Ɗanɗano
*FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
MARUBUCIYAR;
ABOKIN AIKINA
BAƘON YANAYI
A'ISHA
DIJE ƘARANGIYA
AMFANIN FITILA
*Na san wasu za su tuno da ɗayan cikin littafanta. To ku karkaɗe kunnuwanku ku sha labari, yanzu ma ta zo muku da sabon salon labari mai cike da abubuwan al'ajabi, ruɗani da tarin rikita-rikita a cikin wannan littafi na fansar ƙauna. Bayan zallar soyayya mai tsuma zuciyar makaranci. Ku biyo mu sannu a hankali kada ku bari a yi wannan sarƙaƙiyar tafiya ba tare da ku ba.*
ƊANƊANO!
Kano ƙarfe 8:30pm.
Motocin ɗaukar amarya jere da juna suna ta gudun tsere a saman babban titin Ahmadu Bello Way. Sun bi layi suna ƙyalli tsabar sabunta, saboda duhun dare ya ƙara ƙawata su a idon masu kallon wucewarsu ɗaya bayan ɗaya.
Waɗanda ke cikin motocin kuma, sun yi jugum kowa da abin da yake saƙa wa zuciyarsa, yayin da fuskokin wasun su ke ƙumshe da zallar farinciki da hira a tsakaninsu jefi-jefi. A cikin raha da annushuwa abokan amarya suke ta tsokanar ta ganin yadda ta yi ƙuri da ido tana kallon tsakiyar titi ko ƙiftawa babu. Bayan tagumin da ta rafka da murmushin yaƙe tamkar an yi mata dole yin sa a daidai lokacin, tsabar fargaba da tashin hankali sun yi mata lulluɓi gumi ya hau feso mata a goshi, ta shiga fifita da gefen mayafinta tamkar babu iskan A.c a cikin motar.
Shigar jerin motocin a cikin unguwar Nasarawa, da saukar zugar 'yan kawo amarya; ya yi daidai da isowar motar ango da wasu abokansa a ƙofar tamfatsetsen gidan. Wanda ya sha sabon fenti da hasken ƙwayayen lantarkin da ke maƙale a jikin katangar gidan lungu da saƙo, inda hasken ya gauraye ko'ina har cikin gidan da wajensa gabaɗaya.
Guɗa ta kaure a lokacin da ango ya isa bakin motar da aka saka amarya, ya fito da ita da kansa, bakinsa har kunne abokansa da wasu danginta suna ta ihun farinciki. Don tarin dandanzon mutanen da ke wurin bai hana shi rungume ta a jikinsa ba, yana maƙale da ita suka fara tattaki a hankali har zuwa cikin gidan cikin takun isa da taƙama.
Aka bi su ɗii a baya cike da burgewa ga wasu, yayin da hakan ya bai wa wasu 'yan adawa haushi matuƙa suna guntun tsaki. Duba da yadda ya hana gwaggonnin amarya riƙe ta zuwa cikin gidan da kai ta har ɗakinta, kamar yadda al'ada ta tanadar.
Guɗa ta ko'ina sai tashi take yi, hakan ya ƙara raunata zuciyar Nur da ke jefa ƙafafuwanta ido rufe cikin sanyin gwiwa har zuwa ɗakin. Bayan an wuce babban falo aka haye saman bene inda wasu ɗakuna uku suke, sannan da wani ƙaramin falo mai ɗauke da dinning table a gefensa.
Da kansa ya zaunar da ita a saman makeken gadonta wanda ya kusa cinye rabin ɗakin, sanan ya shiga leƙa fuskarta da ke cikin mayafi yana wani irin tsadadden murmushi har dimple ɗin sa ɗaya yana lotsawa. Cike da kunya ta shiga sunne kai a lokacin da ta kai bayan hannunta tana goge guntuwar ƙwallar da ta fito idonta tana ƙoƙarin bin fuskarta. Sosai lallen hannunta ya ɗauki hankalin angont,, saboda ya sha jan lalle da baƙi kuma ya fito fes tamkar don ita aka halicci kalar ƙunshin.
Dole ta saka shi yin kawaicin sakin hannunta da ke cikin nasa gam-gam, sannan ya dinga kutsawa cikin dandazon matan da suka cika ɗakin ya fice cike da shauƙin ƙaunarta a ransa, yayin da wasu abokan wasansa da nata suka raka shi da guɗa bayan zantukan tsokana iri-iri. Amma iya murmushin kan fuskarsa kawai ke nuna sarai ya ji su, saboda bai iya tankawa kowa ba a dalilin sauyin da jikinsa ya yi a cikin ɗan lokaci.
