BAYA DA ƘURA

030

by @nanahaleema11

*BAYA DA ƘURA.*

Fitattubiyar2025


           ©️Nana Haleema.


Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11


*BOOK 1*

*Page 30*

    


  Abban su Bebi lokacin da ya shiga gida Mama ya kira a waya yace tazo da yake yamma tayi sai ta tafi da abinci ta kai masa ta ajjiye ta zauna kamar yadda yake a zaune shi da Mamy tace, "sannu da zuwa."

"Yauwa sannu, ya gida?."

"Lafiya lau."

"Ayyuka sun mana yawa shiyasa kwana biyu komai ya sake lalacewa, ku yi haƙuri komai zai wuce da zarar komai ya dawo daidai." 


Mamy tace, "Allah Sarki." Abba yace, "nasan bana kyautawa amma ayi haƙuri, cikin kwanakin nan zan jima a gidan nan in sha Allah." Mamy tace, "hakan yayi kyau, Allah ya daɗa gyara komai." 


Ya amsa da amin Mamy ta miƙe tace, "ina da baƙi zan je na sallame su, in kuma ban dawo ba sai da safe" ta faɗa tana fita. Mama ya kalla ganin wani wajan take kallo yace, "ran ku nasan a ɓace yake dani, ayi haƙuri kawai."


Mama tayi murmushi tace, "Sai yanzu zaka ce ayi haƙuri?. Kudin ƴar ka ta cikin ka aka kawo aka saka rana baka san anyi ba, aka kai kuɗin Bebi aka saka rana shima baka sani ba. Wanne irin uba ne kai?, Hakan yana nufin kana sauke haƙƙin da yake kan ka wanda Allah ya rayata ya maka kenan?. Yanzu da babu ƴan uwan naka haka yaran zasu zauna basu da wanda zai shige musu gaba a lamuran su?."


Ya sauke ajiyar zuciya yace, "duk na ɗauki laifin, kuma za a gyara in sha Allah." Tayi murmushi na takaici tace, "sai da lokaci ya ƙure za'a gyara kenan?. To ina so ka tunda duk abinda ka ke yi mana sai an yiwa yaran ka wallahi, mu ma ƴaƴan ne kamar yadda naka suke ƴaƴa mu ma haifar mu akayi. Ko me ka ke aikatawa a waje wallahi sai an yiwa yaran ka a suke cikin gida koda kuwa ka saka ƙarafuna kayi musu katanga ne, wallahi sai an samu wani ya ɓalle wannan katangar ko da kuwa mai gadin gidan nan ne."


Kallon ta yayi hakan ya saka ta sake yin murmushi tace, "ƴan matan ka na waje, in soyayya ka ke dasu ba don ka aure su ba kana da ƴan mata a gidan nan ai, in ma lalata su ka ke dasu kaima kana da ƴan...." 

"Hauwa wacce irin magana ki ke yi haka? Kina cikin hankalin ki kuwa?" Ya faɗa yana kallon ta a fusace.


Mama tayi Murmushin takaici tace, “Da hankalina nake maganar kamar yadda ka fahimci abinda nake nufi. Mu matan ka mun zama banza saboda kana da wasu a waje shiyasa ka raina mu kana ganin kamar mu ɗin ba komai bane face wanda suka tsufa, kana da sabon jini a waje wacce tsiyar zamu yi maka?. Kar Ka ga dai ina da jikoki a gidan nan ko?, to hakan bazai hana na bar gidan nan ba walalhi, tura ta fara kaiwa bango ƙiris nake jira, lokaci kaɗan kawai" tana gama faɗar hakan ta miƙe ta fita ya bita da kallo hankalin sa ya tashi sosai. Kenan duk sun fahimci yana da ƴan mata a waje ko me? Kenan da gaske maganar ta zata tabbata na wani zai nemi ya lalata masa yara?. Ya firgita sosai da abinda tace hakan ya saka shi saurin kawar da tunanin amma zuciyar sa bugawa take matuƙa.



     **** Maryam kuwa tun bayan abinda ya faru tsakanin ta da Kamal ta shiga damuwa sosai ko wayar sa bata ɗauka, babban tashin hankalin ta bai wuce abinda ya wakana tsakanin su ba in ta tuna hankalin ta tashi yake yi sosai. Yana kiran ta bata ɗauka, yayi message bata reply domin kuwa bata ga amfanin cigaba da kula shi ba, tayi nadamar abinda tayi sosai haushin kanta take ji.


