7
*FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA IBRAHIM D. AUTA*
*LAMBA TA BAKWAI.*
"Wayyo-wayyo Allahna!"
Abin da ta faɗa kenan daga cikin bayin dafe da kanta ta ƙwalla ƙara iya ƙarfinta. Ido ta shiga zarewa tana ci gaba ihun da kururuwar faɗin ta shiga uku ta lalace a zo a kawo mata ɗauki.
Wannan dalilin ya jawo hankalin maigadin gida ya fito a firgice ya isa bakin ƙofar shiga falonsu yana bubbugawa babu ƙaƙƙautawa yana kiran sunan Jamal. Bayan ya gama zagayen gidan lungu da saƙo da zungureriyar addarsa, yana ta neman inda zai ci karo da wani baƙon fuska ko wata alamar da ke nuna an shiga gidan bai sani ba. Don duk hasken da ke gidan bai hana shi ƙarawa da fitilar hannunsa mai matuƙar haske ba.
Sosai bugun ƙofarsu ya saka Jamal diriricewa, saboda zumbur ya miƙe daga ƙasan da ya baje dafe da mararsa yana kakkarwa. Amma dole ya miƙe dafe da ƙugunsa yana tafiya kamar mai tete, a haka ya sauka daga ƙasan benen da towel a ƙugunsa ya buɗe ƙofar. Don bai tsaya wani jinkiri ba ko ɓata lokacin tambayar wane ne ba. Saboda jin muryar maigadi ya saka shi shahadar buɗewa babu shiri.
"Baba lafiya?"
Tambayar da ya wurga masa kenan a lokacin da ya gan shi tsaye da addarsa a hannu bayan fitilar da yake haskawa gefe da gefensa.
"Ranka ya daɗe sautin Hajiya da na jiyo tana ihu tsawon lokaci ya sa na ji tsoron kada a ce wani mummunan abu ne ya faru ban sani b..."
"Babu abin da ya faru je ka kwanta."
Ya yi maganar ransa a haɗe cike da jin haushin maigadin. Sumui-sumui ya bar wurin yana faɗin, "Allah Ya ƙara tsarewa." Saboda fahimtar inda lamarin ya dosa babu wani abu sai tsabagen rakin amaryar gidan. Duba da yanayin da ya gan shi a birkice sannan da sigar da ya fito a yadda yake ba tare da ya ji kunyarsa ba. Tsaki kawai Jamal ya ja ya rufe ƙofar a maimakon ya amsa masa da amin. Ya koma da sassarfa yana yamutsa gashin kansa da hannun tare da faɗin Ya Salam a cikin bakinsa ta fi a ƙirga.
Ɗakinsa ya nufa tare da kulle ƙofa ya nufi bayi cikin ƙuncin rai ya yi ta sheƙa wa kansa ruwan sanyi, sai da ya ji rabin nutsuwarsa ta shiga jikinsa hankalinsa ya dawo, sannan ya fito kansa yana muguwar sarawa ya kife a kan gado. Ajiyar zuciya ya shiga saki ɗaya bayan ɗaya yana nishi dafe da jijiyarsa da ke harbawa har komai ya lafa masa barci ya yi awon gaba da shi.
Asubar farin ya farka ya yi wanka da arwala ya fice masallacin da ke kusa da gidansa. Zuciyarsa cike da tunanin irin hukuncin da ya dace ya yanke wa Minal idan safiya ta waye. A gefe ɗaya kuma cike yake da jin haushin kansa, har aka gama sallar ya dawo gida bai daina tunanin dalilin da ya jawo masa shiga halin da ya tsinci kansa ba. Saboda tun a daren farkon auren da Nur ta karya masa zuciya bai sake saka wa kansa zai iya shiga irin wannan yanayin a kurkusa ba. Domin ya ci alwashin har Minal ta gama zaman banzarta ta bar masa gidansa ba zai yi mata kallon mace ba. Amma sai ga shi ya kwafsa tun ba a je ko'ina ba.
Minal kam kwanan toilet ta yi idanuwanta sun yi jajir kamar gautan kaji tsabar barcin da ke idon da kukan da ta sha tamkar hawayenta zai tsiyaye. A daddafe ta fito daga bayin a daidai lokacin da ta ji ana kiran sallar asuba. Wayar Gwaggo salame ta shiga kira ana ce mata a kashe take, amma hakan bai hana ta tura mata saƙon taimakon gaggawa ba, da zummar tana buɗe wayar idan ta gani ta kawo mata ɗauki, idan kuma zakara ya ba ta sa'a ta aiwatar da nufinta kuma shi kenan. Saboda ta gama tsorata da lamarin Jamal don ta yi amanna da shaye-shaye yake yi. Shi ya sa da ya bugu a daren jiyan ya so juye mata mayen giyar a saman kanta. Bayan ya gama cewa idan aka cire shigar matan da ke jikinta babu wani bambanci tsakaninta da namiji ɗan'uwansa.
'Gwaggo ki zo da 'yansanda Jamal ya sha giya yana ƙoƙarin kashe ni.'
