Ten
by @mommuhseen
*_💔RANAR YABO💔_*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
By
Mom muhsen
&Asaad
Ten
Da safe da muka tashi Su Jennifer da merry da Sakeena kamar zasu karyani sbd farin cikin ganina da sukai, sbd sun dauka bazan dawo ba duk hankalinsu ya tashi suka rok'eni inyi hkr koma miya faru karya shafi karatuna,nace musu babu inda zanje in sha Allah sannan suka shiga had'a mana abun karyawa ni kuma na shiga wanka bayan na fito ina shafa kiransa ya shigo mun, Merry ta mik'o mun wayar tana cewa "Jiyan nan Fareed ya ban tausayi shida Daddy,don Allah Bia karki sake kwatanta guduwa"
Murmushi nayi mata kawai na dauki kiran na barsu suna sake jajanta mgnr, cikin sanyin murya nayi masa sallama tare da cewa, "Ina kwana"
Muryansa da alamun bacci yace, "How's your night"
"Alhamdulillah,kamar ma baka tashi ba ko?"
Gyara kwanciyarsa naji yana hamma tare da salati sannan yace, "yea,idona naji ya bude sai kuma ya sauka akan wayana, shine na kira naji ya kika tashi"
D'an murmushi nayi Ina cewa, "yau bamu da karatun safe ne?"
"Uhmm"
Na makale wayar Ina cigaba da shafata, bai sake mgn ba nima bance masa komi ba, har na gama shafar na gyara fuskata naji yace can kasan makoshi, "what are doing?"
"Nothing"
"Uhm,kina dressing ne ko?"
Nai masa shiru naki mgn,murmushi naji yana yi k'asa-k'asa kafin yace, "Wane kalar kaya zaki sanya to"
"Zanyi breakfast goodbye"
"Aa,ni ban sallameki bafa"
"Please ki fada mun kinji"
Runtse idona nayi nace , "I will text u later........no pls ni yanzu zaki fada mun"
Dafe kaina nayi jin yadda yake kokarin yimun wata Shagwab'a kamar karamin yaro, "Faa yunwa nakeji fa"
"Please"
"Nita ban saka kayan ba tukunna........Ya salam minayi haka? Cikin sauri na kashe wayar na jefa a gado, Jenny na dariya kasa-kasa na kalleta nace, "Dariyar miye ne?"
"Aa ina ruwanki,kada inyi dariya kenan?"
Na harareta kawae kafin na tashi na dauko kayana riga da siket kananu sannan na zauna mukai breakfast d'in tare,nida Sakeena plate guda suma su biyu plate dinsu guda, koda muka gama bamu fita ko ina ba kowa bitar karatunsa yake, amma ni rabin hankalina yana can gida wajen Daddy,a hankali na ciro wayar na cire blocking din da nayi masa sbd inya kira karta shigo,bazan iya juran ganin kiransa na shigo mun Ina ignoring ba,aiko ko five minutes banyi da ciresa ba kiransa ya shigo mun, runtse idona nayi Ina daukar kiran tare da Sallama........"Rabi'atu fushi kike da babanki ko?shiyasa kikai blocking dina ko Rabibi"
Yana mgnr muryarsa ta karye sosai,naji kwalla sun cika idona yace, "gani nan cikin makarantar ku,na kasa hkr na taho da yanzu zan sa yaron nan ya kira mun ke"
Hawayen suka sauko mun,na kasa cewa komi "kizo inganki kinji Rabibi,kiyi hkr karki k'i fitowa kinji"
Muryata na rawa nace "To Daddy zan zo,kana Ina?"
Ya fada mun inda zan iskeshi na tashi na sanya hijab sannan nace ma sakeena zan je na dawo, tunda na fito nakejin wani kala ba kamar dana hangosu shida Faa suna zaune jikin wani gini.
