IMARA

Chapter 06

by @nanameera08

*Chapter 06*

Da mamaki Maheer ke kallonta yayinda take ƙoƙarin shigowa ɗakin, ajiye hoton hannunsa ya yi ya miƙe tsaye yana nunata da yatsa ya ce"You...!" Gyaɗa masa kai tayi tana murmushi ta ce " ko nayi ƙarye ne?, ba halin ka bane?," girgiza kanta tayi jin yayi shiru ta cigaba da faɗin "halinka kenan, kanada son kanka, baka damuwa da damuwar waɗanda suke kusa da kai, idan kuma har abin da na faɗa ba gaskiya bane to Inason ka nunamin gaskiyar, ka bani kunya, ka barni na tafi inda na fito dan girman Allah" ta ƙarashe maganar tana haɗe hannayenta alamar roƙo. Da idanu kawai Maheer ya bita sai kuma ya bi ta gefenta ya fice daga ɗakin ba tareda y ce mata komai ba, zaman daɓaro Imara ta yi akan tiles ɗin ɗakin da fashe da kuka tana kallon ƙofa, above 5mins kafin ta tashi ta shiga goge idanunta sai kuma ta koma inda ya ajiye enlargement ɗin hoton ta ɗaukeshi. Daskarewa Imara ta yi ganin mai kama da ita sak jikin hoton, hannunta na rawa ta taɓa hoton nan take taji wasu hawaye sun fara sakko mata wanda batasan na menene ba, wacece wannan?,

"KATALINA!"

Wani ɓangare na zuciyarta ya bata amsar, runtse idanunta tayi sai kuma ta sake buɗe su kan hoton, kenan wannan shine dalilin daya sanya Maheer ya ɗaukota?, meyasa suke kama?, wace ita?, mene ne ya rabata da Maheer?, ina take yanzu?. Shiru tayi na ɗan lokaci ƙwaƙwalwarta na ayyana mata abubuwa dayawa, maganar Rania ce ta faɗo mata hakan yasa ta miƙe tsaye kamar wacce aka tsikara ta fice daga ɗakin da sauri.

***Zaune take kan kujerar dake gefen gadonta hannunta riƙe da wayarta tana danna cikeda nutsuwa, wata long sleeve ɗin riga ce a jikinta wacce ta ɗan matseta sosai, ta tukfe gashin kanta waje guda. Wata number ta yi dialing ta zubawa screen ɗin wayar tata idanu har ta katse ba'a ɗauka ba, kwaɓe fuska ta yi ta sake dialing amma kamar ɗazu har ta kashe ba'a yi picking ba. Cilli tayi da wayar kan gadonta ta tashi ta fice daga ɗakin, apartment ɗin Immi ta nufa tana shiga ta isketa zaune suna magana da Shamma, kallo ɗaya ta yi mata ta kalli Immi cikin cool voice ɗinta ta ce"idan kin gama zamuyi magana" murmushi Immi ta yi ta ce"Tom daughter" ganin ta juya zata fita yasa ta kalli Shamma sai kuma ta ce

"Daughter bakiga Shamma ba?" Tana ƙoƙarin fita daga ɗakin ta ce"naganta mana" kafin Immi tayi magana ta fice daga ɗakin tana buga ƙofar, shiru Shamma tayi tana jin wani irin zafi can ƙasan zuciyarta.

"Ki ƙara hakuri kinsan har yanzu yarinya ce" Immi ta faɗa tana dafa Shamma, murmushin yaƙe Shamma ta yi ta miƙe ta ce"anjima ma ƙarasa" jinjina mata kai Immi tayi Shamma ta gyara zaman rigar jikinta ta fice daga ɗakin, wani murmushi Immi ta saki tana bin bayanta da kallo sai kuma ta tashi ta fita domin haɗuwa da Joda.

*8:30pm*

Turo ƙofar ɗakin ta yi ta shigo, wani sassanyan ƙamshi ne ya daki hancinta tayi saurin lumshe idanunta, zaune ta hangesa kan carpet ya tankwashe ƙafafunsa gabansa wani littafi ne yana rubutu akai, a hankali ta shiga takawa har gabansa, sai a sannan ya ɗago dara-daran idanunsa, kai tsaye kuma suka shige cikin nata. Sunkuyar da kanta tayi tana wasada fingers ɗinta, rufe littafin hannunsa ya yi ya ajiye shi gefe yana kallonta ya ce" Marhaban biki" jinjina masa kai ta yi ya yi mata nuni da ta zauna, zama ta yi tana gyaran veil ɗin kanta, kallo ɗaya Ameer ya yi mata ya ɗauke kai cikin daddaɗar muryasa ya fara mata magana

