FANSAR ƘAUNA

8

by @princessdija

*FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA D. AUTA*

*AREWABOOKS: Princessdija.*

*Follow the D. AUTA NOVELS channel on WhatsApp: ***

*Na buɗe channel fatar za ku dinga leƙawa akwai wasu littafaina da zan saki ta can.*

*LAMBA TA TAKWAS.*

Babu shiri ta ƙara ware idanuwanta a kansa sannan cikin wata kalar muryar jin bacci ta ce masa,

"Ni ce zan yi maka wankin motar?"

"Ke..ke..fa...ga ki nan! Ko kin fi ƙarfin ki yi wankin mota ne?"

Ya ba ta amsar a harzuƙe tare da nufo inda take cikin zafin nama, da niyyar ya cakumo wuyan hijabinta ya koya mata hankali. A tsorace ta ƙura masa kallo ƙirjinta yana bugawa, ganin ya nufo ta da gaske fuska babu annuri ta zabura daga kan gadon, jikinta yana rawa ta yi bakin toilet tana faɗin,

"Ai ba cewa na yi ba zan yi ba...kuma ban san ma yadda ake yi ba n..."

"Mu je zan nuna miki tun da kin saba aikin wahala a gidanku ai wankin mota ƙaramin aiki ne a wurin ki."

Ya yi maganar yana bin bayanta don ta riga shi fita daga ɗakin tsabar firgicin da ya saka ta, tana zumɓura baki zuciyarta cike da takaicin rainin da yake yi mata kamar wata sokuwa ta kasa bijirewa. Tare suka fito harabar gidan inda ta ja ta tsaya wuri ɗaya, yayin da shi kuma ya nufi ma'ajiyar kayan wankin motar kai-tsaye. Bokiti ya kawo har inda take tsaye rungume da hannuwa a ƙirji tana harare-hararen gefe da gefenta. Sannan ya gyara tsayuwarsa a gabanta tare da riƙe ƙugu yana faɗin,

"Minti uku na ba ki ki yi sauri ki kammala komai kafin na shirya na fito. Kuma ki tabbatar kin gama ba na buƙatar ɓata lokac..."

Ganin ta a tsaye babu alamun za ta yi aikin da gaske ya sake harzuƙa cikin ɗaga murya ya ce, "Malama tsayuwar me kike yi a wurin da ba za ki wuce ki fara aikin da na saka ki ba?"

Wani mugun kallo ta yi masa ranta a matuƙar ɓace sannan ta ja bokitin ta nufi bakin famfo cikin sauri, tamkar za ta tashi sama tsabar ƙufula da ƙudurin ta yi saurin gamawa ta ƙaddamar da abin da zuciya ta kitsa mata.

Bayanta ya bi da kallo fuskarsa a cure har ta isa bakin famfon har ta tara bokitin ruwan ya fara zuba. Sannan ya bar wurin da sassarfa ya koma cikin gida, zuciyarsa cike da alwashin wahalar da ita har sai ta nemi saki da kaifin ƙafafuwanta idan ta gaji da zaman. A gurguje ya faɗa toilet ya yi wanka, cikin minti goma sha biyar ya fito angonsa shar duk da babu cikakken angwancin a zahiri. Domin ya yi kyau a cikin tsadadden farin yadin da ya saka tare da ɗora wa kansa hular da ta ƙara fito da haibarsa a fili, kuma ɗinkin ma ya karɓi jikinsa sosai. Sai tashin ƙamshi yake yi kansa a duƙe yana gyara zaman agogon da ke hannunsa ya iso wurin. Minal kuwa kamar wadda aka kira takunsa ya sa ta yi hanzarin kai kallonta gare shi. Ƙirjinta ya buga dam-dam a bisa tsautsayi ta rusa masa tsari. Domin garin kallon sa ta danna tiyon ruwan ya fantsama a kan fuskarsa zuwa ƙirjinsa har ya bi tafin ƙafarsa ya malala ƙasa. A ƙoƙarinta na son wanke kumfan da ke saman motar ta wanke masa jiki.

"Ya Salam!"

