019
*BAYA DA ƘURA.*
Fitattubiyar2025
©️Nana Haleema.
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11
*BOOK 1*
*Page 019*
Mubeena haka ta kwana a gida gabaɗaya babu walwala, Manal na lura da ita ta share ta kawai dan haushin ta take ji sosai. Sai da safe Baba ya shigo sun gaisa ya kalle ta tana zaune da wayar a hannun ta yace, "Mubeena zo ɗakina ki same ni yanzun nan." Haushi taji a zuciyar ta tana tunanin yanzu to me kuma tayi, haka ta tashi rai ɓace ta shiga inda ya shiga, ba tsammani taji ya karɓi wayar hannun ta gaban ta ya faɗi sosai yace, "a ina kika samu kuɗin wannan wayar? Waye ya siya miki ita?."
Mubeena ta fara kame-kame cikin rashin gaskiya tace, "ba tawa bace, ta ƙawata Bily ce ta ara min." Yadda take maganar kana ji kasan ƙarya take yi ya girgiza ki ya saka ta a aljihu tace, "to shikenan kice mata tazo ta karɓa a wajena tunda ba taki bace ba, sannan daga yau ɗin nan kar ki sake fita baki tambaye ni ba, duk inda zaki koda bana nan ki faɗawa Manal ta baki waya ki kira ni. Ko makarantar ce kar ki sake zuwa sai na sani.”
Mubeena tayi shiru bata ce komai ba Bab yace, "kin ɓata wayon ki indai wannan hanyar da kika ɗauka kike ganin itace daidai da rayuwar ki Mubeena, zaki yi dan sani a lokacin da baza tayi miki amfanin komai ba." Mubeena tace, "wallahi ni babu abinda nayi Baba."
"Waye ya sauke ki jiya da magariba a mota?." Gaban ta ya faɗi sosai tayi shiru, ya sakar mata tsawar da sai da ta firgita ta kusa faɗuwa daga zaune yace, "tambayar ki nake waye ya sauke ki a mota jiya?” Ya faɗa da tsawar da bai taɓa yi mata irin ta ba.
Tace, "Drivern gidan su ƙawata ne." Baba yace, "ƙarya kike wallahi, ki cigaba da abinda ki ke yi, ke a ganin ki hakan shine wayewa ko? Hmmm Mubeena zaki dana sani indai wannan banzar rayuwar kika zaɓarwa kan ki, kin ga ina bin ki ta lallami shine kike abinda kike so kina ganin babu mai hana ki ko?, daga yau mun saka ƙafar wando ɗaya dake, zamu ga waye mai nasara ni ko ke.” ya faɗa yana tashi ya fita ta bishi da kallo babban tashin hankalin ta itace wayar ta.
Yana fitowa tsakar gidan yaga Mama a zaune da alama taji komai tace, "Wayar mai tsada ce a hannun ta ko Baban Manal? Sannan jiya waye sauke ta a mota?. Ai shikenan Mubeena sai ta kashe ni zata huta."
Baba bai so taji ba yace, "Kar ki saka wannan a zuciyar ki, ta tabbatar min da motar gidan su ƙawar tace na kuma amince da haka, wayar ma ba ta ta bace ta ƙawar tace." Mama tayi murmushi tace, "Ko Manal baza ta amince da abinda kace ba balle ni Baban Manal, ni fa na haife ta. Shikenan ai duk wanda yayi daidai ya sani, wanda bai yi daidai bama ya sani."
Baba yace, "bance ki saka wannan abin a zuciyar ki ba, addu’a zaki mata itace maganin komai." Mama bata ce komai ba Baba ya kalli Manal yace, "ki kula da ita kin ji."
