Chapter 9&10
by @nanameera08
*IMARA💋💋*
*Chapter 9&10*
Waro idanu Jadda tayi sai kuma ta shiga tafa hannu, tsabar baƙin ciki ya sanya ta rushe da kuka tana kallonsa ta ce "Wlh Muhammadu zan nuna maka ɓacin raina da baka taɓa ganin irinsa ba, kayi gaggawar sauya wannan maganar taka" tunda ta fara magana yake kallonta, duk abinda ta faɗa daga cikin zuciyarta yake, da gaske batasan zuwa wajen danginta, ta guji yan 'uwanta, yaushe wannan gabar zata ƙare?. Ganin yanda ta haɗe rai kamar ba ita ba ya sanya ya kamo hannunta cikin sanyin murya ya fara magana
"Jadda dan Allah kiyi haƙuri, mene rayuwar?, abin da ya faru ya shige mana, ki dawo cikin dangin ki, ki daina gudun 'ya'yanki, uhm" kafeshi tayi da idanu bata ce komai ba, ganin yanda idanunta ya fara sauya launi ya sanya ya girgiza kai ya ce"shikenan yanzu ki yi haƙuri zan yi mana booking flight ko zuwa dare ne, kafin nan muje gidan ku gaisa"
"Abaan!"
Yaji ta kira sunansa cikin wata murya mai nuna asalin fushin da take ciki,
"Karka kuskura ka sake furtamin maganar su anan, idan ba haka ba wlh zan saɓa maka, sannan kuma ni bazan je inda suke ba, har abada!" Shafa kansa kawai ya yi sanin halin gaddamar Jadda, cikin sanyin murya ya ce"shikenan bari muje hotel sai nayi mana booking flight"
"Da ka nemawa kanka salama"
Bai sake bi ta kanta ba ya yi gaba tana biye dashi.
*UDAID*
7:35pm.
A hankali ta tura ƙofar ɗakin tana wulla idanunta ciki, babu kowa a ciki sai ƙamshi dake tashi ko'ina an gyara shi tsaf, ƙarar zubar ruwan da taji yasa ta kalli toilet ɗin, sai kuma ta yi tsaki ta ƙarasa gaban madubin hannunta ta ɗora kan drawern ta zubawa fuskarta idanu, abubuwa dayawa zuciyarta ke raya mata.
"Lafiya Maha?"
Ta tsinkayi muryar Imara tana mata magana, wani irin abu taji ya tsaya mata a ƙirji nan da nan fuskarta tayi jaa, ta juya yana watsa mata wani shegen kallo ta ce" lafiyar ce ta kawo haka munafuka!" Baki buɗe Imara ke kallonta, Maha ta cigaba da faɗin
"Saboda ke mahauciya ce baki san me kike ba, shashasha, dabba, me bakin iyaye har zaki nemi ubanmu ko?, saboda ke daƙiƙiya ce bakisan abinda yake daidai da wanda ba daidai ba ko?, saboda ke matsiyaciya ce ƴar matsiyata ko?, kin bani mamaki!, nayi tunanin ke mutuniyar kirki ce ashe ba haka bane, no wonder naga kowa na gudunki a gidan nan ashe su suka san da wacce suke zaune. Ki rasa wa zaki nema ma sai uban mijinki, surukinki!,"
Ɗora hannu Imara tayi aka tuni hawaye suka gama wanke mata fuska cikin rawar murya ta ce
"Wl...wlh...Mah... Wane ya faɗa miki?"
"Sai an faɗa min?, daman kun sanar da wani ne wanda kuke tunanin zai faɗawa wasu?, abin da kuke tattaunawa a cikin ɗaki, nima Allah ne ya yi nufin tonon asirin ku yasa naji kuna maganar, kinyi asara wlh kuma na rantse miki da Allah ba zan bar maganar nan iya haka ba saina tona idan yaso kuwa yaji abin da kuke aikatawa!" Ta ƙarashe maganar cikin ƙaraji sannan ta fice daga ɗakin. Zubewa Imara tayi kan tiles ɗin saidai zuwa sannan ko kukan ma ta kasa samun damar yi, sai wata irin rawa da jikinta ke yi, ta jure jikinta waje guda tana sauke ajiyar zuciya akai-akai.
