BAYA DA ƘURA

027

by @nanahaleema11

*BAYA DA ƘURA.*

Fitattubiyar2025


          ©️Nana Haleema.


Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11


*BOOK 1*

*Page 027.*


Sai da yayi sallar i'sha sannan ya shiga gida, yunwa yake ji matuƙa domin tun da yaci abinci da safe a office bai sake ci ba. Yana shiga wajan Mama ya same ta a zaune ranta a ɓace matuƙa amma bai kula da yanayin ta ba ya wuce kitchen yana cewa, "Mummy yau bamu gaisa ba, na dawo kuna bacci zan fita bakya nan sai yanzu." 


Jin tayi masa banza yasan akwai wani abun ya dawo da abinci a hannun sa ya zauna yace, "Barka da dare Mummy." Bata amsa ba bata kuma kalle shi ba, sai ya kalli Mimi ta masa magana da ido ya kalli kausar itama ta masa alama nan ya fahimci akwai damuwa.


Ya kalli Mimi yace, "Akwai abinda ya faru ne?." Kafin Mimi tayi magana cikin fusata Mama tace, "tambaya ka ke bayan kasan abinda ka aikata?." 

Yayi sak yana tunani kafin yace, "Wallahi Mummy ban san abinda yake faruwa ba, a asibiti na kwana da na dawo ko baccin five hours ban samu ba na koma ban dawo ba sai yanzu."


"Amma da haɗin bakin ka aka je aka samu Hajiya akan maganar Rumana ko?." Gaban sa ya faɗi dan shi ya manta ma sunyi haka da Farida dan ko waya basu yi da ita ba shiyasa bai tuna ba.


 Ganin yayi shiru sai ta sake fusata sosai tace, "Tunda aka yi maganar nan ban sake ganin ka ba sai yanzu da yake kasan kayi laifi, ai ka kyauta Adnan ni zaka haɗa da mahaifiyata ko?." Bebi yayi shiru kansa yan ƙasa tace, "ni zaka tura a kai ƙara wajan wacce ta haife ni saboda ina so ka auri Rumana kai baka so?, duk da na nuna maka ina so hakan bai saka kabi ra'ayina ba sai da ka tabbatar kabi hanyar da za'a dakatar da hakan duk da burina ne, ka zaɓi wata daban a kan farin cikina."


Bebi a raunane ya sakko daga kan kujera ya zauna kusa da ƙafar ta yace, "Don girman Allah ki yi haƙuri Mummy, wallahi ba haka nake nufi ba. Allah ya sani bana......" Mam ta fusata sosai tace, "Wallahi bakin ka ya furta baka son Rumana sai na tsinke fuskar ka da mari, in kana musu kuma ka cemin baka son ta kaga aiki da cikawa Adnan."


Tsitt yayi ya sunkuyar da kai ƙasa Mama tace, "ni zaka dinga kallon ido kana cewa baka son jinin ƴar uwata wacce muke uwa ɗaya uba ɗaya Adnan?, ni ka ke kallo kana ce min baka son yarinyar da na raina a cikin gidan nan?, ashe ko da gaske baka son nata baza ka iya yi kin kara ba taci albarkacina ka aure ta?. Inda ina da wani ɗa namijin ba kai ba zan saurare ka ne Adnan?. Kai kasan bazan bi ta kanta ba, dan kai duk yadda mutum ya kai ga yi maka abin kirki baka gani."


"Ku ka haɗa kai da ƴan uwan ka aka je aka a samu mahaifiyata akace wai baka son Rumana na tilasta maka sai ka aure ta kai kuma baka so, sannan wai ita lokacin da tace bata son ka an ƙyale ta amma kai yanzu an kasa ƙyale ka. Ashe zaman namu da rashin darajar da bani da ita a wajan ka har ya kai haka Bebi?." 


"Ki yi haƙuri" ya furta a hankali zuciyar sa tayi rauni sosai. tayi tsaki tana girgiza kai tace, "haƙuri ai ya zaunar min dole saboda ka haɗa ni da wacce ta isa dani, Tunda ni ina jin maganar ta dole nayi abinda tace. Kai da baka jin tawa ai tsallake abinda nake so kayi ka kai ƙarata wajan uwata. Kaga nima da bana jin maganar ta irin ka da baka jin ta uwar ka sai naje na samu na sama da ita na faɗa masa shima yaje ya yi mata magana."


