13
by @maidambu41
*❤️🩹SO da CIWO❤️🩹*
®©Ramlat A Manga
Mai_Dambu
Paid book
*Assalamualaikum everyone yau mun zo muku da ingantattun maganin mata daga shahararriyar mai maganin nan De Majestic Aprodiasic best kayan mata ever, We have the best kayan mata 100 natural kada ki zama Bora a wurin namiji kada ki zama koma baya a wurin kishiyoyin zo ki gwada ki yadda babu wacce zata d'aga miki kafada macen da tasan ciwon kanta ita take gyara buje 😆🤣 anayi ana sha'anin arziki*
Muna d ingantatun kayan mata kamar hka:
Maganin sanyi
Exclusive Tsumi
Abulbulo
Gumbar Madara
Gumbar budurci
Zumar budurci
Zumar kacha kacha
Royal Honey
Zumar goran tula
Garin Emergency
Garin kwatai
Sallanta
Dan wata bakwai
Spoil her HQ
Back to virgin set
Exclusive zuma
Tsumin Ayu
Man Ayu
Maniyin Ayu
Zumar Ayu
Gaban Ayu
Kazar Mallaka
Kazar sirri
Zabon Amare
Dan Shila
Ciccibi
Dambun nama
Man power
Yajin Maza
Men energy
Gamu bukatar kayanmu su tuntubi wannan number *** we are the best among the other'
13
"Kyale shi Maman Yara, kyale shi ya sayar da Rayuwar yarinya ba tare da yayi nazari ba. Kyale shi ya lalata min rayuwar yarinya ba tare da ya ajiye min hujjar yin auren ba." Yaya ta mike tana me juyawa. "Wannan shine gatar da zakawa Maamah." Murmushi me ciwo tayi tare da barin parlour itama Mama haka tayi suka bar shi a parlourn shi ɗaya, abin da basu tab'a yi ba kenan, a daren ya kira Jamal da Asma'u ya gaya musu abin da ya faru, yana faɗin. "Kasan Allah xan rabu da iyayenka, ni zasu mai da mutumin banza!" "Baffanmu kayi hakuri, amma suna da gaskiya." Sai da yayi jim kafin ya cigaba da cewa. "Maamah tana buƙatar mutumin kirki ne, hanyar yanzu Maamah bata san me zata yi me kyau ko mara kyau, Baffanmu baka san waye Sharahbil ba ne, shi yasa kake fadar haka amma su da suke da Yara matasa a gabansu sun waye shi!" "Kana bayan iyayenka kenan?" "A'a Baffanmu!" Kashe wayar yayi ya kira Asma'u wato Addah Ma'u. Sai da suka fara magana cikin nutsuwa kai tsaye ta ce mishi. "Taya zasu yarda Baffanmu a dauki yarinya irin Maamah a bawa Sharahbil!? Yaron da kowa yasan irin rayuwar da yake a garin Abuja don Allah Baffanmu ka fahimci dalilai da yasa Yaya da Mama zasu bijirewa maganarka!" "Ya kike so nayi da mahaifina?" Gyara murya tayi kafin ta ce mishi. "Iya biyayya kayi mishi, sannan Maamah kai kanka kasan irin tashin da tai, sannan kowa yasan yarinyar nan nutsasiyayya ce, ka ga idan ka ɗauke ta ka bawa Sharahbil akwai matsala!" "Idan kuna iya hada kai don Maamah ni ba zan iya yiwa Mahaifina haka, nayi Imani idan aka daura auren ta zauna da shi zai daina!" "Baffanmu mazan da suke haka, Sharahbil ba na da ba ne ma yanzu ne, amma zamu barka da duk abinda kayi daidai ne!" Shiru yayi na wani lokaci kafin ya mata sai da safe.
Duk wannan rigimar da ake yi ni dai ban sani ba, domin tun lokacin da na mari Sharahbil na manta da wani batunshi, yadda na alakanta haka da baya gaba na ne, sannan maganar aure da ake yi ni dai bana ce ba, kawai abinda na sani shi ne ni da Baffanmu muna son auren, sannan yadda zaka fahimci abin bai sha min kai ba, shine yadda nake hidimata kawai nake.