***Zaune yake gefen gadon nasa sai juya takardar dake hannunsa yake, tunani yake idan abin da ya yi shine abin da ya kamata, amma ya mutane zasu ɗauki maganar tasa?, Allah yasa kowa ya fahimceshi. Wani zazzafan numfashi Maheer ya sauke kafin ya tashi tsaye ya linke takardar ya zura a aljihun trouser ɗinsa sannan ya yi waje, a bakin stairs ɗin ya hangi Joda tana danna wayarta, ƙarasawa gabanta ya yi without making any sound yana zuwa ya rufe mata idanu da hannunsa, ɗan murmushin gefen baki tayi tana riƙe hannayen nasa ta ce
"Wai ka mantani, tun daga nesa na ganka fa"
Waro idanu ya yi yana juyo da ita gabansa ya ce" oh shit!" Tuntsirewa tayi da dariya ta ce "ina zuwa ne na ga kasha kwalliya?" Harararta ya yi ya ce "inda kika aikeni" rufe bakinta tayi da hannunta tana dariya ta ce"au nafa manta ba'a tambayarka inda zaka" girgiza kansa ya yi yana murmushi ya sauka daga Benen.
*DAMEER*
Tunda ya shiga yake kai kawo a cikin ɗakin yana jin ransa babu daɗi, tamkar zuciyarsa zata fito haka yake ji, turo ƙofar ɗakin tayi ta shigo tana kallonsa ta ce"Dameer lafiya?" juyowa ya yi ya kalleta idanunsa sun kaɗa sun yi jajur dasu, yanda ya kafeta da idanu yasa Immi ta ce "ka tsareni da ido, ka sanar dani abin da ke faruwa" wani zazzafan numfashi ya furzar daga bakinsa ya zuba hannayensa a aljihu yana kallonta ya ce
"Immi raina ya fara ɓaci da wannan al'amarin, abubuwa sun fara fin ƙarfinmu, ƙaramar magana na nema ta zama babba, Udaid zata bar hannun mu ki fahimta!" Ya faɗa yana dafa kafaɗarta. Girgiza kai Immi tayi tana janye shi daga jikinta ta ce" wai meke damunka Dameer?, ta ya ya?, bazan bari haka ta faru ba!, dole sai nasan yanda nayi mulkin Udaid ya dawo hannunka, koda kuwa bakada gadonta".
"Immi kin sani na sani ni ba jinin gidan nan bane, ban raɓi Udaid ba!, kin kawo ni a matsayin Dameer wanda ya mutu tun bayan kwana biyu da haihuwarsa, nasha gwagwarmaya sosai a cikin fadar nan, har na girma cikinta ina faɗi tashi na yanda zan samu wani matsayi a cikinta, amma ace har yanzu ban cimma matsaya ba?, banida wani abun dogaro?, ba zai yiwu ba!, wlh ba zai yiwu ba Immi!"
Kamo hannun tayi ta zaunar dashi kan kujera ta dafa table ɗin dake gabansa tana kallonsa ido cikin ido ta ce
"Me kake nufi da wannan maganar taka?, meyasa ka sakota cikin zancenmu?, juyan baya ka shirya yi ne?, so kake wani yaji abin da kake cewa?, karka sake Dameer!, kar ka kuskura ka sake furta irin waɗannan kalaman ko da kuwa dani ne, kai Dameer ne wanda aka haifa cikin fadar nan, so you have to be careful!"
Yanda Immi tayi maganar cikin ɓacin rai ya sanya shi yin shiru, bai ce komai ba ya tashi ya fice daga ɗakin sai sauke ajiyar zuciya yake. Wani gumi ne ya shiga keto mata wanda batasan na mene ne ba, kodan abun da Dameer ya faɗa ne?, kada watarana asirinta ya tonu.
"Never!"
Ta faɗa a fili,
"Ke dawa?"
A firgice Immi ta juyo tana kallon Joda wacce ke tsaye kanta hannunta riƙe da system, doguwar rigar Turkey Abaya ce a jikinta ta ɗaura veil ɗin abayar a kanta, sosai farinta ya ƙara fitowa kasancewar abayar Black colour. A ɗan daburce Immi ta ce
"Aaa...Joda yaushe kika shigo?"
Taɓe baki ta yi ta zauna gefen gadon tana kallonta ta ce"kina can zancen zuci" murmushi Immi tayi tana hamdala aranta da bataji abin da Dameer ya ce ba, ta kalleta ta ce"zancen zucin me zanyi nida babu abin da ke damuna sai naga kin yi aure" kallonta Joda tayi sai kuma ta kwaɓe fuska ta ce"aure kuma Immi taɓ!, nidai a'a wlh" dariya Immi tayi ta ce"ai aure ya zama dole Joda mu duk ba auren muka yi muka haife ku ba?" Yamutse fuska tayi daidai lokacin wayar hannunta ta fara ƙara, sunan da tagani akan screen ɗin wayarta ya sanya ta miƙe tsaye da mamaki Immi ta kalleta ta ce"lafiya dai?" girgiza kai Joda tayi bata samu damar bata amsa ba tayi waje da sauri. A babban parlon ta tsaya tana sake kallon wayar kafin ta ɗaga kiran ya katse.
