3
*FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*Na ji daɗin yadda kuka karɓi littafin nan tun a farkonsa. Kuma in sha Allahu za ku same shi fiye da yadda hasashenku ya bayar. Masu neman littafaina ga su kamar haka; ABOKIN AIKINA, BAƘON YANAYI, JIKI DA JINI (A'ISHA), AMFANIN FITILA, MAKANTAR SO, DIJE ƘARANGIYA, RUWA DA ƘANƘARA, GIDAN AURE. BAKAN GIZO, ZUBAR HAWAYENA, DAKAN ƊAKA.., MUSAYAR ZUCIYA, TARTSATSI, SHAGALALLIYA da sauran su. Ga mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan lambar; ***.*
*LAMBA TA BIYU.*
Minal ta jima a bayin ba tare da ta motsa ko ɗan yatsanta ba, saboda duniyar ta gama juya kanta. Ta yadda bakiɗaya ta kasa fahimtar mene ne mafita, kuma me za ta yi, sannan me za ta aikata?
Ƙwanƙwasa ƙofar da aka yi ya saka ta dawo cikin duniyar hayyacina, tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya. Zumbur ta miƙe tsaye tamkar an tsira mata allura, ta shiga kokawar buɗe ɗakin tare da ƙoƙarin saita nutsuwarta.
"Kada ki sake ɗaga hankalinki a kan wannan matsala, saboda in sha Allahu haɗinki da shi alheri ne, kuma matuƙar ina raye ba zan bari Jamal ya yi miki abin da ya ga dama ba."
Zancen Hajiya kenan, a lokacin da na buɗe bayin ta riƙo hannuna ta zaunar da ni a kan gado. "Ki yi haƙuri, saboda babu wata kalmar da ta wuce haƙurin nan dai duk da ba daɗi ne da shi ba. Mu za mu je gida, sai da safe idan allah ya kai mu."
Ta miƙe tana dafa kanta tare da jera mata wasu albarkatu cike da tausayin ta a ranta. Ta ƙara yi wa auren kyakkyawar addu'ar da ko a cikin zuciyar Minal ba ta ji za ta iya amsa ko ɗaya ba.
Tana ƙoƙarin barin wurin Minal ta yi hanzarin riƙo hannunta, sannan ta durƙushe ƙasa gwiwa biyu tana ƙoƙarin danne kukan da ke son kufce mata. A haka ta yi ƙarfin halin yin magana a cikin sanyin murya ta ce,
"Don Allah idan kin san dalilin da ya sa Nur ta bar mini aurenta ki sanar da n... saboda ba zan taɓa yafe wa kaina ba matuƙar na shiga tsakiyarta da angonta. Idan kuma har da gaske ta gudu ta bar mini masoyinta a irin wannan rana da ta jima tana dakon zuwanta; zan ci gaba da tuhumar kaina daga yau har ranar da na bar duniya. Ki sanar da ni gaskiya don Allah Hajiya, saboda zuciyata ba za ta taɓa nutsuwa ba matuƙar ban san dalilin da ya sa Nur ta bar mini Jamal ba."
"Hmmmmm!"
Ajiyar zuciyar da Hajiyar ta sauke kenan tare da miƙar da ita tsaye, sannan ta shiga bubbuga bayanta cikin sigar rarrashi. Saboda a lokacin hawaye sun ba ta haɗin kai ta hanyar zubowa ziii suna layi a kumatunta.
"Ko ma me ya sa ta bar miki shi; ki bar shi a matsayin ya wuce daga yau. Don haka ki karɓi mijinki kuma ki kwantar masa da hankali ta hanyar da za ku daidaita kanku ba tare da kowa ya sani ba. Saboda Jamal yana da zafi amma yana da sauƙin kai idan aka biyar da shi ta hanyoyin da yake so."
