18
by @maidambu41
*❤️🩹SO da CIWO❤️🩹*
®©Ramlat A Manga
Mai_Dambu
Paid book
*Assalamualaikum everyone yau mun zo muku da ingantattun maganin mata daga shahararriyar mai maganin nan De Majestic Aprodiasic best kayan mata ever, We have the best kayan mata 100 natural kada ki zama Bora a wurin namiji kada ki zama koma baya a wurin kishiyoyin zo ki gwada ki yadda babu wacce zata d'aga miki kafada macen da tasan ciwon kanta ita take gyara buje 😆🤣 anayi ana sha'anin arziki*
Muna d ingantatun kayan mata kamar hka:
Maganin sanyi
Exclusive Tsumi
Abulbulo
Gumbar Madara
Gumbar budurci
Zumar budurci
Zumar kacha kacha
Royal Honey
Zumar goran tula
Garin Emergency
Garin kwatai
Sallanta
Dan wata bakwai
Spoil her HQ
Back to virgin set
Exclusive zuma
Tsumin Ayu
Man Ayu
Maniyin Ayu
Zumar Ayu
Gaban Ayu
Kazar Mallaka
Kazar sirri
Zabon Amare
Dan Shila
Ciccibi
Dambun nama
Man power
Yajin Maza
Men energy
Gamu bukatar kayanmu su tuntubi wannan number *** we are the best among the other'
18
"Sai ka zuba idanun rayuwar Yarinya irin Maamah ya lalace?" Baffa Junaid ya tambaye shi, kasa magana yayi kanshi ya dauki zafi muryanshi a raunane ya ce mishi. "Tow ya zanyi? Ya zanyi?" "Allah ya kawo mana mafita!" Inji Baffa Junaid yana me saka Baffanmu a gaba har parlournshi.
Shigowa Dadah tayi da farin goran zam-zam, ta nufi dakin Yaya ana ta fama har lokacin juyi kaina yake. "Hassanah maza bata addu'ar ta sha Allah ya kara mata hakuri da dangana." Haka kuwa ya faru, ana bani na ji kamar zan yi amai kafin na shanye tas, ta shafa min a fuskana. "Ya ce gobe a je da goran zam-zam a yi mata addu'a na tsawon kwanaki goma, Allah ya jikan Abidah yace makaranta da almajirai sunyi rashin uwar marayu!" Domin duk ranar Alhamis da juma'a ana abincin sadaka da a kwanaki biyu nan. Haka yasa almajirai suke ta kuka idan watan azumi yazo har ayi sallah hidima take da almajirai da mabukata, Yaya ta nemi lahira da duniya.
Tunda aka bani ruwan nayi ta yunkurin amai amma ban yi ba, sai na lafe a jikin Mama, nayi ta sake ajiyar zuciya ina jin wani abu da ya tsaya min a wuya na yana sauka, shafa bayana take a hankali tana tofa min addu'a, kafin wani lokaci barci yayi gaba da ni. Gyara min kwanciya tayi zata mike na bude idanun da sauri. "Mama!" "Na'am Rahmatullah!" "Kada ki tafi ki barni." "Tow Maamah!" Haka tayi ta shafa bayana, har Hamma Abdulhameed ya dawo ya saka min drip da allurai, haka nayi ta barci wuni guda washi gari da na farka nayi sallolin kaina, aka kara bani ruwan addu'a na sha, kafin na zauna nayi ta kuka don sai lokacin nake jin kuka na zuwa min, nayi kuka har na godewa Allah. Mama taso na koma dakinta na ce su bar ni ina jin wani abu kamar Yaya tana raye a kusa da ni, kome na kaina ya b'ace babu lissafin kome sai na kewar Yaya, wannan shine mafi girman ciwon da na fara ji a rayuwata na rasa Mahaifiyata. Tunda na fara iya tashi nayi sallah abinci kuwa saboda da shi har na manta. Bakin tea nake sha kawai shine abincina. Shima ina sha ne don babu yadda na iya domin bana iya jin dadin kome a bakina. Ranar da aka yi addu'ar uku, wasu suka fara tafiya domin ance ba za ayi bakwai ba. Akwai wasu daga cikin Yan uwan Yaya maza da mata wanda suke yan uwa sai wanda suke daki daya. Aunty Zakiya, Hajiya azumi, Umma karama, Aunty Raliya duk sun tafi Dr Mehra a waya yayi mana gaisuwa kafin ya ce a hada shi da Umar dakyar aka nimo shi ya dauki wayar ya tafi can dakin Mama dama har da ita ya nima suka yi magana.
