16
by @maidambu41
❤️🩹SO da CIWO❤️🩹*
®©Ramlat A Manga
Mai_Dambu
Paid book
*Assalamualaikum everyone yau mun zo muku da ingantattun maganin mata daga shahararriyar mai maganin nan De Majestic Aprodiasic best kayan mata ever, We have the best kayan mata 100 natural kada ki zama Bora a wurin namiji kada ki zama koma baya a wurin kishiyoyin zo ki gwada ki yadda babu wacce zata d'aga miki kafada macen da tasan ciwon kanta ita take gyara buje 😆🤣 anayi ana sha'anin arziki*
Muna d ingantatun kayan mata kamar hka:
Maganin sanyi
Exclusive Tsumi
Abulbulo
Gumbar Madara
Gumbar budurci
Zumar budurci
Zumar kacha kacha
Royal Honey
Zumar goran tula
Garin Emergency
Garin kwatai
Sallanta
Dan wata bakwai
Spoil her HQ
Back to virgin set
Exclusive zuma
Tsumin Ayu
Man Ayu
Maniyin Ayu
Zumar Ayu
Gaban Ayu
Kazar Mallaka
Kazar sirri
Zabon Amare
Dan Shila
Ciccibi
Dambun nama
Man power
Yajin Maza
Men energy
Gamu bukatar kayanmu su tuntubi wannan number *** we are the best among the other'
16
Zubewa yayi akan gwiwarshi yana jin kanshi kamar ba a jikinshi yake ba, suke damke rigarshi suka fara jan shi a kasa kamar wani mara galihu, wasu na harbi a cikin gidan, wasu nayi a waje idan na ciki suka yi harbi haka na waje zasu yi, Uwani tsabar tsoro ya kamata bata san lokacin da ta fada rijiya ba, domin tana jin ana yan bindiga amma bata tab'a ganinsu ba sai yau kidimewar da tayi kawai ta bi gugar da take diban ruwa a rijiya da shi, harbin da suka sake yi, Yaya ta fito daga parlournta bakinta dauke da salati. "La'ilallah anntan subhanaka inni kuntun minanal zalimi, Innalillahi wainnalihir rajou Innalillahi wainnalihir rajou Innalillahi wainnalihir rajou!" Abinda take fada kenan tana kallon yadda suke jan Umar da jini yake zuba akanshi. "Hajiya Ina Amarya? Ina wurin amarya muka zo bayan nan bamu da matsala da lafiyar kowa ko shi wannan tsayawa yayi yana kallon Mazaje!" Bakin Yaya yana dauke da salati ta ce musu. "Amarya bata nan!" Dokawa Umar gindin bindiga suka yi a gefen kanshi tuni jini ya fara zuwa a karo na biyu. "Ina Amarya Mama da take tsaye a kofar kitchen jikinta yana rawa ta ce mishi. "Wallahi bata nan ku duba ta ku gani!" Haka suka shiga cikin dakunan su Yaya aka duba har da dakin Maamah babu labarinta. Fitowa yayi ya ce. "Oga bata nan fa!"
"Ok mu an biya mu, ita kawai muka zo gani " kallon ɗaya daga cikin mutanen shi yayi ya ce mishi. "Minti nawa?" "Minti shida!" Murmushi yayi ya ce. "Ina uwar Amaryan?" "Gani!" Bata rufe baki ba sai ji kake "dammm" zubewwa Yaya tayi dafe kirjinta, tana salatin. "Wannan shine sakon amarya dama ita aka aiko mu, tow ni kamar mala'ikan mutuwa nake idan na shiga wuri sai na ɗauka." Sakewa Umar gindin bindiga suka yi ya fadi can, "Hajiya!" Fitsari Mama ta sake wanda bata san na harbin da suka yi ne ko na razana da tayi ne, ita sai ta tsinci kanta da sake fitsari a jikinta bata tab'a ganin irin wannan abin ba, "Mun bar miki sako yadda ba zaki manta damu ba, ita kuma yarku tayi ta gudu domin sai na kamata nayi mata kisar da tafi ta Uwarta." Suka fita da gudu suna sake harbi a sama, da rarrafe Mama ta isa gaban Yaya da take juyi cikin jini, "Yaya Abidah!" Rike hannun Mama tayi tana murmushi ta ce mata. "Ki taimaka min Maamah!" Tari ta fara jini na zuba a wurin ciwon, hawaye na zuba mata. "Maamah! Maamah,!! Hassanah Rahmatullah! Hassanah Rahmatullah kada ki bari ayi auren nan don Allah don Allah, don Allah kada ayi auren nan don Allah ki taimaka min, Hassanah sanyi nake ji!" Ihu Mama tayi tana faɗin. "Babu Al'umma ne? Babu Mutane ne? Ina kuka jama'a" sai da da alamu shigar bazata da harbin da yan bindigar suka yi ya gigita alumma.
