BAYA DA ƘURA

024

by @nanahaleema11

*BAYA DA ƘURA.*

Fitattubiyar2025


          ©️Nana Haleema.


Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11


*BOOK 1*

*Page 024.*




A daren babyn Mubeena ya faka a ƙofar gidan su Bily yana shirin yiwa mai gadi magana sai ga Bily zata shiga gidan ya sauke glass yace, "Sannun ki." Kallon sa tayi ta matso kusa da motar tace, "Yauwa sannu."

Yace, "ina neman Mubeena ne, Tana ina kwana biyu shiru haka?." Bily tace, "Ayya ai sun bar Kano sun koma garin su." Gaban sa ya faɗi sosai ya kalle ta yace, "me kika ce?, dama ba a Kano suke ba?."


"Eh, a Adamawa suke fulanin can ne, daman ai da kaga Mubeena kaga bafulatana. Sun tafi shiyasa da ka aiko da waya ma nace ace bata nan."


Yace, "Adamawa! Ya maimaita cike da mamaki da tsoro kafin ya sake cewa, "kenan nan ba gidan su bane ba?." Bily tace, "eh, gidan mu ne nan, Mubeena ƙawata ce mun zama kamar ƴan uwa a nan take zaune kamar gidan nasu yake." Ya girgiza kai yace, "ki bani lambar ta."

"Kasan ai babu waya hannun ta, a haka ta tafi bata yi sabon sim card ba." Yayi shiru alamun damuwa Biky ta Harare shi ta gefen ido tace, "da yake aure ma zasu yi mata shiyasa suka yi tafiyar gaggawa." Da sauri ya kalle ta da faɗuwar gaba yace, "aure kuma?." Ya faɗa da mamaki zuciyar sa na bugawa sosai domin haka kawai yake ji gaban sa na faɗuwa.


"Eh aure, ina jin in ba'a yi bama an kusa. Sai anjima" ta faɗa tana wuce ta barshi a bayyane tana cewa, "sai na raba ku ai wallahi, haka kawai zaka lalata yarinyar mutane kai ka bar naka a gida" ta faɗa tana shiga gida shi kuma yana motar ya tafi cike da damuwa mai yawan gaske.


Maryam na zaune a motar Kamal tana kallon sa da mamaki tace, "amma kace min ka goge hotunan, meye na dawo dashi kuma?." Yayi dariya yace, "meye na dawo dasu kuma? Gani nake ina tunawa dake." Maryam tayi tsaki kaɗan yace, "wannan ba abinda zaka dinga gani kana tunawa bane ba, don Allah ka goge. Tsaraicina ne fa, kuma yanzu ni ba matar ka bace."


Wani kallo yake mata na bama ki da hankali kafin yace, "zan goge, yanzu gida zan kai ki ko muje nawa gidan?." Kallon sa tayi suka haɗa ido tace, "muje gida, amma nafi son don Allah ka goge hoton nan."

"Wai meye abin damuwar ne? Naga lokacin da aurena a kan ki akayi hoton nan ko? Kuma kema kina da nawa meye na damuwar?."

"Ni bani da naka, auren mu na mutuwa na goge dukkan hotunan dan basu da amfani tunda ba kai ba mijina bane ba."

"Saboda bakya kewata ne, ni da nake kewar ki ai ban goge ba."


Maryam tace, "Gaskiya zamu yi yin faɗa akan hoton nan." Ya sake yin dariya yace, "zan goge kar ki damu my love" ya faɗa yana jan motar sai fushi take yana dariyasuna tafiya. 


A bakin bakin su ya sauke ta ta fita yace, "gwara mu tsaya a nan kafin yayan ki ya gani mu." Bata ce komai ba yaja motar yana dariya yace, "da wannan hotunan tsaraicin naki zanyi amfani na samu abinda nake so a wajan ki, sai na saka Bebi kuka domin sai na tabbatar da kin yi ciki Maryam" ya faɗa yana ƙwafa.


   Tana shiga gidan yana ajjiye mota shima bata kalle shi ba ta wuce shima bai mata magana ba ya fito ya shiga wajan Mama tana zaune kamar ko yaushe a inda ta saba zama tana cin abinci. Ya shiga ciki da sallama ya zauna ta kalle shi tace, "ina kake zuwa ne ka ke kwalliya haka?." Kafin yayi magana Mama tace, "baka je ka samu Daddy akan maganar Rumana ɗin ba ko?."

"Aiki ne yayi min yawa shiyasa, amma zanje."


"In baka je bama ni zanje na same shi na sanar dashi." Mimi ya kalla yace, "Mimi bani abinci naci." Ba musu ta tashi ta kawo masa bata dawo ba sai da ta haɗo da ruwa da lemo gudun kar ya mayar da ita amma ta ajjiyewa yace, "baki ɗauko kofin ruwan ba, koma ki ɗauko ki haɗo min da ketchup kin san bana son cin doya sai dashi ai." Juya tayi ta koma ta kawo masa ta ajjiye ya fara jin doyar bai sake magana ba haka Mama ma.


Sai daga baya yace, "Mummy Tahir mai son Mimi, su Daddy sun gama bincike a kansa har sun bada dama ya turo tunda tana son sa." Mummy tace, "Abban ku ya faɗa min ɗazu, shiyasa ai nake so kayi abinda ya kamata a haɗa bikin naku."


"Ni Mummy ai ban shirya ba, ko gini ba'a ba ina ni ina aure yanzu?."

"In an saka ranar auren zaka mayar da hankali ka gama ai, kana da kuɗin yi ai, in babu baban ka na dasu. Balle ai ba kai ka ke yi ba, Abban ku ne yake maka." Shiru yayi bai kuma magana ba ya gama ci.


