RANAR YABO..!

Nine

by @mommuhseen

💔RANAR YABO💔

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

By

Mom muhsen

&Asaad

Nine

Ina ganin wuce war motar Sakeena wajen sau biyu,sai na sake boyewa a inda nake zaune bayan wani gini nai zama na a wajen, nayi kuka mai sunan kuka tun inayi da hawaye har na koma yin na zuci, bazan iya cewa ga adadin lokacin dana dauka a wajen ba saidai naga gari yayi duhu sannan hankalina ya dawo jikina, tsoro matsananci ya dirar min na duba wayata wacce anyi min kira yakai sha biyar,Daddy da sakeena har ma dasu Jennifer sai kira na karshe da nagani an kira sau biyar Faa ne, na runtse idona inajin sabbin hawaye na zubomun,sbd duk da tsoron daya cika raina bazan iya kiran koda d'aya daga cikin su ba, na fito bakin titi ina kallon hanya motoci nata wucewa da mutane kowa na harkar gabansa, sanyi ya sauko kuma inajinsa sosai a jikina har cikin bargona nakejin sanyin, tafiya na soma yi ban san ina nake nufa ba zuciyata a soye kamar aya, tafiya nayi mai nisa ko gajiya banji nayi ba saida nazo wani lungu na iske wasu turawan samari sunata busa hayakin taba suna buga cacarsu, cak na tsaya kafin nai saurin juyawa Ina sauri tare da waigen su, gani nai sun tashi su hudun suna niyyar zagaye ni, jinai cikina ya juya matsanancin tsoro na kama ni, aguje na juya na fita daga lungun wanda hakan ya basu damar rufa mun suna son kamo ni,inajin babbansu yana basu umurnin su kamo masa ni, gudu nake sosai wanda tunda nazo duniya ban tab'ayin irinsa ba,tun Ina da karfin gudun har ya kare na fara kokarin zubewa, gashi daman banci komi ba tun safe yunwa taci tacinyeni, tuni na zube k'asa yayin da suka iskeni suna daukata kamar kaya a kafad'a, kuka na fashe dashi ina kokowar kwatar kaina amma da yake ba karamin kato bane wanda ya daukan ko gezau baiyi ba, ihu nake ina neman agaji amma kamar babu kowa a cikin area wajen, cikin ikon Allah sun daf da shigar dani cikin lungun nasu wasu motoci suka sha gabansu, ganin yan sanda ne yasa suka direni zasu ruga, aiko yan sandar suka rufar masu suka kamasu su dukan su,harshi ogan basu barshi ba.

Wani daga cikin su ya tadani yana mun sannu, jikina ko ina rawa yake nayi firgai firgai kafafuna har kerma suke,ya kamani ya zaunar a bisa wani table yana ta mun sannu, ya koma gefe yana waya su kuma sukai gaba da yan iskan suka bar dayan wanda shine ogansu, ya dawo kusadani yana tambayata babu dai abunda suka yi mun ko?na d'aga kai kurin sbd a mugun tsorace nake shin Inda wani abu ya sameni fa?

Wani kuka ya kwace mun sbd tunanin hakan kawae da nayi naji tausayin kaina fiye da kima, motace tsaleliya ta tsaya gabanmu cikin sauri dan sandan ya mik'e yana nufar motar, Fareed naga anbude ma motar ya fito yai tsaye rungume da hannun rungume ga kirjinsa,mgn sukai wacce banji mi sukace ba sannan dan sandan ya tafi ya barmu nan.

Kaina na sadda k'asa inajin wani rangwame cikin zuciyata,domin halin dana tsinci kaina a yanzu ya sanya mun matsanancin tsoro,ya sanya mun yanke hukunci koma wa wajen qawayena acan ne kadai zan samu tsaro karkashin kulawar hukumar makaranta, takowa yake zuwa inda nake har ya iso sai ya durk'usa gabana yana son lallai saimun had'a ido amma inaa na kasa hakan.

"Why Rabee'atu?Why?"