Ina karasawa ya tashi cikin sauri ya rungumeni,Karon farko da Daddy yai mun hakan sai naji rauni na ya sake bayyana na fashe da kuka marar sauti sosai, "I'm so sorry Rabibi,I'm very sorry ki daina kukan ya isa haka kinjiko,Ina tare dake babu inda zakije da ya wuce gidana na shirya yafe koma waye akan ki Rabibi domin na tsira da zumuncin dake tsakanina da mahaifinki,amanarki yabani don ya yarda dani ya kuma sanya rai akan karatunki wanda ada ya cire tsammanin zaki sameshi,bazan bari wani abu yasa inyi disappoint dinsa ba,don haka dakin gama exam zaki dawo gida kafin da kaina na kaiki hutun kamar yadda na saba,wannan karon ma zama zanyi mudawo tare"
Duk yana mgnr ne Ina jikinsa ina kuka,kafin na ciro kaina Ina kallon sa na girgiza kaina nace, "Kayi hkr Daddy nayi rantsuwa na gitta raina bazan sake taka k'afata gidanka ba,kayi hkr Daddy bazan koma gidanka ba ka gafarceni, amma nayi maka alk'awarin babu inda zanje har saina kammala jarabawata Ina nan Hostel"
Na rik'e hannuwansa Ina rokonsa ina kuka, "kayi hkr Daddy,zaman gidan can bazai tab'a mun dadi ba a yanzu,sannan rigimar ba zata tab'a lafawa ba amma nayi alkawarin radda duk suka sassauta daga k'iyayyar da suke mun zan dawo,amma ka gafarceni ba yanzu ba Daddy,bazan so in lalata zamanka da Mami da kukai shekara da shekaru a tare ba ace lokaci daya sbd ni komi ya kare,Aa Daddy kayafe mun bazan iya ba kaji Daddy kayakuri bazan iya koma wa ba"
Nazo zan durkusa masa don rokonsa ya barni anan yafiye mun kwanciyar hankali,saurin rik'enu yai idonsa yai jaa sosai yace da sanyin murya "Shikenan,shikenan ya isa daina kuka basai kin duk'a mun ba Rabibi na hkr na barki ki huce na wani lokaci,zan hkr kamar yadda kika ce amma zan kyaleki kiyi rayuwa a wani wajen daban ba bacin ina raye kuma ina cikin kasar nan"
"Fareed ga amanar yarinyata,don Allah ka sa ido akanta kajiko Allah yai maka albarka,bacin kai jiya kila da yanzu ba wannan mgnr ake ba,sbd hankalina ya gushe balle inyi tunanin ayi tracking layinta a ganota,nagode sosai........Daddy ka daina gode mun haka,Rabee'atu nima qanwa ta ce xanyi komi domin ganin wani abu baifl faru da ita ba"
Ya d'an jashi jikinsa side hug yace "Thank you"
Ya kamo hannuna ya dank'a mun kudin da ban ansa ba hannun Fadeel, "ni ubane wajenki Ina da daban baki dukkan abunda yake mallakina ne,dukiyata takice Rabibi babu mai iko da ita sai ni don haka gori ko wani habaici ya daina d'aga miki hankali kinjiko,sannan duk sadda bukatarki tataso karki nemi kowa ni zaki nema kinji ko?"
Kai na na d'aga inajin kaunar Daddy har cikin raina, "Nagode Daddy,Allah yai maka sakayya da gidan aljanna ya kara maka lafiya da zama lafiya"
Murmushi yayi yana shafa gefen fuskata yace "amin"
Sannan ya shiga driver sa yajashi suka bar cikin makarantar,inata sharar hawaye ya taso ya iso inda nake yana kallona, "It's ok kinji"
Na goge fuskata da hannuna sai ya sake van hanky dinsa bacin na jiya ma yana wajena a daki, "kin b'ata kwalliyarki"
Kallonsa nayi da mamaki sbd nasan ni bacin kwalli ban sakama fuskata komi ba, na hararesa ina cewa "ni banyi kwalliya ba ai"
Murmushi ya saki mai kyau yana cije gefen bakinsa yace, "Dagaske nake miki,bakiga idonki ba"
Na sake harararsa kad'an Ina sanya hanky ina goge idon nawa, "kibar gogewa hakanan kina b'ata idonki da bakin abu"
Kallonsa nayi ya d'aga mun kai yana ansar hankyn daga hannuna ya matso sosai gabana yana cewa, "lemme see"
Kawai yakai hanky daidai gefen idona inda kwalli ya d'an b'ata yana goge mun a hankali, na kasa d'agowa sbd tsaf idona zai shiga cikin nashi,yadda yake goge mun zaka dauka wata yar shekara biyu yake ma wa sbd karya ji mata ciwo, "miye sunan abunda kika saka a idon ki?"
