1
*FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*Albishirunku! Ƙorafi ya karɓu, na janye 15 ga watan January da na faɗa zan ci gaba da yin posting. In sha zan ƙoƙarta ta yadda za ku dinga jin motsina har zuwa lokacin da za mu kammala book 1. Masu jiran sai sun ji ana faɗar labari ya yi daɗi su dinga faɗar daga farko ku taimake ni ku fara bibiya tun yanzu. Fatan alheri gare ku gabaɗaya.*
*LAMBA TA ƊAYA.*
Fitarsu daga cikin ɗakin ya saka minal fashewa da wani kalar kuka mai ɗauke da majina. Amna da ke tsaye wuri ɗaya tamkar an dasa ta tana zubar da hawaye, kukan Minal ya saka ta matsawa jikinta cike da tausayi ta dafa kafaɗarta tana bubbugawa a hankali, ba tare da tace komai ba. Saboda ita ma kanta ya gama ƙullewa tana buƙatar ƙarin bayani, don ba ta san me zai sa hakan ta faru ba kai-tsaye ba, sanin tana da cikakken tabbaci a kan Minal ba za ta cutar da Nur ba, kamar yadda Jamal ya yi hasashen ita ce ta ta yi sanadin gudunta.
Sautin kiran da ya shigo wayar Minal, Amna ta yi saurin isa wurin wayar cikin rawar jiki ta ɗauko mata, saboda ganin an saka sunan Innarmu saɓanin tunanin da ya ɗarsu a ranta ko Nur ce ta sake kira. A cikin dasashiyar murya Amna ta ce,
"Karɓi wayarki, Mamarku ce ta kira."
Minal ta cakumi wayar cikin hanzari ta kai kunnenta, wani kuka ya sake kubce mata. Saboda lafazin da mahaifiyar ta fara furtawa mai kama da mummunan albishir.
"Ki yi haƙuri Amina, ke taki ƙaddarar kenan ki yi ƙoƙarin cinyewa."
Cikin hanzari Minal ta shafe hawayen fuskarta cike da mamakin lafuzan mahaifiyarta, saboda ba ta yi tsammanin cewa ita ma ta san wainar da Nur ta toya ba. Cike da ƙarfafa zuciyarta, ta haɗiye kukan da ke cikin bakinta sannan ta yi magana cikin raunanniyar murya ta ce,
"Me kike son sanar da ni Innarmu? Ashe ke ma har kin samu labarin abin da Nur ta aikat..."
"Ina sane Amina tun kafin yanzu, kuma sanin halin da za ki shiga ya sa na kira ki domin na yi miki kashedi. Amma ki yi haƙuri ki rungumi ƙaddararki da aurenki hannu biyu, kada ki kalli ƙalubalen da za ki fuskanta a wurin mijinki. Don Allah za ki yi kuma sakamakonki zai fito daga hannuns..."
Cikin sautin kuka Minal ta katse ta da cewa, "Ban gane ba Innarmu! Ni fa gabaɗaya kaina ya ƙulle! Ta ya ya zan fuskanci abin da nake ji daga bakinki? Jamal angon Nur wanda muka yi taron bikinsu a yau duniya ta shaida; shi kike nufin zan zauna da shi a matsayin mijina na sunnah?"
Ta ƙare maganar tana kore hawayen da ke yi mata fareti a kan fuska. Bayan tsumar da jikinta yake yi tamkar mazari tsabar firgicin da take ciki ya ƙara raunata ɗan sauran kuzarin da ya rage a jikinta.
Ajiyar zuciya mahaifiyarta ta saki kafin ta yi maganar da ta daskare numfashinta, saboda kalamanta sun ratsa zuciyarta sun saukar mata da wani kalar firgici mai saka mutum zaucewa.
"Amina, Jamal ke ya aura ba A'isha ba. Saboda haka ban yafe miki ba matuƙar kika taka ƙafarki wajen gidan da sunan barin sa ba tare da kin bi hanyoyin da za ki sasanta tsakaninki da mijinki ba."
Ƙit ta kashe wayar, ta bar Minal riƙe da wayar a kunne tana zarar ido kafin ta fasa ƙara ta buga wayar ƙasa tare da kwarara wani kalar ihun da guntun fitsari ya kufce wa Amna, tsabar fargaba da tsoron Minal sun gama kama ta.
Hakan ya sa ta kasa motsi sai idon da ta zuba wa Minal da ke ta birgima a tsakiyar ɗakin tana ƙaraji tamkar mai bugun aljannu.
Kasancewar ta ji duk abin da suka tattauna, jikinta yana rawa ta ciro wayarta a aljihun rigarta ta ƙwala wa mahaifiyar Jamal kira, waton Hajiya Mummy.
Cikin sa'a tana shiga ta ɗauka, a kiɗime ta yi magana tsabar ita ma ta kusa zaucewa.