Jajayen idanuna na da suka gaji da kuka na dago ina kallonsa dasu, fuskar sa naga damuwa ainun idonsa naga rikici sosai ya cigaba da cewa, "Ina kike tunanin zakije duk fadin kasar?wa kike dashi da zakije wajensa?miyasa kika zab'i ki guji kowa harda masu kaunarki kamar ransu"

Kallonsa nake sosai jin kalmarsa ta karshe data dakarmun zuciyata ainun, idonsa akaina yace da raunanniyar murya, "Daddy,Sakeena,dasu Jennifer da.....da kuma....ni"

Kallon da nake masa yau ban tab'a yi masa irinsa ba, bakina kuma kamar an rik'e munshi sbd yadda na gigirza na kasa cewa uffan,

"Ina zakije kibarmu?Ina zakije Bee'atu?kinada inda yafi gidan Daddy ne?"

Sai lokacin hawayen suka dawo mun sabbi masu tsananin zafi,na kasa tsayar dasu balle na share su, na sadda kaina k'asa Ina shashshekar kukan muryata na kerma sosai nace, "Mami.......Mami bata son na zauna musu gida,tace idan ban tafi ita....ita zata tafi,bazan so.....bazan so tabar gidan mijinta sbd ni ba"

Huci ya furxar yana duban wani wajen daban,kafin ya dubeni har sannan shashshekar kukan nake kirjina yana d'agawa, hannunsa yake damtsewa Wanda hakan alamace na son yai cooling din kanshi, d'an matsowa kadan yai gabana yana samun hanky cikin hannuna, rik'esa nai sosai ina damtsesa ga hannuna na wani lokacin kafin na sanya fuskata cikin inajin kukan na son kwace mun,

"Miyasa kika zabi yin nesa damu?mai makon kizo garemu mu bazamu tab'a gudunki ba,Rabee'atu kodan karatunki bazan so kibar mkrnta ba,kodan Mahaifinki bazan so kibar England batare da kin cika masa burinsa ba, idan da ace wani abu ya sameki a yanzu fa?ya kike so miyu?ya kike tunanin duk wani masoyinki zaiji?"

Zuwa lokacin kuka nake kasa rik'a sbd ni kaina da ace wani abun yafaru ban San Ina zan sanya rayuwata ba, "Na kira Daddy zai zo nan zaku koma gida........Aa,Aa Fareed ba zan koma gidan can ba ko yazo bazan koma ba, ba......bazan iya cigaba da zama dasu ba,inhar ya matsa mun to zan...zan sake guduwa"

kallona kurin yake kafin cikin tattausar murya yace, "shikenan ya isa kukan it's ok bazai zo ba,amma zan sanar dashi na ganki zan maidaki Hostel sbd hankalinsa ya kwanta, yana can cikin damuwa sosai shida Sakeena"

Shiru nayi bance masa komi ba,ya sauke ajiyar zuciya yana duba agogonsa yace "Ten a clock now,zaki bini na kaiki gasu Sakeena?"

A hankali na d'aga kaina Ina ida goge hawayena, jikkata dake can nesa yashe yaje ya dauko mun yana zuwa ya bude mun bayan motar yana kallona, duk na hargitse jikina ko kallabi babu kaina bazan iya cewa ga inda na yadda shi ba, zufa duk ta sanya gashin gaban goshina sun kwanta,tashi nayi ahankali sai lokacin na lura ashe ko takalma babu k'afata,wajen gudu na jefar dasu.

Shiga nayi ya tattare mun rigata ya sanya ciki,sannan ya rufe ya zagayo ya shigo motar driver ne ke Jan motar ya bashi damar tafiya,motar akwae Ac sannan ga wani sassanyen kamshi na motar dana jikinsa yana tashi gwanin dad'i, kamar ba tafiya muke ba sbd yadda motar ke tafiya kamar a saman gajimare, na had'iye miyau a wuyana daker kafin nace masa,

"Please I need ur help"

Duk da bana kallon sa amma nasan jiyowa yai yana kallona, kafin yace "Ki fad'i duk abunda kike so"

Na share hawayena da hanky dinsa wanda kamshin sa yake mun dadi naja majina kadan sannan nace, "inaso idan mun kammala exam na koma gida,I mean can garinmu"

Shiru yai na wani lokaci kafin ya sauke ajiyar zuciya k'adan "Kina so nayi miki visa zuwa garinku?"

Kaina na daga masa ban dubesa ba, ya sake Jan numfashi kafin yace "kafun nan inaso inasan wace alaka ce tsakaninki da Daddy?sannan idan kin tafi zaki dawo ko kin tafi kenan?"

