Chapter 05
by @nanameera08
*Chapter 5*
"Wace irin matsala ce da har zata gagara sanar da iyalinka?, Ameer kodan lafiyarka ka daure ka sanar mana, kowa ya damu a fadar nan, ka daina walwala kullum saidai kana ɗaki why?" Ta ƙarashe maganar cikin rauni. Bai ce komai ba ya sanya hannunsa ya janyeta daga jikinsa ya tashi ya fice daga ɗakin hannunsa goye a bayansa, baki buɗe ta bisa da kallo har ya ɓacewa ganinta a hankali ta miƙe tsaye ta shiga zagaye ɗakin tana saƙe-saƙen wasu abubuwa a ranta. Library ɗinsa ya nufa dan akwai muhimman abubuwan da yakeson gabatarwa duk da baya jin daɗin jikinsa. Akan wata royal cushion dake gefensa ya zauna hannunsa riƙe da Alqur'ani mai girma, a hankali fuskarta ke yi masa gizo akan idanunsa yana hango ɗan siririn bakinta wanda take masa tsiwa dashi, saurin runtse idanunsa ya yi a hankali ya ɗora hannunsa bisa ƙirjinsa yana jin yanda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi.
"Astgfirullah!"
Shine abin da ya samu damar furtawa yana sake rufe idanunsa a karo na babu adadi, above 10mins yana zaune a wajen ba tare da ya samu damar aiwatar da abin da ya kawo shi ba, kwakwalwarsa gabaɗaya ba a wajen take ba, tunaninsa da zuciyarsa sun karkarta zuwa gare ta.
****
*Al-Udaid Kingdom, North part, backyard*
*9:30pm*
JODA
Tsaye take ta jingina da jikin wani bango, sanye take da wata riga t-shirt milk colour sai wandon jeans Blue colour gashinta ya zubo ta gefen kafaɗarta, idanunta maƙale cikin glasses black colour mai ɗan faɗi, yanayin wajen ya taimaka wajen ƙarawa backyard ɗin kyau. Furzar da iska ya yi daga bakinsa yana kallonta cikin harshen larabci ya ce" ?Limadha tanẓur ilayya (Meyasa kike kallona?". Finger ɗinta ta sanya ta ɗan janye glasses ɗin fuskarta ya dawo kan tsinin hancinta tana kallonsa da sexy eyes ɗinta ta ce cikin harshen turanci" like how? (Kamar yaya kenan?" ɗan basarwa ya yi sanin halinta ya yi murmushi har saida beauty point ɗinsu suka loma ya ce" just move on " jin tayi shiru yasa ya ce"yanzu mene ne plan A?" Kyakkyawan murmushi Joda tayi ta ɗan cije lips ɗinta ta ce"zan tura maka later " jin jina kansa ya yi yana kallonta ya ce" shikenan ina jiranki " . Juyawa yayi ya fara tafiya hannayensa zube cikin aljihu.
"Rasheed!"
Juyowa ya yi yaga bashi take kallo ba sai ya zuba mata idanu, "Kun hadhiran (Ka kula)", ɗan murmushi ya yi wanda ya fito da zallar kyansa ya ce "then you care about me?" Wani kallo ta watsa masa sai kuma ta juya tabar wajen, girgiza kansa ya yi yana jinjina hali irin na Joda kafin ya juya ya tafi shima.
*** Zaune take gefen gadon ta zuba uban tagumi, tunani ne kala-kala cikin ranta gaba ɗaya ƙwaƙwalwarta nema take ta gaza ɗaukan abubuwan dake tunkaro ta, dole ta nemawa kanta mafita. Agogon dake maƙale jikin kusurwar ɗakin ta kalla, 9:45 ta gani a jiki ta sauke idanunta ƙasa tana tunanin wani abu, mene makomar aurenta?, me Maheer yake nufi da ita?, wacece ita a wajensa?. Rashin sanin amshoshin tambayarta ya sanya ta fashe da wani raunataccen kuka ta kwanta kan gadon ta ƙanƙame pillow tana wani irin kuka mai tsuma zuciya, kuka ne wanda yake fitowa tun daga ƙasan zuciyarta, kuka ne wanda yake fassara how sad she is, kuka ne irin kukan komai ya ƙare mata. Meyasa sai ita?, Meyasa ƙaddararta ta zaɓa mata haka? Yaushe zata yi farin ciki?