Duk wannan tashin hankalin da ake akan auren Maamah da Sharahbil, Aunty tana cikin me kara rura wutar inda take kaiwa Alhaji Datti kome da yake faruwa a cikin gidan, zaka sha mamaki a inda take samun labarin, Masu aikinsu Yaya mata biyu ne, Inna Sabuwa wacce ta kasance mai musu tuwo, a bakinta Aunty take jin labarin kome, saboda aunty tana bata yan kudin da bai taka kara ya karya ba. Wannan abin Yaya tayi ƙoƙarin cusawa kanta hakuri da son auren amma ina ta kasa, ba wai don tana adawa da shi ba ne, kawai abinda ta sani tana gayawa Allah kukanta kuma tasan shine zai kawo mata dauki, Hakazalika Mama itama tana kokarinta. Sai dai wani ikon Allah lamarin kara ta'azzara yake sosai, domin ko jiya da dare Salim ya kaiwa Yaya wasu video da aka tura mishi, hankalinshi a tashe wayyo Allah idan hankalin Yaya yayi dubu sai da ya tashi, haka yasa ta nufi bangaren Baffanmu. Ina zaune ina kallon wani Turkiyya drama wato Layla, hankalina ya tafi ga can, yau na lura daga Mama har Yaya hantarana suke,.saboda na shirya zan tafi gidan gyaran jiki Mama ta ce ba zan je ba, na zauna a tsakar gida nayi ta kuka har sai da Hamma Abdulkarim ya shigo ya ga halin da nake ciki ya ce na taso ya kai ni, ni kuka na Baffanmu ya kashe kudi a ce ba zan je ba. Ai ba zai yiwu ba wallahi ba zai kashe kudi a banza ba. Wannan takaicin da na gunsa musu yasa ina dawowa suka kore ni dakina. Kuma sun san dakina babu tv. Haka yasa na koma na roki Mama ta bar ni matar nan ta rufe idanu ta min fada tare da cewa na shigo mata daki sai ta karya kafafunawa masu kama da muciya, shine na wuce bangaren Baffanmu yana waya na nuna mishi tv ya gyada min kai, na saka ina kallon kasancewar ina fahimtar larabci sosai, mayarwa ce bana iyawa amma ina fahimtar abinda suke fada.
Idanuna yana kan Tv ta shigo, nan ina fushi ko inda take Ban kalla ba, na cigaba da kallo. "Wai meye haka Abidah!" "Maganar auren nan ne za a dakatar!" Ta fada cikin fushi. "Akan me?" Ajiye mishi wayar tayi, "wannan iya hoton kenan ban nuna maka idanun ba ka cewa Alhaji Sani ya turo dansa yazo gidan nan ayi musu test!" Gyara zaman medical glass dinsa yayi ya ce mata. "Akan ke wacece?" "Akan ni uwar Rahmah!" Ta fada kamar yadda yayi maganar. "Ok ban lamunce ba, ayi auren koma meye daga baya za a magance." "Are you kidding me?" Ta tambaye shi tana mishi kallon zancen kake so. "Nayi kama da sa'anki? Kin san dai na baki akalla shekaru goma sha biyar!" Cikin nuna ko oho ta ce mishi." Wannan kai ta dama auren nan idan ka ga anyi shi tow Yaron nan ya zo an yi mishi gwajin akan idanuna ne bayan nan wallahi billahi azim koda akan auren zaka sake ni ba za ayi shi ba!" "Abidah!" "Imamu!" Ta kira sunanshi, jikina ne ya dauki rawa, duk kunyar Yaya yau har kiran sunan Baffanmu tayi. "Innalillahi wainnalihir rajou!" Na fada jikina kamar an watsa min kankara domin kerma ko ina na jikina yake har hantar cikina "Kika ce haka?" "Akan Maamah rayuwata zan bada idan zan fanshi nata, karamar yarinya ba za hada ta da masifa a dawo ana danasani ba!" Ta fada a masifance, "na rantse da Allah wani." Shiru yayi ganin yadda na mike jikina yana rawa, "get out of my