Ban San na kallesa ba sbd jin tambayoyin da yake mun, idanmu ya had'u da na juna na seconds kafin zuciyata ta buga mun sosai,na juyar da kaina ina jin zuciyata na ta bugawa.

"Pls"

Abunda ya fada kenan idonsa har sannan akaina, daker na iya saita muryata nace masa, "wanda ya haifin Daddy da Wanda ya haifi Babana, sune suke d'an wa da d'an kane shima kuma uba kawai suka had'a iyayen nasu,bayan duk anhaifi su Babanmu sai yan ta'adda suka rufar ma garin kakannin namu suka sanya musu wuta cikin dare, sbd ana tunanin cewar akwai ma'adanan k'asa a area wajen,wannan dalilin ne yasa dangi kowa ya watse iyaye suka mutu da yan uwa da dama awannan harin, mahaifin Babanmu ya rasu shida Mahaifin Daddy,haka ma matayensu ba wacce ta rayu, y'ay'a suka watse ba asan inda kowa ya nufa ba.

Daman Babana shi kadai mahaifinsa ya haifa Allah bai bashi zuria da yawa ba, kuma shi kadai yayi rai.

Yai neman danginsa har ya gaji mafarin yayi hijira daga wanan yankin na adamawa sukayo nan Maiduguri alokacin su ana zaune lafia ne, ya samu ya soma fafutukar rayuwa da wuya da dad'i har suka had'u da mahaifiyata sukai aure anan cikin kauyen Abadam dake jahar maidugurin,Saida suka shekara shidda sannan suka haifeni watana uku ta rasu, ya jima kafin ya kara aure ya auri wata diyar ogansa a kasuwa,mai suna talatu itace yanzu iyalinsa suna da yara biyu Jabiru da Hajjo,"

Nayi d'an shiru sbd bansan miyasa nake gaya masa duk wannan bayanin ba, amma abunda na sani shine zuciyata ta natsu da Fareed, 100% nakejin bazai tab'a cutar dani ba ban San kuma ma'anar bashi lbrin nawa ba.

Muryarsa tayi cool sosai yace, "Taya Daddy ya hadu da Baba bayan tsayin shekaru?"

Naja ajiyar zuciya nace, "Bazan iya sanin shekarun da suka dauka rabonsu da juna ba,amma abunda na sani shine An dad'e dadewar kuma sosai, watarana muna gona mu duka lokacin ban wuce shekara Shabiyar ba, da yake indai Baba zashi gona to mu duka muke tafiya hadda Inna, mu wajenmu aikin gona ba wani abu bane sbd a garinmu mata ba abunda basa yi a gona,gonar tana cikin birnin Maiduguri wacce surukinsa yake bashi duk shekara yake noma wa,sbd Baba bashida gonar kanshi daker yake hidimar rayuwa ga iyali.

Gonar tamu bakin titi take sai muka ga mota ta tsaya alamun dai kamar ta samu damuwa, driver ya fito yana duba wa mai motar yana baya bai fito ba, tun abun kamar wasa har yakaisu ga faduwar rana gashi suna wajen gari titinma ba acika wucewa ba sosai, muka gama aikinmu zamu koma gida sai Daddy yai ma Babanmu sallama suka gaisa,muma duk muka gaisa dashi yake cewa don Allah zai taya Driver sa a tura motar zuwa gaba inda zasu samu mai,ba musu Baba da jabiru dani muka kama tura masa mota tafiya mai nisa wadda mu bamu dauketa mai nisa ba sbd mun saba, saida muka kawo cikin gari kad'an aka samu mai da ruwa aka sa mata,motar tatashi hakan yai ma Daddy Dadi ba kadan ba yake cewa ya gode sosai daman kuma shiba dan gari bane daurin auren diyar abokinsa yaxo gobe akeyi,saukarsa daga airport kenan.

Yace mu shiga a kaimu har gida,Baba ya nuna aa zamuje mushiga motar haya duk da cewar duhun isha'i yayi, Daddy ya nace masa dole Baba ya hkr muka shiga motar muka dauki hanyar kauyen mu.

Cikin mota fira ta barke tsakanin Su kamar daman sun San junan su, ai kafin mu isa gida tuni sun fahinci cewar yan uwan junane na kusa,sai suka kama kuka sosai sbd kowannen su ya fidda rai da tsammanin sake haduwa da wani nashi, anan mukasan lbrin su Daddy da Babanmu.