"Sanda kika aminta da Ameer matsayin mai sonki, sanda kika yarda da soyayya da kuma ƙaunar da nake nuna miki, sanda kika buɗe zuciyarki har ta karɓi saƙon da Fahad ke aiko mata a kowace rana, ki yarda dani Lolo, ki ƙaunaceni kamar yanda nima nake ƙaunarki na faɗa kuma zan sake faɗa, billahil-azeem nafi Maheer sonki, ni ne na dace dake ba Maheer ba, ki karbi soyayya ta hannu bibbiyu nayi miki alƙawarin farin ciki mara yankewa, zan zame miki garkuwa, zan baki farin ciki, zan kula da lamuranki, zan tsaya miki. Ki karbi ƙaddarar ki yanda take, ni ne ƙaddarar ki IMARA!"
Ameer ya faɗa yana ƙarasa shigowa ɗakin hannunsa riƙe da sandarsa as usual, a firgice ta ɗago tana kallonsa da idanunta wanda suka yi jajur, ta miƙe tsaye tana goge hawayen da suka mata caɓa-caɓa a fuska ta fara magana;
"Eh, tabbas!, tabbas kai ƙaddararta ne, irin ƙaddarar da kowane bawa yake rokon ubangiji ya kareshi daga gareta, irin ƙaddarar da idan ta gaba to ka take hanaka bacci, ka zame mini ƙarfen ƙafa Ameer!, wlh zuciyata gab take da bugawa idan har ka cigaba da furta irin waɗannan kalaman masu muni a gareni, kanada ilimi, sanin ya kamata, nutsuwa ta zuci data zahiri amma shaiɗan ya rinjayi zuciyarka, ka kasa gane abun da yake daidai da kuma wanda yake ba daidai ba." Durƙusawa ƙasa tayi ta haɗe hannayenta waje ɗaya alamar roƙo tana kuka ta cigaba da faɗin;
"Dan girman Allah, dan darajar Annabi, dan alfarmar iyayenka ka manta dani cikin rayuwarka, ka cire wannan tunanin daga cikin ranka, wlh babu kyau ko kaɗan nifa matar Maheer ce, sirika nake a gurinka. Ka taimaka Ameer! Ka taimaka min. Ta zube a ƙasa tana sake rushewa da wani sabon kukan kamar ranta zai fita, tun da ta fara magana Ameer ke kallonta a hankali kuma yake lumshe idanunsa, gefen gadon ya zauna ya dafe saitin zuciyarsa jin yanda take bugawa da ƙarfi. Above 5mins babu wanda ya ce wani abu a cikinsu, a hankali kuma ta fara rage sound ɗin kukan nata sai ajiyar zuciya da take ta saukewa, miƙewa tsaye ya yi ya fara takawa cikin tafiyarsa ta isa ya ƙaraso gabanta. Sunkuyawa ya yi yana kallonta for some seconds sai kuma ya sakar mata kyakkyawan murmushi, saurin ɗauke idanunta tayi tana runtse su saboda yanda taga ya yi mata wani irin kwarjini. Ya ɗauki mintuna akanta kafin ya tashi ya fice daga ɗakin ba tare da ta sani ba.
Washegari.
Tana ƙoƙarin sanya takalmin ta ya shigo ɗakin, fuskarsa a ɗaure babu alamar fara'a, kallo ɗaya Imara tayi masa ta cigaba da abin da take. Saida ta kammala sanya takalmin wanda yake canvas white colour sannan ta tashi tsaye, hang bag ɗinta ta ɗauka ta ratsa ta gefensa zata fita taji ya janyota, gabansa ya dawo da ita fuskarsa dab da tata, kallonta ya shiga yi frm head to toe sai kuma ya wani yatsine fuska bai ce komai ba ya kama hannunta suka fita daga ɗakin.
***Gaba ɗaya jama'ar gidan sun hallara wajen cin abinci, babu abin da ke tashi sai ƙarar spoons da knives, "Ayn Jūdā? (Ina Joda?)," Immi ta faɗa tana sake ɗaga kanta, murmushi Dameer ya yi ya ce" Maybe akwai mutanen da bata son gani yasa bata fito ba.", duk suka ɗago suka kalleshi, Shamma ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba ta ture plate ɗin hannunta ta tashi ta bar wajen.
"Dameer!"
Cikeda ladabi ya kalli Ameer ya ce" Na'am Ameer"
" La tuḥāwilu abadan mā faʿaltahu al-ān (Karka sake irin haka)" cewar Ameer yana tashi tsaye, cikeda ladabi Dameer ya ce " in sha Allah". Bai sake kallon kowa ba ya bar wajen. Miƙewa Immi tayi tana kallonsa ta ce"ka sameni a ɗaki" okay ya ce sannan y tashi yabi bayanta. Tsaye ya sameta tana kai kawo cikin ƙaton parlon dake cikin part ɗinta, da idanu ya bita ganin kamar hankalinta ba a kwance yake ba yasa ya ce "what's going on Immi?" dafe kanta tayi ta ce"Dameer abubuwa na gab da lalacewa, UDAID na gab da barin hannun mu, sirrin da na daɗe ina ɓoyewa nason fitowa fili." Ɗan murmushi ya yi yana girgiza kansa ya kamo hannunta ya riƙe cikin nasa cikin son kwantar mata da hankali ya fara magana
"Haba Immi, wannan ba abu bane mai yiwuwa, nayi miki alƙawarin yin duk wani abin da ya kamata wajen ganin na cika burinki, saboda haka ki kwantar da hankalinki". Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ta gyaɗa masa kai ba tareda ta ce komai ba.
