Chapter 7&8
by @nanameera08
*Chapter 7&8*
Taji Maheer ya furta yana buɗe idanunsa, sunkuyar da kanta tayi ba tace komai ba ta miƙe zata fita, hannunta ya riƙe cikin nasa tayi saurin sauke idanunta ƙasa tana goge hawayen dake zuba a idanunta da hannu ɗaya. Miƙewa zaune ya yi har sannan yana riƙe da hannunta, jawota ya yi ya zaunar da ita kusada shi ya zuba mata idanu yana kallonta, shiru Imara ta yi tana wasada fingers ɗinta sun ɗauki wasu mintuna kafin ya numfasawa cikin sanyin murya wanda bai san yanada shi ba ya ce
"Saboda kina sona kuma kin yarda dani"
Janye hannunta tayi tana girgiza kanta ta ce"hakane amma yanzu na cire wannan yardar da nayi maka, kai ɗin ba abun yarda bane, ka cutar da rayuwata, a lokacin da nake tunanin matsalolina sun zo ƙarshe sai ka shigo cikin rayuwata ka hanani zama lafiya, ka shiga bijiromin da abubuwa waɗanda suka fi ƙarfina. Kakeson ka cimma wata manufarka ta hanyar amfani dani, bazan taɓa mantawa da wannan ba Maheer, bazan manta ba, zan cigaba da tuna irin yanda ka kula dani a baya kafin ka nuna ƙudirinka na aurena!" Tana gama faɗin haka ta fice daga ɗakin kamar zata tashi sama. Ajiyar zuciya ya sauke deep down nasa yana jin babu daɗi abin da ya yi mata domin tabbas ta riƙe shi masoyi kuma abun dogaronta bata taɓa tunanin haka daga gare shi ba, da wannan tunanin Maheer ya ƙarasa yinin ranar dan ko babban parlon bai sake fitowa ba.
Washegari.
Da wuri tagama shirin makarantar ta dan akwai abin da takeson faɗawa Rania kafin su fara lecture, tana ƙoƙarin fita daga ɗakin ya shigo kallonsa ta yi sai kuma ta saki murmushi ta tsuguna har ƙasa ta gaisheshi, amsawa ya yi da fara'a a fuskarsa ta tashi tana sunkuyar da kanta ƙasa
"Makaranta za ki?"
Gyaɗa masa kai Imara ta yi, ya jinjina kansa shima ya ce "ki zo mu fita tare sai driver ya ajiye ki" har zata ce a'a sai kuma ta gyaɗa masa kai ko babu komai zata samu damar kasancewa tare dashi har ta sake fahimtar wasu abubuwan da ya shafi Udaid. Da wannan tunanin ta bi bayansa suka fice daga apartment ɗin,
Tunda suka fara sakkowa ta zuba musu idanu tana kallonsu, wani irin abu taji ya zo ya tsaya mata a ƙirji nan da nan fuskarta tayi jaa na tsananin baƙin ciki, ita kaɗai ce a parlon hannunta riƙe da mug na tea. Imara ce ta kalleta cikin sakin fuska ta ce "Sabahul khair Maha" mayar mata da murmushin tayi ta ce "kin tashi lpy?" "Alhamdulillah" cewar Imara,
"Barka da fitowa Ameer" Maha ta faɗa tana ƙoƙarin barin parlon, jinjina mata kai Ameer ya yi bai ce komai ba ya fice daga fadar, Imara tabi bayansa.
*London*
10:00am.
Tamkar wacce ke magana da statue haka ya yi mata, daga ƙarshe ma ya sanya Bluetooth a kunnensa yana jin karatu, baki Jadda ta saka ganin ya yi mata shiru sai kuma ta kama gefen hijab ɗin dake jikinta ta fara goge kwalla. Gajiya ya yi da zaman ya miƙe hannayensa zube a aljihu ya ce "idan kin gama kukan ki sameni a waje, if not wlh zan tafi na barki ƙasar nan" da harara Jadda ta bisa, sai kuma ta cigaba da haɗa kayan nata tana magana cikin masifa
"Yaro ba mutunci gare shi ba yanzu sai ya tafi ya barni, sallamamme".
***Suna fitowa daga lecture Imara ta kalleta ta ce"kinsan me kuwa?" Girgiza mata kai Rania ta yi ta ce"zo muje zan baki labari" da sauri Rania ta kama hannunta tana dariya ta ce"nidai wlh ki faɗamin anan kawai" murmushi Imara tayi bayan ta zauna kan wata kujera ta kalli Rania tana nuna mata gefenta ta ce"zo ki zauna" babu musu Rania ta zauna ta yi tagumi ta ce"oya ina jinki Maza-Maza" numfasawa ta yi ta ce"ƙawata ta kirani ta cemin taji daɗi shawararki har tafara sanin wasu abubuwan na dangin mijin nata" murmushi Rania ta yi ta ce"To Masha Allah, ta cigaba da kaiwa Allah kukanta in sha Allah komai zai zame mata tarihi" dafata Imara ta yi ta ce"zan faɗa mata in sha Allah, kema kuma ina godiya" harararta Rania ta yi ta ce"banson hauka fa" tuntsirewa sukayi da dariya a tare.