sign!" Juyawa tayi zata fita ta riko hannuna, tirje mata nayi ina girgiza kai alamar a'a kwad'a min mari tayi akan fuskana, take sai ga jini yana zuba a hancina. "Abidah kina kokarin Crossing limit ɗinki!" Juyawa tayi a fusace ta d'aga rigar jikinta, wani babbar mark ne da ya kwanta a farar fatarta yayi wani dabbare ta ci mishi! "Look at this mark ya zame min unforget mark har na koma to Ubangijina ba zan manta da shi ba. Dan uwanta ta fita gawa ita kuwa rayuwata ta bukata, da san zamu wayi gari akan nima mata abokin rayuwa mu samu matsala da kai, wallahi da na zabi yadda taso, anan ta saka kanta! Har yau idan wurin ya tashi da ciwo ina jin shi gaya min Imamu me na bukata? Na tab'a shiga tsakanin auren Yaran gidan nan ne? Da ana raka wata y'a gidan miji wallahi billahi azim da zan raka maamah na zauna da ita har tayi hankali, da yau sharahbil shararancinsa bai wuce tunanin my little pumpkin ba da na hakura na barta ta je ta koyi rayuwa babu yan mata ne a zuriar Kawu Datti? Babu yan mata ne a kafatan familyn na rantse maka ni Abidah Shafi'u Yero ba zan tab'a yarda ka kashe min yarinya ba, domin ko infection aka saka mata sai nayi da gaske idan bai hanata haihuwa ba, Malam ka tafi ka kawo shi ya zo ayi gwajin idan ya tsallake ko gobe a daura auren bani da case." Ta ja hannuna muka fita ina kuka, har dakinta ta kai ni ta min zagin zogale zulan zaria, ritsa idanuna nayi ina kuka.
The next morning, Baffanmu da kanshi ya kira Hamma Abdulkarim ya gaya mishi, ba masu ya gayawa Hamma Abdulhameed, baffanmu ya wuce gidan Dattijo ya gaya mishi abinda Yaya ta bukata, nan Dattijo ya hau fada yana cewa ya fahimci Yaya bata son auren ne shi wallahi ya gaji da abin da Yaya take yi mishi Maamah da Sharahbil duk jikokinsa ne ashe kuwa yana da ikon ayi kome ba tare da tashin tashina ba, don haka ya bukaci ganin Yaya, bayan sallah ishe suka tafi gidan tare da rakiyar Hamma Jamal da Hamma Salim da Hamma Abdulhameed da Abdulkarim, taki Umar ya bita tasan halinsa zai yanko magana ne a bata daya goma bata gyaru ba, duk da ba haka taso ba, shima Hamma Jamal diren asubar din yau ne domin ta kira shi daren jiya take gaya mishi zata bar gidan Ubansu idan basu tayata fadar nan ba, tunda suka isa parlourn.Datti Yaya tana zaune a kasa, Addah Mairoh da Addah Zulaiha suna gefe. Baffa Haruna da Baffa Junaid suna gefen Baffanmu, sai Addah Ma'u da Mijinta. Bayan an bude taron da addu'a, Alhaji Datti ya fara magana ya ce. "Na kira ku ne, na muku kashedi na kuma gaya muku ku jawa Abidah kunne ta fita harkan Sharahbil da Rahmah, dukkansu jikokina ne, lokacin da kika nime kashewa Asma'u aure na kyale ki ne." Wani langwabar da kai Addah Mairoh tayi, Asma'u ta ce. "Sau nawa muna zuwa gabanka gashi nan Baban Sajidah ya sauya abinda yake yi ne? Kafin zuwa mu gaban Yaya sau nawa ina zuwa gaban Addah Mairoh me tayi akai? Sabida shi mutum ne." "Husnah!" Hamma Jamal ya kira sunanta, cikin fulatanci ta ce mishi "Jaɓaa kam, Hamma Jamal, mi haala mi yi'a maandeeji ɗi njiɗi hollude en ngonaa ƴiiƴam galle Mawɗo " (Kyale ni Hamma Jamal nayi magana naga da alamu so ake a nuna mu ba jinin gidan Dattijo ba ne!"