Ta ɗaha kai alamun to har ta fara kuka ya fita. Mubeena ta wuce zuwa ɗakin jiki a sanyaye Manal ta tashi tabi bayan ta tana shiga tace, "in wani abun ya samu Mama ta dalilin ki Allah ya isa ban yafe miki ba Yaya, sannan har abada kar ki tuna ni matsayin ƴar uwar ki daga ranar bazan sake kallon ki matsayin jinina ba, daga ranar bazan sake miki kallon ƴar uwata ba wallahi. Babu ni babu ke kamar yadda kika ɗauki hakan a yanzu. ke bakya son mahaifiyar mu ni ina sonta, in ke kin raina ta ni ina girmama ta, in ke kunya kike ji ace itace ta haife ki ni alfahari nake na nuna ta matsayin wacce ta haife ni.”
Mubeena da take kallon ta tace, "ni kike faɗawa wannan maganar?."
"An faɗa miki, in kinga dama ki dake ni kuma wallahi sai na rama. Meye a duniyar in baka girmama mahaifiyar ka ba? Me zaka tsinka a cikin ta in baka yi biyayya ga iyayen ka ba?, Ke a ganin ki wannan wayewa ce ai ko? To kije ki tayi Allah ya bada nasara. Amma ki tuna daga lokacin da kika saka wani abun ya same ta babu ni babu ke” tana faɗa mata ta fita ta barta a tsaye. Taji kunya sossi amma wayar ta kawai take ji domin ko wanne lokaci za'a iya yi mata waya.
Haka Manal ta wuni kusa da Mama, duk da Maman tayi shiru bata cewa komai kai da ka ganta kasan tana cikin damuwa sosai amma bata nunawa.
Kwanan Mubeena biyu bata fita ba saboda babu fuska wajan Mama gashi Baba ya saka mata ido ko ya ta motsa yana kallon ta ko kuma ya saka ana kallon ta gabaɗaya ta damu zaman gidan ya ishe ta sosai.
Ranar laraba a safiyar Mama na zaune suna hira da Manal kamar yadda suka saba tace, "Manal kin ji yadda nake jin idona ya ɗaure ya daina wallahi, a hankali nake ji yana saki, da alama dai abinda likitan nan ya faɗa zai tabbata." Manal cikin farin ciki tace, "Da gaske Mama?.”
“Da gaske mana.”
“Allah ya tabbatar Mama." Mubeena tazo ta zauna a kan tabarmar da suke tace, "Mama zanje makaranta na dawo."
Mama tayi mata banza kamar bata ji me take cewa ba tace, "kiyi haƙuri ni duk abinda ake zargina a kai ba haka bane ba wallahi.” Mama tace, "in ma haka ne Mubeena rayuwar ki ce ba tawa ba, Dana sani ke zata bibiya ai bani ba domin kowa yayi daidai ya sani. Tashi ki bani waje ai ba tambaya ta kike ba in zaki fita." Mubeena tayi shiru ta kalli Manal da ba ita take kallo ba sai ta tashi ta fita.
Mama ta girgiza kai tace, "Mubeena hmmm!." Abinda tace kenan bata sake magana ba Manal ma bata dawo da zancen ba ta ɗaukewa Mam hankali da hira dan ta kawar da batun Mubeena.
A cikin kwana biyun Bebi ya tabbatar da son Manal yake so na gaske ba na wasa ba, duk yadda yaso ƙaryata zuciyar sa ta dage akan hakan domin duk wata alama ta soyayya ta gama shiga zuciyar sa ta kuma bayyana a ganganar jikin sa.
Kewar ta yake ji sosai, burin sa ya ganta amma ya rasa ta wacce hanya zai bi hakan ta kasance. Ranar bai ma fita ba yana gida tunani yayi masa yawa akan Manal, da ya kulle ido ita yake gani zuciyar sa na harbawa sosai alamun soyayyar da yake mata mai ƙarfin gaske ce. Duk ya damu, tunanin kar yaje an mata miji gashi soyayya ta gama kama shi, hakan ya hana shi nutsuwa gabaɗaya shine dalilin da ya hana shi fita.