Abin da ya furta kenan a lokacin da ruwan ya sauka jikinsa, tare da yin wani tsallen da ya saka shi jan gefe babu shiri ya hau buge ruwan da hannunsa. Rigar ya riƙo ransa a ɓace don ta gama yin sharkaf da ruwan, cike da mamakin abin da ta yi masa ya dinga kallon jikinsa yana ƙare mata kallo. A cikin zafin zuciya ya ya danna wata muguwar ashar, saboda ba ƙaramin ɓata masa rai ta yi ba, hakan ya saka shi nuna ta da makullin motar da ke hannunsa yana faɗin,

"Na gaji da yawan surutun da kike saka ni...don na fahimci so kike yi ki zamo mini wani sabon ciwon kai bayan wanda ke cikin kain..."

"Ka yi haƙuri wallahi ba gangan na yi b..."

Ta yi maganar cikin saurin baki jikinta yana rawa saboda ita kanta ta sani tabbas ba ta kyauta masa ba. Katse ta ya yi da faɗin,

"Yi mini shiru shashasha! Ke har abada ba za ki taɓa wayewa ba! Komai naki a hargitse babu wani tsari ƙauyanci ya yi miki yawa a zuciya."

Zancensa ya datse sauran maganar da ke bakinta, kanta a ƙasa tana sauraron yadda yake magana cikin ɗaga murya tamkar ya rufe ta da mahaukacin duka.

"A yi mata haƙuri maigida."

Maigadi ya yi magana saboda gudun shaiɗan ya tunzura shi abin ya zamo babban abu. Don duk abin da ke faruwa a gaban idonsa ne, tun fitowarsu har badaƙalar da suke yi bai ɗauke ganinsa ba. Farko ya kalli abin a salon soyayya, amma faɗan da ya ga Jamal yana yi ya saka shi jin tsoro, gudun ɓacin rai ya saka shi aiwatar da abin da bai dace ba. Bai ce wa maigadin komai ba ya juya zuwa cikin gidan, da nufin sauya wasu kayan amma bai fasa tsine wa rashin hankalinta ba.

"Allah ma ya sani ni ban yi da niyya ba."

Zancen Minal kenan a a lokacin da ta saki tiyon ruwan yana zuba ƙasa tsabar takaici. Ƙugu ta riƙe tana girgizar jiki tare da kallon gefe saboda haushin maganganun da ya faɗa mata a gaban maigadin sun tsaya mata a zuciya. Hakan ya saka Jamal jan birki ya tsaya cak a inda yake, kafin ya waigo cikin fushi ya sake nuna ta da hannu fuskarsa a yamutse ya ce,

"Ki shiga taitayinki!"

Hararar gefen ido ta yi masa ba tare da ta ce komai ba ta ƙura wa wuri ɗaya kallo, har ya gama tsayuwarsa ya dunƙule hannu ya kai wa iska naushi ba ta sake kallon sa ba.

"A yafe mata maigida ba za ta sake b.."

"Ka tsaya iya aikika!"

Jamal ya ƙare maganar tare da nuna shi da hannu, cikin sauri ya bar wurin amma bakin maigadin bai yi shiru ba sai da ya sake cewa, "Allah dai Ya huci zuciyarka maigida." Ya nufi mazauninsa da ke bakin ɗakinsa yana zancen zucinsa cike da jin haushin kansa a kan shiga harkarsu.

'Ba zan sake shiga tsakaninku ba tun da bayar da haƙurin ma laifi ne. Aure sai ka ce wasar yara daga matar gidan har maigidan kowa da kalar matsalarsa. Um..ku kuka sani dai ni ɗan kallo ne." Daga haka ya kama sabgoginsa.

Minal kam bayan Jamal ta bi da kallo har ya shige ba ta ɗauke idanuwanta a kansa ba. Zuciyarta cike da jin haushin kanta a kan me ma ya sa ta kalle shi har ta ɓata masa jiki. Jikinta ya yi sanyi ƙalau duk da ba ta daina jin haushin maganganun da ya yaɓa mata ba. Kamar an dasa ta a wurin tsawon minti biyar zuwa shida ba ta motsa ba. Har Jamal ya fito cikin wata sabuwar shigar yana baza ƙamshi, tare da tsuke fuska tamkar bai taɓa dariya ba. Ta gefen ido ta kai kallonta gare shi ƙirjinta yana bugawa amma hakan bai hana ta magana daga ita sai ranta ba.