Bayan sun tafi ranar da aka cika kwana hudu da rasuwar Iyayen Sharahbil suka zo, a lokacin naji bana kaunar ganinshi, koda aka ce gashi rufe dakin Yaya nayi na ciki suka yi ta magana ban kula su ba, na tsane shi na tsani na ganshi domin ina ji a raina sanadin aurenshi na rasa kome nawa, har suka fita dakin Mama suka shiga suka gaishe ta. Da yan uwanta waɗanda basu tafi ba. Haka akwai wasu kawayen Hajiya Amrah din, wacce na santa itama Yar Uwarsu Baffanmu ne wato Hajiya shekara ita ce da yake bakinta babu linzami ta ce . "Ba a san irin rabon da yake tsakanin Yaran nan ba, don dama manyan sun ce rabo yana kisa, tow Allah ya jikan rai." Bata dire ba Umma Husainah ta ce mata. "Ba irin wannan rabon yake kisa ba, sannan ai Hajiya Abidah ba cewa tayi bata son auren nan ba, kanwa uwar game cewa tayi a kawo shi ayi gwaji sannan idan aka yi gwaji sai san matsayinsa. Yan fashi suka shigo gidan suka kashe ta ba wayen gari aka yi aka gawarta ba, ita fa mutuwar shahada tayi tunda dai bata yi mafi munin mutuwa da aba son ayi shi ba, tayi irin mutuwan bayin Allah a biyo ka a kashe ka ba tare da ja tsarewa kowa kome ba, ka ji baiwar Allah Ubangiji ka samu yi kyakkyawan karshe karshen da zai zama abin alfahari ga danginmu da al'ummar musulmi bakiɗaya." Umma Gambo ita ce Autarsu Mama ta ce mata. "Amin Ya Allah, irin mutuwarsu Malam Jafar da Albani zariya ba, irin mutuwar da ko makiya sun san sun tafi a dacewa, kai Allah mun gode maka, Abidah fa alkhairinta har dake shekara bata bari ba, kin tuna shekaran 2003 da muka tafi aikin Hajji aka sace miki kudinki baki da kudin awon kayanki dole kika cire wasu zaki zubar ta amsa ta saka a cargonta kin manta ne karshe kayan kamar ya b'ata da tazo Umara ta saya miki makamancin kayan ta kawo miki da sati biyu sai ga kayan sun iso ta kara hada miki ta kawo miki? Hala ita Hajiya Amrah bata san Hajiya Abidah ba, kaf zuriar Datti kowa yasan mace me kamar maza, Matar da ta saka Jamal a gaba da wuta idan baya son Matarshi ya sake ta da yake mata rashin mutunci, danta ne fa amma sai da manyan Unguwa suka taru kanta kafin ta hakura wallahi samun mace irinta a zuri'a haske ne. Addah Hassanah yanzu zuri'an Yaya Abidah sun rataya akanki yakin da ta fara a sai a dasa daga inda ta tsaya ."
"In sha Allah, kamar yadda ta ce idan an kawo Sharahbil aure nan ko gobe ne, idan kuma bai zo ba tow aure ya tashi." Abin da ya bawa Hajiya Amrah mamaki kenan wato tana murnan Hajiya Abidah ta mutu, maganar test ya kare ashe ba Hajiya Abidah kaɗai ba ce akan lamarin har da kishiyarta da sauran dangi baki daya. Abun da dake ta ganin kiri kiri kome yana shirin jagulewa , mikewa tayi tana faɗin. "Allah yasa ta huta!" "Amin Ya Allah!" Suka fada.