Nad'an dago fuskata aiko karaf muka had'a ido jinai zuciyata ta tsaya cak da aiki na yan seconds, cikin sauri naja baya k'adan ina juya baya zuciyata na buga mun, "zan....zan koma Hostel"
Rungume hannunsa yai a kirjinsa yana d'an smile mai tsananin kyau yace yana kallon yadda ta juya masa baya tak'i kallonsa, "I'm feeling hungry,"
Na d'an juyo ina kallonsa, ya barke fuska sosai "jiya ma fa banci komi ba in the night"
Na kasa kallonsa sosai sai kakkauda kai nake yi nace, "Bari naje daki na maka wani abu"
"No,Muje restaurant zaki rakani?"
Kallon sa nayi kafin na sauke idona nace, "Baka gudun a ganka restaurant kana breakfast"
Wayarsa yake daddannawa yana cewa silently, "So what?"
Wayar yasa ga kunne yana kallona da idanunsa tubarkalla farare k'ar dasu,gasu da lashes kamar na mace sannan ba kananu bane haka bazaka gane girman su ba sbd koda yaushe a lumshe suke,wanda hakan natura dinsa ne,ban san miyasa ba yan kwana kin nan bana iya jure kallon da yake mun, da kwayar idonmu ta hadu sai inji zuciyata ta buga da karfi,shiyasa nake kakkaucewa, ban san miya shagaltar dani mu ba saidai mukaga motocin sa sun iso,guard dinsa yazo zai bude mun motar ya hana shi,ya zo ya bude mun da kanshi yana kallona,na d'an bata fuska zanyi mgn ya lumshe mun idonsa yana girgiza mun kai,dole na hkr na shiga ya zagayo shima sannan motocin suka fice daga mkrntar.
After 2 weeks
"Fadeel yau ma ba zaka shiga makarantar ba?kwana uku bakaje ba ka kuma fi kowa sanin exam kuke,sai kace mun kana rubuta wa a online,yanzu exam din online har exam ce Fadeel?"
Mami ke tsaye bisa kanshi tana masa mgn shi kuma yana cikin bargo kamar bayajinta, saida takai aya sannan ya zame duvet din daga kanshi yana kallon ta, yana yinsa data gani yasa ta zauna gefensa tana tab'a goshinsa tace "Fadeel baka da lafia?kan ka da zafi zazzabi kake yi shine baka gaya mun ba?"
Duk tabi ta rud'e tama mance fadan zuwa makaranta take masa, tashi kayi wanka Bari na kawo maka breakfast sai muje asibiti, "Bana son zuwa Hospital Mami"
"Ok lemme call a family doctor saiyazo gida ya dubaka"
Duk ta damu sosai ta sake tab'a kanshi dake da zafi sosai, tatashi tana cewa "make sure kayi wankan kafin na hado maka breakfast din"
Kai kurin ya iya jinjina mata yana maida idonsa ya rufe, kanshi ke wani irin sara masa kuma yasan yana da nasaba da abunda ke damunsa cikin zuciyarsa, ya hana shi kwanciyar hankali baya samun isashshen bacci komi ma bayajin dad'in sa, shiyasa koda aka fara exams din tun da yaje sau biyu bai kuma zuwa ba,sai dai ya kunna system dinsa yayi ta online, saidai idan friend Dinsa sun so ganisa suzo gida,shi ko fita yanzu ba yayi ko party club da suke d'an zuwa da su Bilal yanzu yama mance rabon da yaje ko Bilal din yaxo su tafi cewa yake bazashi ba,jinsa yake lonely kad'aici yakiji sosai a rayuwarsa ji yake kamar babu kowa tare dashi, bayajin dad'in komi abinci yana sawa bakinsa zaiji kamar d'aci yake masa,daker zai spoon uku zuwa biyar ya aje,saidai yasha fresh milk ko fruits.
Banda Mami babu mai kulashi a gidan,Daman yasan Zainab tuni bata yinsa haka Haleem tun bayan zuwan Bia ya sauya masa sosai,har gara Heedaya takan shigo inta ga ta wuni bata ganshi ba ta dubashi,tayi masa fira tatafi.