Yana shirin tashi yaji tace, "Adnan ka jini da kyau, wallahi babu wata mace da zaka aura in ba Rumana ba kaji nace wallahi, wannan kwaliyyar da kake kwana biyu na lura zance ka ke zuwa to ka fita daga idona na rufe, ko wacece ita ka dakatar na faɗa maka domin kana da mata a ƙasa tun baka kai haka ba." Jikin sa ne yayi sanyi jin Mama har da rantsewa, bata taɓa rantsuwa haka ba sai yau shiyasa jikin sa yayi sanyi sosai. baice komai ba ya tashi ya fita shi ya rasa wannan wanne irin abu ne da Mama take masa akan Rumana.


Ɗaki ya shiga ya rasa ma tunanin da zaiyi kawai sai ya kira Farida, tana ɗauka tace, "Bebi ya akayi ne?."

"Ya zanyi da Mummy ne?."

"Me ya faru?."

"Mummy yanzun nan ta rantse akan bazan auri kowa ba sai Rumana." Farida tace, "Mummy na son Rumana ita dai kam, kana ji gobe kazo mu tatttauna nasan abinda za'ayi in sha Allah." Bai ce komai ba ya yanke wayar ya sauke numfashi ya shiga banɗaki bai jima ba ya fito ya saka kayan bacci riga da wando masu kyau ya kwanta.


Da safe da wuri ya shirya da ya shiga wajan su Mama ma bacci suke ya fita kai tsaye gidan Farida ya wuce a lokacin ƙarfe bakwai na safe. Mai gadin gidan ta ya buɗe masa ya shiga yana zaune a motar ya kira ta amma bata ɗauka ba kawai ya fito ya shiga cikin gidan. 


A babban falon ta yara ne guda biyu suna ta shirin makaranta sai mijin ta da yake zaune yana breakfast ya shiga da sallama.


Mijin nata ya amsa yana kallon sa yace, "Adnan yau kai ne a gidan namu?." Ya ƙarasa inda yake suka yi musabaha Bebi yana yamutsa fuska saboda khamshin falon da alama bata jima da gama turaren wuta ba ya zauna yace, "na shigo da sassafe kamar gidan rasuwa, in ba yanzu ba bani da lokaci."

"Haka ne kam, ai kuma ƙoƙari ma sosai Allah ya taimaka." Bebi ya amsa ya kalli babar ƴar ta yace, "ina Mama naki?."

"Tana sama" ya dafe kansa jijiyoyin kansa har sun fara harbawa yace, "kice mata nazo, jeki da sauri" ya faɗa yana tashi mijin mata ya kalle shi yace, " ka hau saman mana."


Bebi yace, "zan jira ta ba sai na hau ba" ya faɗa yana ɗaukar waya sa ya fita daga falon. Bai jima da fita ba ta sauko tace, "A'a ina bebin?."

"Ya fita waje."

"Ohh shifa baya son turare, wannan khamshin ne ya dame shi shiyasa ya fita. Kasan yanzu sai ya saka shi ciwon ko ya fara jiri." Yayi dariya yace, "kowa dai da yadda Allah yayi shi, mu muna so shi baya so." 


Tayi dariya ta fita ta hango shi a kan kujerar ƙarfen da take ajjiye a harabar gidan ta ƙarasa ta zauna kusa dashi tace, "Kai dai ka saba zuwa gidan mutane da farar safiya, badan yara zasu makaranta ba ka sanai ban tashi ba." Ya sauke numfashi ya kalle ta yace, "Lokacin da nake dashi kenan. Duk kin lalata gidan ki da wannan khamshin mai sakawa mutane ciwo." Tayi dariya tace, "mijina yana so nima ina so."


Ya taɓe yace, "ina jin ki, ya zamuyi da Mummy?." Tace, "kai da gaske akwai wacce ka ke so ɗin?." Kallon ta yayi kafin ya girgiza kai yace, "da gaske, lokaci nake jira aje ayi magana a gidan su." Yaya Farida tace, "kasan meye mafita a lamarin nan?." Ya girgiza kai alamun a'a tace, "Hajiya kawai zaka je ka samu kayi mata bayanin abinda yake faruwa, itace gaba da Mama ita kaɗai ce zata ne a bar maganar nan kuma dai an barta."


"Nayi tunanin hakan, amma bakya ganin in na samu Hajiya da maganar ran Mummy bazai ɓaci ba? Zata yi fushi dani sosai." Farida tace, "da wannan gaskiya, Tunda dole zata san kai ne kaje ka faɗa mata zata ga ka tsallake abinda take so ne." Bebi yace, "kin fahimta. Abinda ya kamata ayi ke kije wajan Hajiyar, ki yi mata bayanin komai don wallahi in na aure Rumana na cutar da ita na cuci kanta, bazan iya kallon ta matsayin mata a wajena ba saboda ta riga ta fita daga raina gabaɗaya. Zuwan ki zai fi nawa sauƙi a wajan Mummy, in ni naje sai tafi fusata."


Farida tace, "Anjima in na dawo daga aiki zan biya wajan Hajiyar. Nima bana goyan bayan auren ka da ita wallahi, da farko ai kowa yana so, da taga ɗan hamshaƙin mai kuɗi ai guduwa tayi ta aure shi ko shekara auren bai ba ya sako ta. Amma ban san meyasa Maman ta dage a kai ba, bata ganin itace ta guje ka da farko." 


Ya sauke numfashi yace, "Yanzu dai kije kiyi magana da Hajiya yadda ku ka yi ki sanar dani" ya faɗa yana tashi tsaye itama ta tashi tace, "ji mana, baka faɗa min a ina aka samo matar ba." Ya kalle ta yace, "mu gama da wannan case ɗin tukunna, sai mun yi waya" yana faɗa ya wuce ya shiga mota tayi dariya ta koma ciki.