Shi wallahi gabaɗaya ma komai ya fita daga ransa jin Mama tana faɗa tana cewa bata isa dashi ba, duk sai yaji nadamar abinda yayi ga dabaibaiye shi, ji yake ina ma bai kai kansa wajan Manal ba, ina ma ya tsaya akan Rumana ɗin kamar yadda Mama take so?. nan take yaji zai iya auren Rumana duk da baya so.


"Hajiya tace kar na sake yi maka maganar auren Rumana na barka ka auri wacce ka ke so kamar yadda aka bata dama, zanyi hakan saboda bin umarnin wacce ta haife ni. Sannan zan baka umarni a matsayina na mahaifiyar ka nima, in zaka bi kanka in baka bi bana kan ka, sai kaje ka zauna da wacce ka ke so ɗin tunda ka zaɓi soyayyar ta akan farin ciki na." Da sauri yace, "kiyi haƙuri Mummy, ki yafe min don Allah, ko me kike so zanyi."


"Baka da adalci wallahi, ka san irin kukan da Rumana tayi da maganar nan taje kunnen ta? Kaga yadda ta shiga tashin hankali saboda kai?. Duk wannan bai nuna maka tayi nadamar auren wani da tayi ba kai ba Bebi?, Kai kaɗai ake yiwa laifi ne a duniya? Meyasa baza ka haƙura ba?, meyasa baza ka yi tunanin daman Allah yayi sai ta auri Jawad ba kafin kai? Baka san ƙaddara ba?."


Yayi shiru bai amsa ba dan Mama tayi zafi sosai shirun yafi alkhairi. Mama ta sake cewa, "tunda haka ka zaɓa na amince ka auri wacce ka ke so kamar yadda uwata tace, tace na saka maka albarka a auren zan kuma yi hakan. Amma ina so ka sani sai dai ka auri mata biyu a rana ɗaya." 


Da sauri ya kalli Maman suka haɗa ido ya sake sauke kai ƙasa tace, "in kuma ba haka ba, naji ka fara auren wacce kake so ɗin tunda umarnin Hajiya ne, amma ina so ka sani shekara ɗaya na baka kai da ita ku gama zaman ku, da zarar ranar da aka ɗaura auren ku ya dawo anyi shekara ɗaya a wannan ranar Rumana zata shigo gidan ka matsayin amaryar ka. Ko ka yarda, ko kar ka yarda haka za'ayi, in ba haka ba kaje ka auri wacce kake so ba da albarka ta ba, sannan bazan taɓa kaɓar ta matsayin sirikata ba."


Da sauri ya kalle ta yace, "na amince Mummy, Allah ya wuce zuciyar ki, ki yafe min ɓata miki ran da nayi. Na amince da hakan Alalh ya nuna mana lokacin, Allah ya sa muna da rai da lafiya."


"Kar ma ka amince mana Adnan, kar ka amince ka nuna min budurwar ka ta fi ni."

"Har abada, ki yi haƙuri, ki yafe min tuba nake." Ta harare shi cikin ɓacin rai tace, "Tashi ka bani waje." 


Ya miƙe a sanyaye yana sake bata haƙuri zai fita tace, "Daga yau duk wani shiri da zaka fara na aure ka dinga yin guda biyu, in lefe ne ka siyi na mata biyu, in ma ginin gidan naka ne ka saka a rushe ya dawo baya ayi ginin mata biyu, in baka da ra'ayin hakan ka tabbatar kana gina inda Rumana zata zauna. In kana ganin hakan bai maka ba Hajiya tana raye."


Juyowa yayi ya duƙa yace, "hakan za'a yi in sha Allah. Ki yi haƙuri." Tsaki tayi ta tashi ta wuce ciki ta barshi a wajan, ya fita jikin sa gabaɗaya yayi sanyi ya rasa abinda yake masa daɗi.


Bebi ya kasa nutsuwa gabaɗaya, a haka ya koma ɗaki yayi wanka ya kwanta dan ya huta. Sai dai ya kasa baccin tunanin abinda Mama tace kawai yake yi, tsakani da Allah ta ina zai iya wani aure bayan yayi aure da shekara?, shekarar yanzu da ba’a wani jimawa sai kaga ta dawo, har yaushe ya saba da matar tashi da zai ɗauko wata ya kawo?. Bashi da abinda zai ce dan bazai ce ba a masa adalci ba Mama ce haka ya dinga saƙa da warwara har yayi bacci.