Saƙon da ta tura mata kenan jikinta yana rawa tsabar ta gama tsurewa da lamarinsa gabaɗaya. Kamar ɓarauniya ta fito daga ɗakin cikin sanɗa ta sauka ƙasa da dabara gudun ya jiyo takunta ya sake ya lalata ƙudurin da ta kwana da shi a cikin zuciyarta.
Turus Jamal ya yi a lokacin da ya zo shiga gidan ya ji ƙofar a ƙargame. Kiran sunan maigadin ya yi cikin sauri ya buɗe masa yana faɗin,
"A yafe ni ranka ya daɗe, Hajiya ce ta so tserewa na hana ta fita."
Hango Minal ya yi a tsaye riƙe da ƙugu tana kumbura fuska, bai bi ta kan maigadin ba face kallon sama da ƙasan da ya yi mata ya watsar, sannan ya wuce zuwa cikin gidan ba tare da ya ce da su komai ba. Hakan ya saka maigadin ya sake rufe gidan da kwaɗo ya zare makulli saboda ya gama fahimtar yajin amare ne take shirin dakawa. A ransa ya jinjina lamarin, tare da yin dariyar ashe akwai sauran mutan da masu gudun miji har zamanin da ake ciki a yanzu na buɗewar ido.
"Ki yi haƙuri ki koma daga ciki Hajiya, ni ma zan je na yi sallah na ɗan matse barcin idona. Sannan ki bai wa maigidan haƙuri don alamunsa ya nuna bai ji daɗin ganin ki a nan ba."
Harara ta wurga masa a ƙufule duk da girmansa ta juya zuwa cikin gidan ranta a matuƙar ɓace, saboda ta so tafiya ya hana ta kuma ta so Jamal ya kula ta ta yi masa tijara. Kamar yadda ta so barin gidan ba tare da kowa ya sani ba. Aka yi rashin dace tun daga lokacin da ta fito cikin gidan a kan idon maigadin. Don yanayin ta kaɗai ya sa ya gano babu lafiya ya dakatar da arwalar da yake yi. Musamman ganin abin da take ƙoƙarin aikatawa, kafin ta ƙarasa jikin ƙofar ya kulle gidan da ƙaton kwaɗo cikin sauri. Duk yadda ta so ya buɗe ta fita cikin magiya; amma kukan da ta yi masa bai saka shi tausaya mata ya buɗen ba. Saboda ya san kan aikinsa kuma ya tuno lokacin da ta so barin gidan a karon farko ta ci karo da gwaggo Salame ta taka mata birki.
Idonta a rufe ta fara ƙwanƙwasa masa ƙofa tsabar ta zo wuya tana son a yi komai a ƙare ta kama gabanta. Jamal da ke bayi ya fito ransa a ɓace saboda ya san ba kowa ba ce face ita. Kiciniyar buɗe ƙofar da ta ji yana yi ƙirjinta ya hau bugawa ta yi hanzarin ja da baya riƙe da ƙugu tana girgizar jiki alamun ta shirya a yi komai. Saboda ta yi wa kanta alƙawarin barin gidan ta halin tsiya ko arziƙi, sai dai duk abin da zai faru ya faru amma sai bar gidan ta kowace hanya duk da tsinuwar Innarmu da ke cikin sharuɗan fitar tata.
"Ke wace irin daƙiƙiya ce?"
Ya yi magana cikin wata kalar murya mai ɗauke da ɓacin rai. Minal ta yi masa wani kallo sheƙeƙe sannan ta kawar da fuskarta a gefe tana cewa, "Ka ce da maigadinka ya buɗe mini ƙofa zan je gidanmu."
"Ni na ce da shi kada ya bar ki ki tafi gidan naku ne?"
Ya wurgo mata maganar yana zuba mata idanuwansa da suka yi mugun nauyi tsabar barcin da yake ji. "To ai ya hana ni fita, kuma ni gida nake so na je.."
Ta ƙare maganar tana wurga masa wani kallo da murguɗa baki, hakan ya sake ƙufular da shi karaf ya rufe ɗakinsa bayan ya buga mata tsaki, saboda ganin tana ɓata masa lokaci a banza.
Ɗakin ta sake bugawa tana faɗin, "Ni fa wallahi ba zan zauna a cikin gidan da ake barazana ga rayuwata ba."
Banza ya yi mata duk da ya ji abin da ta faɗa, amma yawan bugun ƙofar da take yi tsawon lokaci ya saka shi buɗewa gadan-gadan ya yi kanta. Maimakon ta gudu kamar yadda zuciyarta ke ba ta shawara; sai ta kafe tana aika masa harara har ya ƙaraso ya cakumo kwalar hijabinta. Ya ɗaga hannu da nufin faffalla mata maruka wata zuciyar ta yi gaggawar hana shi, tare da ba shi umarnin ya ladaftar da ita ta hanyar za ta fi jin tsoron sa.
"Sai na nuna miki na fi ki zama riƙaƙƙen mara kunya...oya nil dawn!"