"Yau kuma tsiwar aka biyo ni har ɗaki a yimin?" Kallonsa ta yi taga ya kalleta tayi saurin sauke idanunta ƙasa, murmushinsa mai kyau ya yi ya ce "then me ya kawo ki?, ko zuwa kika yi ki gaida Ameer?" da sauri ta gyaɗa masa kai, waro idanunsa ya yi ya ce "really?" Ta sake jinjina masa kai. Numfasawa ya yi ya ce"Allah ya yi miki albarka Lolo" cikin sakin fuska ta ce"Ameen Nagode Ameer, saida safe"

"Laylatan sa'eedan"

Cewar Ameer, bata sake cewa komai ba ta tashi ta fice daga ɗakin, girgiza kansa ya yi sai kuma ya ɗauko littafin ya cigaba da rubutunsa.

*London*

*Royal Brompton and harefield hospital specialist care*

*9:30am*

Turo ƙofar ɗakin ya yi ya shigo, turus ya yi ganin yanda take haɗa kayanta dake cikin drawer. Girgiza kansa ya yi bai ce komai ba ya ƙarasa shiga ciki, zama ya yi kusada ita yana kallonta fuskarsa ɗauke da murmushi ba kamar wancen lokacin ba, ɗago kai tayi ta kalleshi ta galla masa harara ta cigaba da abin da take, gyara zamansa yayi yana murmushi ya ce"matar wa ya ɓata miki kai?" Yanda ya yi maganar cikin zolaya ya ƙara fusata ta ta kalleshi kamar zatayi kuka ta fara magana cikin harshen larabci

"A'a kar ka fara wlh, tunda an san ni aka cuta dole ka ce wa ya taɓa ni, to wlh bazai yiwu ba kuma ni yau bazan sake kwana ƙasar nan ba kaji na faɗa maka" shafa kansa ya yi wanda yasha gyara yana murmushi ya kamo hannunta cikin kwantar da murya ya fara magana"haba matar me ya yi zafi haka?, kiyi haƙuri nan da 3days za'a yi discharging naki" janye hannunta ta yi tana watsa masa wani kallo ta ce"a'a, inaaaa, ni zaka yiwa siyasa?, wlh baka isa ba!. Ni yau nakeson barin ƙasar nan haba!, nagaji" ganin yanda take masifa ya sanya ya tsuke fuska kamar ba shi ba ya kalleta cikin wata husky voice ya ce" to tashi ki tafi mana" juyowa ta yi ta kalleshi ganin yanda ya haɗe rai ya saka ta fasa faɗar abin da tayi niyya ta cigaba da haɗa kayanta tana cewa"mutum sai baƙar zuciya, Ka sauya hali!".

*Al-Udaid Kingdom*

*10:00am*

Zaune take gefen gado tana linke kayanta kasancewar yau Saturday babu lecture, gaba daya hankalinta baya jikinta, ƙwaƙwalwarta tayi nisa cikin tunanin da take, tana da buƙatar sanin abubuwa masu yawa game da mijinta da kuma Udaid gaba ɗaya, amma wa zata tunkara?, wane wanda zai warware mata wannan al'amarin ta fahimceshi?

"Ameer!"

Wani bangare na zuciyarta ya bata amsa, girgiza kanta tayi ta ce a fili"amma zai sanar dani komai?, ta yaya?" Ajiye rigar hannunta tayi ta kwaɓe fuska kamar ƴar baby ta zuba uban tagumi, above 5mins kafin ta miƙe tsaye ta sanya ɗan ƙaramin hijab kan Abayar jikinta ta fice daga ɗakin da sauri.

A hankali ta tura ƙofar ɗakin bakinta ɗauke da sallama, babu kowa a ciki sai ƙamshin turarensa mai matuƙar daɗi wanda ya haɗe da sanyin ɗakin ya bada wani irin yanayin mai daɗin gaske, tamkar mayen ƙarfe haka Imara taji ana janta zuwa cikin ɗakin kai tsaye kuma inda royal bed ɗinsa yake ta nufa. Zama tayi gefensa tana shafa katifar tana jin wata nutsuwa na saukar mata, kalle-kalle ta shiga yi a ɗakin, komai tsaf yake tamkar ba babba mutum bane a ɗakin ko ba'a faɗa ba Ameer ɗan gayu ne ajin farko. Tashi tayi ta ƙarasa gaban dressing mirror ɗin dake kallonta ta ƙurawa kanta idanu tabbas ta rame sosai kuma hakan nada alaƙa da halin data tsinci kanta a ciki, sarƙar dake maƙale a wuyanta ta kalla, ta kai hannu ta shafi sarƙar wacce ke tuna mata rayuwarta ta baya, inama da ta dawo mata, inama ranakun farin cikin da suka shige su sake maimaita kansu, ɗumin da taji akan fuskarta ya tabbatar mata da kuka take, hannunta ta sanya ta goge hawayen nata nan da nan fuskarta tayi jajur.