A ranar yayi mata message sama da goma tayi banza bata bada amsa ba, kawai taga an turo mata hoto a ƙasan hoton an rubuta, _Ko dan saboda wannan ki amsa wayata Maryam._ gaban ta yayi mugun haɗuwa ganin hoton ta babu suttura irin wanda take tura masa a lokacin da take gidan sa matsayin soyayya. 


Jikin ta rawa yake sosai, hankalin ta ya kai ƙarshe wajan tashi kallon hotun take yi cikin kiɗima da nadama mara amfani. yana kiran wayar hannu na rawa ta ɗauka daga can ɓangaren yace, "har ni ina miki waya ki daina ɗauka? Na baki haƙuri meyasa baza ki haƙura ba Maryam?." Maryam tace, "Kamal kace min ka goge hotunan nan."


"Akan me za'a goge bayan gashi yayi min amfani yanzu?."

"Kamal ya kamata ace ka goge shi saboda ni ba matar ka bace ba. Barin tsairicina a wayar ka haram ne."

"Zan goge, amma Ina so ki fito anjima ina so mu yi magana."

"Bazan sake zuwa inda kake ba, na daina zuwa inda ka ke, baza ka kuma ganina ba ko me zai faru." Yayi dariya yace, "Maryam kenan, kina so kice kin daina ganina?."

"Na daina ganin ka, na kuma daina zuwa inda ka ke, kuma ka fita daga rayuwata."


"Ni kuma wallahi yanzu na fara jin daɗin rayuwa dake, a baya ji nake kamar ma ban taɓa wata mu'amala dake ba kamar yadda ya faru yanzu. Maryam ki fito mu haɗu yanzu in ba haka ba wallahil azim zan ɗora hoton nan na ki a Facebook da tiktok." Gaban ta ya faɗi matuƙa, ta wara idanu hannun ta yana kan ƙirjin ta saboda rashin hankali. Murya a sarƙe tace, "me ka ce?." Yayi dariya yace, "ai kin ji abinda nace, ko ban saka hoton fuskar ki ba zan saka na jikin ki, ke kina gani kin san jikin ki ne. Kuma zai zaga ko Ina babu inda bazai je ba ke kin san yadda hoton tsaraici yake zaga ko ina, Balle ma da fuskar ki zan ɗora dan babu amfanin kullewa."


Kasa magana tayi shiru hankalin ta ya tashi sosai ta rasa ma abinda zata ce, gaban ta faɗuwa yake yi nadama ta mamaye ta lokaci ɗaya har zazzaɓi take ji. Kamal ya katse mata tunani yace, "in kin shirya ganin hoton ki a social media kar ki fito Maryam, in kuma baki shirya ba zan miki text na inda zamu haɗu ki tabbatar kin je wajan. in ba haka ba wallahi!, wallahi!!, wallahi!!, kin ji uku ko?, sai na watsa hoton nan media, ke kin san ba iya hoto nake dasu ba har videos ina dasu. Videos ɗin ma sun fi komai kyaun gani, saboda....." sai kuma yayi dariya yace, "Na san ma kin sani, Sai na jiki" yana faɗa ya katse wayar. Faɗuwa tayi a wajan jagwab hankalin ta ya kai maatuƙa wajan tashi, me hakan yake nufi...? kenan blackmailing ɗin ta Kamal yake da hotunan tsaraicin ta wanda take tura masa a zaman auren su ko kuma me? Yanzu ya zata yi? Dama zata ɗauka ko haggu?.


Zina zata je ta aikata dashi saboda kar ya watsa hotunan ta?, in kuma bata je ba ya watsa hotunan ta da wanne ido zata kalli yaran ta guda biyu?, da wanne ido zata kalli duniya ma gabaɗaya. Ta daki katifar gado ta dafe kai a bayyane tace, “ya zan yi ni Maryam, ya zanyi?. Aikata zina ko kuma yaɗa hotunan tsaraicina?.”



     Bebi ya fito daga cikin asibiti yana shiga mota Huzaifa ya buɗe gaba ya shiga, Bebi ya kalle shi Huzaifa yace, "ka ajjiye ni a gida please, motata na kai ta gyara sai gobe zan ɗauko." Kana kallon fuskar Bebi kansa ransa a ɓace yake sosai yace, "sai akace maka kuma hanyar da zaka yi zan yi ni?." 

"Ko ba nan zaka yi ba kaje duk inda zaka je ka sauke ni." Ƙaramin tsaki yayi ya ja motar ya bar asibitin zuciyar da zafi take akan ƙaryar da Manal tayi masa.


