BAYA DA ƘURA

021

by @nanahaleema11

*BAYA DA ƘURA.*

Fitattubiyar2025


          ©️Nana Haleema.


Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11


*BOOK 1*

*Page 021.*



Mubeena kuwa a daren suna zaune a falon gidan su Bily su Mummyn sun je wata dubiya su dawo Mubeena sai ƙunci take yi Bily tace, "wai duk akan an ƙwace miki waya shine kike wannan ƙuncin? Ni Baba yayi min daidai domin kuwa wannan shegen mutumin iskanta ki zaiyi wallahi."


Mubeena bata ce komai ba mai gadi ya shigo da sallama Bily ta amsa yace, "akwai wanda yazo yace ayi masa magana da Mubeena shine nazo na sanar da ku." Mubeena ta kalle shi tace, "waye?." Mai gadin yace, "ban san shi ba, amma babban mutum ne." Kafin yace wani abun Mubeena ta miƙe ta yafa mayafi ta fita Bily ta bita da kallo tana girgiza kai cike da jin haushin ta.


Waje ta fita taga motar tasa ta buɗe gaban motar ta shiga ya kalle ta yace, "kin wahalar dani Baby, yau kwana biyu wayar ki a kashe baki neme ki ba, wallahi ko abinci bana iya ci. Duk akan abinda ya faru ne kike min wanna horon? To kiyi haƙuri bazan sake ba." Mubeena itama kewar sa take yi sosai a zuciyar ta sai ta fara kuka ta gigita shi lokaciyace, "Haba Baby, me kuma don Allah? Kina so nima nayi kukan ne?."


Bata amsa ba yace, "Don Allah ki faɗa min abinda ya faru, in akan abinda nayi ne nace ayi min afuwa ko?." Mubeena ta goge idanun ta tace, "wayata ce ta faɗi kuma bani da lafiya."

"Me ya same ki Baby? Wani abun yana damun ki?." 

"Ciwon kai ne, amma naji sauƙi sosai." 

"Yaushe wayar taki ta faɗi?."

"Tun washe garin da muka rabu."


"Amma da sai ki saka Gmail ɗin ki a wata wayar ki ɗauki number ta ki kira ki sanar dani, na damu sosai baby." Ta share idanun ta tace, "ban yi wannan tunanin ba." Yayi murmushi yace, "to shikenan, indai waya ce za'a sake siya miki wata dan ma dare yayi ne da yanzu za'a kawo miki amma gobe da safe ki shirya karɓar waya. Sim card ɗin fa?." Mubeena tace, "zan canja wani kawai, daman bana son wancan damuna ake da waya." Yayi murmushi yace, "an gama ranki ya daɗe, zan aiko ayi miki register har gida ba sai kinje kin bi layi ba."


Tayi murmushi tana turo baki ya bita da kallo kurilla yace, "Ina kewar ko baby." Ta kalle shi itama tace, "Nima haka" ta faɗa tana kallon sa tana tuna abinda yayi mata sai tsigar jikin ta ta tashi. Hannun ta ya riƙe yace, "yaushe zaki raka ni Abuja? Ina so naje na gana da president kinga sai muje ko?." Mubeena Jin ance president sai ta kalle shi tace, "Mummy baza ta barni ba, faɗa zata yi min." Yayi murmushi yace, "to yanzu ya za'ayi? Ina so kiyi min rakiya muje mu dawo a ranar."


Mubeena tayi shiru tace, "a ranar muje Abuja mu dawo?." Yayi dariya yace, "sosai, jirgi zamu hau kuma private get ne sai lokacin da naso muje mu dawo." Jin haka sai ta sake jin daɗi tayi dariya tace, "to zan duba na gani in zanje." 

"Zaki je ma kawai Baby." Tayi murmushi shima yayi tare da yiwa hannun ta kiss yace, "hankalina ya tashi akan rashin magana dake, yanzu dana ganki sai na samu nutsuwa." 