"Lolona"

A ɗan firgice ta juya sai kuma ta sunkuyar da kanta ganin ya zuba mata idanu, taku biyu yayi ya ƙaraso gabanta ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallonta ya ce "why are you crying?" girgiza masa kai tayi alamar babu komai, murmushi ya yi cikin nutsuwar da ta gama ratsa shi ya ce"ajiye ina sonki a gefe, daga yau na zama friend ɗinki, a good friend saboda haka feel free and tell me what's wrong with you, I'm here with you" kallonsa tayi a karo na farko, kallo na tsanaki ta ce cikin muryar kuka

"Are you sure?"

"Absolutely sure"

Ya bata amsa, goge hawayen fuskanta tayi ta gyaɗa masa kai, ya miƙa mata hannunsa kallonsa tayi sai kuma ta kalli hannun da ya miƙa mata kafin ta ɗora nata a kai, bai ce mata komai ba ya fara tafiya da ita, Library ɗinsa ya nufa da ita, suna shiga ta zauna kan kujera shi kuma ya nufi inda fridge yake, ruwa mai sanyi ya ɗauko mata da cup ya dawo ya zauna kujerar dake facing tata ya ɓalle bottle ɗin sannan ya miƙa mata, ko kallon cup ɗin bata yi ba ta kafa bakinta jikin bottle ɗin ta fara shan ruwan, cikin sakkanin da basu shige uku ba ta ajiye empty na robar ya kalleta ganin yanda take sauke numfashi a hankali. Tana matuƙar bashi tausayi, yana ɗaya daga dalilan daya sanya yake sake jin sonta cikin zuciyarsa. Sun ɗauki mintuna kafin yaga ta dawo cikin nutsuwarta, ya gyara zamansa yana facing ɗinta sosai ya ce"now tell me" numfasawa tayi cikin sanyin murya ta ce "Ameer"

"Lolona"

"Kome na tambayeka zaka bani amsa?" Jinjina mata kai ya yi, ta cigaba da faɗin

"To dan Allah Ameer waye Maheer?, meyasa ya aureni?, wace Katalina?, meyasa nake ganin komai ba daidai bane?, meyasa Maheer ya tsaneni?, meyasa kake sona?" Tunda ta fara magana Ameer ke kallonta fuskarsa fal da tausayinta. Jin ya yi shiru yasa ta fashe da kuka tana rufe bakinta da hannunta take faɗin

"Ba zaka faɗa min ba ko?, ba zaka iya ba ko Ameer?, kace kai abokina ne, kenan bazaka iya taimakona ba?, kafison na cigaba da zama cikin fadar nan har baƙin ciki ya kasheni?." Sakkowa tayi daga kan kujerar ta tsuguna kan gwuiwarta ta haɗe hannayenta waje ɗaya alamar roƙo ta cigaba da faɗin "dan Allah dan Annabi Ameer ka taimakeni, ka sanar dani waɗannan abubuwan ko nasamu wani tudu da zan kama wajen ganin na sauya rayuwata, ka zame mini aboki nagari kaji dan Allah karka bari na rasa rayuwata saboda wannan takaicin dan Allah Ameer dan All...Allah...dan..." Ta kasa cigabawa saboda kukan da yaci ƙarfinta. Shiru Ameer ya yi yana sauraren kukan nata wnada yake jinsa har ƙasan zuciyarsa,

"IMARA!"

Ɗago jajayen idanunta tayi ta kalleshi cikin shassheƙar kuka ta ce "Na'am" "stop crying!" Daina kukan tayi ta shiga sauke ajiyar zuciya da sauri da sauri. Numfasawa Ameer ya yi ya haɗe hannayensa biyu waje guda idanunsa bisa carpet ɗin ɗakin ya fara magana cikin tsaftaccen harshen larabci;.

