018
*BAYA DA ƘURA.*
Fitattubiyar2025
©️Nana Haleema.
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11
*BOOK 1*
*Page 018.*
Da safe Mubeena da wuri ta shirya ta taho zuwa gida, lokacin da ta shiga gidan Mama da Manal suna zaune kamar ko yaushe suna cin abinci a kwano ɗaya da alama sai lokacin suke karyawa. Yatsine fuska tayi ganin tuwo ma suke ci abinda ta tsana gabaɗaya a duniya, ta ƙarasa da sallama Mama na jin maganar ta taji hankalin ta kwanta amma bata nuna ba har ta ƙaraso ta zauna tcae,
"Mama ina kwana, ya jikin ki?. Naje asibitin lokacin kina kwance kina bacci gashi muna da jarabawa a makaranta shiyasa ban dawo ba." Mama kamar tana kallon ta tace, "ki dinga jin tsoron Allah Nusaiba, ba haka mahaifiyata take ba, a ko yaushe in na tuna sunan ta kika ci ina dana sanin saka miki sunan ta a rayuwata." Mubeena ya zauna tana zunburo baki tace, "Mama nace makaranta naje fa, kuma me nake yi don Allah?."
Mama tace, "babu abinda kike yi Mubeena, komai kike yi daidai ne." Ta kalli Manal da take kallon ta itama ta zabga mata harara Manal ta taɓe baki bata ce komai ba.
Baba ne ya shigo ya shirya da alamun tafiya wajan nema ganin Mubeena sai yace, "A'a Mubeena."
"Na'am Baba, Ina kwana" ta faɗa tana gaishe shi ya amsa yana faɗin, "ina kika shiga?."
"Baba makaranta ce fa ta ɓoye ni, kuma ina nan zoo road gidan su Bilkisu ƙawata a can nake kwana saboda tare muke karatu." Baba yace, "Allah ya taimaka, zo ina son ganin ki" ya faɗa yana yin cikin gidan ta tashi rai a ɓace ta bishi ta zauna yace,
"Mubeena shi wannan rawar kan da kika saka a gaba ba komai zai amfana miki a rayuwa ba face dana sani, mu da kike rainawa kina ganin baki dace ace iyaye ki bane saboda kina da kyau mune gatan ki yanzu da nan gaba. Ɓacın ran da kike sakawa mahaifiyar ki kema ganin ki shine burgew?kin san da ɓacin ranki a ciwon zuciyar babar ki? Kin sani?."
Mubeena tayi shiru batayi magana ba yace, "Ki bi duniya a sannu, shi kuɗi da kike gani ba komai bane face takardar, ba kowa Allah yake bawa ikon amfanar ba sai wanda y zaɓa. In kina ganin mahaifiyar ki bata dace dake ba saboda tana da lalaurar ido da kuma tana aurena saboda bani da kuɗi kuma sannan itama bata da kuɗi kin yi kuskure, baki san wacece mahaifiyar ki ba, in zancen kuɗi ake kafin a lisaafo wanda kike bi saboda kuɗi za'a lissafa ta a jerin su. Koda yake ke ba wannan lissafin kike ba, baza kuma ki gane inda na nufi a yanzu ba wataƙika sai nan gaba. Abinda nake so dake Mubeena ki nutsu kiyi hankali ki tabbatar da abinda kike aikawa ba burge bace ko kuma darajar ki bane, babu inda wannan hali zai kai sai tashar dana sani."
Mubeena bata ce komai ba tayi shiru ya miƙe yace, "nasiha nake miki matsayin uba a wajan ki, in kin ɗauka Mubeena ke zata amfana, in baki ɗ'auka ba shima ke zata cuta. Allah yana gani ina iya bakin ƙoƙarina wajan na miki tarbiyya mai kyau, na barwa Allah lamarin ki ina kuma faɗa masa kullum. Ki sani haƙƙin mahaifiyar ki ba zai bar ki ki zauna lafiya ba, ba kuma zai bari ki samu abinda ki ke so ba. In ma yawo ki ka fara ki sani kafin ke anyi irin ki dubu, babu wacce tayi riba a yawon banza, a ƙarshe da ciwo suke ƙarasa rayuwar su a wulaƙance" ya faɗa yana fita. Baki ta turo bayan ya fita ta fito tsakar gidan ta zauna tana kallon su kamar basu san tana wajan ba saboda babu wanda ya tanka mata.