Ficewarsa daga ɗakin, ya bai wa wasu damar tofa albarkacin bakinsu, ta hanyar yi musu addu'ar zaman lafiya da yabon tsarin da aka yi wa gidan da kayan adon zamani masu ban sha'awa.
Mintuna a tsakani aka shiga shelar 'yan kawo amarya su zo a mayar da su gida. A hankali mutane suka dinga ficewa zuwa ƙofar gidan bayan sun yi mata sallama da addu'ar zama lafiya. Har aka bar ta da amintattun ƙawayenta guda biyu. Waɗanda suka sha ado tamkar su ma amaren ne. Musamman Minal wadda kusan komai nata iri ɗaya da amarya, kama daga kan lallensu, shigar kayansu da kalar ƙamshin turarensu duka. Saboda Nur da kanta ta feshe Minal da turaren bayan ta gama saka wa jikinta tana cewa,
"Ya dace ita ma ƙawar amarya ta yi ƙamshi."
Bayan fitar 'yan kawo amaryar; Nur ta miƙe cikin sauri ta nufi ƙofar fita daga ɗakin cikin sassarfa, babu shiri ta waigo saboda hannunta da Minal ta cafko da zummar yin magana. Nur ta riga ta yin maganar jikinta yana rawa muryarta tana sarƙewa ta ce,
"Ku..ku ɗan jira ni Amna..., ku..ku..bari zan karɓo saƙona a hannun Aunty Jamila kada ta manta da shi ta wuce gid..."
Cikin zafin nama ta fice, ta bar Minal da Amna suna kallon ƙofar kamar masu nazartar samfurinta. Cike da tsumayen dawowarta kusa kafin su sauke ajiyar zuciya a lokaci ɗaya tamkar sun yi shawara da juna. Amna ta miƙe tana ƙara gyara shimfiɗar gadon sannan ta ƙara feshe ɗakin da turarukan ƙamshi tana faɗin,
"Yau dai hankalin kowa zai kwanta, mun kawo wa Auncle J matarsa an huta."
Minal ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan cikin sanyin murya ta ce, "Ni ma yau zan yi bacci har da minshari, babu tunanin za a yi kaza gobe ko wuri kaza za a je tun da sassafe."
Suka yi murmushi dukansu kafin kowanensu ya shiga danna waya shiru ya ratsa ɗakin. Tsawon minti goma da fitar Nur amma har lokacin ba ta dawo ba. Minal ta miƙe cike da fara'a saboda tuno halin Jamal da aika-aikarsa a kan Nur ba ya shayin idon kowa.
"Kada fa ta shanya mu a nan, dare ya yi mana ango ya raka mu da doguwar sanda. Bari na je na nemo su a kammala komai mu ma mu yi gida mu yada haƙarƙari."
Amna ta yi hanzarin faɗin, "Jira! Jira ni na je da kaina, kin san halin Auncl J ba ya jin bari a kan matarsa, wataƙila yana can ya riƙe mana ita su shanya mu a iska."
Amna ta fice tana gyara zaman mayafinta a kafaɗa, ta bar Minal a tsaye kafin ta ja ƙafafuwanta zuwa jikin window, laluben tagar ta janye tana kallon farfajiyar gidan da tsirarun abokan angon da ke ta shewarsu kamar sun manta duhun dare ya lula, saboda komai tarwai kasancewar haske ya wadaci ko'ina tamkar rana. Ƙarar shigowar saƙon da ta ji a wayarta ya sa ta bar jikin tagar ta nufi jakarta ta fiddo wayar tana furzar da iska mai zafi a bakinta.
Idonta a kan fuskar wayar cike da mamakin ganin Nur ce mai turo saƙon, ta shiga karantawa cikin fargaba tare da zaro ido waje. Kafin tashin hankalin da ya game jikinta ya sa ta ɗora hannu a ka ta shiga kurma ihu iya ƙarfinta babu ƙaƙƙautawa.