A hankali abubuwa da dama sukayi ta faruwa, Iyayen Sharahbil basu kawo takardan test ba, ni kaina ina nan ban san me yake faruwa ba. Sai a lokacin Heemah ta dawo jikina, shima tana zuwa bayan minti kadan za a turo kiranta. Wai inji Aunty haka yasa nake jin kamar ni daya na rage yayuna mata sun zauna a gidan har aka cika sati daya, ranar da aka yi addu'ar bakwai Innani zata tafi itama ranar daurewa nake amma ni daya nasan yadda nake ji, rana a gaba suka saka ni suna kuka, Mama ta shigo tayi ta musu fada tana cewa don Allah su kyale ni kada su d'aga min hankali. Haka suka tafi suka koma gidajensu, Innani ta koma Gombe, gidan ya rage daga ni sai Mama da Uwani dasu Hamma Umar, wanda muka maida zaman dakin Yaya kamar tanan, an bincika ko ana bin ta bashi aka samu ita take bin wasu ma, masu tsoron Allah sun kawo aka ce idan ta cika kwana arba'in za a raba mana gadonta. Haka muka yi ta rayuwa da Mama. Idan nayi barci kasancewar akwai maganin barci a cikin drugs dina, cikin dare baffanmu yake zuwa ya kai ni dakin Mama. Kusan rabin rayuwata nayi shi da Mama ne, domin sai daga baya nake ganewa Mama ita ta haife ni ba, shi yasa shakuwa bai shiga tsakaninmu ba, sai da na fara zama yan mata, idanun Yaya ya tsaya a kaina. Saboda yadda muke ƙawance da Raheemah. Gani take yadda nake son Raheemah ba wani abu ba ne akwai abin da yake faruwa a tsakaninmu, sai ga shi. Ta samu babu kome kawai kaunar zumunta nake mata, da asuba ina sallah xan dawo dakin Yaya na karasa kwanan, haka muka yi ta gurguwara har aka samu sati biyu, a lokacin maganar auren ya kara tasowa a ranar na fahimci koda Allah ya dauki Yaya bai bar ni haka ba, domin a yau naji Mama tana sa"in"sa da Addah Mairo, wanda har take cewa saboda yaya take d'aga musu kafa wallahi idan basu lalata shirin da suka yi ba sai ta bawa kowa mamaki, wasa wasa sai na fahimci Mama ta danne zafinta ne don ta bawa Yaya damar zama shugaba a cikin gidan, yanzu da babu Yaya Mama ta amshi ragamar shugabancin gidan da na dangi, Tsayawar da Mama tayi wasu na fada a dangi tana biyan alkhairin Yaya ne, domin har yau babu wata yarinyar dakin Mama da take da matsalar miji, a yau da ake sa'in'sa sai da ta cewa Addah Mairo cewa. "Idan har kin ji zafi yanzu ki turo min Addarsu gida, akan auren Maamah babu wnada ba zan b'ata da shi ba, idan ta kama aurena ne zan hakura da shi amma ba zan tab'a ja da baya ba san na tsayawa Maamah a kowani bangaren.". Tunda na ji haka na koma tattara kayana, na koma dakin Mama, ma bar dakin Yaya ina hawaye na ce ni daya domin wani lokaci sai naji kamar ina tare da Yaya ne. "Kin ce ba zaki bar ni ba haka, Mama ta dawo inda kike ta tsaya min Yaya wallahi nima bana son auren tunda ke da Mama baku so " ba fada cikin shashekar kuka. "Dama waye zai miki auren dole my princess, ai ko lakutanki aka yi sai inda karfina ya kare balle kuma ina tare da my little princess." Juyawa nayi na kwantar da kaina a kafad'arta ina faɗin. "Mama da ke da Yaya na rasa waye nafi so, na rasa waye yafi sona a cikinku. Na rasa waye nake nafi so a cikinku." Shafa kaina tayi yana faɗin. "Ya Abidah ta bani ke ne saboda tana jin kunyar a ce ita ta haihu lokacin Ma'u tana goyon Sajidah, Salaha tana da cikin Ibrahim. Shi yasa har nono ni da ita muka shayar da ke, domin muna sonki sosai, kina tare da iyayen da su ke sonki, and listing to me carefully. Babu yawo babu chat wayar tana wurina."
Daga nan muka koma dakinta da zama, amma ba zan boye yadda nake kewar Yaya ba, an hanani fita kuma an saka tsaro a kofar gidanmu, saboda yadda suka ce zasu zo domin ni.