"Assalamu alaikum" aka faɗa ana shigowa duk suka juya a tare ita da Mubeena. Manal ganin wanda ya shigo sai tayi dariya tace, "Laaa Yaya Harun." Dariya yayi shima ya ƙaraso yace, "Manal." Mama jin muryar haruna sai tayi murmushi tace, "Mutanen ƙasar Riyad ne a tafe kenan." Yayi dariya ya zauna kusa da Mama yace, "mu ne wallahi Mama, ina kwana."
"Lafiya lau Haron, saukar yaushe?."
"Ɗazu da safe nazo, ashe bBaba bai faɗa miki ba."
"Ya sha'afa. Ya hanya?."
"Alhamdulillah Mama, ya ƙarfin jikin? Baba yace jiya kika dawo gida daga asibiti."
Mama tace, "Da sauƙi Haruna, naji sauƙi sosai."
"Allah ya ƙara Lafiya" ta amsa da amin ya kalli Manal yace, "nifa fushi nake dake ko kiran wayar nan ma bakya yi ki nemi." Tayi dariya tace, "wayar tawa ce sai a hankali Yaya, ba wani damuna tayi ba ko datar na saka na shiga na kalli video abinci na kashe shine aikina."
"Daman ke ai babbar mai dafa mana abinci ce." Sukayi dariya a tare ya kalli Mubeena da bata ma san ya shigo ba kamar zai mata magana sai ya share ta ganin ta kawar da kanta gefe.
Ji tayi yana kallon ta a jikin ta sai tace, "Sannu da zuwa" ya amsa bai kalle ta ba ya saka hannu aljihu ya ɗauko waya ya miƙawa Manal yace, "ga waya na tawo miki da ita a cigaba da kallon abinci, shiyasa na bayar a gaban Mama nasan zaki ce Mama baza ta bari ba" ya faɗa yana kwaikwayon muryar ta sai sukayi dariya har Maman.
Mama tace, "Haruna harda hidima haka? Waccan wayar ma kai ne ka bata fa."
"Babu komai Mama, Manal ai ƙanwata ce da nake ji da ita." Manal ta karɓi wayar tana duba ta cikin murna tana kallon jikin wayar, baƙa ce ta gabaɗayan baya an saka Samsung S10.
"Na gode sosai Yaya,Allah ya saka da alkhairi ya kai mu bikin ka mu sha biki." Yayi dariya yace, "Amin Manalin Mama, sannan duk sanda datar ki ya ƙare ki faɗa min zan saka miki ki cigaba da kallon abinci, dan so nake ki iya sosai nan gaba ki zama shararriya a duniya."
"To Allah ya biye bakin ka Yaya."
"Amin ƙanwa, zan saka a duba makarantar koyar da girki ma ki fara shiga tun yanzu. Akwai wacce na biiya miki online ma wajan wata Leemars_Delicious, ta iya girki ina ganin ta a Ig shiyasa da naga zatayi online classes sai na tura mata kuɗin, zata saka ki a group ki koya da kyau ƙanwata."
Mama tace, "A'a Haroun kar hidimar tayi yawa kuma."
"Haba Mama, Manal da ƙanwata ce dan nayi mata ai ba komai bane." Mama tace, "haka ne, Allah ya saka da alkhairi." Ya amsa da amin.
Wayar Mubeena aka kira ta ɗauka wayar ta duba ganin mai kiran sai bata ɗauka ba, hanyar fecewa kawai take so ta samu amma babu dama.
Haroun ne ya kalli wayar hannun ta amma sai bai yi magana ba fa tashi ta shiga falo shi kuma yau sallama ya fita.
Haka ta kai bayan azahar a gidan gabaɗaya a takura take gashi tana ta kiran Baby bai ɗauka ba duk ya damu. Sai da akayi sallar la'asar sannan taga message ɗin sa an saka, _Sorry baby, kina ta jira na ko? Na dawo ina gida a kwance bana jin daɗi sosai Baby. Kizo ki ganni._ hankalin ta ya tashi sosai ta kira shi a lokacin ya ɗauka tace, "Baby me yake damun ka?." Murya can ƙasa yace, "Zazzaɓi ne Baby, gashi ina gida ni kaɗai ko abinci bansamu naci ba."
