5
*FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA IBRAHIM D. AUTA*
*LAMBA TA BIYAR.*
Shiru Hajiya mummy ta yi masa, saboda babu wata amsar da za ta iya ba shi a daidai lokacin. Hakan ya sa ta kawar da kanta gefe kawai tana share hawayen da ke bin fuskarta, zuciyarta cike takaicin abin da ya faru, wanda ya yi silar ciwon da ke barazana ga lafiyarsa.
Amna ta matsa jikin gadon tare da dafa hannunsa ta yi magana cikin sigar rarrashi ta ce masa,
"Ka yi hakuri Uncle J, ni na sani Nur za ta dawo maka, saboda ita ma tana son ka. Kuma abu ne wanda kowa ya san da hakan ba za ta iya rayuwar da babu kai a cikin ta ba. Don haka don Allah ka taimake mu ka taimaki rayuwarka Uncle J, ka kuma ƙarfafa kanka da zuciyarka ka yi ƙoƙarin cire damuwar komai a ranka Allah yana sane da komai da ya far..."
"Laifin me na yi mata za ta guje ni?"
Ya wurgo mata tambayar cikin sauri saboda ya kasa shanye takaicin, kuma tambayar da ke ransa kenan tana yawo a ƙwaƙwalwarsa.
"Ka bar zancen nan Jamal. Za a yi shi daga baya idan ka samu lafiyarka."
Maganar Hajiya kenan cikin kakkausar murya, duk da take ƙoƙarin danne da abin da ke cikin zuciyarta. Saboda ko kaɗan ba ta fatar ta yi asararsa kamar yadda likita ya yi mata mummunan albishir. Daga hakan Jamal bai sake cewa komai ba, sai kawar da kansa da ya yi gefe tare da runtse ido ƙirjinsa yana bugawa da sauri da sauri.
Bacci mai nauyi ya ɗauke sa, zuwa lokacin asibitin ta cika da danginsu, 'yan'uwa da abokan arziƙi. Mutanen nesa da suka kwana gidan Hajiya mummy fiye da rabinsu suna asibitin ana jajanta lamarin. Gidansu Minal ma Hajiya ta kira ta sanar da su halin da ake ciki, sannan ta bai wa 'yan aikinta umarnin su yi abin karin safiya su kai wa Minla. Saboda tashin hankalin da take ciki bai hana ta tunawa da amanarta da aka ba ta ba.
Wannan dalilin ya sa Innarmu da Gwaggo Salame suka dira asibitin ganin Jamal. Daga can suka zarce wurin Minal bayan sun gama tattaunawa da Hajiya a kan yadda za a shawo kan matsalar cikin sauƙi. Kuma an bar zancen a tsakaninsu ba tare da an sanar da Minal halin da yake ciki ba, gudun ta ƙara tuburewa ta bijire wa auren kuma ta lalata musu sabon shirin da suka tsara.
****
Minal kam maganganun Gwaggo Salame sun rage mata kaso huɗu a cikin goman damuwarta. Kuma ta karɓi ƙaddararta, duk da tana jin ba ta gamsu da ingancin auren ba har a cikin zuciyarta ba. Saboda iya sanin ta dakalolin tarihin auren da ta ji ba ta taɓa jin kalar abin da aka yi mata ba. A take zuciyarta ta shiga ziga ta da shawarwari mabambanta, waɗanda ta tsayu a kan wadda zuciyarta ta karɓa, kuma ta riƙe a matsayin makamin kare kanta daga farmakin da ke cikin auren, sannan da riƙon amincin da take yi wa alaƙarta da Nur.
Jiki babu kuzari ta ja abincin da Hajiya ta aiko mata ta ƙara ci. Sannan ta fitar da sauran ga maigadi yana ta godiya. Sai dai abin da ya so ƙara saka ta cikin damuwa zamanta shiru a cikin gidan tun bayan zuwan su Innarmu, babu wanda ya sake zuwa gidan har dare. Sannan ta kira Amna ya fi sau goma, amma har wayar ta gama ringing ba ta ɗauka ba. Hakan ya ƙara tunzura ta, ta shiga neman lambobin Nur cike da ƙunar rai, da zaman turaata saƙonni da zummar ko da za ta buɗe wayar ta gan su. Saboda duk kiran da ta yi a sanar da ita layukan duka a rufe suke.
Daren ranar ma ta yi kwana rabi da rabi, saboda rashin nutsuwar zuciya da kaloli tambayoyin da take son amsarsu amma babu damar hakan. Abincin daren da Hajiyar ta sake aiko mata ma sai cikin dare ta samu damar ci, a lokacin da yunwa ta hana ta sukuni saboda barcin ya ƙi ba ta haɗin kai. Karfe biyun dare ta duƙufa kai kukanta ga Allah, a kan ya kawo mata sauƙin matsalar da take ciki, sannan ya dawo da Nur ga mijinta ita ma ta auri wanda take so. Saboda katangar kashedin da Innarmu ta yi mata da Aminunta ya hana ta neman sa a waya ta ji halin da yake ciki.
