6
*FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA IBRAHIM D. AUTA*
*LAMBA TA SHIDA.*
Minal tana zaune falo tana kallon ƙarfin halin da Gwaggo Salame ta saka ta yi. Saboda ita ce ta ba ta umarnin zaman kallon har zuwa lokacin da Jamal zai shigo gidan, kuma ta ce kada ta kuskura ta bar falon ba tare da ya dawo ta gabatar masa da abincinsa ba. Tare da jaddada mata kada ta bari wahalar girkin da suka yi ta tashi a banza. Kuma duk abin da take ji kada ta yi sakacin barin sa ya yi kwana da yunwa. Saboda Hajiya ta sanar da ita ba ta bari ya ci abinci a wurin ta ba, saboda kada ya ƙi cin na gidansa.
A haka ta zauna tana kallon MBC2 da tagumi har zuwa lokacin da ta ji buɗe gate da shigowar motarsa. Ƙirjinta ya ƙire ya faɗi a lokaci ɗaya jikinta ya hau rawa ta shiga wara idanuwa tana neman inda za ta ɓoye, kada ganin ta ya sa haukar son Nur ta motsa masa ya nemi illata ta a banza.
'Ko da wasa kada ki sake ki nuna kina jin tsoron sa. Saboda wannan ne damarki ta farko da za ki yi amfani da ita ki nuna masa ke ma kin san kanki.'
Tuno kalaman Gwaggo Salamen ya sa ta fara faɗar hasbunallahu wa ni'imal wakil don samun nutsuwar zuciyar da ta bar jikinta tsoro ya mamaye jarumtar da take ƙarfafa kanta. Saboda sautin huɗubar gwaggon da take ji a cikin kunnuwanta tamkar a lokacin take yi mata jan kunnen da gargaɗi. Hakan ya sa ta yi hanzarin gyara zamanta tare da tsuke fuska tana nanata kalmar lahaula wa la ƙuwwata illah billah. Har ta ji motsin buɗe ƙofar falon ƙasa tare da takunsa yana hawa saman cikin sauri.
Dam-dam ƙirjinta ya shiga bugawa da sauri da sauri a lokacin da ya kunno kansa cikin falon. Idanuwanta a kan tv ba tare da ta kai kallon ta gare shi ba gudun ya gano halin da take ciki ya nemi cutar da ita babu mai ceton ta. Don a cewar Gwaggon idan ya fahimci tana mugun tsoron sa zai raina ta yawa ta yadda zai dinga yi mata abin da ya ga dama koyaushe. Hakan ya sa shigowarsa bai sa ta kai duban ta gare shi ba duk da hankalinta yana kansa. Sannan bai yi sallama ba ballantana ta amsa, sai jin sa ta yi ya saki ledodin da ke hannunsa suka zube ƙasa, bakinsa yana rawa ya kira sunan Nur cikin ɗaga murya yana cewa,
"Nur! Yaushe kika dawo ban sani ba?"
Wani kallo ta yi masa kamar ta yi masa babu yabo babu fallasa, amma a zuciyarta sosai ya ba ta tausayin da ya so karya mata zuciya. Sai dai hakan bai hana ta waige gefe da gefe ba cikin basarwa ta ce,
"Ina ka ga Nur a nan?"
"Ya Allah!"
Jamal ya faɗa cikin wata irin murya yayin da ya yi hanzarin dafe kansa da ke sarawa babu shiri. Saboda hango Minal a matsayin Nur ya tayar masa da mikin da yake ƙoƙarin dannewa a ransa. Saboda gizon da ta yi masa sak Nur da ƙamshin turaren Nur da ya ji a cikin falon, wanda tun asali shi ne ya fara yi masa maraba kafin ya isa bakin ƙofar shiga falon. Ƙirjinsa ya hau bugawa babu ƙaƙautawa ya shiga nuna ta da hannu yana faɗin,
"Ko da wasa kika sake saka turaren Nur a cikin gidan nan sai na sauya miki kamanni...kuma kin ci sa'a na yi wa Hajiya Mummy alƙawarin zama da ke da a yanzun nan sai kin bar gidan nan wallahi...ahhhh!"