Murmushi yayi ya mai da mata da maganar da cewa. "Heddii ko wonaa huunde fotnde ummineede ko fayti e nuunɗal Yaya, nde tawnoo ko jarribo tan waɗata hakkunde jombaajo e jommbaajo Islaam rokki en wiɗtude diine e cellal jogorɗo reseede kadi mo resndata, mi sikkaani so wonaa yahrude yeeso kadi so a ƴeewii ɗum yeru ko e Baffa Haruna "
(Ya isa haka ba wani abu ba ne, da za a d'aga hankali a kai Yaya tana kan adalci, tunda kawai test kawai zaa yi tsakanin amarya da ango, ai yanzu an cigaba ko a church sai pastor ya tabbatar da lafiyar amarya da ango ake aure balle mu da Muslunci ta bamu damar bincike akan addini da lafiyar wacce za a aura da wanda zai aura, ina ga ba wani abu ba ne cigaba ne kuma idan an duba ai misali yana tare da Baffa Haruna) Shiru parlour yayi wato a tsannake maganar da Yaya zata yi ya zama tashin hankali, Kanal Jamal Imam Umar Datti yayi a ruwan sanyi, shiru Dattijo yayi kafin ya gyara murya ya sake murmushi yana faɗin. "Shi kenan Jamal ya nimawa Uwarsa alfarma zan kira Sani ayi wannan abin, idan kuma wani abu ya dawo zan ture duk wani abu za a gane da ni ake zancen." Ko ba kome Yaya ta nuna musu ita kura ce, ta fi gaban a wulantatta, kamar yadda suka shirya mu mata wankin babban bargo. Sai gashi Jamal da Asma'u tare da Abdulhameed da Abdulkarim, har zasu mike Abdulkarim ya cewa Dattijo. "Datti gidan Abdulhameed babu lafiya, Shamsiya tana d'aga mishi hankali, a nawa mahnagar a dakatar da auren zumunci domin dai idan ka cigaba da haka wata rana za ayi samun asarar rai, idan kana tunanin haka shine mafita hada kanmu tow wannan kalaman dai a zaune suke a matsayina na lauya ka ga dole zan tsayawa wanda aka zalunta ne." Ya kuna wayar muryan Shamsiya, tangarar ta cewa. "Na rantse da Allah idan har muka ci gaba da zama haka idan aka samu gawar Abdulhameed wallahi nice, domin nace bana sonshi, yasan cewa Yarana ba na shi bane na saurayi na ne akan me zai cigaba da rike igiyar aurena ya sake ni na tafi nayi rayuwata." Ta fada da karfi tana kara rantsuwa zata kashe Abdulhameed. Jikin Yaya ne ya hau rawa. Tana kallon Abdulhameed da ya fita da sauri. "Karya ne wallahi wannan sharri ne anyi ne don a bata mata suna." "Amma muryan Shamsiya ce " "eh Alhaji!" "Ku tara min su gobe idan Allah ya kai mu!" Addah Mairoh kamar tayi kuka wannan lokaci bai mata dad'i ba, itama Addah Zulaiha, tsoron yarta Fa'izah dasa tayi irin haukar da Shamsiya tayi, har zata fita ta koma can bangaren Yaya, dakinta ta shiga da sallama suka gaisa sama sama,.tsoron abin da zai biyo baya yasa ta ce mata. "Ina Abdulkarim?" "Yana dakin Hassanah!" "Tow sai da safe!" "Allah ya kai mu!" "Maamah babu magana ne!" "Sannu Addah;" na fada ina kallon Yaya da take dame domin, sun biyo ta zasu mata bayani ta d'aga musu hannu, ban san me yasa kwana biyu gidan is messed with some problem, basu shigo ba ina kwance a dogon cushions ina kallon tiktok. Can dakin Mama ta samu Abdulkarim, yana faɗin "ba fa zai yiwu ba ne Mama ni yanzu kara aure xan yi, ba zan iya da auren zumunta nan ba!" "Amma ai kai barista baka da matsala da Fa'izah." "Yes bani da matsala da ita domin tasan limit dinta, kuma bata min gangancin da Shamsiya takewa Abdul domin wallahi ko kwanaki da ta dauki wayata ta ga maganrmu da yarinyar da muke nima, nayi mamakin da ban ga tashin hankali ba, sannan bata kara min magana ba. Ina sane da haka so ban san meye plan dinta ba, amma naga mata gaskiya xan yi aure ta ce Allah ya tabbatar da alkhairi, idan yayi hauka ni bani da hakurin Abdul sai ta dawo gida ina dalili!"jin wannan bayanin yasa tayi baya, tun kafin ta isa gida ta kura Fa'izah ta ce mata kada ta sake tayi wani abu da zai saka mijinta ya korota, Yes yaran Yaya maza ne irin wanda kowacce Uwa zata yi burin da fatar yarta ta aura, suna kashewa mace kudi, sannan suka yiwa mace hidima ga tattalin iyali domin kuwa kullum cikin musu hidima suke daga sutura har abinci, kuma abin burgewa Idanun Yaya baya kan Yaranta maza da iyalansu kawai ita kowani bangaren tana tsaye akai imma ta surukanta ko Yaranta.