******* "Wai yanzu akan yarinyar can ka damu haka? Mata nawa ka rabu dasu kafin ita hankalin ka bai tashi ba sai a kanta?." Alhaji Mu'azzam Alhassan ya kalli abokin sa yace, "baza ka gane yadda na ƙwallafa rai akan yarinyar bane, Taya akayi hakan ta faru?, meyasa bata faɗa min aure zata yi ba?."


"Ta gama neman abinda zata samu ta samu ba dole ka neme ta ka rasa ba?."

"Bata yi wannan wayewar ba, ban amince da kalaman ƙawar ta ba dole akwai wani abun wallahi. Ya zama dole kuma na saka a nemo min ko meye yake faruwa."


Alhaji Magaji yace, "ya kamata ka dinga taka tsantsan fa, sunan ka sannen ne a kunnen al'uma, kana da yara da kuma jikoki da mata a gıda. Ka dinga ɗaga ƙafa kodan su." Alhaji Alhassan ya kalle shi yace, "yarinyar bata san waye ni ba, in fact ban faɗa mata asalin sunana ba a fuska ta kawai ta sanni,duk abinda nake yi ina sane bazan yi abinda zai lalatawa iyalan suna ba."


Alhaji Magaji yace, "in tayi maka video fa?." 

"Na faɗa maka bata yi wannan wayewar ba, bata san komai ba ni ne nake ƙoƙarin sanar da ita. Sabuwa ce dal babu abinda ta sani ni nake so na sanar da ita. Taya za'a ce lokaci ɗaya sun bar gari bayan mu haɗu da ita tace min wayar ce ta faɗ? Akwai lauje cikin naɗi a maganar nan."


Alhaji Magaji yace, "ka daina bibiyar yarinyar nan, ka koma harkar Abuja kamar yadda aka saba. Iyalan ka a kano suke, ka daina bin mutane Kano kar ka bar baya da ƙura." 


Ya kalle shi yace, "zan daina da zarar na samu Mubeena, hankalina bazai kwanta ba in ban same ta ba, ya zama dole na saka ayi min bincike a kanta" yana faɗa ya tashi da sauri ya ɗauki waya ya fito ya shiga mota driverm sa yaja suka fita daga gidan.



    A ɓangaren Manal haka ta kwana babu walwala saboda tunanin maganar Mujahid. da safe bayan ta idar da sallar walha wacce ta zamar mata jiki Mama na gefe duk da bata gani amma ta fahimci canji a tare da ita, hakan ya saka tace, "Manal zo nan." 


Ba musu taje inda take Mama ta riƙe hannun ta tace, "faɗa min abinda yake ranki, bakya ɓoye min komai Manal, sanar dani abinda ya faru kika canja haka.” Manal tace, "Mama dama jiya ne da naje gidan su Surayya sai Maman su ta aike mu, a hanyar mu ta dawowa shine muka haɗu wani ya min magana sai na tsaya shine yake cemin shi abokin Dr Adnan ne, kuma wai wallahi Dr Adnan ɗin ba sona yake ba, zai yaudare ni ne daga ƙarshe ya gudu. Kuma Mama na taɓa ganin hoton shi abokin a office ɗin Dr tare dashi dasu Huzaifa. Na rasa tunanin da zanyi Mama, zuciyata tana ganin kamar da gaske ne hakan."


Mama tayi ƙaramjn tsaki tace, "kawai dan kinga mutumin da baki sani yace miki wanda yake son ki ba mutumin kirki bane sai ki amince?."

"Mama har hoton su tare na gani, shiyasa ma na amince da hakan a zuciya ta." Mama tace, "wani lokacin ai baki da wayo Manal, meye abin amincewa da wannan maganar?. Ke kin san inda halin sane baban ku bazai barki har yanzu tare dashi ba?, yayi bincike a kan sa sosai an tabbatar masa da nagartar sa da kuma girmama mace da yake yi a duniya, a cikin labarin da aka bawa mahaifin ki babu zancen yaudara, ance ya taɓa yin wata budurwa amma tayi aure bayan ita babu wata da aka san su tare. Wajan aikin sa da ko ina an tambaya an tabbatar ba’a ganin sa da mace in dai ba mara lafiya ba. Ke kina ganin da yana da wannan halin zai ɓuya ne? In wani bai sani ba wani tabbas zai sani.”


Manal ta girgiza kai tace, "Haka ne Mama."