'Ka gode mini a yanzu har ka fi kyau m...'

A daidai lokacin ya buga wani ƙaƙƙarfan tsakin da ya saka bugun zuciyarta ƙaruwa. Saboda hango ruwa a jikin motar ya nuna ba ta goge masa ba bayan ta gama wankewar. Cikin sauri ya fito da wani towel a boot ya shiga goge motar a ransa yana faɗin,

'Wawuyar banza ita komai sai an ce ta yi sannan take yi.'

Ya faɗa motar bayan ya gama gogewa ta ya shiga ba ta wuta, maigadi ya yi hanzarin buɗe masa gate tun kafin ya umarce shi. Saboda ya ci burin tsayuwa iya aikinsa ba zai sake shiga sabgar da ke tsakaninsu ba. Minal kuwa kafewa ta yi a inda take duk ƙugin da motar ke yi ba ta sa ta matsa ba. Ganin ba ta da alamun ba shi hanya ya wuce kamar yadda yake so, yana ƙoƙarin yin kwana ya leƙo kansa cikin fushi ya ce,

"Ke wace kalar mahaukaciya ce da ba za ki janye ba sai na yi magana...zan kakkarya shamulallun ƙafafuwanki a banza wawuya kawai...mitsssss..."

Ya ƙare maganar da tsaki a lokacin da ta ɗaga masa hanya ya nufi bakin gate yana ci gaba da faɗar duk abin da ya zo bakinsa. Magana ya yi da maigadin ƙasa-ƙasa sannan ya fice gidan. Allah Ya tsare ya shiga yi masa yana ɗaga hannu har ya wuce, amma kafin ya rufe babbar ƙofar Minal ta ƙaraso wurin ita ma. Wuff ta yi da nufin faɗawa waje ta fice ta ƙaramar ƙofar gidan, don ta gama haɗa komatsan tunaninta a wuri ɗaya, a kan yanke iyakar zama da Jamal har abada don ya gama ci mata zarafi a banza.

"Ki yi haƙuri Hajiya, maigida ya ce kada na bar kowa ya fita a cikin gidan nan, yau babu shiga babu fita."

Wani kallo ta yi masa sannan ta yi magana a ƙufule tana cewa, "Shi maigidan da ya fita me ya sa ba ka hana shi ba sai ni da ka raina?"

Yana kulle ƙaramar ƙofar gidan bayan ya sha gabanta ta koma ciki ya ce, "Umarni ne daga shi, kuma aikina nake yi Hajiya. Amma ko yanzu ya kira ni ya ba ni damar barin ki fita an gama zance."

Ta jima a wurin tsaye zuciyarta sai ingiza ta take yi a kan ta yi masa rashin kunya ko zai bar ta. Yayin da wata zuciyar ke ba ta shawarar ta zagaya ta bayan gidan ta haura katanga. Kafin ta yi ƙwafa ta bar wurin tana cika tamkar wata kububuwa. A haka ta koma cikin gidan ranta a ɓace ta faɗa ɗakinta tana kuka wiwi. Bayan ta rage ƙuncin zuciyarta ta nemi wayarta kaf ɗakin ta rasa, bayan kuma ta san a kan gadon ta bar ta.

Idanuwanta suka kai kan agogon ɗakin babu shiri ta zaro ido, ganin lokacin ya yi gudu da yawa ga kuma ƙugin yunwa da hanjinta suke yi. Don ƙarfe sha biyu na rana har ta wuce, waton ƙarfe ɗaya saura kaɗan ake harare. Kitchen ta nufa faka-faka da niyyar neman abin da za ta ci, jiri yana kwasar ta tsabar yunwa da bacci sun gama ladaftar da ita jikinta. A gurguje ta yi wanka ta yi sallah sai zuba hamma take yi wata bayan wata, sannan ta baje tana wani irin mugun barci mai ɗauke da kalolin minshari.

***

Sadam kuwa daga gidansa wurin Hajiya Mummy ya nufa. Saboda nazarinsa ya gama ba shi akwai abin da Hajiyar ta saka masa a cikin kunun ayar da ta ba shi. Kamar yadda ta dinga ɗirka masa maganin ƙarfin maza da sunan na sauƙin zuciya.