"Ha..Hajiya Mumm...mummy ki zo gidan Auncle J babu lafiya!"
Daga can muryar Hajiyar ta fito raɗam tana cewa, "Ki yi ƙoƙarin kwantar mata da hankali ina kan hanyar zuwa gidan yanzu. Abokansa sun sanar da ni ya fisgi mota ya bar gidan ba mu san me zai faru da shi b..."
Ta ƙare maganar cikin muryar kuka sannan ta katse kiran. Jikin Amna ya yi sanyi ƙalau, cike da ƙarfin hali ta isa wurin Minal da ke ta birgima har lokacin ta fara magana.
"Ki yi haƙuri, na san dole ne ki shiga irin wanann yanayin a sanadin abin da ya faru. Amma ki sani komai na duniya fararre ne kuma ƙararre. Ki rungumi ƙaddararki kamar yadda Innarmu ta faɗa, wataƙila hakan zai iya kawo sanadin alheri a gab...."
"Yanzu har sai na tsaya yi miki bayanin Jamal Nur yake so ba ni ba? Ta ya ya zan iya zama da wanda ba ya so na? Yanzu a gabanki kin ji yana faɗar sai ya kashe ni, mutumin da ke dakon yi wa rayuwata kisan gilla ake so na zauna da shi a matsayin miji da mata? Ba zai yiwu ba...ni ma ba na farincikin rabuwarsa da Nur saboda na sani ita ma tana son sa."
Ta ƙare maganar tana zuƙe majinar kuka a cikin zafin zuciyar da take jin hayaƙinta yana ƙoƙarin rufe mata hasken ido. Cikin sanyin murya ta sake magana bayan ta yi durƙuso a gaban Amna gwiwa bibbiyu tana cewa,
"Ki taimake ni ki taimaki rayuwar Jamal a matsayinki na 'yar'uwarsa. Don Allah idan Hajiya ta zo ki ce ta roƙi Innarmu ta jaye Allah Ya isarta a kaina. Saboda ko zan bi duniya na yi alwashin sai na bar gidan Jamal, kuma ko da ina fita ƙofar gidansa bakinta zai kama ni na fara ɗaiɗaicew..."
"Dakata Minal! Kada ɓacin rai ya sa ki jefa kanka cikin fushin Ubangiji. Ki yi haƙuri ki bari mu ga yadda abin zai kasance, ba tare da kin yanke hukuncin da zai taɓa rayuwarki b.."
Minal ta yi hanzarin miƙewa tsaye ta fara taku a tsakiyar ɗakin tana faɗin,
"Rayuwa ta ba ta da wani amfani tun da har aka aiwatar da wannan ɗanyen aikin ba tare da sanina ba. Don haka ba zan yi wa kowa Allah Ya isa ba, amma tabbas ba zan taɓa yafewa b..."
"Minal!"
Amna ta kira sunanta da ƙarfi cikin wani sabon tsoro da ɓacin rai. Saboda jin furutanta kamar tana so ta wuce iyakar hankalinta duk da haƙurin da take ba ta.
"Ki bar ni ina da ikon faɗar komai tun da aka yi mini abin da aka ga dama. Saboda ko za a mutu ba zan iya rayuwar aure da Jamal ba, kuma idan aka matsa kafin shi ya kashe ni ni da kaina zan fara aika kaina zuwa lahira."
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Wannan masifa da me ta yi kama?"
Furucin Hajiya Mummy kenan a lokacin da ta faɗo cikin ɗakin har tana cin tuntuɓe saboda kalaman Minal ne suka tarbe ta.
"Na sani ba a kyauta miki ba saboda ba a yi shawara da ke ba kafin a aiwatar. Amma ki kwantar da hankalinki babu abin da zai faru sai alheri. Ni ce mahaifiyar Jamal, kuma na faɗa na nanata ban yafe masa ba matuƙar ya sake ki."
Wani sabon kuka ya suɓuce wa Minal, hannunta a ka ta shiga kwarara ihu saboda tana ji a ranta gabaɗaya an gama raunata rayuwarta. Daidai lokacin da aka kira wayar Hajiyar, ta dakata daga yunƙurin rarrashin ta da take yi ta ɗauki wayar. Bayan jin abin da aka sanar da ita a wayar ta yi magana cikin haɗe fuska ta ce,
"Adamu miƙa masa wayar!"
Ɗaya daga cikin abokan angon ne suka kira ta, kuma babu ɓata lokaci suka ba shi wayar muryarsa ta fito a ɗashe cikin wayar yana cewa.
"Hajiya Mummy ba zan dawo gida ba sai da tare da matata. Ki ce kowa ya yi tafiyarsa a bar ni zan nemo Nur da kain..."
"Ni na ce ka dawo, ga ni a cikin gidan naka kai kawai nake jira."