"Kar wani ya sake kawo miki irin wannan tunanin ki amince Manal, akwai mutanen da suke faɗar gaskiya akwai saboda kar ka faɗa halaka, akwai wanda suke faɗar ƙarya dan su cutar dake ko su cutar dashi. Barin wannan yayi tasiri a zuciyar ki ba abu bane mai amfani, kamar ma baki yarda da Adnan ɗin ba duk tarin girmama ki ɗin da yake yi tun kafin yace zai aure ki.” Manal ta sauke numfashi tace, "Haka ma Surayya tace ban yarda, amma yanzu na amince da batun ki Mama bazan sake ba."


"Yafi miki dai. Ashe da kin fasa auren nasa ban sani ba ko?." Manal tace, "ina tunani dai." Mama tace, "baki da wayo ne Manal, bazan amince a aurar dake babu bincike ba domin naga illar hakan, ko ni da kaina zan fita na bincika Adnan balle da baban ku a raye. Abinda baki sani ba akan Adnan yanzu ya sani shiyasa ya amince dashi ɗari bisa ɗari dan ya tabbatar zai kula dake kula mai kyau. Shiyasa kika ga na amince nima, bai wa dan yana da kuɓi ba sai dan kawai ya cancanci a zaɓe shi. Ni kuɗi ba baƙona bane Manal, babu wani mai kuɗi da zai zo ban amince dashi na bashi ke.”


Sai a sannan tayi murmushi tace, "haka ne Mama." Mama tace, "ko kefa, da kina ta yin tunanin banza da wofi. Ina Mubeena?."

"Tana kwance." Mama bata sake magana ba tayi shiru Manal ta tashi tace, "Mama bara na siyo mana kayan cefane, yau dambu zan mana." 


Mama tayi murmushi tace, "sai kin dawo" ta faɗa tan fita. Tana fita gidan ta ɗauki waya ta kira Dr Huzaifa akayi sa'a ya ɗauka ta saka a kunne tace, "Dr ina kwana?."

"Lafiya lau Manal, ya jikin Mama?."

"Taji sauƙi sosai."

"To haka ake so, Allah ya ƙara Lafiya."

"Amin. Daman tambayar ka nake so nayi don Allah in babu damuwa."


Yayi dariya yace, "Ina jin ki amaryar Adnan." Sai tayi murmushi tace, "Don Allah a cikin abokan ku akwai Mujahid?." Da sauri yace, "an ina kika san shi?."

"Dama jiya ne yazo ya same ni yana min magana akan wai in na amince da auren Dr yaudara ta zaiyi ba aure na zaiyi ba, ya saba yiwa mata haka ba nice ta farko ba Magana dai kala-kala, hankalina ya kasa kwanciya shiyasa na kira ka."


Huzaifa yace, "Innalillahi! Wai kina nufin har gidan ku yazo?." Manal ta amsa Huzaifa yace, "kar ki damu da abinda yace, yana yi ne dan ya raba Adnan da abinda yake so, duk wani farin cikin Bebi baya so, so yake yaga ya jefa zuciyar sa cikin ƙunci baya ƙaunar yaga Bebi yana murmushi a duniya. Wallahi ba ina faɗa miki dan na kare Bebi bane, ina faɗa miki gaskiya ne domin ke kanwata ce bazan miki ƙarya akan abinda yake gaskiya ba, in na cutar da rayuwar ki kaina na cuta. Mujahid da abokin mu ne kafin mu rabu dashi saboda wata ɗabi'a tasa ta banza, Bebi shine yayi silar da aka kwace lasisin sa na zama likita, shikenan ya tsani Bebi yake so ya raba shi duk wani abun da yaga yana so. Bebi yana sonki Manal, babu macen da yake so in ba ke ba na tabbatar da hakan, Mujahid yaga haka ne shine yazo dan ya raba ku Allah bai bashi nasara ba."


Manal ta girgiza kai cikin gamsuwa da abinda yace tace, "na gode sosai, na kuma fahimta.”

“Yauwa ko kefa, ko da zai sake dawowa kar ma ki saurare shi.”

“In sha Allah, Amma don Allah kar ka faɗa masa, kar kayi masa zancen gabaɗaya don Allah." Huzaifa yace, "kar ki damu, bazan faɗa masa ba."

"To na gode." Daga nan suka yi sallama ta kashe sai a sannan hankalin ta ya kwanta dan tana son Bebi itama.