a lokacin zaki gane cewa maza maza ne kuma ba zaki iya yin komai ba a wannan lokacin, shiyasa nike gayamiki kiyi amfani da damar ki tun kina da lokacin ki” 


Dariya ce ta suɓucewa Hanifah tace. 


“Rasi, for get about it because wannan ranar ma ba zai taɓa zuwa ba” 


“Hanifah bazan kira ki da yarinya ba, 8years in marriage kin wuce a ce baki san minene aure ba. while I don't blame you Saboda ba rayuwar auren tsantsa kike practicing ba daga ke har mijin ki baku san ma daɗin auren ba. But idan kika shirya rayuwar auren ta gaske watarana zaki ce na faɗa miki haka” 


Taɓe baki Hanifah tayi tace. 


“Rasi! yanzu dai duk abinda kike so nima shi nike so, tunda har Abdulfatah ya katangeki daga taimakon wannan yarinyar, me I will do that Ko don na kare miki mutuncin ki daga idon ta” 


Cikin tsantsar farin ciki Maman Khadijat tace. 


“Thank you, thank you Hanifah, wallahi ban san taya ya zan iya gode miki ba, thank you so much” 


“Mention not Rasi, kinfi haka a wurina, tunda kin ƙi ki kore ta ya na iya, dole in so abinda kike so” 


Rungume ta tayi tace. 

"Naji dai, thank you matar Farooq.... Oya! Tashi muje bana so a tsaya wani jinkiri kuma kada wani abu yazo ya biyo baya” 



***************



BAHIYYA 



Tun ina zaune har sai da na kai ga gincirawa ba tare da na kawo komai a raina ba na zauna zaman jiranta, tunda har mijinta ne dole na san zata tsaya sai ta gama da shi sannan tayi ta tawa. To kuma ina nan zaune sai naga Ƙawarta ta shigo, hakan yasa na ƙara gyara zama domin na san dole itama sai ta bata time ɗin ta kafin ni. 


Ganin har lokacin sallar Asr yayi yasa na miƙe naje na ɗoro alwala na zo na gabatar da sallah. Ina zaune Ina addu'a suka shigo tare da ƙawar ta ta. 


Gaishe su na ƙara yi tare da baza kunne ina jira in ji tace na tashi mu tafi,sai dai ganin sun samu wuri sun zauna yasa ni jin wani abu ya ɗan ɗarsu a zuciyata. 


“Bahiyya!” 


Ɗagowa nayi na kalli Maman Khadijat nace 


“Na'am” 


“Tun ɗazu ina ciki da Baban Amed banki na yaƙi ya fitar da wannan kuɗin mai yawa, nayi ta gwadawa yaƙi bayar da haɗin kai shi yasa kika ga na jima ban fito ba, amma Alhamdulillah! Ga Ƙawata nan Hanifah in sha Allahu zaku tafi tare ita ce zata biya kuɗin babu wata matsala” 


Rusunawa nayi inata gode musu wanda har sai dai Maman Khadijat taji tausayi na ya ƙara sarƙafe mata zuciya. A hankali tace. 


“Bahiyya ba buƙatar duk wannan please, fatanmu dai shine Allah ya bata lafiya....” Sai kuma tayi murmushi tace. 

“Bahiyya kin san ɗan Adam da kuɗi, tunda kuɗin nan yaƙi fita a banki na naji Zazzaɓi yazo ya kamani lokaci guda, bana jin daɗi jikina a yanzu ba zan iya fita ba, saboda haka kice ina gaida maman ku kinji ko, Allah yasa ayi cikin nasara. Tashi kuje” 


Duk da cewa ban san abinda ke faruwa ba, wani irin abu naji mai sanyi ya mamaye zuciyata da gudu naje na ƙanƙame maman Khadijat ina ta rusa kuka tare da sakin sabbatunda ni kai na ban san mi nake cewa ba. 


Daga haka muka tashi muka tafi a motar wadda ta kira da Hanifah. 

Har muka isa asibitin ni da ita babu wanda yayi magana kowa da irin abinda ya ke saƙawa a cikin ransa. 

 

Bayan mun isa bakin asibitin na miƙa hannu da nufin buɗe motar tace min. 


“Dakata, akwai maganar da nike so muyi da ke..............” 














           *OUM AMEER*