Jim Hajiyar ta yi tana kallon gefe, yayin da kan Minal yake ƙasa tana shesshekar kuka. Cike da son kawar da zancen Hajiyar ta sake cewa,
"Dare yana ƙara yi Amina, ki yi haƙuri na manta da abinci a mota Amna za ta kawo miki kafin mu wuce. Kuma ki saki jiki ki ci kada ki yi wa kanki horon yunwa. In sha Allahu komai zai wuce kuma za ki ji daɗin zama da shi idan kuka daidaita."
Waɗannan maganganun nata suka sa ta gama sarewa a kan za ta samu amsar tambayar da ta yi mata. Idonta a kan bayansu suka fice daga ɗakin tare da takun saukarsu a ƙasan benen har zuwa lokacin da ta daina jin motsinsu. Ta jima a tsaye inda n'take ba ta motsa ba, kafin ta ja ƙafafuwanta n'ta ɗosana ɗuwawunta a bakin gado. Amna ta dawo da foodflaks a hannunta ta ajiye gabanta cikin sauri ta fice, ba tare da ta ce da ita komai ba.
Shiru ya ratsa falon sai sautin agogon bango da ke ta aikinsa yana harbawa ƙit-ƙit. Hakan ya sa ta cira kai tana ƙare masa kallo cike da mamakin ganin adadin lokacin da agogon ya nuna mata. Karfe ɗaya da minti goma na dare 1:10am, amma ba ta gasgata ba har sai da ta duba ƙaramar wayarta da ke cikin jakar hannunta, a nan n'ta ga zahirin abin da agogon ya sanar da ita babu ƙarya.
Nan take wani sabon tsoro ya shige ta, saboda ba ta da masaniyar ita kaɗai ce a cikin gidan ko akwai wasu mutanen. Saboda ko kaɗan ba ta yi zaton ƙiyayyar da Jamal ya nuna mata ta bar shi kwana a cikin gidan ba. Sai dai tuno akwai maigadin da ke kula da shiga da ficen gidan ta ɗan rage jin tsoron. Amma tabbas ba ta tunanin zuciyarta za ta samu nutsuwa matuƙar ba ta yi ido biyu da Nur ta amsa mini tambayoyin da ke zuciyarta ba.
Hakan ya sa ta shiga ƙwala wa lambobinta kira ɗaya bayan ɗaya amma babu wadda n'ta samu. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi tare da furzar da wani iska mai zafi daga bakina.
Gadon ta sauko ta rafka tagumi hannu biyu, don ta gaji da zaman har ƙafafuwanta sun fara kumbura. Saboda ba ta san ta yi zurfi a tunanin da ta lula ba sai da ta sake duba agogon wayarta ta ga 2:30am ƙarfe biyun dare daidai. Kenan ta kwashe awa ɗaya har da wasu ɗorin mintuna a zaunen ba tare da ta sani ba. Guntun tsaki ta ja tare da Allah wadai a kan abin da ya faru, musamman da ta tuno maganganun Nur a lokacin da aka ce ga motocin ɗaurkar amarya sun zo. Da irin diriricewar da ta yi ta faɗa bayin da ke cikin ɗakinsu har ƙawayensu suna tsokanarta.
Jimawar da ta yi a bayin ya sa Minal bin ta tana faɗin, "Malama ki fito ke fa ake jira!"
Nur ta buɗe bayin tana dariyar yaƙe, domin alamunta duka ya nuna kuka ta yi a cikin bayin, cikin wata kalar murya sassanya ta ce,
"Ba sai kin kore ni ba, na sani yau za ki yi kwanan farinciki."
"Ke fa wata irin mutum ce wallahi, yanzu rabuwa da ke shi zai sa na yi kwanan farincikin?"
Minal ta jefa mata tambayar tana hararar ta cike da jin haushin abin da ta faɗa. "Kwantas Hajiyata, in sha Allah daga yau sai kin jima ba ki saka ni cikin idanuwanki ba."
"Ke dai kika sani, kuma komai za ki faɗa ki faɗa, daga yau dai mun sauke nauyinki a kanmu."
Zancen Minal kenan wanda ya saka Nur juyawa tana yi mata wani kallo mai ɗauke da ma'anoni da yawa. Kamar ta ce wani abu amma ta yi hanzarin tsuke bakinta gum, fuskarta a cure ta bar wurin tana ƙoƙarin saita kanta a lokacin da mata suka cika ɗakin da guɗa.
