RANAR YABO..!

Eight

by @mommuhseen

*_💔RANAR YABO💔_*



*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*



By

Mom muhsen

&Asaad



Eight



Tunda muka iso daki na canza kayan jikina zuwa na bacci nayi shafa'i da wutiri sai lokacin na samu natsuwar yin adduar danaso inyi dasun a masallaci na kasa,yanxun ma inayi hawaye na zubo mun sbd har cikin raina inajin tsoron hukuncin da Mami zata dauka akaina wannan karon,sbd shekara shidda da zuwana gidan ban tab'a ganin fushi irin wanda tayi ba a yau, na gama na zubo d'an abinci kad'an naci sbd yunwar dare, inajin Merry da jenny suna waya da samarinsu, Sakeena har tayi bacci abunta, gadon na haye najawo duvet na rufa zuwa kirjina,idona ba bacci kwata-kwata sbd tunaninnikan dake cunkushe cikin zuciyata.


Wayata na dauka Ina duba sakonnin what's app dina duk da ba wani chat nake ba yawanci ma duk yan ajinmu ne nake da contact dasu,sai yan gidan su Fadeel suma banda Haleem da Yah Zee ba mai yin chat dani.


Shiga cikin chat din Fareed nayi naganshi online,na duba time karfe shabiyu na dare na duba grps din mu na mkrnta ba fira yake da kowa ba,daman kuma ban tabajin yai mgn ba.


Na masa typing d'in "I'm sorry"


Kamar daman nidin yake jira ya duba sakon,ya jima baice komi ba sai daya mula yasha iska sannan yace, "Im Sorry too"


Na zaro idona ganin abunda yace, sai kawae na masa typing "goodnight"


Ya maido mun da "OK"


Raina a dak'une na aje wayar shi baisan wannan miskilancin nashi haushi yake banba, kuma yafi mun haka in har na masa abunda ransa ya baci akai,bansan yaushe bacci yazo ya sace ni ba.

********

Washe gari tun seven muna class muna karatu anayi ina hamma sbd bacci ke idona sosai jiyan nan ban samu isashshen bacci ba, sama-sama ma nake daukar karatun a kaina.


"Ina ganin mu tsaya anan karfe biyu sai mu sake had'uwa naga wasu kamar basuyi bacci ba jiya"


Kowa ni ya kallo sbd sun san dani yake,na sha murr daman kuma koda nazo ban gaisa dashi ba,kuma ban kalli fuskar sa ba duk da inajin idonsa akaina.


Kafin ma kowa ya fita na riga su tashi damn doguwar hijab na zumbulo har kasa saman kayan baccina riga da wando,can nesa na tsaya na jira Su Sakeey karar wayata naji na duba wayar naga shine ya mun text,


_“goodmorning Rabee'atu”_


Tsaki naja na kyalesa na daina kallon ma inda yake sbd daya fito daga class din tsaye yai ya rungume hannu yana kalloni, saida su Sakeey suka iso Jenny tace,


"Nifa bangane wannan abun ba?"


"Nima Ina bukatar karin haske"


Cewar Merry suna kallona, nai kamar bansan mi suke nufi ba, Sakeena tace "Kunga, abunda ba ruwanka dadin kallo gareshi sadda zasu shirya ba zaku sani ba, yanzu inkuka shiga zakuji kunya"


Na Mata wani kallo nace, "Har wata alakace tsakanina dashi da har in aka shiga tsakaninmu za aji kunya?"


Tab'e baki tayi tace "Aa malama karki huce haushinki kaina, gaya can maza kije ki huce kanshi don nasan shine ya b'ato miki.........jikkar hannuna na Maka mata ta falla da gudu tana dariya, tana cewa da d'an karfi "zaku gama gulmace-gulmacen ku daga karshe kowa ya bayyana abunda ke zuciyarsa"


Idona waje nake binta da kallo sbd dakarfi tayi mgnr wanda hakan ya tabatar mun da Yajiyota, cikin sauri na waiga na hangeshi shida Jamil jikin motar Faa d'in, dariya naga Jamil nayi Fareed ya kai masa duka yana gocewa.


