FANSAR ƘAUNA

4

by @princessdija

*FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA D. AUTA*

*Masu neman littafaina ga su kamar haka; ABOKIN AIKINA, BAƘON YANAYI, JIKI DA JINI (A'ISHA), AMFANIN FITILA, MAKANTAR SO, DIJE ƘARANGIYA, RUWA DA ƘANƘARA, GIDAN AURE. BAKAN GIZO, ZUBAR HAWAYENA, DAKAN ƊAKA.., MUSAYAR ZUCIYA, TARTSATSI, SHAGALALLIYA da sauran su. Ga mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan lambar; ***.*

*LAMBA TA UKU.*

"A hir ɗin ki amina! Wallahi ki fita idona na rufe. Yaushe arziƙi yana kiran ki tsiya tana korar ki da gudu! To ban son shashancin banza, don ke Allah ya bai wa mijin ba A'isha ba, kuma ita da kanta ta bar miki shi ba matsa mata aka yi dole sai ta aikata ba, yo ɓata lokacinki na me za ki dinga yi a kan abin da kina zaune allah ya ba ki ba tare da kin roƙa ba?"

Fusatattun kalmomin Innarmu kenan waɗanda tsabar haushin da Minal ta ba ta ya sa ta miƙe tsaye tana neman hanyar kai mata duka. Ƙur Minal ta kafe ta da ido cike da zargi ta sake cewa,

"Yanzu ya zan yi da Aminu? Wanda kowa ya san yadda yake faɗi-tashi a kaina?"

"Yi mini shiru sakarya! Shi Aminun idan kika aure shi zai ajiye ki irin gidan nan ne? Ki faɗa mini a kaf cikin danginmu waye ya samu arziƙin zama irin wannan gidan? To ba ki isa ki yi mana baƙinciki ba, dole ne ki zauna ko kina so ko ba kya so! An riga an ɗaura aurenki da shi, kuma babu uban da ya isa ya kunce auren nan! Ke ko mutuwa za ki yi sai dai a fitar da gawarki ehe!"

Innarmu ta ƙare maganar tana kumfar baki da zaro wa Minal ido, alamun ƙiris ya rage ta jibge ta don ta gama kaiwa bango a kan lamuranta. Minal ma tsaye take kanta a duƙe tana kallon yatsunta fuskarta a kumbure bayan bakin da ta turo tana gunguni. Tafasar da zuciyarta ke yi ya sa ta yi maganar da take jin dole sai ta amayar da ita ko za a kashe ta. Domin idanuwan da Innarmu ta kafe ta da su ba su hana ta furzar da abin da ke cikin bakinta ba.

"Ni fa wallahi ko kaɗan kuɗinsa ba sa gabanta..."

"Mu su ne a gabanmu! Na ce miki mu su ne a gabanmu ki je ki faɗa wa duk uban da za ki faɗawa. Kuma za mu ci sai inda karfimu ya ƙare, matuƙar muka samu damar cin sai mun ci...ke Amina wallahi na kusa nakasa ki! Ni za ki gwada wa ƙarfin imani da taƙawa? To idan kin so ki ce da mu kwaɗayayyiya ai ba a kanmu aka fara son abin duniya ba. Wawuyar banza ana nuna miki hanyar arziƙi kina runtse ido. Kuma Aminu da kike zancensa a yanzu babu ke babu shi har abada! Saura kuma na ji labarin kin neme shi ko shi ya neme ki ki ga irin matakin da zan ɗauka a kanku. Sakaryar banza sai na shayar da ke gubar mamaki matuƙar ba ki shiga taitayinki a kan auren nan ba....Salame ni na tafi idan kin gama ki same ni waje ina jiran ki..."

Martanin Innarmu ya ƙara lalata nutsuwar Minal, ta kasa shanye zafin maganganun a ranta tun kafin ta dire zantukan, waɗanda ta ji mugun ɗacinsu a zuciya har cikin bakinta. Bayan ta gama kumbura ta fashe da wani kalar kuka cikin ɗaga murya tamkar wadda ake tsula wa bulala. Innarmu tana gama faɗar batutuwanta ta fice daga ɗakin a fusace tana ci gaba da faɗar duk abin da ya zo bakinta cikin faɗan da sautinta yake tashi.