Karshe kauyenmu Daddy ya kwana suka raba dare suna labarin yan uwa da iyaye suyi kuka suyi dariya, kowa yaba dan uwansa lbrin bayan rabuwarsu,Shi Daddy ya samu ubangida nagari mai adalci da ya tafi dashi kasar waje mafarin zamowarsa kenan acan da babban muk'amin Wanda yake rik'e dashi a can.

Kafin Daddy ya koma england ya nuna son zai tafi damu gaba d'aya nan take Babanmu yace inaa shi bazai bar kauyen nan ba,sbd yanajin dadinsa da mutanen cikinshi kuma rayuwarsa anan tafiye masa ta kasar turai masu jajayen kunnuwa, ba yadda Daddy bayyi dashi ba amma yace aa bazamu bisa can ba,sai yace to yai masa alfarma guda ya bashi ni yatafi dani ya inganta rayuwata ya sani boko nayi ilimi mai zurfi hadda na addini,nan ma saida suka yi daga gaske saida Daddy yai fushi sannan ya yarda, atakaice Daddy saida ya jira akaimun komi da komi na shirin tafiya sannan cikin wata gudan dayai a jahar Maiduguri ya inganta mana muhallinmu,aka tada ginin bulo da bulo akai mana ginin zamani Wanda ko gidan mai garin kauyen bai kama kafar namu ba,sannan aka sanya tayils duka dakunan, akayi kuma bayi kowane daki,aka fidda mun nawa dakin ciki da falo da kewaye in nazo hutu in sauka,inna talatu dakinta kamar na amaryar birni haka ma Babanmu tsakar gidan aka sanya interlock,aka kajawo mana ruwa sannan aka dora tanki aka siya mana generator da zai ringa halba ruwan,sannan aka fidda kan famfuna waje yadda za a ringa ba mutanen kauye.

Wannan abun yajawo ma Daddy farin jini kauyenmu,addua ake masa baji ba gani sbd yakashe kudi kamar baisan ciwon su ba,Saida ya tabbatar bamu da bukatar komi na rayuwa sannan muka shirya tafiya england,munyi kuka sosai nida yan uwana Da Baba yana ta jaddada mun na rike ibada na rike gaskiya da amana,naji tsoron Allah a duk inda nake,sannan na zauna lafia da iyalinsa da y'ay'ansa inyi hkr da duk kalubalen dazan fuskanta acan,nasiha sosai yayi mun sannan mukabar Maiduguri cikin yardar ubangiji,wannan shine asalin zuwana Uk Faa kuma shine asalin k'addarar dake samuna ayanzu, sannan inaji ajikina cewar ba karshen k'addarar kenan ba,amma Ina fatan ace komi zai biyo baya yazo mun Ina tare da ahalina acan abadam"

Motar tayi parking dai dai get din Hostel dinmu na mata,ya juyo yana kallona ido cikin ido bazan iya fassara wannan kallon nashi ba,kamar yadda bazan iya jurar sa ba na sadda kaina k'asa Ina wasa da yatsuna, ban tsammata ba naji sa a kusa dani sosai sabanin da da yake can jikin kujera, Saurin kallon sa nayi ganin ya rik'o hannuna cikin nashi, zuciyata sosai take bugawa tsoro fargaba yana kamani duk da nasan cewar bazai mun komi ba,amma wannan shine karon farko a rayuwata da wani namiji baligi kamarsa ya rikemun hannuna.

"Rabee'atu"

Runtse idona nayi na kasa kallonsa,Sbd sai nakejin kamar bada ainahin muryarsa ya kira sunana ba,wannan kalarta da sautinta ya ratsa mun zuciyata, bai matsa mun saina kallesa ba ya cigaba da cewa, "Daga yau Fareed ya zama guad naki,sannan duk wuya duk dad'i zan kasance a bayanki zanyi bakin kokarina wajen ganin wani abun bakin ciki ko na kunci baisake samunki ba,koda ya sameki zan kareki yadda bazai hurting d'inki ba,tabbas bazan so ace zumuncin dake tsakanin Daddy Da Baba ya lalace ta dalilin ki da iyalinsa ba,amma a wannan gab'ar ya zama dole ki nisancesu na tsawon lokaci har sai insune suka buk'aceki,sannan kamar yadda kike fata da burin zuwa Gida zan taimaka miki komi kikeso Rabee'atu innace komi ina nufin komiye,inhar ni Fareed wazeer zan iya to zanyi dominki"