*SHAMMA*.
"Ƴaƴana?, Ƴaƴana?, ku ba Yarana bane!, wlh dana riƙe ku matsayin ya'ya gara na mutu na bar duniyar, koda wasa bana ƙaunarku, tunda har kun zaɓeta matsayin uwa to nima na haƙura na sallama mata ku, ta raine ku, ta baku kulawa, amma har abada babu ni babu ku!"
"Shamma dan Allah kar kiyi haka, ke uwace nasan kina son mu, karki bari a rabamu dake, ki jiƙanmu a matsayin mu na yayanki, dan Allah Shamma, karki ji mata ciwo ki taimaka Shamma!" A fusace ta riƙo hannun ƙaramar yarinyar da bazata shige 4-5yrs ba ta hankaɗata, wata razananniyar ƙara yarinyar ta saki dalilin tafasasshen ruwan heatern data zubo a jikinta, da gudu yaron ya saki hannunta ya ƙarasa wajen yarinyar ya shiga jijjigata saidai duk inda ya cire hannunsa sai fatarta ta biyo hannunsa ganin haka yasa ya saki wata irin ƙara, nan take idanunsa suka kaɗa suka yi jajur tamkar gauta, jijiyoyin kansa suka firfito. Tamkar wanda aka zabura haka ya miƙe tsaye naman jikinsa na wani irin rawa wacce ke nuni da ɓacin ran da yake ciki, hannunsa ɗaya ya sanya ya tattare gashin da ya rufe fuskarsa ya maƙaleshi gefen kunnensa, ya kafeta da manyan idanunsa bakinsa na rawa.
"Shamma! Shamma!", girgiza kai Maha tayi ta ƙaraso gabanta ta dafata, a firgice Shamma ta ɗago kanta tana kallonta, sai kuma ta ɗauke idanunta tana ƙoƙarin ɓoye hawayen dake cikin idanun. Zama Maha tayi gefenta cikeda damuwa ta ce "Shamma something went wrong with you but you couldn't tell anyone why?" Kyakkyawar fuskarta ta larabawa Shamma ta kalla sai kuma tayi murmushi ta ce cikin harshen larabci " karki damu baby, ina lafiya" girgiza kai Maha tayi ta ce"shikenan Allah yasa haka ne" "Ameen ya rabbi" Shamma ta faɗa tana kaƙalo murmushi. Tashi Maha tayi ta ce"daman fita zanyi shine nazo na faɗa miki saina dawo bye" hannu kawai Shamma ta ɗaga mata dan batajin zata iya cewa wani abu ta fice daga ɗakin. Tana fita Shamma ta ɗora kanta gefen pillow ta fashe da wani sabon kukan mai cin rai tana nadamar abubuwan da suka faru a baya.
*Education City, Doha, Qatar*
_DOHA INSTITUTE OF GRADUATE STUDIES (DI)_
3:30pm.
Zaune suke cikin capteria kowa na duba abinda zai yi order, ganin hankalinta gaba ɗaya baya wajen yasa Rania ta taɓa ta, a ɗan firgice ta kalleta sai kuma ta sakar mata murmushi tana murza idanunta wanda yayi jajur dashi, ajiye Menu book ɗin Rania tayi ta juyo tana fuskantar ta ta ce cikin harshen larabci "Katalina meke damunki?, tunanin me kike?, me yake hanaki bacci naga idanunki sun koma haka?" Rania ta jero mata tambayar tana kafeta da manyan idanunta, kasa cewa komai Imara tayi kawai sai ta faɗa jikinta ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi. Dafa kanta Rania tayi bata ce komai ba, saida ta barta tayi kukan mai isarta sannan ta fara sakin ajiyar zuciya a hankali tana shassheƙar kuka, ɗago fuskarta Rania tayi tana kallonta ta ce"now tell me what wrong with you?" Ɗan murmushi Imara tayi tana goge hawayen idanunta ta ce"babu komai fa, kawai na tuna wani abu ne shikenan." Baki buɗe Rania take kallonta sai kuma ta girgiza kai
"Me kika tuna da yake sanya ki kuka?, ko shikenan Allah yasa hakane abinda kika faɗa"
Jinjina mata kai Imara tayi ta ce"hakane ma" ta faɗa tana lumshe idanunta. Shiru suka ɗauka na wasu sakkani kafin Imara ta sake kallonta ta ce"can I ask you friend?" "Why not?" Rania ta bata amsa tana kallonta with full attention. Numfasawa Imara ta yi sai kuma ta ce cikin harshen larabci" inada wata friend so tana cikin matsala nikuma na kasa bata shawara shine nake neman taimakon ki ki bani shawara " jinjina kai Rania ta yi, Imara ta cigaba da faɗin"zan baki ɗan labarin abin da ke damunta sai ki bani shawara Please".