Ajiyar zuciya Gwaggo Salame ta saki mai ƙarfi kafin ta riƙo Minal ta zaunar da ita a kan gado. Jarumtar rarrashin ta ta shiga yi har ta samu ta rage sautin kukan da take yi. Sannan ta yi jim na tsawon mintuna kafin ta yi ƙarfin halin faɗin,

"Kowace rayuwa da kalar tata jarabawa, ke taki jarabawar ita ce wannan. Don haka ki bar wa Allah lamuranki kada ki yi jayayya da ƙaddararki, saboda ba a sani ba ko ita ce alherinki kina ƙoƙarin turewa."

Shiru Minal ta yi ba tare da ta ce uffan ba, saboda maganganun Gwaggo Salame sun shiga jikinta, ta share hawayenta ta koma ajiyar zuciya wata bayan wata. Duk da a ranta ba ta jin ta karɓi cushen da aka yi mata a matsayin ingantaccen auren da ake yi wa kowace mace. Amma kuma ta fi jin daɗin maganganunta a kan na Innarmu masu kama da ana yaƙi.

"Abu biyu zuwa uku nake so ki riƙe gam kafin mu ga kamun ludayin tafiyar." Maganar Gwaggo Salame ta farauto hankalinta wuri ɗaya, ta nutsu tana sauraron ta ba tare da ta yi motsin kirki ba

"Na farko ki yi haƙuri a kan ba a nemi amincewarki ba, amma ki kalli hakan a matsayin gata ne da wasu iyaye suke yi wa 'ya'yansu. Na biyu ki riƙe Ya Wadadu ɗari huɗu bayan kowace sallar asuba, tana ƙara danƙon soyayya da kwarjini bayan farinjini na yankan shakku. Na uku kuma ki lizimci raya dare da nafilolin biyan buƙatu a wurin Ubangiji. Na san kin sani akwai su kala-kala, amma kafin mu je ɓangaren abin da za ki yi ki jawo hankalin mijinki; zan sanar da ke nafilar da nake yawan yi, wadda ni ma na gwada kuma nake ganin amfaninta, saboda ina so ke ma ki amfana."

Shiru ya ziyarci ɗakin tsawon sakonni kafin Gwaggo Salame ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ta ce. "Ki tashi misalin ƙarfe ɗaya na dare zuwa biyun daren, ki yi nafila raka'a biyu kacal kuma kowace ki karanta fatiha da Suratul Ahad, waton surar ƙulhuwallahu Ahad. idan kika sallame sai ki yi wata sujuda kada ki ɗago kanki sai kin karanta La'ilaha Illa antassubhanaka inni kuntu minazzalumina sau arba'in. Kada ki bar sujudar har sai kin faɗa wa Allah buƙatunki. Ina mai tabbatar miki za ki ga aikin addu'ar tamkar yankan wuƙa da yardar Allah...."

Kiran wayar da aka yi wa Gwaggon ya sa ta yi hanzarin fito da ita daga aljihunta, ganin Innarmu ce mai kiran; hakan ya sa ta tuno ashe ita take jira a waje. Ta miƙe tana gyara zaman lulluɓinta ta ce,

"Mu za mu tafi, zuwa anjima za a aiko miki wasu daga cikin kayanki, sauran kuma za a raba wa ƙannenki da wanda Allah ya ciyar. Amma don Allah ki tsayar da hankalinki wuri ɗaya ki nemi zaɓin Allah. Ubangiji Ya ba ku zaman lafiya, kuma ki riƙe sirrin mijink..."

Kiran da Innarmu ta sake bugo mata ya sa ta fice da sassarfa ta bar Minal a daskare bakin gadon, don ta kasa motsa laɓɓanta ta yi mata sai anjima ballantana ta raka ta. Bayan idon da ta bi ƙofa da kallo tsawon mintuna da fitarta ba tare da ta ɗauke kanta ba.

***

Jamal kuwa, tun da ya fice daga ɗakin bayan ya gama jaddada wa Hajiya ba ya son Minal. Cikin ƙunar rai ya buga motarsa jikinsa yana rawa ya nufi gidansu. Sai dai kuma Allah ne ya kai shi gida lafiya, saboda mahaukacin gudun da yake yi tamkar an koro shi ko kaɗan ba ya cikin nutsuwarsa. Uban horn ɗin da ya dinga bugawa babu ƙaƙƙautawa; ya sa Baba maigadin gidansu ruɗewa jikinsa yana rawa ya buɗe gidan bayan ya tabbatar shi ne ba gizo ya yi masa ba. Amma zuciyarsa cike da mamakin dawowarsa cikin gidan a daidai lokacin, wanda ya dace a ce yana tare da amaryarsa a matsayinsa na sabon ango mai zumuɗi da daren farkonsa.