***
Rano
Kuwa abin mamaki baya karewa, domin duk yadda Laraba ta ci alwashin ganin bayan Boɗɗo sai gashi ko tari ta kasa abin da ya bata ran yadiko kenan, domin kowa ya san ba a dawo da Labibah ba, abin bai bawa Sahura mamaki ba domin tasan matukar Innar Ayuba tana raye ba zata tab'a barin wani ya ji kunya ba, tana mamakin halin yadiko jiya tana jin yadda suke ta zagin Innar Ayuba din Mijinta yana shigowa ta tsare shi da mita kamar zata dake shi ta ce mishi. "Kana da bakin yin magana akan Innar Ayuba bayan yadda Yaranta suke tsaye akan Dan Mama? Wallahi ka ji tsoron Allah ka rabu da Yaya Bashir hassadartasa ta kare mishi, duk wanda aka yi irin wannan tabargazan a gidanshi ya goyi bayan aikata haka kana tsammanin mutum ne? Ai wallahi ka kiyaye kanka da shiga shirginsa domin babu alkhairi a tare da shi domin ba mutumin kirkin da dansa zai yi haka ya ce sharri aka mishi." Daga haka ta sake labulen dakinshi ta wuce dakinta. Tana mita ita taba son rashin mutunci, taya zai nemi rusa mata goben danta, tsakaninta da danta kayan masarufi idan yazo hutu hatta abinci da kudin kashewa Ibrahim yake bashi, tsaki tayi tana faɗin. "Haukar banza da cutar hassada ban da haka taya zasu daurawa wacce babu ruwanta laifi."
Kwanan Lantanah biyar a rano ta koma kano, inda ta ga jikin Ma'aruf yayi kyau gwanin ban sha'awa, duk wanda ya Ganshi sai ya ce yaron ya samu lafiya, sannan ana saka ran za a mishi aikin da za a gyara mishi duburansa, Innar Ayuba taso dawowa gida, amma haka ta hakura bata dawo ba tunda Inna Lantana ta roketa ta zauna ayi aikin. Kuma Alhamdulillahi tana dawowa da kwana biyu aka yi aikin, idan ka gansu hankalinsu duk ya tashi, musamman Labibah da take ta kuka gashi yarinyar tayi farin jini don maza hari suke ta kai mata
Amma ita ina zuciyarta da bugunsa yana ga Iro don ma ba karamin haukar sonshi take ba, anyi aikin cikin nasara washi gari asabar suka zo da matarshi da itama bata da lafiya, tunda ta ga Hajjo ta bar dakin tare da kwasar kayan wankin, anan Ibrahim yake gaya mata suma tun jiya suka zo suna asibitin, Hajjo bata da lafiya ne. "Meke damunki Haajara?" "Ciwon ciki ne tun kafin haihuwar Awwab!" "Ikon Allah! Kun yi hoton kuma?" "Eh mun yi muna jiran sakamako ne!" Shiru Innar Ayuba tayi tana kallon Hajjo. "Yanzu ya jikin naki!" "Da sauki Innah!" Ta fada a sanyaye, duk ta zube idanunta yayi yellow, "kuma baku maganin shawara?" Girgixa kai tayi tana faɗin. "Yanzu zamu fara ganin sakamakon ne kafin mu san nayi!" Ganin kamar basu son na gida itama Innar bata matsa ba, sai ta musu fatan Allah ya bata lafiya domin har ta yaye Awwab din duka - duka watanshi Bakwai ne. Yanzu abun da ya kara d'aga musu hankali, da duk inda suka yi test din ana fatar hanta ne, shi kanshi Ibrahim an ce ya fara amsar riga-kafi idan hantar ce. Shi yasa suka yaye yaron, akwai gidan Yayar Hajjon can ya kaita daga asibiti, ya dawo ya samu Innarsa ya warware mata kome, zuba masa idanu tayi jikinta yayi sanyi ranar da zulumin Ibrahim da Matarshi ta wuni, ranar Lahadi ya koma Kaduna domin ranar Monday Hajjo zata shigo asibitin, haka kuwa aka yi, dake innar Ayuba ta gayawa Labibah halin da take ciki abin tausayi sai ta fara kuka ta gama jin labarin don ita kanta tausayi Hajjon take ji, koda tazo ta gaishe ta. Ta amsa ta fi
ta ta bar su dakin. Anan ta karya kafin ta je ganin likitan...