Wani irin kuka take, a lokacin da abin ya faru Makota sun yi kokarin Kiran Mazajensu kasancewar abin ya faru wurin karfe sha biyu saura na rana, kiraye kirayen da ake yi isa har aka samu Baffanmu da Abdulkarim, Wayyo Allah na, yadda suka iso gidan sai ka ji kamar zuciyarka zata buga. Da gudu Abdul ya nufi Yaya tare da taimakon Baffanmu suka ɗauke. Da gudu Abdulhameed ya "Umar na can a kwance dauko shi!" Dakyar Yaya ta bude idanunta cikin murmushi ta ce mishi. "Zan tafi na barku da nauyin Rahmah yan fashin nan sunce rayuwarta suke bukata, my poor baby." Shiru tayi hawaye na zuba mata ta kara bude idanu a hankali, kafin ta ce. "Allah ka zama gatan Rahmah! Ya Allah a daidai wannan gabbar karusa shirin nakiya da makircinsu akan Rahmah,.ya Allah ka bata miji na gari me tausayi da jin kanta, Ya Allah na bar maka zabin rayuwar Rahmah Ya Allah gani gare ka ya Allah na kusanto gare ka, Ya Allah ka lalata shiri da yunkurin da ake na lalata mata rayuwa, Ya Allah duk wanda ya saka hannu aka daura auren nan ya Allah kamar yadda zan zo gare ka ka hana shi." "Yaya ki yi shiru!" Kwantar da ita suka yi idanunta rufe. "Ku bani ruwa zan sha!" "A'a kada ku bata muje asibitin, Baffanmu dauki dankalinta ka toshe kishinta da jinin yake zuba." "Ruwa!" Ya kuma fada, a karo na biyu, cikin wani irin kidima Baffanmu ya nufi bakin pampo ya saka hularshi ya bude ruwan ya kawo mata. Da sauri ta kama hular tayi ta sha tas ta shanye ta ce mishi. "Karo min!" Gidan ya cika!" Haka ya qaro mata ruwan tasha sosai kafin ta sake hular jini da ruwa suna fita da inda aka harbeta, a hankali ta sake murmushi jikinta ya sake bakiɗaya, "Muje Abdulhameed!" Suka fita da gudu, wasu na biye dasu, tsirarun mutane suka rufo gidan an manta da Uwani da take rijiya. Babban asibitin Yola aka wuce da su. Kanta na cinyar baffanmu tana juyawa taba salati, suna shiga asibitin tayi shiru bata kuma motsi ba, sai jinin da yake zuba kamar da bakin kwarya, jini zuba yake kamar an bude pampo, kafin wani lokaci jini ya ya wanke kasar ER, koda Dr Hammad Baita da Dr Suraj Sheikh suka tsaya kanta Yaya tana fama da rayuwa ne, domin akan idanun Dr Baita ta cika bakinta yana dauke da salati, kallon agogon ER din yayi ya ce. "She pass away da karfe daya da minti uku, bayan harbin da aka mata a kahon zuciya, Hajiya Abidah Shafi'u Yero, Mahaifiyarta Dr Abdulhameed Imam Umar Datti, Matar Imam Umar Datti, Uwa ga Kanal Jamal Imam Umar Datti!" Yana fada yana wani irin shashekar kuka, jikinshi yana wani irin rawa, yasan Yaya ba karamin sani yayi mata ba. Mace mai dattako da sanin ya kamata mace mai kirki da adalci, bayi manta lokacin da zai auri matarshi Iyayenshi suka ki domin musulunta tayi, haka ya saka Yaya a gaba ita ta saka baki iyayenshi suka amince ya auri matarshi da yau danginsa suke alfahari da ita. Jin kukan Dr Baita yasa Abdulhameed ya shiga Tare shi Dr Suraj Sheikh yayi yana faɗin. "No no!" "What fuck!" Ya fada da karfi yana ture shi, ganin ana rufe Yaya yasa shi nufar kanta. "Yaya!" Ya kira sunanta da ƙarfi, ya zo kan gawar yana tab'ata amma ina Yaya tafiya yayi nisa. Da kyar aka riko hannunshi suka fito, yadda yake kuka wiwi tare da zubewwa akan gwiwarshi, yana fadin. "Innalillahi