Sautin ihun nata ya sa ango da abokansa tare da Amna rige-rigen isa cikin ɗakin. Ido tsakar ka suka shiga kallon ta baje ƙasa tana wani irin kalar kuka tamkar wadda aka yi wa saƙon mutuwa. A ruɗe suka shiga tambayar mafari, zancen ya yi mata nauyi faɗi dole da hannu ta yi musu nuni ga wayarta, bayan ta sassauta sautin kukanta tana rafka salati cikin wata kalar murya. Inda ta jefar da wayar ɗaga cikin abokan angon ya ɗauko a lokacin da kira ya sake shiga wayar tana ta ɓurarin. Jikinsa yana rawa ya miƙa mata wayar ta karɓa cikin kyarmar hannu tsabar bugun da zuciyarta ke yi, shiga buɗe lambobin sirrin wayar Amna ta yi hanzarin fisge wayar ta ɗaga kiran ganin sunan Aminiya tarwai a jikin fuskar wayar.
"Minal, izuwa yanzu na sani kina cikin tashin hankali saboda ganin saƙona. To ki kwantar da hankalinki Allah ne ya ba ki Jamal."
Ƙit wayar ta katse, Amna ta bi kiran cikin sauri amma tamkar almara ta ji layin a switch off. Cikin sauri Adamu abokin Jamal ya karɓe wayar a hannunta ya shiga karanta saƙon Nur da ya gani a rubuce.
_'Minal na yafe miki Jamal duniya da lahira, saboda ke ce amaryarsa kuma da ke aka ɗaura auren ba da ni ba. Ki yi masa biyayya sau da ƙafa kuma ki yafe mini laifin da na yi aminiyata.'_
"Ba zai yiwu ba! Sam ba zai yiwu ba!"
Furucin angon kenan a lokacin da ya ji saƙon Nur da abokinsa ya gama katantawa a fili. Wayarsa ya fitar daga aljihu jikinsa yana rawa ya shiga kiran ta, sai dai duka layukanta uku babu wadda ta shiga duk wadda ya kira a kashe yake jin ta.
Hularsa ya jefar ya shiga yamutsa gashin kansa a haukace kafin ya hau zarya a tsakiyar ɗakin yana cizon haƙoransa, bayan ya cire babbar rigar da ke jikinsa ya wurgar yana tsuma. Cikin hanzarin ya dafe kansa saboda wani mugun bugun da ya ji a tsakiyar ƙwaƙwarsa a kan harbawar da jijiyoyonsa suke yi. Idonsa ya rufe ruf tsawon minti ɗaya sannan ya sake buɗewa babu shiri ya sauke su a kan Minal.
Saboda wani tunanin da ya ɗarsu a ransa bai san lokacin da ya isa gabanta ya shaƙo wuyanta ba. Domin riƙon da abokansa suka yi masa da ƙoƙarin ɓanɓare hannunsa a wuyanta bai hana shi zare idonsa da suka rine cikin ƙanƙanin lokaci ba. Magana ya yi cikin kakkausar murya tamkar wanda ba ya cikin hayyacinsa.
"Ko ki fito mini da matata ko kuma na zamo ajalinki a cikin wannan dare! Ba ki isa ki raba ni da farincikina ba! Nur rayuwata ce ko mutuwa ba ta isa ta shiga tsakanina da ita ba.... ƙarya ne! Na ce ƙarya ne Nur ba za ta guje ni b...."
Kukan da ya sarƙe muryarsa ya sa jikinsa raunin da abokansa suka ci galabar ƙwatar wuyan Minal daga mummunan riƙon da ya yi mata. Tamkar ƙaramin yaro, ya shiga rera kuka wiwi yana faɗar maganganun da babu komai a cikinsu face zallar son Nur da ƙaryata abin da ya faru. Tare da alwashin yi wa Minal mummunan kisa idan ba ta yi gaggawar fito masa da matarsa ba. Da ƙyar abokansa suka fitar da shi daga ɗakin yana nuna ta da hannu, saboda yadda yake ji a ransa idan ya sake furta wata kalma daga bakinsa; zuciyarsa za ta iya fashewa tsabar nauyin baƙinciki ya danne numfashinsa.
Oh Allah! Wannan babbar badaƙala ce mai zaman kanta. Ku ci gaba da biyo ni domin jin yadda za ta kaya. Kada ku manta sunan littafin FANSAR ƘAUNA. Ranar 15 ga watan January zan ci gaba daga inda muka tsaya.
A taya ni sharing fisabilillahi!
D. Auta✍🏼