Ya yi magana cikin ɗaga muryar da tsoro ya saka ta kai gwiwowinta biyu a ƙasa babu shiri. Jikinta yana tsuma ta shiga zubar da hawaye tare da haɗa hannu wuri ɗaya tana faɗin,
"Don Allah.. don darajar Manzon Allah..don albarkacin..."
"Yi mini shiru!"
Ta yi saurin haɗiye maganar bakinta jikinta yana kyarma ƙirjinta yana bugawa ta ƙura wa gefenta ido.
"Ɗaga hannunwanki sama ki rufe idanuwanki. Kuma idan kika yi gangancin tashi dukan da zan yi miki a yau sai na cire miki haƙorin gaba. Kada ki ga abin da ya faru jiya ki yi tsammanin ko da son raina na aikata ki nemi raina ni...to ni ma ban san wace kalar ƙwaya na sha jiyan ba har ta fitar da ni cikin hankalina."
'Da ma sai ƙwayar. Ashe da gaske shaye-shayen yake yi.'
Zancen zucinta kenan cike da alhini a lokacin da ya yi hanzarin komawa ɗaki saboda kiran wayarsa da ake ta yi, cike da mamaki ya rarumi wayar yana tsaki ya danna kore ganin sunan Gwaggo salame a kan fuskar wayar.
"Me ke faruwa ne tsakaninka da Amina?"
Jamal ya yi jim kamar ba zai bayar da amsa ba, sai da ta sake maimaita tambayar sannan ya fesar da iska mai zafi daga bakinsa ya ce,
"Babu abin da ya faru, gida take son zuwa maigadi ya hana ta."
Ajiyar zuciya Gwaggon ta saki sannan ta ce, "Don Allah ka ƙara haƙuri da ita, saboda tana buƙatar a tausaya mata ko don ta rage firgicin da take ciki."
"Babu damuwa."
Iya abin da ya faɗa kenan ya ajiye wayar, saboda ya gaji da magana kansa ya yi nauyi kuma yana yi masa ciwo sosai. Amin kawai ya faɗa a can ciki a lokacin da ta gama yi musu addu'ar zaman lafiya da haƙuri da juna.
Nannauyan barci ya ɗebe shi mai ɗauke da mafarkai barkatai har ƙarfe tara na safiya bai farka ba. Caraf tunaninsa ya kamo masa Minal da ya bari a cikin falo tana karɓar horo, cikin sauri ya faɗa toilet bai jima ba ya fito yana haɗe rai kamar wanda ya yi arba da kashi. Ganin ta a inda ya bar ta baje ƙasa tana barci; cikin zafin rai ya kai mata harbi da ƙafa har sau biyu. Ta zabura tana wara jajayen idanuwanta da ke cike da bacci tamkar wadda ta bugu da maye.
"Wa ya ba ki damar yin barci?" Ya jefa mata tambayar a fusace.
"Allah ne."
Ta ba shi amsa a taƙaice saboda tsoron sa bai hana ta mayar masa da raddi ba. Baki ya buɗe cike da mamakinta ya shiga nuna kansa ya sake cewa,
"Ni za ki yi wa rashin kunya?"
"Faɗar Allah shi ne rashin kunya kuma?" Ita ma ta amsa cike da jarumta.
Ya yi kamar zai kai mata mangari ta yi baya cikin zafin nama ya fisgo gefen hijabinta, babu shiri ta fasa ƙara jikinta yana rawa ta fara ba shi haƙuri tare da rantsuwar ita ma ba ta san barcin ya kwashe ta ba. Tsaki kawai ya buga ya nufi kitchen bai ce da ita komai ba, mintuna a tsakani ƙamshin girkinsa ya fara cikawa Minal hanci. Sai a lokacin ta tuna ashe fa ita ma tana jin yunwa, musamman da ya kammala ya fito da tiren ya ajiye a kan dinning table yana faɗin wash Allah.
A gabanta ya yi karin safiya ƙamshi yana dukan ta tana rakuɓe gefen kujerar da yake kai da tagumi, har ya cinye komai tas ya miƙe yana gyatsa zai shige ɗakinsa ta ce,
"Zan iya tashi?"
Ta yi maganar jiri yana ɗibar ta, tsabar yunwa da baccin da ke cikin idanuwanta. Don ƙarfe goma na safiya har ta haura.
Mugun tsaki ya ja sannan ya shige yana miƙa, jim kaɗan ya fito daga ɗakin fuskarsa a haɗe ya kai dubansa ga ƙofar ɗakinta ganin babu kowa a cikin falon ta tafiyarta. Murmushin mugunta ya yi sannan ya nufi ɗakin nata da niyyar ya sake tunzura ta da gangan.
"Ke!"
Abin da ya faɗa kenan cikin kakkausar murya a lokacin da ya hango ta bakin gado tana bacci. Zabura ta yi tare da tashi zaune tana murtsuka ido saboda dishi-dishi take ganin sa.
"Tashi ki wanke mini motata, sauri nake yi fita zan yi yanzun nan! Sannan ki tabbatar kin share mana harabar gidan kaf kafin na dawo."
D. AUTA CE ✍️