Da ido Baban ya bi shi baki buɗe har Jamal ya shige sashen da ɗaƙinsa yake ba tare da ya bi ta kan motar da ya bari a kunne ba, ballantana ya rufe murfi bayan fitarsa. Saboda idanuwansa ko gani ba sa yi daidai ya faɗa ɗakinsa ya datse ƙofa, a sukwane ya isa bayi ya dinga zuba wa kansa ruwan shawa ba tare da ya cire komai na jikinsa ba. Ya ɗauki tsawon minti talatin idanuwansa rufe ba tare da ya yi dogon motsi ba. Zuciyarsa danƙare da ƙuncin da yake haddasa mata bugawa da ƙarfi tamkar ta ɓalle daga mazauninta ta fito ƙirjinsa.

Wata nannauyar ajiyar zuciya ya saki mai ƙarfi, kafin ya fara atishawa wata bayan wata kuma har lokacin ruwan yana sauka kansa zuwa jikinsa. Da lalube ya rufe shawar amma ya kasa ɗagawa daga wurin tsawon mintuna. Saboda zuciyarsa ta ci gaba da hasko masa fuskar Nur tana feshin tsadadden murmushinta har dimple ɗin ta biyu suna lotsawa. Hoton zuciyarsa ya hasko masa ita ne a wani lokacin da suka je yawon shaƙatawa, inda ya ba ta cake a baki tana tauna tana yi masa wani kalar kallon da ya saukar masa da kasala.

"Ya Allah!"

Furucinsa kenan a lokacin da kansa ya ƙara sarawa tamkar an kwaɗa masa guduma. Dafe da kan ya fito yana layi saboda jirin da ke kwasar sa har ya zube kan gado riƙe da kansa yana faɗar kalmar Innalillahi fili da zuciyarsa. Nan take ya fara rawar sanyi jikinsa ya hau fisga babu ƙaƙƙautawa, cikin mintuna kaɗan numfashinsa ya fara sarƙewa, kafin ya yi luf bayan ya gama tari sama-sama yana dafe da zuciyarsa, saboda idauwansa sun gama kafewa numfashinsa ya tsaya cak.

Ya kwashe tsawon lokaci a halin da yake ciki kafin dawowar Hajiya, bayan ta gama neman sa a waya ba ta samu ba. Kuma maigadin gidansa ya tabbatar mata da lalle ya fita. Cikin tashin hankali ta kira maigadinsu sannan ta samu nutsuwar faɗawa mota direban da ya kawo ta ya juya da su zuwa gida. Saboda jin Jamal yana gidan ya rage mata kaso bakwai a cikin goman tashin hankalin da ta afka. Don zuciyarta ta gama tsinkewa cike da tsoron faruwar abubuwa biyu, na farko kada ɓacin rai ya saka shi barin garin ba tare da ta sani ba. Na biyu tsoron kada ya yi tsautsayi ya ja shi ya yi haɗari, don a halin da yake ciki bai dace ya yi tuƙi ba.

Makullin motarsa da maigadinsu ya ba ta tare da yi mata bayanin yanayin da ya shigo gidan; jikinta ya yi sanyi ƙalau, amma hakan bai hana ta isa ƙofar ɗakinsa da sassarfa ba. Amna biye da ita a cikin firgicin suka shiga bugun ƙofarsa tare da kiran sunansa a lokaci ɗaya. Ganin babu motsinsa ballantana alamun zai buɗe ƙofar, ga tagoginsa duka a rufe. Hakan ya sa Hajiya ta sa Baba maigadi ya ɓalle ƙofar iya ƙarfinsa.

Hajiya Mummy da Amna ihu mai ƙarfi suka fasa yayin da suka yi ido biyu da Jamal a kan gado. Baba maigadi ya hau salati saboda alamunsa ya nuna babu numfashi a tattare da shi. Hajiya Mummy ta faɗi ƙasa tana kuka bakinta ɗauke da kalolin salati saboda idanuwanta sun gama tabbatar mata da Jamal ya jima da barin duniya. Amna kuma jikinsa ta haye tana ihu tare da faman jijjigarsa a kan ya tashi cikin ƙaraji da zaucewa, bayan kururuwar da take yi a kan don Allah a kawo musu agaji.

Hmmm!😪

D. AUTA CE✍️