Ya ƙare maganar yana dafe kansa ya wuce jiri yana kwasar sa ya faɗa ɗakinsa. Kamar da gayya a ɗakin ma turaren Nur ne ya fara yi masa oyoyo. Gado ya yi hanzarin kwantawa dafe da kansa yana murza goshinsa tare da bubbuga kansa a hankali. Ya bar Minal da ƙamewa wuri ɗaya tamkar an dasa ta, saboda furutansa sun ƙara lalata ƙarfin halin da ke zuciyarta.
Zumbur ta miƙe gudu-gudu sauri-sauri jikinta yana rawa ta faɗa ɗakinta, babu ɓata lokaci ta hau cire kayan Nur da ke jikinta. Sannan ta nufi bayi da sassarfa ta shiga darzar jikinta da sabulu tana haɗa kumfa, a ƙoƙarin ta na son raba kanta da ƙamshin Nur saboda gudun ta shiga haƙƙinsa da yawa ciwonsa ya ƙara tashi ta yi sanadin sharri. Don Hajiya ba ta ɓoye mata komai ba ta sanar da ita duk abin da likita ya faɗa a kan ciwon nasa tun kafin ya dawo gidan. Kuma ta nemi alfarmar ta kula da shi tare da juriya a kan halayensa har a shawo kan matsalolin da ke cure su warware.
Sai da ta ji fatar jikinta ta fara zafi sannan ta haƙura da wankan ta fito daga bayin. Jikinta a mace ta sake shiri ta fice saboda tuno abincin da take son yi masa ta yi kada ya kwana da yunwa. Ta ɗauki minti biyar a bakin ƙofarsa tana tunanin yadda za ta shiga ɗakin da irin sakamakon da zai biyo bayan shigarta. Kamar wata mara gaskiya haka ta shiga ɗakin nasa tamkar wadda ƙwai ya fashewa a ciki ƙirjinta yana harbawa. Nesa da shi ta tsaya tsawon minti biyu ba tare da ta iya furta masa ko kalma ɗaya ba. Alamun mutum da ya ji a kansa ya yi hanzarin tashi zaune yana ƙare mata kallo cike da mamaki. Kafin ya haɗe girar sama da ta ƙasa ya yi magana cikin kakkausar murya ya ce,
"Malama lafiya kika shigo mini ɗaki ko sallama babu!"
"Abin..ci...abin...cin...na ce.."
Kalmomin da ta yi ƙarfin halin harhaɗawa kenan cikin ininar da ba ta san ta iya ta ba sai a ranar. Saboda ya kafe ta da ido tamkar wadda ya kama da laifin kisa ko ta yi masa babbar sata.
"Abinci-abinci kika ce me?"
Ya maimaita maganarta cikin sauya murya a sheƙeƙe alamun ya kai maƙura da takaicin ta a ransa. Tana kallon yatsun hannunta ta mayar masa da amsa fuskarta a haɗe kanta a duƙe ta ce,
"Abinci ne na dafa, idan za ka ci sai na kawo maka."
"Abinci!"
Ta yi hanzarin ɗaga kai a tunaninta ta yi masa gwaninta, amma jin tsawar da ya daka mata da maganganun da ya baibaye ta da su; ya sa ta yi hanzarin ficewa sum-sum daga ɗakin cike da tsoro bayan rawar da jikinta ya hau yi.
"Ni ne kike zaton zan ci abincinki? Ke mahaukaciyar ina ce da za ki yi tunanin zan iya cin abin hannunki ma ballantana ƙazamin abincinki?"
Ganin ta bar masa ɗakin ya fito falon yana ta balbala mata masifa duk da ta shige ɗakinta, amma bai haƙura ba cikin ɗaga sauti tamkar bai san dare ne ba ya zazzaga mata zafafan maganganu tamkar ana yi masa wahayin su.
"Idan na sake ganin jemammun ƙafafuwanki a ɗakina sai na saka gitta na sare su gabaɗaya! Daga yau kada ki sake shiga duk sabgar da ta shafe ni...idan kuma ganganci ya ja ki na illata ki a banza na ga wanda zai tsaya miki baƙar wawuya bagidajiya! Kuma ki buɗe kunnuwanki da kyau ki ji ni; matuƙar ba ki sanar da ni inda Nur ta je ba sai na ga bayanki baƙar munafuka mai raba ƙauna!"