MAHEER.
Zaune yake cikin office ɗinsa sai juyi yake kam kujerar tasa, abubuwa dayawa suna neman shigowa rayuwarsa, tunani yake wani hukunci zai yanke akan Imara tunda dai yanzu ya gano ba ita ce wacce yake muradin yin rayuwa da ita ba, kodai ya maidata garinsu?, ko dai ya sanar da ita gaskiyar daya daɗe yana ɓoye mata?, amma wane kallo zata yi masa?
"Calm down Maheer, calm down!" Ya faɗa yana dukan kansa, ganin tunani na neman hargitsa ƙwaƙwalwarsa yasa ya miƙe ya ɗauki car key ɗinsa ya fice daga Companyn gaba ɗaya.
***Fitowa Joda tayi daga motar tana ƙarewa wajen kallo kafin ta saki handle ɗin motar ta fito tana tafiya cikeda taƙama, hango shi tayi zaune idanunsa maƙale cikin glasses baƙi ta ƙarasa wajen tana murmushi, zama tayi gefensa cikin fara'ar da batasan tana da shi ba ta ce "welcome yallaɓai" murmushi ya sakar mata shima cikin jin daɗi ya ce "thank you beauty" murmushi tayi har saida beauty point ɗinta ya loma sannan ta ce"ka yar dani ko?" Waro idanunsa ya yi ya ce "ni ɗin?" ta gyaɗa masa kai tana kwaɓe fuska, girgiza kansa ya yi ya ce "nikam karki min sharri, tunda kika baro turkey baki nemeni ba sannan ni yanzu ki ce na watsar dake?" rufe bakinta tayi tana dariya ta ce "kawai a bar maganar, tunda naga ƴar tone tone ce" dariyar shima ya yi ya ce "kinsan ai kece bakida gaskiya kawai" murmushi ta yi ta ce"shikenan naji let bygone be bygone, yanzu me zaka ci?".
Wani banzan kallo Maheer ya watsa masa ya miƙe ya ce"kai naga ba'a abun arziki dakai nayi ta nan" tuntsirewa ya yi da dariya yana riƙe rigarsa ya ce"haba friend wlh wasa nake zo kaji" doke hannunsa ya yi ya ce" just leave me " shafa kansa Asad ya yi yana dariya ya ce"zama ka dawo ne yaro".
6:00pm.
Tafiya suke a tare suna ɗan taɓa hira gaba ɗaya sun gaji kasancewar yau sai yammaci suka tashi daga lecture, ganin yanda take ta kwaɓe fuska yasa Rania ta ce "wai yaushe kika zama haka ne?, ke da bakida son jiki amma ji yanda kike yi yanzu haba!" kallonta Imara tayi sai kuma ta yi murmushi tana sake ƙanƙame books ɗin hannunta ta ce "to ai da kika sani" shiru Rania tayi ganin kamar ba son maganar take ba, waro idanu Imara tayi ganin wanda yake gabato inda take, gaba ɗaya guards sun zagaye shi ko ba'a faɗa maka ba kasan babban mutum ne wanda ƙasar ke ji dashi. Murmushi Ameer ya sakar mata daidai lokacin da yazo dab da ita, baki buɗe Imara ke kallonsa kafin ta haɗiye yawun bakinta cikin sanyin murya ta ce "ba dai laifi nayi ba?" girgiza mata kai ya yi ya ce " zuwa nayi tafiya dake" baki buɗe Imara ke kallonsa sai kuma ta ce"ai da baka zo ba bama yanzu zan tafi, kuma..." shiru tayi ganin yanda Ameer ya kafeta da idanunsa, da hannunsa ya yi mata nuni da ta shige ta tura baki gaba sannan tayi gaba tana ɗagawa Rania hannu, murmushi Rania tayi itama tana ɗaga mata hannun. A back seat ta zauna tana sake ƙanƙame books ɗin hannunta haka kawai take jin ta uncomfortable musamman da daga Ameer na zaune gefenta duk da ba ita yake kallo ba ɗan ƙaramin azkar ɗin hannunsa yake ja. Har suka ƙarasa gida babu wanda yace komai a cikinsu kowanne da abin da yake saƙawa cikin zuciyarsa, tana ganin motar tayi parking ta kama handle ɗin zata buɗe amma ta ji shi ƙam da alama lock aka sakawa motar, gyran murya ya yi driving ya fice daga motar Imara ta juyo ta kalleshi tana rarraba idanu, ganin har sannan bai ɗago kansa ba yasa kamar zatayi kuka ta ce " zan sauka" ɗago kansa ya yi ya kalleta, saurin runtse idanu Imara tayi ganin yanda idanunsa suka sauya launi sunyi jajur dasu sun ƙara fitowa. Cikin rawar murya ta ce
"Am...Ameer lafiya?, wani abu yana damunka?, ko bakada lafiya?" Ta jera masa tambayoyin lokaci guda, lumshe idanunsa ya yi kawai nan take wani ruwa ya kwanta cikin idanun, hannunta ta kai zata taɓa shi ko me ta tuna kuma sai ta janye jiki a sanyaye ta ce
"Mene ne yake maka ciwo?, ko na faɗawa Maheer?, bari na kira Shamma" ta juya tana kama handle ɗin ƙofar a karo na biyu, tattausan hannunsa ya sanya ya riƙe nata hannun tana juyowa ya girgiza mata kai, kwaɓe fuska tayi ta ce"to kuma kai bakada lafiya ba za'a faɗawa kowa ba, ko so kake ka mutu?" Wani murmushi ne ya suɓuce masa, Imara sakar baki tayi tana kallonsa ganin yanda ya yi wani irin kyau tamkar ba tsoho ba, ganin kamar tayi nisa cikin tunani ya sanya ya ɗan girgiza ta kallonsa tayi ta ce "ni ka saukeni"
"Baki son Ameer ɗin?"