Tunda Imara ta fara magana Rania ke bin ta da kallo irin na mamaki, da daɗe bataji abin da ya gigita mata lissafi ba irin wannan, wane irin son zuciya ne wannan?, wace irin duniya muke ciki ne? Inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun, shine kawai abin da take iya furtawa gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi. Ganin yanda tayi yasa Imara tayi murmushi tana taɓa ta ta ce " karki damu kanki fa, kawai shawara nakeson ki bata" numfasawa Rania tayi tana kallonta ta ce
"Imara na daɗe ban ji abin da ya bani tsoro ba irin wannan, kuma da gaske nufi yake ta rabu da ɗansa?" Jinjina mata kai Imara ta yi ta cigaba da faɗin;
"Shawara anan shine kawai ta cigaba da addu'a even through nasan tanayi but ta ƙara, na biyu kuma tana iya using wannan opportunity ɗin wajen ganin ta samu amsar tambayar da take nema, I mean ta tambaye shi wasu abubuwa game da mijinta da kuma matar da yake magana akai, ta nan ne zata gane abin da mijin ke ɓoye mata da kuma wanda ya faru a baya. Idan tayi haka zata iya gano bakin zaren daga nan sai ta yankewa rayuwarta hukunci dan wannan ba ƙaramin al-amari bane!"
Murmushi Imara tayi ta ce"yawwa Friend Nagode sosai in sha Allah nima zan sanar da ita Allah yasa a dace" Ameen ya rabbi Rania ta ce sannan suka cigaba da duba abincin.
***Zaune yake gefen gadonsa idanunsa maƙale akan wani Enlargement na hoto ya zuba mata idanu, fuskar dake jikin hoton sak Imara babu abin da ya raba su. Yanayin shigar dake jikinta ne kawai ya bambanta domin ita wannan ƙananun kaya ne a jikinta gashin kanta kuma a buɗe babu veil.
Da gudu ya ƙarasa sauka daga saman yana tafe yana ture mutane, can ya hango su suna tsaye kana ganinsu kaga ɗalibai, ajiyar zuciya ya sauke sanda ya hangeta fuskanta a sake sai murmushi take, tana ganinsa ta saki murmushi da gudu ta tawo ta shige jikinsa, murmushin shima yake ya riƙeta gam, sun jima a haka kafin ta sake shi tana kallonsa ta ce cikin cool voice ɗinta "you kept me waiting" ta faɗa tana tura baki gaba, hannunta ya kama ya riƙe cikin nasa yana dariya ya ce "I'm sorry na tsaya duba patient ne" langwaɓar da kai tayi ta ce" shikenan kaje sai mun haɗu anjima"
"Really?"
Jinjina masa kai tayi ya bata peck a goshi sannan ya juya zai bar wajen.
"Maheer!"
Juyowa ya yi jin tayi kiran sunansa abin da ya daɗe bai ji ba a rayuwarsa, ɗaga mata gira ya yi ya ce"what?" Murmushi tayi har saida beauty point ɗinta ya loma ta ce" don't forget with me, I love you" yanda tayi maganar jiki a sanyaye ya sanya yayi murmushi ya gyaɗa mata kai
"Har abada Peanut", murmushi ta saki ta ɗaga masa hannu alamar bye shima ya mayar mata sannan ya juya ya shige motarsa.
"PEANUTTTTT..."
Ya faɗa a fili yana shafa hoton, ɗumin da yaji a fuskarsa ya tabbatar masa da cewa kuka yake kuma daman ya cancanci ya yi kukan, he missed her, ƙaunar da yakewa Katalina daban take a cikin zuciyarsa amma ta tafi, she left him without even say goodbye to him, why? Why???.
"Saboda baka yi deserving rayuwa da ita ba, kanada son kanka, kana fifita buƙatarka akan ta wani, kana iya salwantar da wani abu matuƙar kai zaka samu biyan buƙata, you are too selfish Maheer!"
# *Bestnovel
# *Nanameera
# *Imara
# *2025.