Minal ta rushe da wani irin kukan da ba ta san lokacin da ya suɓuce mata ba. Saboda kalamansa na ƙarshe sun yi matuƙar gigita mata kwanya. Kuma sun shiga jikinta ta yadda ita kanta ta shiga tunanin laifin me ta yi wa Nur ta yi mata irin wannan sakayyar, ta gudu bayan ta ɗora mata jakar tsaba a ka kaji suna aikin caccaka. Tun tana kukan da hawaye har ta koma yin na zuci tare da ajiyar zuciyar da babu komai a cikin ta sai nadamar zamanta gidan ba tare da ta tsere kamar yadda Nur ta yi ba.
'Matuƙar ba ki sanar da ni inda Nur ta je ba sai na ga bayanki baƙar munafuka mai raba ƙauna.'
Maganganunsa sun daki zuciyarta, hakan ya sa suka fara yi mata amsa-kuwwa a cikin kunnuwa babu ƙaƙƙautawa ta shiga jujjuya kanta tana faɗin,
"Nur ki dawo tun kafin raina ya zamo fansar guduwarki."
Jiki ta ja tana jan ɗuwawu ta isa bakin gado ta jingina bayanta tare da ɗora kanta saman gadon tana haɗiyar zuciya da shesshekar kukanta a hankali. A haka barci ɓarawo ya sace ta daga zaune tana tunani da ajiyar zuciya lokaci bayan lokaci har a cikin barcin.
Shi kam sai bayan ya gama sababin da surutan shi kaɗai sannan ya kwanta rigingine yana kallon sili, zuciyarsa cike da tunanin ta wace hanya zai ci gaba da neman Nur. Zuciyarsa ta tsayu a kan zai bayar da cigiyar ta gidan rediyo da kuma posting a social media. Ta yadda abin zai zama viral ya watsu a ko'ina ko za a dace. Da wannan nazarin ya miƙe a lokacin da cikinsa ya fara ƙugin yunwa. Kitchen ya nufa ya yi tsaye bakin ƙofa yana ƙare masa kallo bayan ya kunna ƙwan lantarkin da Minal ta kashe a lokacin da suka gama aiki.
Bincike ya dinga yi har ya haɗa kan indomie ya haɗa ta da ƙwai biyu cikin ɗan lokaci ya dafa. Kasancewar ya iya hannunsa tashin hannun Hajiya ɓangaren abinci abubuwa kaɗan ne bai iya ba. Duk da gatan da take yi masa hakan bai hana shi koyon wasu ayukan mata ba.
Bayan ya cinye indomin ya tuna da kunun ayar Hajiya, ƙaƙƙarfan tsaki ya ja sannan ya fice daga ɗakin ya nufi bakin ƙofar shigowa babban falon ya kwashe ledodinsa da ya watsar.
Kasancewar akwai wadatacciyar nefa kuma akwai ƙanƙara a cikin frizer da ke kitchen. Wadda ya gan ta a ƙanƙare wajen binciken da ya gama yi lungu da saƙo har zuwa store da ke ƙuryar kitchen ɗin. Sai da ya kwankwatsa ƙanƙarar ya jefa a kunun ayar, wanda ya bulbule a cikin dogon jug sannan ya faɗa wanka. Zuciyarsa babu daɗi ya gama wankan ya fito yana tsane jikinsa yana tsaki cike da takaicin Minal ya sake faɗin,
"Wawuyar banza mai ƙaton kai! Duk inda Nur ta je ta sani, kuma gobe idan ba ta sanar da ni gaskiya ba sai na ɗauki mummunan mataki a kanta. Ban san me ta yi mata ba don kawai ta gudu ita ta aure n....don ubanta ko za ta mutu ba zan yi zaman aure da ita ba tun da ba na son t...mitsssss!"