Ta tsinkayi daddaɗar muryasa, kallonsa tayi taga kamar ba shine ya yi maganar ba dan kwata-kwata ma ba ita yake kallo ba, langwaɓar da kai ta yi ta ce "ayyah Ameer magrib yana yi kuma zaka je masallaci" ta faɗa ba tare da tabi ta kan waccen maganar ba, shiru ya yi mata bai bata amsa ba yasa ta haɗe rai cikeda ta tsiwa ta ce " ni ka buɗe motar na fita, haba!" Murmushi ya yi ya ce "rigima kuma za'a min?" shiru ta masa dan gaba ɗaya ya fara fusatata ya ce "tom ji ke saida safe" kafin ya rufe bakinsa ta buɗe ƙofar motar tayi waje tana yarfe hannu.
Ajiyar zuciya Maha ta sauke tana sakin window ɗin, da gaske ne Ameer neman Imara yake!, yaushe Ameer ya zama haka?, me yake damunsa da har zai iya aikata irin wannan ɗanyan aikin?, kenan da gaske cin amanar Shamma yake?.
"No, bazai yiwu ba!, bazan bari ba, dole sai nayi maganin wannan matsalar" Maha ta faɗa cikin ɗaga murya, cikin hanzari ta fita daga ɗakin nata tana tafe kamar wata zararriya.
***
Tunda suka shiga cikin jirgin bata sake ganin gilmawarsa ba, ta zuba uban tagumi tana tunanin inda ya shige ya barta, ƙofar VIPn ya buɗe ya fito yana sanye da wasu English wears t-shirt milk colour sai three-quarter coffee gashin kansa wanda yasha gyara sai sheƙi yake ya zubo har wajen kafaɗarsa, tafiya yake kamar baya so sai yamutse fuska yake har ya ƙaraso gabanta. Wani nannauyar ajiyar zuciya Jadda ta sauke kafin ta kalleshi ta galla masa harara cikin faɗa take faɗin
"Kai dai wannan yaro ka sauya hali!, banda kai sallamamme ne ka yi tafiyar ka ka barni cikin jimamin inda ka shiga, saboda rashin imani irin naka, to wlh kaida Allah, kaje idan ka zalunceni ni na yafe maka dan bazan maka baki ba, amma dai ka sauya hali!" Ta ƙarashe maganar tana nuna shi da yatsa, wani kallo ya yi mata wanda ya sanyata sauke idanunta ƙasa cikin kwantar da murya ba kamar ɗazu ba ta ce
"Haba mijin sai ka tafi ka barni bayan kasan yanda na damu dakai, banason na mutu banga aurenka ba" ta kama gefen mayafin jikinta tana goge hawaye, ji ya yi jikinsa ya yi sanyi ya kamo hannunta ya riƙe cikin nasa yana murmushi ya ce
"Ke da zakiyi shigar amare ranar bikin ai kina nan ma, ko amaryar na tabbata ba zata faɗa miki kyau ba" washe baki tayi tana kallonsa cikeda fara'a ta ce "to to Masha Allahu, wa ya ganni bikin mijin ai baza'a gane ni ba" murmushi kawai ya yi ganin hankalinta ya kwanta kuma daman abin da yakeso kenan.
Maƙalewa Jadda tayi jikin matattakalar jirgin tana ƙarewa garin kallo ganin ba inda ya dace su kasance ba, zuwa ya yi ya shige ta gabanta tayi saurin figoshi tana kallonsa ta ce "kai ina ne nan ka kawo ni?" Bai ce mata komai ba ya zare hannunta daga jikinsa ya ƙarasa sauka daga jirgi, cikin saurin ta irin na tsoffi ta ƙaraso gabansa ta ce a fusace
"Hala da Fatima kake magana da kayi shiru ko?" A fusace shima ya juyo ya ɗora hannayensa a ƙugu kamar mace yana zazzare mata idanu ya ce" me
kika ce?"
"To ni kuwa me zance ɗan nan?, kawai tambaya nake ina ne nan?"
"Ƙasarku na kawo ki ki gani!".