Yana zaune yana wannan tunani Huzaifa ya kira shi ya ɗauka Huzaifa yace, "Bebi baza ka fito bane har rana tayi?." Bebi ya sauke numfashi yace, "gaskiya ba zan shigo ba sai zuwa yamma."
"Amma akwai mutanen da suke jiran ka, akwai wanda aka kawo ma yanzu kuma matsalar zuciya ne. Da zaka daure da kazo ɗin ka san David da Yasir suna off.” Ajiyar zuciya yayi yace, "gani nan" ya faɗa yana yanke wayar ya tashi daga inda yake ya saka kaya ya fito.
Ganin motar Abba tana nan sai ya shiga wajan sa ya same shi a zaune da alama bai san ya shigo ba duk da yayi sallama, Abban yana zaune yana magana shi kaɗai yana cewa, "Wai me yake damun wayar yarinyar nan ne? Kwana biyu a kashe Allah yasa ba fushi tayi ba."
Girgiza kai yayi domin kuwa ya fara tabbatar da Abban su yana harka da ƴan mata a waje, duk da bai san alaƙar su ba amma a yadda ya damu hakan ya nuna ya damu da yarinyar sosai.
"Asslaamu alaikum". Bebi ya sake faɗa yana kallon sa, sai a sannan ya juya ya ajjiye wayar yace, "Wa'alaika salam, Bebi yau ba'a fita ba?."
Ya ƙarasa ya zauna a ƙasa yace, "barka da rana."
"Barka dai, ya aiki?."
"Alhamdulillah. Yanzu zan fita sai naga motar ka na shigo mu gaisa."
"Ka kyauta sosai, Allah ya taimaka." Ya sauke numfashi sannan yace, "Amin" ya miƙe yace, "a tashi lafiya" ya faɗa yana fita.
Yana fitowa compound na gidan Lubna na shigowa, haka nan bai amince da ita ba duk da hankalin sa ya kwanta kwana biyu baya ganin Kamal baya ganin Mujahid amma yanayin yadda take murmushi ita kaɗai kamar bata da gaskiya.
Ganin yana kallon ta sai ta tsargu ta ƙaraso inda yake tace, "ina wuni."
"Daga ina kike?."
"Mamy ce ta aike ni?."
"Shine sai ki fita ke kaɗai?." Lubna tace, "ita tace naje." Baice komai ba ya wuce ta bishi da harara ta wuce ɓangaren su itama.
Yana shiga wajan Mama bata falo ya wuce ɗaki ta ya samu tana ɗaura ɗankwali ya zauna tace, "kace min yau babu inda zaka je gashi naga ka shirya." Bebi yace, "ana nema na ne a asibiti shiyasa zan tafi." Ya sake kallon ta yace, "Mummy Abba ya dawo." Mama tace, "na sani, sai me?."
"Mummy gaskiya a rashin zaman da Abba baya yi a gida nan wallahi da saka hannun ku ciki." Mama ta kalle shi tace, "Bebi akwai abinda baza ka gane bane shiyasa, mahaifi ne a wajan ka shiyasa bana son buɗe bakina a gaban ka, amma in kana yi min irin haka wata ran zan faɗi kalmar da zaka kwana baka manta ba."
Bebi yace, "shikenan yanzu haka za'a zauna kenan? Kamar ba mijin ku ba don Allah?." Mama bata ce komai ba sai ta canja maganar tace, "da alama dai wannan yaron saurayin Mimi shine mijin ta, dan Yayan ku yace yaje ya samu Daddyn ku a kan maganar da." Bebi ya gigita kai yace, "Allah ya tabbatar da alkhairi." Ta amsa da amin ya miƙe yace, "sauri nake Mummy sai na dawo."
"Allah ya kiyaye, dole ka gudu ai saboda kar nayi zancen Rumana, daɗin ta a nan zan kwana ai." Baice komai ba ya wuce dan kuwa haka ɗin ne, yanzu zata masa zancen yaje ya samu Yayan mahaifin sa da suke kira Daddy da maganar Rumana shi kuma baya so.