Wannan nazarin ya ƙara ɗaukar lokaci kafin Minal ta gano kwanan zaune ta yi. Saboda bacci bai ɗauke ta ba sai da asuba ta kawo jiki. Kasancewar ana yanayin zafi hakan ya sa ta ƙara bajewa ƙasan tayis tana nannauyan baccin mai ɗauke da mafarkai kala-kala.
Ba ta tashi farkawa ba sai da ƙarfe 9:11am na safiya. ko shi kiran waya ne ya tayar da ita, a firgice ta farka tana dube-duben da ya tabbatar mata ba gidansu ba ne, kuma da gaske abin da ya faru ba almara ne.
Cike da ƙuncin zuciya ta nufi bayi, saboda kiran ya katse kuma lokaci ya ƙure mata ba tare da ta yi sallar asuba ba. A gurguje ta nemo hijabi a cikin wardrobe ɗin kayan Nur, ta miƙa raka'a biyu ta tofa addu'ar da ba ta san me ta roƙa ba. Allah Ya taimake ta tun kafin a fito da amarya ta yi sallar Isha. Da ba ta yi sallar ba wataƙila tashin hankalin da ya kunno mata kai ba zai bar ta nutsuwar yin sallar a cikin daren ba.
Ta jima saman sallayar da tagumi kafin wani kiran ya sake shigowa cikin ƙaramar wayarta. Muryar Hajiya ta jiyo ta yi hanzarin gaishe ta ba tare da ta amsa ina kwanan da take yi mata ba. Saboda ganin ita ce ya dace ta gaishe ta a matsayinta na babba.
"Ki ƙara haƙuri kin ji! Na aiko miki da abinci ki sauka ƙasa ki karɓa. Kuma ki ƙara haƙuri da yardar Allah komai zai daidaita."
"Babu komai."
Iya abin da Minal ta faɗa kenan saboda bakinta ya yi nauyin da ba za ta iya cewa komai ba. Sannan ta sauke wayar idonta a kan abincin da Amna ta kawo mata cikin dare wanda ko buɗewa ba ta yi ba ballantana ta san mene ne a ciki. Jiki babu kuzari ta miƙe ta ɗauki foodflaks ɗin ta fice, zuciyarta tana jin babu wani abinci da zai burge ta a daidai lokacin. Saboda ko yunwar ma ba ta ji kuma ba ta jin sha'awar cin komai. Amma dole ta isa harabar gidan tana wara ido kafin ta hango maigadin gidan yana nufo ta da wani madaidaicin kwando.
Cikin ladabi ya gaishe ta ita ma ta amsa babu yabo babu fallasa kafin ta karɓi kwandon ta miƙa masa foodflaks ɗin ta juya ba tare da ta ce da shi ƙanzil ba. Tana ƙoƙarin shigewa cikin gidan ta ji sautin maigadin yana cewa,
"Me za a yi da wannan Hajiya?"
"Abinci ne, ka je ka ci."
Amsar da ta bayar kenan ba tare da ta juya ba. Ranta yana tafarfasa ta koma saman ta zauna a kan bedside tare da rungume hannuwanta a ƙirji tana cizon leɓenta. Hawaye ta shiga gogewa a kan fuskarta saboda kanta ya yi ƙullewar da ba ta san ta ina za ta fara ba. Saboda tunanin a wane hali saurayinta yake wanda bai zo a ranta ba sai da safiya ta waye ta tabbatar abin da ya faru babu wasa a ciki. Saɓanin kallon da take yi wa abin kamar shirin da zai ƙare Nur ta dawo ɗakinta ita ta koma gida.
Zumbur ta miƙe, ta shiga watso kayan Nur da ke cikin wardrobe ɗin ɗakin ta shiga birgima a cikin su. Saboda tuno lokacin da take jera mata kayan da hannunta cike da farincikin burin aminiyarta ya cika ta auri wanda take so. Kayan ta shiga runguma tana shinshina ƙamshin turaren Nur da ta feshe mata kayan da shi yayin jera su.