Bayan sun gaisa fuskarsa babu yabo babu fallasa ya amayar da abin da ke cikin bakinsa kai-tsaye. Inda ya sanar da ita bai ji daɗin abin da ta yi ba. Don bai shirya zaman aure da Amina ba, sannan ya ƙara da cewa,

"Yarinyar nan ita kanta damuwa ce mai zaman kanta Hajiya. Kuma idan ina tare da ita ciwon da likita ya faɗa yana gaf da afkuwa komai ya faru a kaina. Saboda zama da ita tamkar barazana ce ga rayuwata Hajiy..."

"Ka yi haƙuri, ni da ma farincikinka nake nema. Amma tun da nawa tsarin bai yi maka ba ka je ka yi duk abin da kake so. Sai da ka sani ko da Nur ta dawo ba zan taɓa bari ka yi zaman aure da ita ba, tun da har ta iya tsallakewa ta gudu alamu ya nuna ba ta son ka. Kuma duk wanda ba ya son ka ni ko lahira ba na fatar haɗuwa da shi."

Tana ƙare maganar ta ja bakinta ta tsuke bayan ta haɗe rai da fuska alamun babu wani sauran sassaucin da za ta yi masa a kan hakan.

"Haba Hajiya, ke fa kika sanar da ni ba da Nur aka ɗaura aurena ba na ɗauki ƙaddarata a yadda ta zo mini, sannan kuma a yanzu ki koma ganin laifinta ki koma a kan guduwar da ta yi don ba ta so na ne? To me zai hana ta guduwa bayan an raba ta da abin da take so? Ina son Nur Hajiya kuma zan nemo ta a duk inda take, ko da a yanzu ita ta daina so n...."

"Ni kuma matuƙar ba ka kula da Amina kuka zauna lafiya ba; ban yafe maka ba idan har ka tafi neman wadda ba ta san muhimmancinka ba. Sannan kada ka manta; ko danginta sun gaji da neman ta sun bar wa Allah saboda tsarinta ne aka bi kuma ganin damarta ne...kai a taƙaice aurenka da Amina ma ita ce ta haɗa komai...to a kan me za ka lalata damar da Allah Ya ba ka a kan neman wadda ba ta ra'ayin ka?"

Shiru ya yi mata ba tare da ya ce komai ba, saboda maganganun sun shiga jikinsa sun dakar masa zuciya. 'matuƙar ba ka kula da Amina kuka zauna lafiya ba, ban yafe maka ba idan har ka tafi neman wadda ba ta san muhimmancinka ba.'

Ya shiga maimaita zancen a ransa nan take damuwa ta ƙara yi masa lulluɓin tashin hankali.

"Ta ya zan zauna lafiya da Amina bayan babu so a tsakanina da ita? Me ya sa za ki yanke mini irin wannan hukuncin bayan kin sani Nur ita ce rayuwat..."

"Ka mutu a yau ɗin nan Jamal idan har da gaske ita ce rayuwar taka! Saboda wallahi ka ji na rantse da Allah ba zan taɓa yafe maka ba matuƙar ka bar matarka ta sunna ka je yawon neman wadda ba ta san darajarka b...shin har sau nawa zan faɗa maka ita ce ta nemi haɗin aurenka da Amina? Ko so kake yi sai na yi ta shela da lasifika ina bayani sannan za ka fahimce ni? To Nur ba ta son ka, don da tana sonka ba za ta nemi a cusa maka Amina ita kuma ta tsallake ka ta bi duniya ba. Na faɗa na koma faɗa ba zan lamunci ganin cigaban rayuwarka ya tsaya a sanadin wata macen banza ba Jamal!"

Tana ƙare maganar ta bar masa falon ta shige ƙuryar ɗakinta tana goge hawaye, hawayen kukan da ta so dannewa tana kokawar kada su fito amma suka kasa ba ta haɗin kai.

Wai ya abin yake ne?🤔🥺

Ga link;

***

Masarauta group masu tambayar a saka su group da masu buƙata su ma su yi joining.

D. AUTA CE ✍️