Bebi koda ya fita sai ya samu kansa da bin unguwar su Manal, umarnin zuciyar sa kawai yake bi a lokacin ban da son ganin ta babu abinda yake so. a daidai layin ya faka motar yana kallon layin zuciyar sa na wani irin bugawa tana tura shi akan yaje gidan nasu amma ya kasa.
Kamar ance ya juya ya ganta riƙe da leda a hannun ta ita da Haroun tana murmushi shima haka sun jera sun shiga layin gidan.
Gaban sa ya faɗi sosai saboda abubuwa biyu da suka haɗar masa a lokacin wanda yake gudun faruwar sa, na farko ganin da yayi mata ya saka gaban sa ya faɗi haka kawai, na biyu kuma ganin ta da Haroun ya saka zuciyar sa a ruɗani, domin bai san alaƙar su da shi ba duba da murmushin da yaga tana yi masa.
Numfashi ya sauke ya kwantar da kansa a kan sitiyarin motar yace, "kaiii! Meyasa zan faɗa soyayya cikin ƙaramin lokaci haka? Meyasa?!." Ya jima a haka kafin ya miƙe zaune ya kunna motar ya ja ya tafi jiki a sanyaye gabaɗaya bashi da kuzari. Bai je office ba sai da ya fara ganin wanda aka kawo ɗin tun a ƙasa kafin ya wuce office yaga mutanen da suke gaban sa.
Tashi yayi ya fito suka haɗu da Dr Hadiza tace, "Dr akwai meeting yanzu." Ya kalle ta yace, "kuje ku yi bazan iya attending."
"But why?."
"Please!" Ya faɗa kawai yana barin wajan a lokacin Huzaifa yazo ta kalle shi tace, "yace bazai attending meeting ɗin ba." Huzaifa yace, "share shi muje muyi abinda yake gaban mu kawai."
Cikin mota kawai ya koma ya zauna ya rasa abinda yake damun zuciyar sa a wannan lokacin, ji yake kamar ya fashe da kuka saboda abinda yake ji yayi masa nauyi a cikin zuciyar sa. Ya rasa yadda zai sarrafa kansa, nauyi yake ji a ƙirjin sa ya rasa inda zai saka kansa yaji daɗi.
Har suka fito daga meeting ɗin yana cikin mota a zaune sai waya ake masa amma ya kasa kallon wayar ma balle ya ɗauka dan baya cikin nutsuwar sa. Kulle motar yayi kawai ya kunna ya ja motar ya fita daga gidan. Babban asibiti ya wuce bai jima ba ya sake wucewa gida ko wajan Mummy bai shiga ba ya shiga ɗakin sa yana ji kamar ya zubar da hawaye saboda kaifin soyayyar da take sukar zuciyar sa.
Bayan sallar magriba Huzaifa da Hamza suka zo gidan wajan Bebi, har wajan Mummy suka je suka gaishe ta take cewa, "mutumin naku ma da ya dawo bai shigo min ba, na lura tun ɗazu kamar bashi da lafiya." Hamza yace, "Mun ga hakan, yau ko damu bai haɗu ba ya dawo gida." Huzaifa yace, "bara muje wajan sa Mama." Ta amsa suka fita suka shiga wajan Bebi suka same shi a kan kujera ya harɗe hannayen sa waje ɗaya yana kallon ƙasa.
Hamza ya zauna kusa dashi yace, "Me yake faruwa ne ka koma haka Bebi?." Ɗago kai yayi ya kalle su ya sauke numfashi yace, "ni kaina ban sani ba, wani iri nake ji a zuciyata kamar nayi kuka. Zuciyata tayi min nauyi sosai, na rasa gane kaina nima.”
Huzaifa yace, "me ya kawo hakan?."