"To baby ka saka ayi maka take away mana."
"Babu kowa Baby, ban san ya zanyi ba ji nake kamar zan mutu."
Cikin tashin hankali tace, "to yanzu ya za'a yi?."
"Ki zo ki ganni Baby, ganin ki kawai zai saka naji daɗii." Shiru tayi bata amsa ba yace, "amma in baza ki iya zuwa ba ki damu babu komai." Mubeena tace, "A'a zan zo, sai dai bazan jima sosai ba kaga yamma tayi."
"Okay Baby, gashi babu kowa balle ma turo a ɗauke ki. Bara na kira driver na duk inda yake yazo ya ɗauko min ke." Ta amsa da to ta kashe wayar tana tunanin ta wacce hanya zata bar gidan su.
Mubeena da ta fito daga ɗaki ta ga Mama ita kaɗai zaune da alama Manal gidan su Surayya sai tace, "Mama an yi mana kiran gaggawa daga makaranta zanje na dawo." Mama tayi tsaki tace, "tambaya ta kike daman in zaki fita Mubeena? Wacece ni da zaki nemi izinina?."
Mubeena tace, "Mama kiyi haƙuri in dan na kwana a gidan su ƙawata ne kike fushi dani." Mama bata ce komai ba tayi mata banza Mubeena tasan bazata cs komai ba hakan ya saka tace, "Mama zanje na dawo yanzu" tana faɗa ta fice bata ma jira mai Maman zata ce dan driver ya fara yimata waya.
Tana fita ta ɗauki wayar ta sakaa kunne tana yin titi da sauri. A lokacin Manal da Haruon suna tsaye suna kallon ta yace, "Manal waye ya bawa Mubeena wannan wayar ta hanun ta?." Manal tace, "Wallahi ban ma kula da wayar hannun ta ba." Haroun ya girgiza kai yace, "babar waya ce sosai fa, a hannun yaran masu kuɗi ma bata da yawa saboda bata jima da fitowa ba, kuɗin ta yayi miliyan uku da wani abun wallahi."
Gaban Manal ya faɗi tace, "Yaya miliyan fa? A ina Yaya ta samo ta? Ko dai sata tayi ko kuma ta ƙawar ta Bily ce?." Ya girgiza kai yace, "bama ce ba, amma zan faɗawa Baba maganar dan wannan ba abinda za'a bari bane, shi ya tambaye ta a ina ta samu wayar." Manal cikin tsoro tace, "ni na fara jin tsoro."
"Kar ki damu, kar ki sanar da Mama wannan ki bari na faɗawa Baba." Jiki a sanyaye ta amsa yace, "jeki gida na tsayar dake" ta amsa da to ta juya ta tafi tana tunanin waye ya bawa Mubeena wayar fin naira miliyan 3?.
Bebi kuwa ranar bai samu ya fita da wuri ba dan daren jiya sai dare ya dawo gida saboda theater da suka yi a babban asibitin Murtala. Bayan ya tashi daga Murtala asibitin su ya wuce, yana shiga kawai sai Manal ta faɗo masa a zuciya musamman inda take tsaye tana yi masa murmushi a lokacin da ransa yake ɓace bai tsaya ya saurare ta ba ya wuce.
Numfashi ya sauke yana inda yake tsaye yace, "gabaɗaya taƙi barin tunanina."
"Wacece taƙi barin tunanin maka?" Hamza ya faɗa yana kallon sa ya juya ya kalle shi yace, "har ka fito kenan?."
"Mun fito, sai yanzu ka shigo?."
"Uhum, na jima a can ne kuma kasan jiya muna team work shiyasa ban samu ma na fita da wuri ba."
"Wacce taƙi barin tunanin naka naji kana maganar? Kodai an samu madadin Rumana ne?." Bebi ya girgiza kai yace, "bana ce ba, haka kawai na kasa mantawa da ita musamman....." sai kuma yayi shiru yace, "forget it kawai. Ina Huzaifa?."
Huzaifa da yake tunkaro wajan yace, "gani, da labari ne?." Hamza yace, "akwai labari, da alama wata ta kama zuciyar Bebi fa." Huzaifa yace, "haba don Allah, da gaske?."
"Wallahi da gaske, shi kaɗai naji yana zancen ya kasa mantawa da ita kuma shima ya faɗa min."