Ta kashe wayar idonta a kan Minal da ta yi tsaye kamar an dasa ice ta kasa motsin kirki. "Ku kwantar da hankalinku in sha Allahu babu abin da zai faru sai alheri. Aure ne an riga an ɗaura, kuma babu yaji ballantana saki sai dai mutuwa ta raba da yardar Allah."
Wani kallo Minal ta yi wa Hajiya Mummy kafin ta koma cizon yatsanta tana wassafa yadda za ta bar gidan a cikin daren. Saboda ta ci alwashin haramta wa kanta Jamal har zuwa lokacin da Nur za ta dawo gare shi.
Da rarrashi da ban-baki Hajiya ta samu Minal ta yi shiru. Amna tana gefe da tagumi saboda tuno wasu abubuwan da Nur ta yi yayin hidimar bikin, waɗanda sai a lokacin ta gano ma'anarsu da abin da take nufi.
Shiru ɗakin ya yi ban da ƙarar Ac babu abin da ke motsi idan aka cire kukan tsuntsayen da ke saman bishiyoyin gidan. Kowa da abin da zuciyarsa take saƙa, duba da yadda suka shiga nutsuwarsu tamkar an saka musu dokar yin shirun.
Hajiya Mummy ce ta kawar da shirun, ta hanyar duba agogon wayarta sannan ta sake doka wa Jamal kira. Ranta a mutuƙar ɓace ta sake ba shi umarnin dawowa gida a cikin biyar kacal, saboda ta fahimci idan ba ta yi masa jan idon gaske ba; rashin tawakkalinsa zai iya karya mata zuciya. Kuma faruwar hakan tamkar gayyatar wani sabon tashin hankali ne a cikin ahalinta.
Gama wayarsu babu jinawa suka jiyo ƙarar sautin shigowar mota a cikin gidan. Ƙirjin Minal ya shiga bugawa dam-dam saboda sanin arba da Jamal a lokacin tamkar arangama da mutuwarta ne. Musamman da ta tuna irin muguwar shaƙar da ya yi mata yana ƙoƙarin aikata lahira.
Zumbur ta miƙe tsaye tana rabon ido a lokacin da takun tafiyar ke ƙarato ɗakin. Buɗe ɗakin da aka yi ya yi daidai da faɗawarta cikin toilet a sukwane, cike da matsanancin tsoron da ya mamaye mata zuciya.
Ƙasa ta sulale bayan ta rufe toilet ɗin da makulli, jikinta yana rawa ta shiga wani irin marayan kuka mara sauti. Wanda babu hawaye sai gunjin da yake ƙara yunƙuro mata takaicin ɗaurin talalar da aka yi wa rayuwarta.
'Me ya sa kika yi mini haka aminiyata?'
Tambayar da ta jefi kanta da ita kenan a zuciya, saboda ta kasa fahimtar dalilin da ya sa Nur ta zaɓi guduwa ta bar Jamal duk da zazzafar soyayyar da take yi masa.
'Shin Nur ko ta ga wani abu a tattare da ni wanda ke nuna son Jamal nake yi ba tare da na sani ba?'
Zargin da ta yi wa kanta kenan wanda babu tabbacin faruwar hakan, idan saɓanin fahimta ne ya jawo Nur ta yi mata irin wannan yankan baya.
"Ki dawo ga masoyinki ƙawata, ni ban taɓa ji ina son sa ba."
Zancenta kenan a fili tamakr an faɗa mata idan ta yi maganar Nur za ta ji ta, wanda ta yi a cikin sanyin murya da raunin zuciya.
Daidai lokacin da ta fara jin sautin Hajiya Mummy a sama tana faɗa. Jikinta ya hau tsuma wata ƙwalla mai zafi ta fara bin fuskarta. Saboda duk abin da take faɗa da amsar da ya ba ta a cikin kunnuwanta.
"An ɗaura aurenka da Minal ne a bisa wani uzuri mai girma. Don haka ba zan taɓa yafe nonona da ka sha ba matuƙar ka saki igiyar aurenka da ke kanta. Kuma ka sani A'isha ba matarka ba ce don ba a ɗaura aurenka da ita ba. Idan ka yi biyayya ga zaɓin da Allah Ya yi maka za ka ga amfanin hakan a gaba. Idan kuma ka tayar wa da 'yar mutane hankali za ta bar ka saboda ita ma cushen ka aka yi mata ba tare da ta sani b..."
"Hajiya ba zan taɓa son ta ba. Na faɗa miki ne don ki sani saboda ba zan iya yi mata kallon mace ba. Don babu abin da zan so a jikinta duk tsawon zaman da za ta yi cikin gidan nan. Bambancinta da namiji a wurina shigar mata ce kawai..."
Kallon da Hajiyar ta wurga masa ya saka shi miƙewa jiri yana ɗibar sa ya sake cewa, "Gaskiya na faɗa miki, saboda Nur na tsara rayuwata kuma zan nemo ta a duk inda ta je a faɗin duniyar nan."
D. Auta ce👩🏻🦯