Aiko da mukazo daki tasha duka da filulluka saida karfina ya kare na hkr na kyaleta, mukai wanka muka zauna yin breakfast kasancewar Sakeey tazo da komi na buk'ata haka su Merry, koda ba addininmu daya ba bama nuna kyama agaresu saidai abubuwa da dama muna kokarin kiyayewa sbd martabar addininmu,bacci na koma wajen ten lokacin baccin da ko minty sha biyar banyi da fara shi ba kiran Daddy ya shigo wayata idona a manne na duba wayar ina ganin kiran saidai na nemi baccin na rasa, cikina ya hautsina na dauka cikin faduwar gaba......."Daddy Ina kwa......kizo gida yanzun nan inason ganinki"


Wayar ta silale k'asa idona a rufe,Sakeey ta kalleni tana daga bisa gadonta tana danna system tace, "lafia"


"Daddy ne ke kirana"


Na bata ansa cikin raunin murya, ta rufe system din tace tashi muje daga can muje Shopping Abbie ya turo mun kudin siyayya dazun"


Kai na jinjina mata na sauko na shiga toilet na wanke fuskana nafito na gyara jikina, text d'in Faa na gani na duba yana cewa "kin sa an kaini station sbd shi thank you"


Zuciyata saida ta doka da wannan sakon,wanda na rasa fahintar sa sosai haka muka fito nida Sakeey duk bana cikin natsuwata, Shopping din naga mun fara nufa na kalleta da kallon ya haka?


"Na fahinci inhar mukaje gida yanzu karshe a harzik'a miki tunanin da bazamu iya zuwa siyayyar ba"


Kasa cewa komi nayi haka mukaje babbar supermarket din da Daddy ke kaimu muyi siyayyar Salla in tataho,inhar dashi zamu fita to nan yake kawomu mu dauki komi mukeso.


Koda mukazo wajen biyan kudi kawai gani nayi anyi mana packaging kayan anbamu bayan sun duba komi da kudinsa, kasa hkr nayi na kalleta da muka dauki hanyar gidanmu, "Sakeey banfa gane ba?taya zamuyi siyayya kuma ba mu biya kudi ba mutaho"


"Fareed nima ya sanya ni kuma kaf kayan nakine yace kar inbari ki sani,"


Fuskata na ya mutsa Ina cewa, "kimun yadda zan gane malama"


"To supermarket din ta baban shine,duk kudaden da ake kashewa a wurin account dinsa suke zuwa, so no need to pay don ya sani munyi siyayya a wajen"


Bakina ma wlh ya rufe na rasa abunda zance, na sake juyawa na kalli uwar siyayyar ban san sadda nace, "Sakeena bazan anshi koda tsinke a cikin kayan nan ba,ina zan kaisu?miyasa zaimun haka?nace masa ina buk'ata ne?"


Hankalinta kwance tace, "Ba abunda za a maida a ciki wlh, ba rok'a kikai ba ganin damarsa ne yai miki alheri duba da irin abunda Fadeel ya miki cikin mutane akan kina cin arxikin babansu"


Hawaye suka zubo mun nace, "miyasa zai damuni haka to?Sakeey miya shafeshi da issue dina da Fadeel har zai sanya kanshi ciki, ko kinsan text ya mun wai nasanya an kaishi Station"


Hankalinta na kan tuki tace "Babu laifi don ya nuna damuwarsa akan ki Bia,sannan babu laifi don ya shiga case dinki da Fadeel domin kina bukatar guiding na namiji inba haka ba Fadeel saiya hanaki shan ruwa a cikin mkrntar nan"


"Sannan KO rantsuwa nayi bazan kaffara ba Daddy bazai iya shari'a da Fareed ba,domin mahaifinsa Shine *PRIME MINISTER* na kasar nan..........What!"