"Zan sanar dake abin da kika buƙaci ki sani, wanda kuma bayan ke babu wanda ya san da hakan, kema kuma zan sanar dake ne domin na wanke kaina daga zargin da kike mini, tabbas Imara ina sonki, kuma naji ina ƙaunarki, saidai bansan dalili ba har yau, ina ji kamar na taɓa rayuwa dake a baya, mun saba kuma mun shaƙu sosai, tun ranar da Maheer ya kawo ki gidan nan naji sonki ya ɗarsu cikin zuciyata, bansan wane kalar so bane, ban san dalilin samuwarsa ba, amma naji inason ki kasance a gefena har na ƙarshen rayuwata. Amma na rantse miki da Allah ban taɓa miki so wanda yake bana daidai ba, kuma nasan abinda na aikata ba laifi bane dan na furta ina sonki, ko a wajen Allah ban aikata abin da yake haramun ba" kallonsa tayi kawai ba tareda ta ce komai ba ya cigaba da faɗin

"Maheer, ya kasance ɗa a wajena, ina kuma matuƙar alfahari da hakan, Maheer mutum ne mai sauƙin kai saidai idan ba'a fahimceshi ba, amma yana da sauƙin mu'amala. Rayuwarsa ta shiga wani hali shekaru biyu da suka shige, ya faɗa cikin wani mawuyacin hali, ya maida damuwa abokiyar rayuwarsa, shin kinsan dalili?"

Girgiza masa kai Imara ta yi ya jinjina kansa ya cigaba da faɗin

"Katalina! Saboda Katalina, ta kasance budurwa a wajensa, yana ɗaya daga cikin masu yi mata lecture a school, two years back ta shirya yin tafiya, a ranar sun haɗu da Maheer a makaranta bayan ya dawo gida aka kira shi aka faɗa masa ta yi hatsari ta rasu, Maheer bai yarda ba saida ya je har gidansu, amma iyayenta suka ƙi bashi damar shiga ya ganta, tun daga sannan rayuwarsa ta canja sabon da yayi da Katalina ba ƙarami bane takai ta kawo kowa ya gani sunanta yake kira, daga nan muka kai shi asibiti, anyi iya bakin ƙoƙari kafin a samu kan Maheer lokacin Katalina ta yi shekara da rasuwa. Bayan ya dawo hankalinsa ne aka tura shi aikin kwangila ƙasar ku, tun ranar daya fara ganinki ya kirani a waya hankalinsa a tashe ya ce ya ga Katalina, Ni kaina sanda ya turan hotonki saida na gazgata cewa ita ce, nan yaƙi yarda yace sai ya tawo dake shine dalilin da aka ɗaura muku aure, saidai tun da kuka dawo ƙasar nan ya fuskanci ke daban Katalina daban shikenan ya shiga muzguna miki, duk a tunanin Maheer ke Katalina ce kawai kin rabu dashi ne saboda daman can iyayenki Basu san alaƙarku, amma ni tun ranar dana ganki na tabbatar da ke ba Katalina ba ce! Kuma na yarda da ke, nake sonki nake ƙaunarki. Ruwa ya ɗauka yasha sannan ya cigaba da faɗin "maganar UDAID kuma bazan iya baki labarinta ba domin nasan ba zaki taɓa fahimta ba, amma idan har kina cikinta watarana zaki gane abinda ta ƙunsa."

Wata nannauyar ajiyar zuciya Imara ta sauke kafin ta ɗago ta kalleshi cikin sanyin murya ta ce "yaushe zan koma gidan mu?" Kyakkyawan murmushi ya yi yana girgiza kansa ya ce "bansani ba nima" kwalla ce ta kawo idanunta ta ce "zan nemi Maheer ya sakeni na koma gidanmu, tunda ba ni ce wacce yake so ba, duk da zan so sanin dalilin daya sanya muke kama amma zan bar wa Allah komi zan koma Nigeria na cigaba da rayuwata kamar yanda nafara ta" shiru Ameer ya yi bai ce mata komai ba, badan bai ji abin da ta ce ɗin ba, sai dan bai san amsar da zai bata ba dukda yasan abune mawuyaci barinta da Udaid. Ganin bai ce komai ba ya sanya ta miƙe tayi hanyar waje tana tafiya jikinta a sanyaye ba kamar yanda ta shigo ba. Saida ta kai bakin ƙofar sannan ta juyo ta kalleshi taga ita ya ke kallon muryarta na rawa ta ce "Nagode sosai Ameer, nagode da kulawa" lumshe idanunsa ya yi bai ce komai ba ta juya ta fita. Da mamaki Shamma ke kallonta har ta shige nata apartment ɗin, me ya kaita wajen Ameer?, yaushe ma Ameer ya fara magana da ita?, me suke tattaunawa da har ta daɗe haka a ciki?.