Suna zuwa bakin layin gidan su Manal ya tsaya ya ɗauki waya yana kiran ta, Huzaifa yayi dariya yace, "sai kace min zance kazo ai, daman kana zuwa da ƙananun kaya ne?." Bai kula shi ba ya kira ta a lokacin tana kwance ciwon marar da take fama dashi duk wata ya dame ta sai kuka take, gashi ita in bata da lafiya dole sai ta ji ta a jikin Mama take samun sauƙi-sauƙi, amma bata son damu Mama saboda bata da lafiya sai ta fito tsakar gıda ta zauna.


Tana wannan kukan kiran sa ya shigo ta duba kamar baza ta ɗauka ba sai kuma ta ɗauka ta saka a kunnen yace, "Kizo Ina bakin layin ki saƙo zan baki." Yana gama faɗa ya kashe wayar bai jira yaji abinda zata ce masa ba. Manaltabi wayar da kallo tana mamaki, bai taɓa cewa tazo bakin layin su ba sai yau, hakan ya saka ta daure ta tashi tunda ciwon bai yi zafi ba ta shiga wajan Mama tace, "Mama wai Dr Adnan ne ya kira ni nazo bakin layin nan zai bani saƙo."

"Saƙo kuma Manal? Meyasa bazai shigo ba?."

"Ban sani ba wallahi."

"To jeki, amma kar ki jima dai kinga dare yayi sallar i'sha za'a yi" ta amsa da to ta saka Hijjabai ta fita zuwa bakin layin.


Hango ta Huzaifa yayi sai ya kalle shi yace, "Wai daman a mota ku ke zance ne Bebi?, gaskiya hakan ba daidai bane tunda kai ma baka so a yi haka da ƙannen ka. Ban taɓa ganin ka bar su suna zance a mota ba, kaima bai kamata ka yi ba.” Bebi ya gaji da maganar Huzaifa a ƙufule yace, "ya ishe ka Malam, in baza ka zauna ba ka fita ban nemi zaman ka ba ko?." 


Kallon sa Huzaifa yayi ganin da gaske ransa a ɓace yake sai yace, "bazan fita ba sai mun gaisa da ƙanwata. Kuma haka zata ƙaraso ka wani ci magani kamar wani boss?.” Banza yayi masa ta ƙaraso gaban motar ta gane motar sa ce amma bata ganshi a tsaye a bakin motar ba. Sai da ta ƙaraso sannan ya sauke glass ya kalle yace, "zaki iya shigowa?." Ta girgiza kai alamun A'a ya buɗe motar ya fito yana kallon wajan da babu jama'a sosai daman layin nasu bashi da mutane.


A jikin motar ya tsaya yana kallon ta itama haka yadda fuskar sa take haka ta ta fuskar take dan ciwon da yake damun ta ba kaɗan bane, jira take taji me zai ce ko mai zai bata amma yayi shiru. Ya kalle ta sosai yace, "abinda kika yi kin kyauta kenan Manal?." Ta kalle shi alamun me tayi yace, "na faɗa miki tun farko bana son ƙarya meyasa kika min ƙarya?."


"Wacce ƙarya nayi maka?" Ta faɗa tana kallon sa da mamaki. 

"Meyasa baki faɗa min Baba ba ƙanin mahaifin ki bane?, meyasa baki faɗa min mahaifin ki bai rasu ba?, meyasa baki faɗa min aura ne kawai tsakanin Mama da Baba amma babu alaƙa ta jini a tsakanin ku?." Gaban Manal ya faɗi sosai ya kalle shi tace, "me kake nufi?."

"Kin san me nake nufi, meye amfanin ɓoyewar?."

"Dakata mana, ni ban fahimci akan abinda kake magana ba" ta faɗa dan taga da faɗa yake mata magana kamar wanda ya haife ta.


"Kin san dukkan abinda yake faruwa, na faɗa miki ƙarya tana sakawa mutum ya fita daga raina lokaci ɗaya amma baki ji ba. Sannan meyasa baki faɗa min yayar ki ba makaranta take zuwa yawo take tafiya?." Da sauri Manal ta kalle shi dan ta gane me yake nufi da kalmar yawo ɗin da ya ce, Ya wara ido aka fuskar ta yace, "eh!. Shi kuma wanda kika ce min yayan ki ne ashe saurayin ki ne, ke a ganin ki wannan daidai ne?, a ganin ki kin kyauta?."