Na fada cikin dimauta da yadda mgnr ta shigeni, "Babu ta inda Fadeel zai iya cin nasara akan Fareed ta KO ina, duk wani gata da yake tak'ama dashi Fareed ya fishi domin shi shikad'aine namiji kwalli daya tal a wajen iyayensa kuma suna son shi fiye da komi a duniyar nan,yayyensa uku mata shine karaminsu kuma shikadai a wajen uwargidan Prime minister, kinga kuwa babu ta yadda za'ai Daddy ya iya shari'a dasu, illa iyaka ayi katanga tsakanin su sbd gaba"


Bakina na ma ya bushe sbd na sakeshi bud'e tsabar mamaki,haba shiyasa Fareed yasha banban da kowa a mkrnta,komin sa na daban ne mgnrsa tafiyarsa komi da komi nashi na daban bane, tun daga kamewar sa da isarsa da miskilancin sa zaka San cewar d'an babban gidane, ashe ashe sukeda k'asar ma?


Mun shigo compound din gidan naji zuciyata ta doka na kalli sakeena nace, "jinake kamar karna shiga a tsorace nake sakeena"


"Kiyi addua kafin kishiga sannan kishiga kina yin adduar Allah bazai basu damar cutar dake ba"


Jinjina kai nayi muka fito na ga motar Anty fadeela hankalina ya sake ta shi, wannan matar masifarta yawa ne da ita haka dai nayita furta Hazbiyallahu wani imal wakhil har muka shigo Babban falon, Tsaye na iske daddy Mami na zaune tana jijjiga k'afa, Fadeel kwance cikin three siter daga yadda yai kwanciyar kad'ai ya nuna idonsa biyu,Haleem na nan Heedaya ma haka har ma Yaya Zee kenan duk danni akai wannan zaman?


Assalamu alaik...........Shak'ar da Anti Fadeela ta kawo mun ta sanya sallamar koma wa cikin cikina,ta makani ga bango tana bala'i "Shegiya yar iska Tsintacciyar mage wacce bata mage..........FADEELA!!!"


tsawar Daddy ta cika falon wanda Shakar da tayi mun bai hana tsawar rikita dodon kunnena ba, "Idan Hannunki ya sake kaiwa jikinta Sai na.......Sai kayi me?Nace Naseer sai kayi mata me?zaka tsine mata ne sbd Bare? Ashe lalacewar har takai ka K'i naka kaso na wani?Yarinyar da tunda ta shigo rayuwar mu bamu zauna lafiya ba dakai ba?rabon da kayi mu'amala damu kamar baya tun kafin zuwanta cikin mu, wane irin so kake mata da har baka baka iya ganin laifinta iye?kaff y'ay'anka ba wanda ya tab'a dalilin zuwanka station ba sai ita, na rantse da Allah daya halicceni.......saurin rufe mata baki yayi yana girgiza mata kai yana cewa, "A gaban yaranmu muke,karkiyi abunda zai jawo mana dana sani,ki bari inyi mgn da Rabi inji dalilin faruwar komi,sbd na tabbata ba zatayi wani abun don cutarwa ga D'an uwanta......Allah shi kyauta masa yai yan uwantaka da waccen mujiyar,Naseer ka daina wani boye-boye"


Shiru tayi duba da irin kallon da yake mata wanda yasa dole ta rufe bakinta badan ta shirya ba, jiyowa yai gareni kaina k'asa jikina na rawa muryar sa ta dishe yace, "Zo nan Rabibi"


Kafafuna na hard'ewa na isa na durkusa gabansa,shima ya zauna ya danne duk bacin ransa yace "ki natsu mgn zanyi dake"


Bakina na rawa nace, "T...to Daddy"


"Daga wajen y'an sanda muka dawo,sbd abunda akaima Fadeel Mahaifiyarsa ta shigar da karar wanda yasa akai mai wannan dukan,sai alokacin ne muka fahinci ko da waye ma kike tare har haka ta fariu, anje an taho dashi bai k'i xuwa ba yaxo saida yaxo muka gane cewar munzo jefa kanmu cikin hatsari D'an prime minister ne muka shigar da kara,nan take aka kashe case d'in sannan suka ja layi tsakanin su,ko ince suka jama Fadeel kunne akan ya daina shiga gonar yaron,domin komi na iya faruwa."