Daddy kam bama shiba kowa na gidan rabon dasu sanya shi idonsu harsun mance, sbd tsakar dare zai dawo kuma da abincin sa yake dawowa,yaci ya shige part d'insa yai kulle da mukulli kuma asubar fari zai fice ba mai ganinsa sai maigadi shima sbd bude get.
Gaba d'aya gida yai masa bak'i sannan idan za'a shak'e masa wuya bazai kya fitowa farat d'aya yace ga dalilin shigarsa wannan halin ba,amma kuma deep down yasan cewa cikin ransa akwai wani abu,akwai abunda babu da yasa rayuwarsa ta koma upside down.
Sadda mami zata shigo ya fito wanka yana goge jikinsa, ta tsaya tana kallon yaron nata wanda takejin kamar bata tab'a haihuwa ba sai akanshi,sbd yadda take masifar jinsa a ranta, ko Heedaya da take k'arama bata jinta yadda takejin Fadeel cikin zuciyarta,duk girman sa hakan bai hana ta tayasa shiryawa shi harma ya saba indai baya lafia to kusan komi Mami yi masa take,
"Na kira Doctor yana hanya yanzu kasha tea ga planten nan na soya maka da egg ai zakaci ko?"
Shifa babu ma appetite bakinsa ko ruwa jinsa yake babu dad'i, amma ganin duk ta damu shiyasa ya zauna bayan ya shirya cikin kananun kaya da sukai masifar karbar jikinsa sai zuba k'amshi yake,ta soma bashi a baki yana ansa a hankali yana duba wayarsa, time d'in jarabarwar su ta yau yake duba wa yaga karfe hud'un marece zasu shiga su fito six, anya zai iya kasadar sake shiga makaranta?inama akwai wata hanyar da zai gujema ganin abunda yake sashi rashin lafia yai exam dinsa ya yatafi ba tare daya gani ba,amma babu wata hanya illa rashin zuwan,to yau kuma dolensa yaje sbd lecture baya dora exam dinsa online,ko waye kai dole ka shigo makaranta ka rubuta ko kuma kafad'i course din.
"My son"
Mami ta kirasa cikin damuwa ganin yadda fuskarsa ta bayyana halin da zuciyarsa ke ciki, "Whats wrong with u,I don't want to see u in this mood zuciyata tana tuhumata akan ko na gaza maka wani abunda zakai farin ciki ne?"
Lumshe idonsa yai baisan mizai ce mata ba,dai-dai nan wayarta tayi ring taga doctor ne ya iso, ta dauki kiran tace "ka iso kawae doctor muna tare dashi dakinsa"
Ta sauke wayar ta sake kai cup din tea bakinsa, yad'an sha rabi yace ya koshi kallon plate din tayi tana cewa, "Shiyasa duk ka rame dubi yadda wuyansa ya nuna,haba mana Fadeel?"
"Mami bakina babu appetite,komi nake ci banajin dan danonsa"
Ta shafi gefen fuskar sa tace, "Insha Allah zaka warware kayi masa bayanin komi kajiko"
Duk abunda ya dace Doctor Arham yayi masa yayi mashi ya kuma rubuta drugs sannan yace, "Idan har baka daina rashin baccin ba,da kuma rashin cin abincin kayi contacting dina sai muga what next da zamu yi"
Mami ta tura drugs d'in ta waya za'a kawo yanzun,ta kasa tafiya ta barshi shi kuma yana son ya kad'aice shi d'aya.
"Mami kije zanyi bacci yanzu"
"Ka tabbata babu wani damuwa bayan wanda ka sanar da Doctor?"
Shiru yayi sbd bai saba mata karya ba,amma kuma bazai iya fadar abunda ke cinsa a rai ba, sai yace "I'm missing Daddy a lot Mami,ko a waya baya picking naje office nasu rannan ma hanani shiga security sukai wai baya son hayaniya,Mami Ina jin babu Dadi"
D'an gajeran tsaki taja duk da ya sosa mata inda ke mata kai-kai amma ba zata nuna sarewarta ba,tanaso taga ita dashi waye zai gaji ya sauko?waye bai iya rayuwa saida guda tana so tasan wannan,"
"Inhar akanshi kake wannan damuwar dama ka bari,Daddynku ba abunda yakeso sama daku da farin cikin ku,wannan punishment d'in da yake ganin yana mana bazai canza komi ba,Ina mai tabbatar maka duk inda yake yama fimu jin ba dad'i,kuma soon zai sauko ya dawo fiye da dacan kafin musan wannan la'ananniyar yarinyar"
Jiyai kamar an buga masa guduma cikin kanshi,ya runtse ido yana kiran sunan Allah zuciyarsa na zafi kawae sbd wannan zagin da Mami ta mata, gabansa ya hau fad'uwa sosai.