Tayi dariya bata ce komai ba yace, "in badan ke ba bana driving da kaina, amma bazan iya zuwa da wani wajan ki ba Baby" ya faɗa yana ɗauko leda a bayan motar ya ajjiye akan cinyar ta.


Buɗe ledar tayi taga kayan ciye-ciye ne kawai a ciki, tayi murmushi tana kallon ledar sai ji tayi ya mata kiss a kumatu ta kalle shi ya ɗaga mata gira sai suka yi dariya a tare. A haka suka rabu ta koma ciki shi kuma ya ja motar domin baya so Maubeena ta guje masa bai samu abinda yake so ba, in hakan ta faru yayi babbar asara.


Mubeena bata dawo ba sai goma na dare Baba yana zaune a ƙofar gida yana jiran yaga ta inda zata ɓullo dan lamarin ta ya lura sai ana mata yi jan ido, ai kuwa ya hango ta shigo layin, baiyi magana ba har ta shiga cikin gidan sannan yabi bayan ta ya kulle gidan dan a wajan Mama yake ya shiga ciki.


"Daga gidan uban wa kike?." Jin abinda Baba yace sai da gaban ta ya faɗi ta juyo tana kame-kame, ya ɗauke ta da mari mai zafi kafin ta dawo hankalin ta ya sake marin ta sai ta zube a wajan tana gani biyu-biyu dan rabon da a mare ta har ta manta yace, "ni zaki mayar ɗan iska? Dan kinga ina bin ki a hankali sai ki mayar sa'an wasan ki? Daga ina kike a cikin daren nan?.” Baya yayi ya ɗauki igiyar shanya yace, "Wallahi ko ki faɗa min ko yau na zane miki jikin ki, daga gidan uwan ban wa ki ke a daren nan?."


Mubeena ta tsorata sosai karo na farko da Baba yayi mata haka,jiki na rawa ta rasa abinda zata ce kawai taji ya fara dukan ta dan ta gama ɓata masa rai. 


A guje Manal ta fito jin maganar Baba da ƙarfi ganin ana dukan ta sai jikin ta yayi sanyi ta fara kuka tana daga tsaye Baba yace, "baza ki faɗa min ina kike zuwa ba?."

"Makaranta naje, sune suka tura mu wani aiki sai yanzu na dawo."

"Ƙarya kike, har makarantar taku na saka an duba bakya nan, ko faɗa min inda kikaje ko yau sai na lahira ya fiki jin daɗi, ko ki faɗa min uban da yake goya miki baya yake zuga ki ko yau na karya ki.” Ganin Baba dukan nata zai sake yi da sauri tace, "Wallahi Ina can, ina can babu inda naje" ta faɗa tan kuka sosai dan ta daku.


Baba yace, "duk abinda kike ganin daidai ne a wajan ki Mubeena ki yi, ki cigaba da ɗurawa babar ki baƙin ciki, ki cigaba da bari tana zubar da hawaye a kan ki. Daga lokacin da kika yi sake tayi miki baki daga wannan lokacin zaki gane kuskauren da kika tafka a rayuwar ki wanda baza ki gyara ba. Ina so ki sani, daga yau babu ke babu zuwa makarantar na soke, sannan daga yau kar na sake gani kin fita ko da gidan su Surayya ne. wallahil azim kika sa ke aikata wani abun sai nayi miki illa, sai na karya ki gida biyu" ya faɗa yana cillar da igiyar ya shiga ɗakin sa cikin ɓacin rai sosai.