Huzaifa yayi dariya yace, "Wacece wannan Bebi?." Kallon Huzaifa yayi kafin yayi magana ya riga shi yace, "kamata yayi kayi hanzarin ko wacece a yi a wuce wajan saboda damuwar Rumana." Bebi yace, "nifa bance son ta nake ba, kawai dai na kasa mantawa da ita ne, nasan kuma saboda abinda nayi mata ne bayan wannan babu komai" ya faɗa yana barin wajan ya ƙarasa inda office ɗin sa yake ya shiga duk suka biyo bayan sa.
Bebi ya kalle su yace, "ina da wanda zasu zo nan fa meye na biyo ni?."
"Sanar damu zaka yi wacce wannan ta kamo zuciyar ka haka?." Bebi yace, "ku bari na tabbatar sai na faɗa muku amma yanzu ban tabbatar ba." Buɗe ƙofar akayi aka shigo da takardu Bebi yace, "kun gani ko? Patients ɗina sun zo sai anjima" ya faɗa yana karɓa ya zauna suka fita ya fara duba mutane.
Sai bayan ya kammala sannan yayi shiru yana tunani zuciyar sa na bugawa a hankali da ya rufe ido fuskar Manal yake gani musamman ranar da ta saka black hijab tana dariya. Numfashi ya fesar daga bakin sa yace, "wai me hakan yake nufi ne? Daga ɗan sabawa da ganin ta sai na fara tunanin ta? Meyasa na kasa mantawa ne?."
Glasses ɗin idon sa ya cire ya ajjiye amma bai daina jin wannan bugun zuciyar ba yayi shiru ya zubawa waje ɗaya ido yana kallon inda ta zauna ya saka mata magani a ƙafar ta.
"Oh my god!" Ya furta a hankali ya rasa ma tunanin da zaiyi yaji daɗi.
A cikin asibitin yayi sallar magriba ya tashi ya buɗe window yana kallon masu shigowa da fita iska na shigowa kaɗan da khamshin ganyayyaki. "To wai har magana sau nawa muka yi ne da zan saba da ita haka? Adnan me kake yi ne?" Ya faɗa yana sake kulle ido ya buɗe sai ya kulle window ɗin ya ɗauki key na mota ya fito ya shiga ya tafi gida.
**** Mubeena tayi mugun tsorata tana zaune tana kuka da shima yana kusa da ita yace, "Haba Baby, meye na wannan damuwar haka? Kawai hug ne da kiss ba wani abun kika yi ba, kuma gashi kin taimaka min na samu Lafiya amma meye na shiga damuwa haka?."
Mubeena tsoron ta ya riga ya gama bayyana ƙ'arara tace, "Ba abinda kace zanyi ba kenan, ni dai gaskiya banji daɗin hakan ba, bamu yi hakan da kai ba.
"Nima ban san hakan zata faru ba ai Baby, shauƙin son ki ne ya warkar min da rashin Lafiya, da kuma murnar maganin ki kusa dani shine har hakan ya faru. Amma babu komai kar ki damu, baza'a saka ba wannan ɗin ma kuskure ne."
Mubeena jikin ta gabaɗaya ya gama yin sanyi ta kalli danƙwalin ta da yake gefe da mayafin da ta sako yace, "muje kiyi wanka ko?." Ta girgiza kai tace, "A'a sai naje gida."
"Kiyi a nan, in kika bari sai a gida za'a ce wankan me kika yi kina dawowa daga unguwa, nan yafi kwanciyar hankali tashi muje" ya faɗa yana riƙo hannun ta suka ƙarasa inda banɗaki yake yace, "ki shiga kiyi wanka da kin fito sai a kai ki."
Kai ta daga ta shiga ciki yayi murmushi bayan ta shiga yana shafa fuskar sa a bayyane yace, "Yarinyar nan tayi, laushi jikin ta kamar mage, ga wani daddaɗan khamshi da take yi, zaƙin bakin ta kuwa kamar alawa. Wow komai yaji akwai halitta kam a tare da ita, Ta ya zan bari wannan ta kubce min?" Ya faɗa yana murmushi tuna yanayin da ya shiga ina kuma ga anyi mai gabaɗaya.
Yana zaune ta fito kamar ma bata yi komai ba dan ta mayar da kayan ta tun a banɗakin ya kalle ta yayi dariya yace, "muje a sauke ki."