Don abu ne da ta sani dole ne hankalinsa ya tashi a lokacin da ya ji an yi wa neman aurensa ƙarfa-ƙarfa. Sannan ita ma Nur za ta dawo ga Jamal komai daɗewar lokaci, hakan ya sa ta dinga amfani da kayanta na gida duk da ba su da yawa. Kayan Nur kuma ta mayar da su akwatunan lefenta da ke ajiye gefen gado. Saboda ta saka wa ranta zaman wuccin-gadi ne za ta yi a gidan ba zaman dindindin ba, don haka babu abin da zai ruɗe ta ta saki jiki a inda babu lasisin zamanta.
Ba ta samu bacci mai daɗi ba har sai da ta gama sallar asuba, daga lazumi ta ɓingire a wurin sai barci. Haka ta ci gaba da rayuwar kaɗaici ita kaɗai a gidan Jamal har tsawon sati ɗaya, babu mai zuwa wurin ta idan ba Gwaggo Salame ba. Abin da ya fi ɓata mata rai kenan ganin yadda aka wofintar da 'yancinta bayan an tauye rayuwarta da gingimemen laifi. Hakan ya sa a cikin 'yan kwanakin gabaɗaya ta zuge, saboda ramar ƙarfi da yaji ta dira jikinta har idanuwanta sun zurma tamkar mai ciwo. Saboda wa'azi da nisihar gwaggon Salamen, tare da kulawar da Hajiya ke ba ta kowace safiya; ba su cire ta daga cikin ƙuncin da zuciyarta ke abota da shi ba. Sai ga wani ƙarin tashin hankali, Hajiya ta kira ta a waya tana sanar da ita Jamal zai dawo ranar ta shirya yi wa mijinta girki.
Shiru kawai ta yi bayan ta sauke wayar daga kunnenta ƙirjinta yana bugawa ta shiga sharar ƙwalla. Saboda jikinta ya ba ta gara zaman gidan ita kaɗai da rayuwa wuri ɗaya da Jamal. Duba da irin tozarcin da ya yi mata da yunƙurin kisan tun a tashin farko.
"Ba zan iya zaman aure da shi ba."
Furucinta kenan a lokacin da ta miƙe jikinta yana rawa ta ja dogon hijabi ta zumbula. Da sassarfa ta sauka ƙasa jikinta yana tsuma ta isa bakin gate, maigadi yana tambayar lafiya ganin yadda ta fito gidan kamar an koro ta. Amma ƙanzil ba ta ce da shi ba ta buɗe ƙofar za ta fice. Kiciɓis ta yi da gwaggo Salame tana ƙoƙarin shigowa gidan har kansu ya gwabru da juna.
"Subhanallahi!"
Furucin gwaggon kenan a lokacin da ta yi ido biyu da Minal, nan take zuciyarta ta hasko mata abin da take ƙoƙarin aikatawa. Fuskarta a cure ta dinga kallon Minal tana nazarin yanayinta, ganin ta ja gefe tana kumbura fuska bakinta ɗauke da gungunin a saman leɓonta. Fuskarta a cure ta yi mata magana cikin kakkausar murya ta ce,
"Me ya fito da ke kuma ina za ki je?"
Minal ta ɓare baki kamar ƙaramar yarinya ta yi magana cikin kuka ta ce,
"Wallahi ni ba zan zauna daga ni sai shi a cikin gidan nan b..."
Ta yi maganar tare da rushewa da wani sabon kuka har da buga ƙafafuwa. Baki a sake gwaggon ta bi ta da kallo bayan ta shigo gidan ta rufe ƙaramar ƙofar. Ta fara fa hannnuwa tana salati saboda ta rasa me za ta faɗa. Ganin maigadi yana tsaye yana kallon su ya sa ta ja hannunta tana tirjiya da buga ƙafa har suka koma cikin gidan. A falon sama ta zaunar da ita kan kujera ranta a matuƙar ɓace ta shiga nuna ta da hannu kafin ta samu damar faɗin,
"Yanzu Amina sau nawa zan ce ki yi haƙuri? Kenan duk abin da nake faɗa a bayan kunnuwanki yake bi yana wucewa? Saboda Allah duk lokacina da nake ba ki a kwanan nan ashe ba ki gani ba? Ko kin manta ina da tarin abubuwan da nake jinginewa na zo rarrashin ki? Ashe ban sani ba kallon mara aikin yi kike yi mini da nufin na yi a banz.."
"Gwaggo ni ba na son zama da shi ne kawai...saboda ya faɗa ba zai mini kallon mace ba kuma ya ce sai ya kashe n..."
"Ya kamata zuwa yanzu ki fahimci mijinki ba zai iya cutar da ke ba. Don ko kiyashi ba zai iya kashewa ba ballantana mutum. Saboda duk tsawon kwanakin nan da ba ya kwana gidan yana asibiti ana kula da lafiyarsa. Ya yi ciwo na tsawon kwanaki a yanzu ta kansa yake yi da abin da ke damun sa. Don haka ki kwantar da hankalinki babu abin da zai iya yi miki idan ba alheri ba. Idan ma ya yi miki Allah ma ba zai bar shi ba, kuma hukuma ba za ta ƙyale shi ya ci bulus ba dole ne a ɗauki mataki kans..."