Haka washi gari aka zauna meeting Shamsiya sai da idanunta ya rena fata, domin Datti ya saka an kwashe kayanta anje anyi musu test, ana jiran ya fito da kanshi ya zabi asibitin ya kuma kira Manager na asibitin ya danga mishi amanar test din,.yadda kowa yake fusace yasa shamsiya ta sha mari a wurin Yayanta, mijin Addah Ma'u Baban Sajidah. Datti ya ce kowa ya je Addah Mairoh ta tafi da yarta da Yaran, cikin kuka Shamsiya ta ce mishi. "Datti wallahi Yaranshi ne nayi haka ne don ya saki ni!" "Abdulhameed! Ni na baka auren Shamsiya ko? Ka sake ta." Kallon Abdulhameed Mama tayi don Yaya taki zuwa haka kawai take jin kamar wani shiri ne, zasu iya amfani da hakan domin yakar Yaya. Don haka tace matukar aka bashi zabin rabuwa da Shamsiya ya ce yanzu ya fara aurenta kuma Yara ko ba nashi ba ne ya riko su, domin yau da safe Dadah ta shigo mata da wani zance mai nauyi kuma ta bata hakuri, sannan ta gaya mata ba iya ita ɗaya ba ce bata son auren sharahbil da Maamah har itama bata son auren saboda akwai abin da yake faruwa da matuƙar taji abin ba zai yi dadi ba.
Haka yasa ta bawa Abdul din shawara, abin mamaki ya ce musu. "Nifa ina son Matata dari bisa dari, Yaranma ina sonsu Aure ya bani ikon rike su." Kallonshi Datti yayi ya jinjina kai, ya ce su tafi gida zai nime su. Haka suka fito daga karshe Addah Mairoh sai da tazo tayiwa Yaya godiya.
Anyi haka da kwana biyu Datti ya kira Alhaji Sani ya gaya mishi abin da yake bukata, nan hankalinsa ya tashi ya manta dole a bukaci takardun shaidar lafiyar Yaron, don haka yayi ta kame-kame, don haka ya lallaba Datti da wasu mahaukatan kudi akan sharahbil baya kasan ya tafi cotonou idan ya dawo kafin bikin zasu kawo shaidar lafiyarshi.
Ita kuwa Yaya ta rantse ko zata mutu ta dawo ba zata yarda da wannan auren ba, domin a cikin kwanakin Datti ya kira Baffanmu ya ce kada ya kara jin maganar check up, don Iyayen Yaron sun tabbatar da lafiyarshi lau...
***
Rano
Jikin Ma'aruf fa yaki dad'i domin wasu kananun cututtukan sunyi yawa a jikin Yaron, abin tausayi Ibrahim da Ayuba sun zo sun ga jikin Yaron a ranar Lantanah tayi wani irin Nadama domin kuwa su da take zagi yau sune suke taimakonta idan ka cire Matan gidan da suka hade kai suka ki zuwa ganin jikin Yaron......