"Inhar akan ra'ayina ne yake duk wannan wallahi tallahi bazan sauya ba Ina kan bakana nidashi shege ka fasa"
"Ka kwanta kayi baccin ka indai Daddynku ne zai zo gida ya mance komi,sai idan baiji bakada lfy ba kasan irin son da yake maka kuwa?"
Shidai kwanciyar yayi yana rufe idonsa yasan kozai kai gobe haka baccin ba zai zo masa ba,sbd zafin data had'a masa a kwalwarsa da zuciyarsa.
Mami tana fita ta koma part dinta sbd tana up bata da aiki office,system dinta ta kunna tana wasu abubuwan,ita kanta tasan neman abunda zai dauke mata hankali daga tunanin mijinta take,sbd idan tace batai kewarsa karyarta tasha karya,darare nawa suka shud'e idonta biyu kan kunnenta zai dawo kan kunnenta zai shige part dinsa ya sanya mukulli,tunda abun yafaru bata tab'a yunkurin koda kiransa a waya ba,balle taje ta dubashi a office sau da dama zatace to ko bashida lafia ne,sai kuma ta danne zuciyarta ta kawar da abun ita ala dole sai yagane muhimmancin ta,da kuma nuna masa cewar shine marar gaskiya ba ita ba.
Duk abunda take tunanin zatayi ya kawar mata da tunanin son jin halin da yake abun ya faskara, ta rufe system d'in tana dafe kanta dai-dai nan Zainab ta shigo falon.
"Mami bakida lafia ne?"
Danne damuwarta take koKarin yi tace "Aa stress ne kawae"
"Stress kuma mami?keda kike up bakya zuwa aiki kusan kwana biyar kenan,kuma gidanma ba abunda kike sai hutawa shine kuma zakice stress"
Cikin borin kunya tace, "Ina zakije ba kin dauki hutu na?"
Zama tayi gaban Mamin cikin karyar da kai da neman alfarma,ta rik'o hannunta cikin roko tace "Mami don Allah ki janye waccen mgnr da kikai akanmu game da Bia,ban hanaki fushi akan lamarinta ba bance kuma ki sauka daga ra'ayinki ba,amma kibarni na ringa zuwa ganinta mkrnta don girman Allah Mami..........Zainab!"
Mamin ta fad'a cikin wani irin fushi daya taso mata lokaci guda,daman kuma neman inda zata sauke pressure dake kanta take, ta nuna ta da hannu tana cigaba da cewa "Wannan shine karo na karshe da zaki sake zuwar mun da mgnr wannan yarinyar,wallahi tallahi zainan zan iya yafeki cikin y'ay'ana akan wannan tsinanniyar,ke ko kishina bakya yi?duk sbd ita muka shiga wannan halin a cikin gidan nan,Duk saboda ita ne ubanku ya juya mana baya ya daina hudd'a da kowa cikinmu,tunda ta shigo rayuwar mu ban sake zama lafia da ubanku ba,shine kike son na yarke miki kici gaba da mu'amala da ita ko?to kizab'a ni ko ita bazan miki dole ba amma dole kiyi d'aya cikin biyu"
Hawaye Zainab din keyi masu k'una tace, "Ki yafe mun Mami,ki gafarceni bazan sake miki mgnr Bia ba har abadan,bazan sake tada mgnr ta ba har abadan ki yafe mun bazan iya zabar wani akanki ba Mami ke uwace kina sama da komi,kiyi hkr"
Tatashi ta fice daga falon tana jin wani irin tausayim Bia na mamayarta,fitar da zatai ma ta fasa daman kuma sbd ta biya ta ganta ne ta tsiri fitar,to yanzu kuma ina zata?
Mami ta dafe kanta cikin jin komi ma ya kunce mata,sai kawae tatashi ta dauki key d'in motarta tayi rolling da veil sannan ta fito bata cema kowa ga inda zata ba sai kawae ta shiga mota ta fice daga gida aguje.
Mom muhsen✍️