Manal da take kallon ta tana kuka tace, "Ko yaushe burin ki ran Mama ya ɓaci, bakya damuwa da wanne hali zata shiga saboda son zuciya da son kuɗi ya riga ya rufe miki ido. Ki yi abinda kike ganin ya dace, abinda baki sani ba nasan ba makaranta kike zuwa ba Yaya akwai inda kike zuwa in kika fita, bana zargin ki a baya, amma yanzu ina zargin kin fara wata ɗabi’ar da baki da ita. Kije ki yi ke zaki dana sani, ke zaki nadama a lokacin da bata da amfani, ke abin zai bibiya har mutuwar ki” tana faɗa ta shige ciki ta barta a wajan tan kuka sosai. Mama duk tana jin abinda yake faruwa tayi kamar tayi bacci nan kuwa idon ta biyu babu wanda ya kai ta jin baƙin ciki a zuciyar ta.


Tana jin wucewar Mubeena ɗin tana kuka bata ma ɗaga kai ta kalle ta ba balle tayi mata magana. A haka suka kwana kowa rai a ɓace. Da ciwon ƙirji Mama ta tashi sai da Manal ta bata magani sannan ta ɗan ji daɗi. Mubeena na ɗaki taƙi fitowa ko cin abinci balle wanka babu wanda ya neme ta duk suka share ta.


Gab da sallar azahar Bily tazo gidan Baba yana nan dan bai fita ba saboda case ɗin Mubeena, Bily ta gaishe da Mama suka gaisa da Manal kafin tace, "Manal Baba yana nan?." Manal tace, "eh yana nan, amma yana wancan gidan." Bily tace, "muje ki raka ni wajan sa na zo" Ta amsa da to ta tashi ta saka mayafi suka fita.


A lokacin zai fito daga gidan suka haɗu a soron gidan, Bily ta gaishe shi ya amsa kafin Manal tace, "ƙawar Yaya ce Baba, tace tana son ganin ka." Baba yace, "Allah yasa Lafiya."

"Ba Lafiya ba Baba, magana ce akan Mubeena."

Baba ya nutsu yana kallon ta yace, "Ina jin ki."


"Baba tun shekarar mu ta farko aka kori Mubeena daga makaranta saboda bata maida hankali akn karatun, duk wata ƙarya da take yi akan makaranta ƙarya take wallahi bata da register babu sunan ta a jerin ƴan makaranta, tana dai taya ni zama mu dawo. To yanzu ta daina zuwan ma saboda akwai wani Alhaji da yake wure mata kunne da sunan zai aure ta, baban mai kuɗi ne sosai a garin nan, har waya ya siya mata mai tsadar gaske. Nayi shiru da ban faɗa ba, amma yanzu rawar kan nata yafi na baya, shiyasa naga in nayi shiru naci amanar ku dalilin da ya saka nazo na faɗa a saka mata ido domin a kansa babu abinda baza tayi ba."


Baba ya girgiza kai cikin mamakin Mubeena yace, "Ya sunan ki?.”

“Bilkisu.”

Baba yace, “Na gode Bilkisu, Allah yayi miki albarka, Allah ya saka miki albarka a rayuwar ki." 


Bily tace, "Amin Baba. Nayi anyi da ita akan ta bari taƙi shiyasa na yanke hukunci nazo na same ka, kuma daman gidan mu shine mafakar ta, a nan take wuni har dare sannan ta tawo.” Baba yace, "kin kyauta da kika faɗa ɓin, na gode sosai Allah yayi miki albarka" ta amsa da amin tayi musu sallama ta wuce. Manal ta koma ciki jikin ta duk babu daɗi jin abinda akace Mubeena ɗin nayi.




Manal da ta shiga gida kai tsaye inda Mubeena take ta wuce ta shiga ta zauna kusa da ita tace, "ni kaɗai ce ƴar uwar kuma wacce zan faɗa miki gaskiya Yaya, ni kaɗai kike da ita ko kina so ko bakya so. Rayuwar da kika ɗauka ba komai bace face watsewa da kuma lalacewa, in kina ganin hakan da kike yi shine daidai kuma shine wayewa wallahi rashin hankali ne da kuma rashin wayo da lalacewa. Zai jawo miki dana sanin da har ki mutu baza ki daina ba a lokacin da bazai miki amfanin komai ba, ita wannan duniyar kayi daidai ma ya ka cika balle baki yi daidai ba?. Kabi iyayen ka ya ka zauna balle ka raina iyayen ka?."