"Idan haka ne Gwaggo a sanar wa da 'yansanda tun yanzu, saboda su san halin da ake ciki su hana shi kada ya sake yunƙurin kashe ni...don wallahi ranar ƙiris ya rage ya cire mini maƙogwaro."
Dariya Gwaggo Salame ta yi sannan ta zauna kusa da ita tare da janyo ta jikinta, saboda zancenta ya sa ta fahimci firgicin da ya saka ta ne ya sa take jin tsoron zama da shi tun a daren farkon auren. Hakan ya sa ta shiga kwantar mata da hankali har ta saki ranta. A gefe ɗaya kuma tana jinjina ƙarfin son da yake yi wa Nur cikin tausaya wa halin da yake ciki. A ranta kum ta shirya yadda za ta shawo kansa ya daina jin haushin ta su nemo hanyar da za a gano Nur a duk inda ta shiga.
Saboda kwanansa uku a asibitin aka sallame shi, a kwana na huɗun ne Hajiya ta ce ya kamata ya koma gidansa da kwana tun da ya ji sauƙi. Amma fafur ya kafe a kan shi da gidan har abada, ta so tirsasa masa kwana gidan a ranar; amma wasu daga cikin dangin Alhajinsa suka ce ta bi komai a hankali. Hakan ya sa ta ci alwashin kora shi gidansa cikin dabara, saboda babu adalci a bar Minal ita kaɗai a gidan shi yana kwana gida.
A son ran Hajiyar ma daga sallamar sa a asibitin ya yi wa gidansa tsinke su sasanta da matarsa, amma shawarar da likitan ya ba ta a kan a bi komai a sannu har zuwa lokacin da zai warware ya sa ta ɗaga masa ƙafa. Sai dai kuma a gefe ɗaya ta shiga nata aikin da ta ce idan ya san wata bai san wata ba. Don maganin ƙarfin maza ta dinga ɗirka masa yana sha ba tare da ya san amfaninsa ba. Ko da ya tambaya kuma ce masa ta yi maganin ciwon zuciya ne, duk da bai gamsu ba amma hakan bai sa ya yi kokwanto a kansa ba, saboda cikakken sanin da yake da shi a kan ta fi shi son kansa, kuma ba za ta iya cutar da shi ba.
Abokansa ma ta ba su aikin dannar sa tare da rage masa damuwar rashin Nur. Hakan ya sa suka shiga nuna masa alfanun haƙuri da kowace irin jarabawa. Saboda iya binciken da suka yi sun tabbatar Nur ba ta garin, ta yi tafiyar da babu wanda ya san inda ta je. Da taimakon abokan nasa masu ƙarfafa masa gwiwa ya dinga shan maganin Hajiya. Sai dai inda gizon ke saƙar sauyin da ya fara ji a jikinsa, inda ya fara zargin maganin da tayar masa sha'awar mace. Saɓanin yadda ya saƙa wa ransa har abada tsakaninsa da mace, matuƙar Nur ba ta dawo ba babu shi babu kowace irin mace a duniya komai nagartarta.
Dole ƙanwar na ƙi Hajiya ta shawo kansa a kan zai koma gidansa da kwana. Daɗin amincewarsa ta aika wa Minal cefane, tare da sanar da ita abincin da ya fi so ta girka masa da kanta. A nan gidan ma Gwaggo Salame ce ta taimaka mata da girkin har suka kammala. Sannan ta saka ta yin wanka da ado a cikin ɗaya daga cikin sabbbin kayan lefen Nur, waɗanda sai da ta sha fama da ita sannan ta saka kayan. Sai dai a a ranta ta ci burin tana fita za ta cire, saboda ta yi wa kanta alƙawarin zama d Jamal har zuwa lokacin da Nur za ta dawo.
Kunun aya Hajiya ta haɗa wa Jamal, ta ce ya tafi da shi ya sha tare da Minal, saboda sanin yana mugun son sa, wannan dalilin ta yi masa tarkon da zai kama shi daren ranar. Bayan ta gama yi masa wa'azi da jan kunne a kan zama da Minal bisa amana ko da ba ya son ta. Ganin hawaye a idonta ya saka shi karɓar alƙawarin zama da ita a cikin gidan ba tare da ya yi mata korar karen da ya kitsa wa ransa ba da ya je gidan.
Har ya fice da motarsa cikin gidan tana zuba masa addu'ar tsari da abin ƙi tare da neman kwanciyar hankali a cikin rayuwarsa. Cike da jin daɗin addu'o'in nata ya baro gidan cikin karfin zuciya, amma bai fasa hasko hoton murmushin Nur a idanuwansa ba. Hakan ya ƙarfafa masa gwiwar zai ci gaba da neman Nur a duk inda ta je a faɗin duniya.
Wasar za ta fara🫠
D. AUTA CE✍️