Wani sabon kuka ya zo mata, wanda ta kwashe lokaci tana juya zantuka a ranta babu mai rarrashin ta. Kafin ta ji takun tafiyar mutane yana nufo ɗakin da sautin maganganu sama-sama. Amma ko kaɗan hakan bai saka ta motsawa ba, har aka fara ƙwanƙwasa mata ɗaki ba ta yi magana ba ballantana ta tashi ta buɗe.
Muryar Innarmu ce a gaba kafin ta jiyo muryar gwaggonta Salame, waton ƙanwar Babanta. Da ido kawai ta bi su, ganin salatin da suke yi a kan hango halin da suka iske ta cikin sa.
"Ahir ɗin ki Amina! Wallahi ki kiyaye ni tun muna shaida jun..."
"Dakata Binta, abin fa sai da rarrashi. Kuma abin da kike so ta bi ba zai biyu ta daɗin rai ba. Don haka ki bar mini komai ni zan shawo kan matsalar."
Zancen gwaggonta Salame kenan cikin tausasa murya. Sannan ta nufi inda Minal take kwance cikin kayan Nur, ta kama hannunta ta miƙar da ita tsaye tana faɗin,
"Kwantar da hankalinki Amina, ai ita rayuwar duniya mai sauƙi ce idan aka bi ta a hankali. Yaushe za ki hana kanki zama lafiya a kan abin da ke ma kina da ikon taimakon kanki da kanki? Don Allah yi shiru share hawayenki lamarin duniya ba a yi masa gaggawa. A sannu ake bin komai har cim ma nasara cikin iyawar Allah."
Da waɗannan kalaman Gwaggo Salame ta yi nasarar hana Minal wani kuka, sannan cikin dabara ta zuba mata abinci ta shiga tsakura duk da shesshekan kukan da take yi jefi-jefi. Amma ko kaɗan ba ta son haɗa ido da Innarmu, saboda hararar da take wurga mata kamar ta rufe ta da mugun duka. Bayan ta ɗan ci abincin ta kai ta bayi da kanta ta haɗa mata ruwan wanka ta baro ta, tare da ba ta lokacin da za ta kammala ta fito tana jiran ta.
Minal ba ta ɓata lokaci a bayin ba, ta yi wankan a gaggauce ta fito. Gwaggo Salame ta miƙa mata ɗaya daga cikin kayan Nur da ta gama gyara ta mayar wardrobe kamar yadda suke tun farko. Minal kayan ta kalla sannan ta kawar da kai ƙirjinta yana bugawa ta ce,
"Ba kayana ba ne."
Gwaggon ta matsa kusa da ita cikin ƙarafafa gwiwa ta ce, "Duk abin da kika gani a cikin gidan nan naki kuma haƙƙinki ne. Don A'isha da ta bar miki mijin har da komai nata ta bar miki, tun daga kan kayan ɗakinta har zuwa suturarta."
"Gwaggo kayan Nur..."
"Kada ki ce komai saka kayan kawai."
Ta yi hanzarin katse ta saboda ganin tana so ta kawo mata wasa. Minal ta buɗe doguwar rigar lesin ta saka, wadda ta sha adon aiki mai ɗauke da ɗinki stone work. Sannan gwaggo Salame ta ɗaura mata ɗankwali tana faɗin,
"Ko ke fa! Kin ga yadda kika yi kyawu kuwa? Ma sha Allah ki tsaya a haka kada na sake ganin kuka a idonki."
Nur ta yi marau-marau da ido ƙwalla ta cika idonta ta saka gefen hannunta ta share. Sannan ta zuƙe majinar kukan tana cewa,
"Don Allah Gwaggo ku tausaya mini, wallahi ba zan iya zama a gidan nan ba. Saboda mutane za su zarge ni a kan na ci amanar Nur. Sannan shi kansa angon nata ba zai taɓa karɓa ta a matsayin matarsa b..."
Ohh Allah 😔
D. Auta ce🙋