Ya ƙaaraso kusa da ita ya riƙe kafaɗunta yace, "bana son wannan damuwar da nake gani a fuskar ki, Haba mana Baby ba fa wani abin muka aikata ba na faɗa miki, da nayi miki wani abun da yanzu kin ji a jikin ki kema. Ki kwantar da hankalin ki wannan ma soyayya ce ba laifi bane dan kin nuna min yadda kike shauƙin sona. Kefa wayayyiya ce Baby ban ɗauka wannan zai dame ki ba, ina ganin ki big girl ya kike so ki mayar da kan ki baya?."
Mubeena tace, "Nidai bana so kawai, kar a sake maimaitawa."
"An gama ranki ya daɗe" ya faɗa yana mata jinjina suka fito tare ya saka a kaita har gida shi kuma yana jin farin ciki sosai a zuciyar sa. Sai bayan ta tafi sannan ya hau mota shima ya nufi gidan iyalan sa, yana fakawa kai tsaye ɓangaren sa ya wuce bai nemi ko wacce a cikin su ba har garin Allah ya waye.
Bebi da wuri ya tashi ya yi wanka ya fito zuwa ɓangaren Mama bai ma san Abba ya dawo ba sai a lokacin yaga motar sa ya shiga wajan Mama yana cewa, "Mummy yaushe Abba ya dawo?." Mama da take zaune ta kalle shi tace, "au ya dawo?."
"Yanzu naga motar sa a ajjiye."
"Ban ma sani ba" ta faɗa ban tare da ta kalle shi ba.
Ya zauna ta kalle shi tace, "Ka tashi ka ɗauko abinda zaka ci babu mai yi maka jeka ka dawo bacci suke yau." Yayi dariya kaɗan baice komai ba Mama tace, "Murmushi yana yi maka kyau Adnan amma gaba kake yi dashi, kai kullum fuska a haɗe kamar mala'ikan mutuwa. Shiyasa ake fassara ka a mutum mara kirki, dariyar ma sai ka saba da mutum ka ke yi."
Yayi dariya yace, "to Mummy kawai sai na dinga dariya kamar wani mara hankali?."
"Lallai, mu da mu ke yi duk bamu da hankalin kenan ko?." Ya wara ido yacec "Ni na isa?."
"Sak Alhajin mu kayi, shima bashi da fara'a sai kun saba zaka ga dariyar sa, amma in baku saba ba kallo ɗaya zaka ce bashi da kiri. Allah ya jiƙan sa." Ya amsa da amin.
Tashi yayi ya shiga kitchen ɗin sai gashi ya fito da kofi a hannun sa yace, "Mummy ashe anyi min kunu."
"Eh gashi nan nayi karanbani nayi maka, Allah yasa kar a sake bani kunya ace babu daɗi." Ya zauna yana dariya yace, "ai yayi daɗi matuƙa." Tayi dariya bata ce komai ba shi kam kallon ta yake gabaɗaya tausayi suke bashi saboda halin da mijin su ya saka su a ciki.
Mama ta katse masa tunani tace, "Da alama Mimi saurayin nan mata dai yayi mata Bebi." Yace, "na tura shi wajan Yaya ni maganar ya bar hannun kuma ai." Mama tayi shiru kafin tace, "ya zancen Lubna ɗin?." Yace, "na sanar da Yaya komai akan waye wanda take so ɗin ya tabbatar da bazai bari ta aure shi ba."
Mama tace, "Bebi kana da saurin fushi amma na rasa meyasa ka kasa fushi akan lamarin su Lubna." Yace, "Mummy ai ba dan su nake yi bane shiyasa" ya faɗa yan ajjiye kofin ya tashi yace, "zan tafi Mummy."
"Shikenan har ka ƙoshi?."
"Eh, in naje zanci abinci."
"To sai ka dawo, kofin an barni na ɗauke ko?." Ɗaukar kofin yayi yace, "Tuba nake." Ta Harare shi tace, "yau ka saba?, a ɗauko maka kuma a ɗauke maka, dan gata. Shiyasa in na tura ɗakin ka plate ɗin da na manta dashi ma zan ganshi." yana ji murmushi yayi kawai ya fita daga falon. Wajan Abba ya shiga amma bai ji motsin sa falon ba hakan ya saka shi fitowa ya hau mota ya tafi.