"Shamma!"

Firgigit ta juya tana kallonsa sai kuma tayi murmushi ta ce "Lafiya son?" Girgiza kansa ya yi ya ce "sorry I scared you" murmushi ta yi ta ce "ba komai, ka ci abinci?" Shafa cikin nasa ya yi ya ce "I'm not hungry Shamma, so you don't have to be worry" harararsa tayi ta ce "hakane" ganin ta dauke idanunta ya sanya ya saƙalo hannayensa a wuyanta yana murmushi ya ce "I'm sorry to zan ci in sha Allah"

"Promise?"

Jinjina mata kai ya yi ta ce"oya Maza kaje ka ci nima zani wajen Ameer ne" shiru ya yi sai kuma ya ce"kin gano meke damun nasa?" girgiza kai tayi ya ce " amma why Shamma?" Numfasawa tayi ta ce "Maheer kasan halinsa yana da kafiya akan abu, nayi nayi ya sanar dani meke damunsa yaƙi" girgiza kai ya yi ya ce"let me talk to him" jinjina masa kai tayi, ya yi gaba tana biye a bayansa.

***Tunda ta shiga ɗakin take kai kawo ta kasa zama guri ɗaya, me kunnuwanta suka jiye mata? Ameer yana son Imara? Inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun, wane irin abu ne wannan kamar a Film ko a littafai? Maha ta tambayi kanta. Kasa jurewa tayi ta ɗauki wayarta ta shiga dialing numbern Joda sai kuma ta katse kiran tana girgiza kanta a fili ta ce

"No bai kamata ba, babu wanda zan sanarwa, zan cigaba da riƙe abun a raina tunda babu wanda ya sani"

"Me zaki cigaba da riƙewa a ranki?"

Daga bakin ƙofa taji an wullo mata tambayar, Shamma ce ta shigo hannunta riƙe da mug sai tiriri yake, murmushin yaƙe tayi dukda yanda ƙirjinta ke bugawa na tsananin tashin hankali ta ce "babu komai Shamma, akan wasu coursemates ɗina ne suke soyayya shine basu san kowa ya sani Ni kuma na sani shine da nake tunanin na faɗawa sauran" mug ɗin hannunta ta ajiye ta kama hannun Maha tana murmushi ta ce"kul, karki zama mai tonawa mutane asiri, duk abin da kikaga Allah ya rufe shi to babu shakka ya kasance a rufen shine mafi Alkhairi, a duk sanda kikaga wani ɗan uwanki musulmi na cikin matsala ki taimakeshi, idan yana neman rufin asiri ki rufa masa sai kiga kema Allah ya rufa miki asiri ranar gobe ƙiyama"

Wasu zafafan hawayene suka shiga sintiri kan fuskarta, na tsananin tausayin Shamma, koda wasa batayi tunanin Ameer zai iya furta irin wannan kalaman ba, sai gashi yana furta yana son wata, watar ma kuma matar ɗansa. Ganin kamar tunani take ya sanya Shamma ta shiga goge mata hawayen fuskarta

"Daga yi miki faɗa sai kuka kuma Maha?"

Murmushi tayi tana share hawayen ta ce"thank you Shamma, Ana ahubbuki( ina sonki)" murmushi tayi tana jan kumatunta ta ce" nima haka".

A hankali ta tura ƙofar ɗakin ta shiga bakinta ɗauke da sallama, hangensa tayi kan gadon ya rufe jikinsa da duvet da alama bacci yake, around 12am ne tasan ba ƙaramin al'amari bane zai sanya ya kwanta a wannan lokacin, ƙarasawa tayi ta zauna gefen gadon ta zubawa kyakkyawar fuskarsa idanu, Allah sarki haka rayuwa take dama, a lokacin da kake muradin rayuwa da wani abu a lokacin yake barinka, watarana ayi farin ciki watarana ayi baƙin ciki, a duk halin da mutum ya tsinci kansa ya godewa Allah shine kawai abin da ya fi masa, daga sanda ka kasance mai godiya ga Allah, daga sannan matsalolinka zasu zama tarihi. Ajiyar zuciya ta sauke tana sake tunano abin da Ameer ya ce mata, da gaske Maheer baya sonta, da gaske Katalina yake so, amma meyasa ita kullum take jin sonsa cikin zuciyarta?, meyas

a take jin kamar shine abokin rayuwarta?, meyasa take kasa jin zafinsa?

"Soyayya!".

***.

# *IMARA*

# *Bestnovel*

# *2025*

# *Nanameera.*