Bazan Iya hana idona kallonsa ba,sbd kalaman da yake anfani dasu wajen yimun mgn suna ratsa mun zuciyata,suna sanya mun jin wani iri sosai lumshe idanunsa yai yana tabbatar mun, "Faa"

Sai mgnr ta mak'ale mun,matsa hannuna yai kad'an wanda yasa naji tsikar jikina tatashi,naso anshewa ya hanani calmly yace "Fadi duk abunda ke ranki"

Miyau na hadiye daker Ina cewa, "ban.....bazan so na shiga rayuwar ka na sanya ka cikin matsalolin ba,bakai kama da masu hayaniya ba,baka sabada pressure ba karka sanya kanka cikin jarabawar rayuwata pls"

Jiyo da fuskata yai muna fuskantar juna,Ya ilahi na anbata a zuciyata sbd yadda ya tsayar da fuskar daidai tashi yana kallona, saurin risinar da kwayar idona nayi sbd bazan iya ba.

"Why bazan sanya kaina ba,kefa musulmace kamar ni,kinga kuwa duk inda musulmi yake d'an uwan musulmine,inhar ka cika cikakken mai sani a ilimin musulunci bai dace kaga wani cikin damuwa da matsalar rayuwa kana da damar agaza masa ka kasa yin komi akai ba,karki sake fada mun haka ni yayanki ne uwa daya uba daya ki dauki hakan har a zuciyarki,kuma zanyi komi domin farin cikin ki"

Hawaye suka silalo mun masu zafi,bazan iya kwatan ta abunda nakeji ba da irin wannan karamcin nashi, "Dare yayi sosai da safe zamu ida mgnr,sannan pls kidaina damuwa kin gani exam tana hanya bazan so ki samu matsala ba kinji"

Kaina na d'aga muryata ta d'an dishe nace, "Na...nagode"

D'an murmushi yayi ya bude motar ya fito ya zagayo ya bude mun, ganin k'afata babu takalmi sai ya duk'a ya cire cobus d'insa masu tsananin kyau duk da zasuyi mun yawa,amma ba sosai ba ya durkusa ya kama kafana ya sanya mun.

Kallon juna mukai ya lumshe mun idonsa kurin yana bani wuri na sauko,yaban bag d'ina sannan yai tsaye yana jiran na shiga get din,

Saida nazo bakin get din na jiyu ina kallonsa,murmushi yayi yana mun bye na jinjina masa kai kurin na shige get din mai gadi yana rufewa.

Su sakeena duk sunyi bacci nayi wanka na fito na shirya na duba abunda suke dashi na dafa tea naci da bread,duk da yunwar amma na kasa ci da yawa sbd zuciyata babu dadi cike take da abubuwa da basan ta yadda zan warwaresu ba.

Sallolina na gabatar nayi karatun qur'ani sannan na koma gadona na kwanta bayan na sanya wayar a caji nan gefena jikin socket, text d'insa na gani kafin na shiga duvet yana ce mun,

"Have u eating something?"

Idona na lumshe wani abu na mun yawo a raina, na masa reply da cewa "yes I did it"

"Lemme call u"

Abunda ya maido mun kenan,na gyara kwanciyata na shiga duvet ina kallon kiran nashi na shigowa da yake silent take,kamar zanga fuskarsa a jikin wayar yadda nake kallon ta, kafin ta tsinke na dauka ina yin shiru kawae,

"Are u sleeping?"

Na girgiza kaina saina tuna ba gani yake ba nace, "Aa,yanzu dai zanyi"

Yai d'an shiru na wani lokaci sai numfashin juna kawae mukeji kafin yace, "ok kiyi addua saiki kwanta Goodnight"

Lumshe idona nayi kafin nace murya can k'asa, "Goodnight"

Na sauke wayar na rufe idona Ina addua na gama tas sannan na kwanta,tunanin nika suka cika zuciyata harma na rasa wanda zan dauka a ciki,amma Wanda yafi kowanne karfi Tunanin firarmu da Faa, bansan miyasa duk tashin hankalin da nake ciki bai tsaya mun ba sai mgnr da mukai dashi,a haka dai barawo bacci yazo ya saceni cike da mafarkai daban daban.

Mom muhsen✍️