wainnalihir rajouna Allahu Akbar, Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar, Ya Allah mun tuba Ya Allah mun gode maka, Ya Allah mun yarda gare ka Yaya ta koma, Ya Allah Ya Allah Maamah Wayyo Allah na My poor sister." Kukan da yake yasa Baffanmu zuba mishi idanu, ya rasa me ke mishi dad'i, kalamanta yake yawo a kanshi. " "Since zuwan Maama suka yi!" Wannan kalaman da mutuwar Yaya haifar mishi da gagarumin hautsinewa ƙwaƙwalwa wanda ya haifar da saka shi zubewa a wurin ba tare da yasan me ya faru ba. Kafin wani lokaci yan sanda da sojoji sun cika wurin ana can ana fama da Umar da Mama, kafin zuwan karfe uku hankalin Baffanmu ya dawo gare shi, ya mike zubur yana me nufar inda gawar Yaya yake. "Ina Abidah?" Nuna mishi inda gawar yake aka yi ya, zuwa kanta yayi ya tsaya yana jin hawaye na zuba mishi. "Na zata kece zaki raka ni? Na zata zaki tsaya ki taya ni kula da abinda na bari, ashe kece zaki bar min aiki!" Ya fada muryanshi yana rawa, a hankali ya fara magana da irin abubuwan da ya faru ne yasa zata tafi? Me yasa zata mishi haka, sai da aka d'aga shi a kan gawar, Mama ta koma kamar wata robot bata hum bata hmm, amma tana ganin Baffanmu ya mike ta bi shi, suka fita tare, aka ɗauki gawar Yaya aka saka a mota, sai hawaye ne yake zuba a idanun Mama, har suka isa gida. A lokacin an ciro Uwani a rijiya, duk ta firgice kamar zata zura da gudu.
Haka aka shigo da gawar Yaya aka wuce Parlour Baffanmu da ita, ana sauketa a hankali. Kafin wani lokaci gidan ya cika da al'umma da makota gidan sai kuka suke. Salim ya samu labari, haka Matar Jamal da suke Barrack ta ji labarin, domin Jamal ya gaya mata, za ayi jana'izar karfe biyar na yamma, sannan take gaya mishi ga Maamah a gidan kwance, tun dazun take gidan Salim ya kawo ta. "Ki bari zan zo da kaina kada kiyi wani abu da zata fahimci yaya ta rasu."
"In sha Allah, baban Munifah" suka yi sallama.
Maamah.
Ina ga kamar duk abinda za'a maka a duniya duk soyayyar da za a nuna maka a duniya babu wanda zai fi tsaya maka a rai kamar soyayyar Uwa, ina kwance amma zuciyata a cunkushe take da soyayyar Yaya, wani irin kauna nake mata wanda tun tashina ban shaku da ita kamar kwananki da nayi a tare da ita ba, domin kuwa ni kaɗai nasan yadda nake kwana a jikinta, kamar wata jinjira. A gadonta nake kwana duk lokacin da zan juya ko naje fitsari zan farka naga an tare min inda xan fadi da pillow, idan na tashi zan same ta tana addu'a hannunta a sama, nasan bana cikin Yara marasa jin magana haka yasa zai yi wahala ka ji na batawa wani rai, abu daya na sani ni wawuya ce ni wawuya ce kamar yadda kowa ya sani. Wauta a cikina kamar yar fari amma nafi alakanta haka da autancin da Mama ta koya min, Yaya ita ce kaso mafi girma a duniyata, duk wanda zan so ko zai nuna min so bayan Yaya ce. Yau nake hango duk wasu abubuwan da suke faruwa a rayuwata wanda take hanani nayi ta jin haushinta, na farko lokacin da na gama primary school naso Bodi school ta hana a kai ni,tana faɗin "Maamah ce za a kaita makarantar kwana? Hmm babu inda zata domin zuwa zata yi tayi ta musu bauta." Daga haka ta rusa Maganar makarantar kauna. Sai da ta kai hatta abu idan aka saya matukar bai mata ba, zata ce kada ma a bani bai dace da