Tsaki yayi a bayyane kafin yace, "Wata yarinya ce, haka nan na kasa daina tunanin ta." Hamza yayi dariyar shaƙiyanci yace, "shine ka shiga wannan damuwar Bebi?, Kamata yayi kayi murna ai ka samu wacce kake so ko babu komai ka samu mafita akan lamarin Rumana."
Huzaifa yace, "Yanzu akan wannan ne duk ka tayar mana da hankali?, wallahi na ɗauka wani babban abu ne yake shirin faruwa ko ya faru.”
Bebi yace, "ni ba ɗaga hankalina nayi ba, na tabbatar ina sonta na amince tun ban amince ba na yarda yanzu, amma abin ne yayi min yawa a zuciyata, kwata-kwata magana sau biyar bana tunanin ta shiga tsakanina da ita, amma yadda nake ji zuciyata na bugawa soyyayar ta tayi yawa." Hamza yace, "tsakanin so ɗin kenan Bebi. Kuma shi so ina ruwan sa da baku yi doguwar magana ba? Daga kallo ɗaya ana faɗawa soyayya.”
Bebi a raunane yace, "tun yanzu?, Tun kafin mu saba ina jin haka a kanta ina ga nan gaba?. Wallahi bana son soyayyar da zata wahalar dani Allah ya sani, bana son soyayyar da zata hanani sukuni. Can you imagine ɗazu kafin na tafi office sai da naje bakin layin su kawai ko zan ganta?. Na kuwa ganta ɗin, amma ita da wani namiji da ban san alaƙar su ba. Yanzu wannan soyayyar da na sakawa zuciyata in an yi mata miji fa ya zan yi?.”
Huzaifa ya girgiza kai yana murmushi, Allah ne ya kama shi ko yaushe gani yake shi zai saka soyayya a zuciyar sa dan haka sai yadda yaso, Gashi Allah ya nuna masa iyakar sa, ya nuna masa shi ke saka soyayya a zuciyar bayin sa. Huzaifa yace, "Wannan ba abin damuwa bane, kayi addu'a akan lamarin ta?."
"Nayi, tunda na fara tunanin ta na fara addu’a, sai bayan nayi addu'ar nake ji tana sake shiga raina sosai." Hamza yace, "magana ta ƙare kawai, kaje ka nemi izinin ganin ta wajan iyayen ta, kaga in kaje in ma da maganar auren a kan ta zaka ji."
Ya girgiza kai yana kallom su da manyan idanun sa yace, "ina niyar hakan, amma zuciyata baza ta jure ace na yi mata miji ba Hamza, a yadda nake ji in akace an yi mata miji zan….” Sai kuma yayi shiru yana girgiza kai.
Hamza yayi dariya yace, "kar ka damu khairan in sha Allah, mallakin ka ce wannan yarinyar da izinin Allah." Huzaifa dariya yake yi sosai yana kallon Bebi kafin yace, "Bebin Mummy manya, Wai wacece yarinyar ma?." Hararar sa yayi dan kuwa bazai faɗa musu ba sai ya tabbatar komai ya tabbata sannan zasu san wacece.
Hamza ma dariyar yake yi yace, "ka share batun Huzaifa, kaje gobe ka samu iyayen ta akan maganar." Bebi ya wara ido yace, "har sai gobe? Meye amfanin yau?." Hamza da mamakin gaggawar Bebi yace, "kana da theater amma kace yau ko?."
"Eh amma sai goma na dare ai, in banje ba bazan samu nutsuwar yin aikin yadda ya kamata ba, so nake naji an tabbatar min babu maganar aure a kanta.”
Hamza yace, "to maza ka shirya kaje yanzu mutumina, Allah ya bada sa'a." Kamar mai jiran umarni sai kuwa ya miƙe ya shiga ɗaki. Hamza da Huzaifa suka ƙyalƙyale da dariya har suna tafawa. Sun ji daɗin yadda Allah ya kama shi tun ba a je ko ina ba, cika baki akan soyayya ya ƙare tunda ya samu wacce yake yiwa son da bai yi zato ba.