"A ko yaushe burin ki ɓatawa Mama rai, bakya ganin girman ta bakya darajata dan ta kasance a wannan gidan da kika raina kuma bata gani, ke a ganin ki Allah bai miki daidai ba da ya yo ki a gidan nan. Ba ƙarya kowa yasan kina da kyau amma meye amfanin kyau babu kyaun zuciya? Meye amfanin kyaun da zai kai ki wuta da ƙafar ki?. Ke a tunani ki wannan ɓacin rai da kike saka Mama bazai iya kai wuta ba? Ko hawayen da kike saka ta a kulluɓ ruwa ne yake zubewa daga idanun ta Yaya?." 


Mubeena tayi shiru bata ce komai ba Manal tace, "duk abinda kike aikatawa in ya kamata kin sani wallahi, kome kike yi ki na sane domin kuwa da hankalin da kuma ilimin ki, ki sauke tunanin da ya shiga kan ki, ki yi rayuwa mai kyau in ba haka ba dana sani zata riske ki a lokacin da hakan bazai miki amfani ba. Na faɗa miki haka ne a matsayin ki na ƴar uwata ta jini, bani da kamar ki shiyasa na faɗa miki gaskiya, in kin ga zaki gyara kanki, in baza ki gyara ba kan ki" tana gama faɗa mata haka ta tashi ta fita dan in tana zaune kusa da ita ji take kamar ta mare ta.


Ɓangaren Bebi haka ya kwana ya yini cikin karsashi da farin ciki da annushuwa, koda yaje asibiti sun lura da yadda yake komai da kazar-kazar kai da ka ganshi kasan akwai wani abu mai daɗi da ya same shi.


Lokacin da yake asibitin su na getting better babu wani conjunction na marasa lafiya in ma akwai ba ɓangaren da bane da yawa ɓangaren su Hamza ne da ƴan team ɗin sa, hakan ya saka shi zama kawai yana tunanin Manal da abinda zaice mata in yaje wajan ta a ranar.


Bai jima sosai ba ya tashi zai tafi sai a sannan suka haɗu da mutanen nasa Hamza ya kalle shi yace, "Ahha Bebi wannan yanayin da na ganka a ciki duk soyayyar ce?." Ɗaure fuska yayi gudun kar su jawo masa raini ganin basu kaɗai bane a wajan, hararar su yayi yace, "ku kuka sani" yana faɗa yayi gaba suka yi dariya suka cigaba da abinda suke yi shi kuma yayi gida.


Yana shiga gidan Maryam tana shigowa itama ya bita da kallo, gabaɗaya baya amincewa da yawan fitar da yake gani suna yi ita da Lubna su kaɗai, amma da yake idanun sa basa ganin abinda baya so a tare dasu bai wani damu ba. 


Ciki ya wuce ya shiga wajan Mama ya samu Yayar sa Farida a zaune ita kaɗai tana danna waya. Ya zauna yace, "saukar yaushe?."

"Na jima a nan, ya aikin?."

"Alhamdulillah. Ina Mummy?."


"Tana ciki. Ya batun Rumana ne?, Mama ta matsa a kai fa, yanzu ma kafin ta tashi maganar take yi min, maganar ta taso da gaske ne?." Ya kalli hanyar da Mama zata ɓillo yaga bata nan yace, "zan zo gida mu tattauna a kai."

"Ya dai kamata, ni sam-sam bana so yanzu wallahi, da dai naso ka aure ta amma yanzu abin ya fita a kaina haka kawai."

"Hmm! Kema dai kya faɗa."


Mama ce ta fito tana cewa, "A'a Bebi an dawo?." Yayi murmushi yace, "eh Mummy, na dawo" ta ƙaraso ta zauna tana kallon sa tace, "to Sannun ka."