ni ba, Maamah bata damu da ni kamar yadda ta damu da sauran yan uwana, tsakanina da ita harara da faɗa. Lumshe idanuna nayi ina jin kamar na rasa wani abu me daraja a rayuwata, bugun zuciya yana beating more than yadda nake jin shi, ji nayi kamar an lullube ni da danyen nama, wani irin sanyin yana tsaye a ilaihirin sassan jikina. Zazzabi da wani irin tsoro ya cika zuciyata. Hawaye na tsinkewa daga idanuna, gashi tun ranar da Yaya ta kwance wayoyina ban sake bin ta kansu ba, ina ganinsu a dakinta ita da kanta take saka su a charger, amma a kashe suke wurin karfe uku nayi sallah la'asar. Duk da arba'in da tara, ina zaune a akan abin sallah a dakinsu Munifah. "Assalamualaikum!" D'ago kai nayi na kalle shi Hamma Jamal ne tsaye a kaina cikin kakin sojoji. "Waalaikumunsalam!" Na fada ina kuka me yawa. "Kukan me nane?" "Zanje Yaya ne!" Jan hancinsa yayi yana murmushi ya ce min. "Ok let go!" Ya riko hannuna, muka fito yana kallona sai kuka nake. "An miki wani abu ne!" "No I wanna see Yaya ne kawai" "ok Baby stop crying!" Ya fada yana kallon matarshi da ta fito tare da Munifah da yake Allah bai bashi haihuwa da wuri ba, munifar sai yanzu take da shekaru biyar. Gaba ya saka ni, in zama na kifa kaina akan cinyata. Sai da ta rufe gidan muka bar Barrack din, tare da wasu sojoji masu uniform da marasa uniform. Tunda tunda muka daukar hanya amsa wayarshi yake yana faɗin. "Amin Ya Allah! Biyar aka saka na gode sosai, yanzun na iso wallahi ban isa gidan ba akwai Abdulhameed da Abdulkarim akan kome dai Alhajinmu. Amin Ya Allah Nagode sosai Allah ya bada lada, tow Allah ya kawo ku lafiya." Ya kashe wayar d'ago kaina nayi na ce mishi. "Hamma is something else?" Girgiza min kai yayi yana kallon titi, har muka isa gidanmu. Wanda tun daga nesa na hango dubbanin mutane da suka yi dandazo ana tsaye wasu sun yi alola wasu na kan alola. "Hamma me ya faru?"
"Babu kome ya fada yana kusa Motarshi har kofar gidan, kafin ya tsayar da motar na balle na fita da gudu. A daidai compound dinmu na gaba mutane nan ma a shake, ji nayi kamar bana gani yadda kasan mahaukaciya haka nake jifa kafana,ji nayi an rike hannuna. "Ki nutsu Maamah!" D'ago kai nayi ina kallon Hamma Jamal ne ya shigo a guje. "Me ya faru?" Na jefa mishi tambayar, rike ni yayi muka tafiya don yaki ko da kallona ne, sai nake jin kamar bani da kome a rayuwata irin kamar ka zama holoko baka da kome a jikinka kamar empty ji na nake kamar ba wani abu me amfani a jikina, haka muka isa cikin gidan yayuna mata suka taso zasu yo kaina nayi maza ma k'amkame jikin Hamma Jamal tare da rintsa idanuna, dakatar dasu yayi ina sauke wani wahalallen ajiyar zuciya, a hankali ya wuce da ni dakin Mama da ake ciki. Har gabanta ya kai ni ta mika min hannu, makalewa nayi ina jin yadda hawaye ke zuba daga idanuna. "Rahmah!" Sake shi nayi ina jin kamar Muryan Yaya da sauri na juya zan fita. "Ina zaki!" "Yaya!" Na furta ina kallon hanya. "Rahmah!" Sake kallon kofar nayi ma fita tare da tsayawa a waje tartsatsin jinin da na gani ne an wanke bai fita ba. "Jinin waye anan?" Na tambaye su bakiɗaya aka rasa me bani amsa, dakinta na nufa a hankali na bude parlourn an rufe ne saboda ba son a shiga ayi barna. "Rahmah!" Na sake