Ran Manal itama ya ɓaci sosai musamman kiran Mubeena da yayi wai tana yawo, kalmar tafi komai ƙina mata rai hakan ya saka a fusace tace, "duk wannan maganar da ka ke akan ban faɗa maka abinda ban sani ba shine ka ke yi?."

"Amma na faɗa miki ai bana son ƙarya,ƙarya tana sakawa naji mutum ya fita daga raina na faɗa miki wannan tun farko ba yanzu ba" ya faɗa cikin fusata sosai yana kallon ta kamar zai dake ta.


A wuya itama take jin ta, daman ga ciwo ga kuwa ɓacin ran da yake faɗa mata ya sake tunzura zuciyar ta, katse ta yace, "I'm higly disappointed, banyi wannan tunanin daga wajan ki ba."


"Duk wannan maganar da kake yi kana so kace ka fasa aurena kenan?, gashi kana maimaita min ƙarya tana sakawa abu ya fita daga raina kenan na fita. To ka fasa mana Adnan sai meye in ka fasa?, fasawar ka bazai hana wani yazo yace zai aure ni ba. sannan kar ka sake kuskuren cewa Yayata tana yawo, Yayata bata yawo duk wanda ya faɗa maka ƙarya yake yi. Dan kawai kana son ka ce ka fasa aurena ka faɗa kan ka tsaye ba sai kazo kana min maganganun da babu su a cikin rayuwata ba. Ka fasa auren sai me? Waye ya ragu ni ko kai?." katse ta yayi ta hanyar cewa, 


"Ai bazan tsaya a gaban ki ina miki ƙaya ba dan na burge ki ko dan wani dalili nawa, ya kamata ki san waye ni." Ganin mutane suna wucewa ana tafiya masallaci ya saka Manal danne ciwon da take ji tace, "ka furta ka fasa aurena sai me waii? Daman ai an gargaɗe ni naƙi ji nace ba haka ka ke ba, ka fasa auren nawa wannan ba komai bane. Wallahi ban da kai ɗin ne ina ganin girman ka saboda abinda ka yiwa mahaifiyata wallahi da yanzu ka fara dana sanin sanin wacece Manal a duniya, ka turo a karɓar maka kuɗin auren ka da ka kawo, ko kai baka fasa ba ni Fatima bazan aure ka ba!. Adnan ka je ka ssmu shugabar masu gaskiya ka aura, ka bar maƙaryaciya mai ɓoye maka abubuwan da ya kamata ace ka sani. Ko baka furta ba na fahimce ka, to na hutar da kai furtawar, ni Fatima Manal na fasa auren ka, ba shikenan ba?” tana faɗar hakan ta juya ta bar shi a wajen dan ciwon marar ya dame ta sosai. 


Da kallo ya bita zuciyar sa na bugawa sosai, ɓacin ransa ya ninka na baya sau babu adadi. kamar shi tayi masa laifi yazo yana faɗa ta dinga yi masa wannan faɗan har da tafiya ta bar shi kamar wani sa’an ta?. Tsaki yayi yana ji a zuciyar sa dole ma ya fasa auren nata!.


End of book 1.


_Tofa ana dara ga dare yayi, ya ku ke ganin salon zai kasance nan gaba?. Shin mahaifin Adnan zai samu galaba akan Mubeena?, to in hakan ya faru wanne irin abun kunya za’a tafka?. Hmm da gaske auren Manal da Adnan babu shi ko kuwa zasu shirya nan gaba?, ya matsayin Maryam da Kamal?, zata amince ta sake aikata zina daahi saboda hotunan tsaraicin ta ko kuwa zata ƙi amince shi kuma yayi posting?. Ya batun Lubna, shin Mujahid zai aure ta bayan ya raba ta da budurcin ta?, anya lubna bata yi gangancin amincewa da Mujahid ba?. To wai wacece Maman Manal ne?, ina mahaifin su Manal yake?, Waye shi?, yana da rai ko ya mutu?. Ya batun Rumana da Adnan? Auren nasu zai yu ko kuwa zai sake bijirewa Mama?. Hmmm kwamachala ɗin kenan._💃🏼😃


_Duka amsoshin wannan tambayoyi suna cikin book 2&3, akwai soyayya, akwai taɓa zuciya, akwwi nadama, akwai dan sani, akwai zallan kishi a cikin littafin BAYA DA ƘURA BOOK 2&3. Zai fara zuwa 20/1/2025 in sha Allah. A arewabooks zai fara sauka daga yanzu zuwa ko wanne lokaci. promo is over za’a biya asalin kuɗin littafin._ ***.