Hawaye kawae nake Ina saurarensa, ya cigaba da cemun "Rabi garin yaya kike alak'a da wannan yaron haka?shin Soyayya kuke ko mi? Da har zai shigar miki gad'a har yasa a dakar mun yaro"


Daker nake jawo mgnr sbd kukan dake kirjina, "Dad....Daddy kayi hkr,don girman Allah kayi hakuri kaida Mami ku yafe mun,wallahi tallahi babu alakar soyayya tsakanina da shi,hasalima duka duka bamuyi wata uku da fara mgn ta fatar baki ba,kamar yadda nake dasu Sakeena haka nake dashi kuma in bacin karatu wallahi Daddy babu abunda ke had'amu,Sakeena da sauran yan grp dinmu sune shaidata sai kuma Allah,"


"Miya faru tsakaninki da Fadeel"


Ina Jan majina na zayyane masa komi tun daga zuwansa wajena har faruwar komi, "kutumar uban caan"


Cewar Mami tatashi tsaye jin cewar na marar mata d'a,bacin ni marin da yasha yi mun Bazan iya k'irga adadinsa ba zuwana gidan, "Wallahi tallahi Yarinyar nan ta gama zaman gidan nan,komi zai faru saidai ya faru amma na gama kwasar bakin cikinta, Naseer yau nakeson ka zab'a koni ko wannan yar iskar yarinyar, billahi kaji na rantse bazan zauna gida d'aya da ita ba"


"Mami wallahi bazakije ko Ina ba,nan gidanki ne kuma kece kike mulkinsa ita din banza ita din wofi,wallahi saidai tabar gidan amma bake ba"


Fadeela ke fada mgnr tana wucewa bangarenmu ta shiga kwaso duk abunda yake nawa tana watsowa waje, "yau dai kitafi wani wajen mu huta uwarmu ta huta, wallahi da raina Mami ba zata cigaba kuka sbd ke ba"


Duk yadda Daddy yake mata tsawa yana mata mgn amma kamar bata da kunne,ya juya ga Mami wacce ta cika tayi famm yana mata mgn cikin fushi amma bata d'ago ta dube sa ba,ganin cewar fushin sa da tsawar sa basa komi sai ya soma lallashinta, "Hussaina Annabi ya hanamu yanke hukunci cikin fushi, kiyi hkr mu zauna anjima inkin sauko zamu sake mgn........"Wallahi tallahi bazan canza mgn ba yau kuma yanzu nake son nasan waye kafiso tsakanin y'ay'ana dani da waccen yar iskar,inhar ka zab'eni kana nufin nidai y'ay'ana ka zab"a inkuwa ka aka samu akasin haka,dagani har y'ay'ana zamu bark......... "Aa Mami,Aa hakaba zata tab'a faruwa ba,Zan....zan barku,zan tafi Mami insha Allahu nida gidan nan har abadan,kiyi hkr ki yafe mun banzo rayuwarku don son raina ba nima tilasta mun akai,kuma daga yau na fita rayuwarku in sha Allahu"


"Rabibi babu inda zaki,Kar ina sake jin wannan mgnr"


Girgiza masa kaina nake Ina kuka sosai inaja baya na rik'e hannun Sakeena gamm kamar Zan b'allata, "Daddy......Dad....Daddy kayi hkr"


Ina fadin haka na fice daga falon da guduna inajin yadda yake kwala min kira amma naki koda jiyowa balle in tsaya, na bude get na fita nai tafiya mai nisan gaske ma samu waje na zauna na sanya kaina cikin guiwata na fashe da wani marayan kuka,Wanda yake tasowa tun daga kasan zuciyaata, ban tab'ajin tausayin kaina irin yau ba shin Ina zanje?


Maiduguri zan nufa in koma kauyen mu?taya Zan iya tafiya gida abunda duk sadda zanje k'afata k'afar Daddy, yai mana visa da komi da komi yakaini ya jiyo,in Zan dawo haka da kanshi zaizo ya daukan mu dawo,to yanzu taya Zan iya kai kaina gida?ya zanyi da karatun da Babana ya kwallafa ransa akai?mi Zan gaya mashi ya fahinta?


Kuka nake sosai Wanda nakejin zuciyata kamar an soya mun ita, zafi nakeji sosai a raina jinake kamar na bude ido inganni gaban Baba.






Mom muhseen✍️