jin kiran da muryanta sak. Uwar dakinta na shiga bata nan, ba bude kofar ban daki bata nan. "Maamah me kike nima?" "Yaya nake nima tana parlourn Baffanmu ne?" Na tambayi Addah Ma'u da ta biyo ni tana danne kukanta. "Addah why are you crying?" "Wani abu ne ya fada min a idanu. Tow ke me yasa kike kuka?" "I'm missing someone!" Na fada ina leka har wardrobe na duba kasar gado fita tayi tana kuka, na fito ban ga Yaya ba, leka dakin Mama nayi na ce mata. "Mama ina Yaya ta je?" Na fada ina kuka na kara mata da cewa. "Me yasa kowa ke kuka? Ina Baffanmu?" "Rahmatullah!" Naji muryan Baffanmu. Juyawa nayi na kafe shi da idanuna kayan shi ya b'aci da jini da sauri na isa gare shi tare da rike hannunsa. "Baffanmu, me ya same ka? Ka ji ciwo ne?" Rike hannuna yayi zai ja ni nace mishi. "Baffanmu baka ji Yaya tana kirana ba ne? Bari na duba kitchen gata nan tana min magana!" Na fada domin ni dai na ganta tsaye a kofar kitchen sanye da kayan da na barta da shi. Murmushi take min nima na sake murmushi ina faɗin. "Baffanmu tsaya bari na je ga yayana!" Parlourn shi ya wuce da ni, idanuna ya sauka kan mutum kwance an rufe mishi kai ga zanin Yaya sabo. "Baffanmu waye?" Zaunar da ni yayi a gaban gawar. "Waye Ubangiji?" "Ubangijina Allah wanda ya yi halittar kome da kome a cikin kwanaki shida wasu rawayan sunce a kwanaki bakwai ya halicci kome da kowa." "Good kinyi yarda Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, Manzon Allah ne?" Na gyad'a kai ina faɗin. "Shine shugaban manzannin cika makin annabawa limamin manzannin Allah!" "Kin yarda da mutuwa?" Rike hannunshi nayi ina kallonshi. "A cikin Alqur'ani Allah ya fada kowacce rai zata dandanni zafin mutuwa!" A hankali ya kai hannuna ya ce min. "Yadda kika bani amsa very strong ki mata addu'a." Mai da hannuna baya nayi ina faɗin. "Waye?" "Just check it!" Girgiza kai nayi na ce mishi. "A'a ina jin tsoro!" Bakiɗaya dakin ya dauki sautin kukan yayuna da suke tsaye a kaina. "Try it" kasa budewa nayi ina me sauke ajiyar zuciya akai akai, ina kallon gawar. "Ki bude ke musulma ce, na fison ki bude da kanki kada wani ya bude ya zame miki ganin da zai dame ki, ki gani yadda babu wani abu da zai kara baki tsoron ganin shi." A hankali na kai hannuna jikina na rawa, na ja rintsa idanuna nayi domin wani irin bugu zuciyata take. "Rahmah!" Da sauri na bude idanuna, Yaya ce kwance fuskarta dauke da murmushi, kana ganinta zaka ɗauka barci take yi, no ba barci ba ne tafiya ce ta nisan zangon, tafiya ce ta fara shi, wanda isarsa sai ranar tashin alkiyama. Ban san ya aka ba sai ji nayi na ce musu. "Barci take ne?" "A'a Maamah Yaya ta rasu ne " "yaya ta rasu, ta mutu yanzu bani da Mahaifiya kenan? Yanzu Ni marainiya ce bani da wanda zai janyo ni a jiki kamar yaya? Yanzu kaf gidan nan mutuwa ta rasa wacce zata dauka sai Yayana? Kaf duniya a rasa wanda za a dauka sai Yayana? Ni mai nayi da zafi haka? Idan kuna wasa ne akan tace bata son auren nan yaya na tuba wallahi bana son auren nabi Allah na bi ki, ki rufa min asiri ko dawo kin ji ni na yarda da abinda kika yanke don Allah ki dawo gare ni, kin ce min ni Little Princess ce, sannan ni kamar kyakkyawar kabewa ce ta cikin cinderalla, Please kada ki tafi kin ji."