Ya ƙare maganar da jan dogon tsaki ya ja jug ɗin kunun a tsaye ya kafa masa baki ya fara kwankwaɗa. Garɗi da daɗin kunun, haɗi da sanyin da ya yi bai san lokacin da ya tayar da jug ɗin ba ya ajiye kofin yana gyatsa. Bakinsa ya goge bayan ya koma toilet ya yi brush ya kwanta da towel a jikinsa yana haki kamar wanda ya sha gudu.
Da tunanin Nur bacci mai nauyin gaske ya kwashe shi. Kamar almara cikin dare ya fara jin jijiyarsa tana miƙewa, zumbur ya zabura saboda kakkarwar sanyin sha'awa da ya shiga yi. Kansa ya dafe yana salati saboda yanayin da yake ji bai taɓa tsintar kansa a makamancinsa ba. Zarya ya fara yi a cikin falon dafe da kai jijiyarsa a miƙe kamar mai koyon tafiya. Babu shiri ya yi zaman 'yan bori a tsakiyar ɗakin saboda ya kasa juriyar tsayuwa da ƙafafuwansa da ke kakkarwa.
"Ya Salam!"
Ya yi ta jerawa a bakinsa yana maimaitawa tamkar wanda aka saka yin hadda. Nan take gumi ya hau keto masa yana sharewa da hannu har ta kai ya dafe mararsa yana salati. Tsabar harbawar da jijiyarsa take yi tamkar numfashinsa zai shiɗe yake ji. Halin da yake ciki ya saka shi miƙewa babu shiri ya fara tafiya yana layi ya faɗa ɗakin Minal jikinsa yana tsuma. Ƙafafuwanta ya jawo da ke shimfiɗe a bakin gado, babu shiri ta baje a tsakiyar ɗakin tare da farkawa a haukace cikin wani sabon firgici. Saboda mafarkinsa take yi wai ya zo da wuƙa a kanta yana faɗar ko ta faɗa masa inda Nur ta ɓoye ko kuma ya kashe ta.
Ihu ta fasa iya ƙarfinta ta buge shi ya faɗi ƙasa dabas tare da sakin towel ɗin da ke ɗaure a ƙugunsa. Wataƙila halin da yake ciki ya mantar da shi babu komai a jikinsa, a haka ya miƙe jijiya miƙe ya nufe ta gadan-gadan zai kamo ta. Ta sake ƙwalla ƙara tare da zurawa da gudu ta faɗa toilet a sukwane, sai dai kafin ta rufe ƙofar suka shiga kokawa a tsakaninsu. Yana ƙoƙarin shiga ciki yayin da ita kuma take ƙoƙarin tura ƙofar iya ƙarfinta a kan ba zai shiga ba, saboda kuzarinsa ya rage ya kasa shigar kamar yadda ya so.
Ganin za ta ɓata masa lokaci ya yi baya da nufin banke ƙofar da jikinsa ko da za ta ɓalle in dai zai samu biyan buƙatarsa. Sai dai yana yin bayan ta datse ƙofar tare da hanzarin saka makulli ta rufe ruf jikinta yana kyarma tamkar mazari. Don a iya tarihin rayuwarta ba ta taɓa shiga tashin hankalin da ya kai wannan ba, don ba ta taɓa yin ido da babban mutum babu tufafi a jikinsa ba, sannan da yunƙurin yi mata fyaɗe ko a mafarki. Hakan ya ƙara ɗaga mata hankali ta shiga zunduma ihun neman agaji.
Shirun da ta ji tun daga lokacin da ta rufe ƙofar bai nemi buɗewa ta ƙarfi ba; amma hakan bai sa ta fasa kururuwar da take yi ba. Jamal kam ganin ta yi nasara a kansa ya koma ɗakinsa da sassarfa ya ɗauko ɗaurin kuɗi 'yan dubu-dubu har bandur ɗaya sababbi kar ya tsaya bakin ƙofar toilet ɗin yana magana cikin rawar baki tsabar yadda yake ji a jikinsa.
"Idan har ba za ki bari na yi don Allah ba to ga shi zan...bi.. biya ki...tun da...da ma can ke..ba kya... tsoron Allahhhhh...."
Cabɗijam!🙆
Na yi kudi🏃