"Ina su Mimi?."

"Sun je gidan Yayan ku."

"Me ake yi?."

Mama ta kalle shi da mamaki tace, "Sai ana wani abun zasu je gidan Yayan su? Meyasa ka ke haka ne wai?."


Baice komai ba yayi shiru ya tashi ya shiga kitchen sai gashi da abinci yana yamutsa fuska san baya son macaroni amma gashi an dafa kuma jellop duk tayi sanyi ba yadda yake so ba. 


Mama ta kalle shi yana ci yana taɓa baki yace, "Bana son wannan abar Mummy."

"Sai ka ajjiye ai." Baice da yawa ba kuwa ya ajjiye ya kalli Farida yace, "dama zaki min girki da naji daɗi." Hararar sa tayi tace, "ashe zaka kwana baka ci ba wallahi." Ya taɓe baki Mama tayi dariya tace,

"Kema dai , ai da sai kice ya jira ki zaki dafa masa, in kana son girki na kira Rumana nace ta kawo maka."


Ya girgiza kai yace, "A'a Mummy ƙyale ta, zan san abinda zan ci" ya faɗa yana tashi ya fita. Mama tayi dariya bayan ya fita tace, "duk zilliyar ka sai ka auri Rumana Adnan." Farida bata ce komai ba dan itama ba so take yi ba.


Sai bayan sallar magriba sannan yayi wanka yayi kyau cikin manyan kaya kamar jiya, yana ta ƙhamshi mai sanyi dan shi baya ƙhamshi mai ɗaukar hankali, baya son turare mai ƙarfi kowa ya san da wannan indai kuna tare. Falon ya shiga ya tarar da Mama da Farida dasu Mimi duk sun na nan ganin sa sai suka tsaya kallon sa dan ya yi musu kyau sosai. 


Farida tace, "Sai ina?." Mimi ƙasa-ƙasa tace, "Kamar dai mai zuwa zance" ta faɗa tana kulle bakin ta tana dariya.


Mama ta kalle shi tace, "ma sha Allah Bebin Mummy, kayi kyau sosai, ina zaka je haka?." Yayi murmushi Yace, "zanje wani waje mai mahimmaci Mummy, kiyi min fatan samun nasara" ya faɗa yana ƙarasowa inda take ya cire hular kansa ya tsiguna a gaban ta ɗora hannun ta a kana tace, "Allah ya bada nasara, ko ina kaje kai ne mai nasara ai Adnan." 


Ya mayar da hular ya tashi ya kalli Farida da suke gulmar sa ita da su Kausar yace, "me kuke cewa?."

"Cewa nayi yanzu wataƙila dan wata kayi wannan kwaliyyar ko?, Ko da yake Kausar tace ko wacece bata san wanda zata ɗauko bane shiyasa".


Yayi ƴar ƙaramar dariya yana kallon su yace, "munafukai." Ganin har darıya yayi sai suka suka yi dariya suka samu ƙarfin guiwa Mimi tace, "wallahi kayi kyau Yaya, kuma yau naji kana khamshi kuma naga baka son turaren." 


"Na gode. ƙaryata ni ki keso kiyi kice daman dai ina sakawa ko?." Ta girgiza kai tace, "A'a, kawai dai nayi mamaki ne da na ji ƙhamshin yanzu, ban taɓa jin khamshin mai yawa haka a jikin ka ba, nasan ana ji amma sai anzo inda ka ke sosai."


"Ke dai munafuka ce, to dan kin ji turare a jikina sai ki cigaba da sakawa kizo inda nake" sai ya faɗa cikin wasa suka yi dariya. Mama dai kallon sa take tace, "wannan kwaliyyar kamata yayi ace ta Rumana ce, ina zaka je haka ne?."

"Zan sanar dake Mummy sai na dawo" yana faɗa ya fice suka cigaba da gulmar sa suna dariya.