Yadda na rikice ina surutu yasa Baffa Junaid ya ce musu. "Kanal biyar da ashirin fa!" Ya fada yana me ja da baya, saboda shigowar da aka yi da makara. "Wayyo Allah na, don Allah ku bar min Yayana don Allah ku bar min Uwata Wayyo Allah na me yasa ni sai da ban girma ba, me yasa ni?" Am as why me? Me yasa na rasata a kankanin shekaruna. D'agani aka yi akan gawar don na burkice musu. Yadda nake ihu da kuka da dambe zai tabbatar maka bana cikin hayyacina. Dakyar aka fitar da gawar Yaya a parlourn saboda damben da ake da ni na hana a fitar, ban san cewa im strong ba sai a ranar. Watsar da su nayi kamar me aljanu na nufi kofar da gudu ana rike ni, amma ina na fita a bakin gate din gidanmu Hamma Abdulhameed ya tare ni. "Ina zaki?" "Su dawo min da Yayana!" "Tow shi kenan muje su baki yayarki!" Ya fada tare da bani hanya zan bude kofar sai ji nayi ya caka min abu a wuyana. "Wash me aka yi min? You cheating me? Yaya zasu dauke min? Ka bari na tafi na fada ina buɗe kofar a hankali na ji kamar anyi sama da ni. Tare ni yayi ya mai da ni dakin Mama. Domin kuwa kaf jama'ar gidan sun fito raka yaya, a gaggauce ya juya ya fita Mama tana zaune ta zubawa gefe guda idanun. Babu lokaci haka ya fito har an gama sallah, masu tafiya makabarta suka raka yaya sai a lokacin ya dawo ta mikawa Addah Rukayya kayan aiki ya ce mata. "Ki saka mata ruwa ita da Mama ga alluran barci nan ki sakawa Yay, Mama kai." Ya fada hawaye na zuba mishi. Ya nufi waje Mashin din dan makota ya hau suka nufi makabarta.
Yaya ta samu jama'a, yaya ta samu jama'a sosai wurin shida suka dawo aka ana kiran sallah aka yi Magariba. A dakin kuwa Mama daga ita har Maamah barcin allura suke musamman Mama da ba don an saka mata alluran barci da ruwa ba, jininta yayi mugun hawa, a tsawon shekaru aru-aru na zamansu ko tankiya basu tab'a ba, asalima tunda suka san dangi guda suka fito sai suka kama kansu suka zauna lafiya, Yaya ita ce akan Yara da kome na gidan, Mama ita ke rike da hidimar abinci da wani abu da ya shafi kaiwa da komowa, hatta kudin kashewa da kayan sallah da duk wani abu na kashewa Mama ce. Abin da ya shafi makaranta asibiti, tafiya da wasu abubuwan Yaya ce, idan kuma wani abu ya shafi dangi ita ce, Mama tana zaune lafiya da Yaya haka Yaya tana zaune lafiya da Mama, Yaran Mama suna dakin Yaya haka yaran Yaya, Yaya Fara ce Mama baka ce shi yasa ake alakanta ni da Mama ce ta haife ni ba yaya ba, kai ko abu ne ya taso a dangin Mama tow Yaya take tsaye a kai haka dangin Yaya Mama ce a kai sai Mama ta je Gombe sau goma Mama bata je sau biyu ko uku ba, wannan zaman nasu tun farkon Auren Mahaifin Yaya da Mahaifin Mama suka tara su, tare da jan kunne kada su ji labarin sun lalata musu zumunci zaman lafiya suke bukata a cikin zuriar. Yau zaman lafiya da zumuncin da suka yi mutuwa ta datse musu shi, hakuri da suka yi da juna mutuwa ta raba su. Duk inda zaka shiga ka fito tabbas mutuwa tayi musu yankar shakku.
Ko yaran daga baya suke ganewa Yaya ce ko Mama ce ta haife su, shima lissafinsu ce take basu. Akan Yaran Yaya bata da wasa amma bata da saurin hannu banbancinta da Mama kana tinzurata zata sha bugu, yaran har sun son Yaya ta hukunta su domin tana da saurin saukowa daga fushi, wanda Mama ba haka take ba, sanyinta bai haka ta ci kaniyar Yaro. Hakurinta zaka kalla ka fahimci tafi Yaya zafi domin ita yaya bata daukar reni, sha yanzu maganin yanzu. Mutuwa tayi musu yankar kauna.
Washi gari.
Mutanen Gombe a garin Yola suka karya, musamman Innani wacce take kuka tana faɗin. "Da nasan zaki mutu ki bar min duniyar da ban miki furucin da nayi ba, da nasan zaki tafi k