"I'm outside"
Taga text message ɗin ya shigo wayarta, tamkar wacce aka cirewa laka haka taji, ta kasa gaba ta kasa baya. Nan da nan hawaye ya kawo idanunta, ganin lokaci na shigewa ya sanya tayi waje da sauri,
Duba gabaɗaya farfajiyar gidan tayi bata hangi kowa ba sai masu aiki da kowa ke abin da ke gabansa, mayafin kanta ta saki ta yafa sannan ta fice daga gidan da sauri, daga can tsallake ta hangeshi tsaye ya juya baya kwantaccen gashin kansa mai kama da na mata ya zubo wajan kafaɗarsa, da gudu ta tsallaka ba tare da ta kalli titin ba dukda motoci na shigewa tana zuwa ta ƙanƙameshi ta baya tana sakin wani raunataccen kuka, wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana ɗan jan numfashinsa, hannunsa ya sanya ya jawota gabansa ta sake shigewa jikinta tana cigaba da kukan, numfashinta har ɗaukewa yake hannunsa ya sanya ya rungumeta sosai ya shiga shafa kanta ba tareda ya ce mata komai ba, sun ɗauki lokaci a haka kafin ta fara sauke ajiyar zuciya tana jan numfashi, ɗago kanta tayi tana kallonsa ta shiga shafa fuskarsa hannunta na rawa
"Ak...Akhi...Akhee!"
Hannunsa ya ɗora akan nata yana ɗan murmushi ya shafi kanta ya ce"kina lafiya?" Kasa magana tayi ta sake fashewa da kuka tana rungumeshi ta shiga girgiza kanta, ɗago fuskarta ya yi ya zuba mata idanu gaba ɗaya fuskarta tayi jajur da ita idanunta sunyi jaa, ko ba'a faɗa maka ba daga ganinta kasan y'ar uwarsa ce dan har kamar tasu ta ɓaci. Saida yaga ta sami nutsuwa sannan ya janye hannunsa cikin sanyin murya ya ce
"Duk sanda na sake zuwa kikayi kuka bazan kuma dawowa ba!" Girgiza kanta ta shiga yi tana rufe bakinta gudun kada kukan nata ya fito ta ce "to kayi haƙuri bazan ƙara ba" yanda tayi maganar Cikin shagwaɓa ya sanya ya harareta ya ce"yaushe zaki girma Joda?" Turo bakinta tayi gaba ya yi murmushi wanda ya fito da zallar kyansa ya ce "shikenan ki koma ciki, duk sanda kike buƙatar wani abu just let me know kinji" rau-rau tayi da idanunta kamar zata yi kuka ta ce "tafiya za kayi?" Gyaɗa mata kai ya yi yana ɓame bakinsa kamar yaro ƙarami, wasu sabbin hawayen ne suka fara sintiri kan fuskarta ya waro idanunsa yana murmushi ya ce"ɓaure sarkin kuka, zo nan" ƙarasawa tayi ta shige jikinsa ya shafa kanta yana murmushi ya ce"ki fito da miji nayi miki aure" fashewa tayi da kuka tana dukansa s ƙirji ta ce cikin wata shagwaɓaɓɓiyar murya
"A'aaaa ni banaso!"
Dariya ya yi ya ce"ai ko dole kiyi aure yarinya" ɗago kanta tayi ta hararesa ta ce "to kai ma kayi auran" murmushi ya yi ya ce"ai daman na kusa watarana zan nuna miki matata" murmushi ta yi ta ce"tom Allah ya kaimu" janyeta ya yi a jikinsa ya ce"I'm coming" jinjina masa kai tayi ya juya inda ya yi parking motarsa ya buɗe, wasu ledoji ya ɗebo sannan ya dawo wajenta yana murmushi ya ce"guess what?" Lumshe idanunta tayi ta bude ta ce"chocolate?" dungure mata kai ya yi ya ce"kwaɗayi" turo baki tayi tana shafa goshinta ta ce"wollah da zafi yaya" "to bari na ƙara miki" ya faɗa yana kawo hannunsa, saurin yin baya tayi tana tuntsirewa da dariya ta ce"ni dai a'a" murmushi ya yi ya ce"nidai riƙe zan shige" shiru tayi tana kallonsa ta karɓi ledojin kamar zatayi kuka ta ce
"Yayaaa!"
Kama hannunta ya yi yana murmushi ya ce"ƴar ƙaramar kanwata " rungumeshi tayi tana fashewa da kuka ta ce"ni karka tafii, karka barni dan Allah" shafa kanta ya yi yana sakin ajiyar zuciya ya ce cikin sigar rarrashi
"Kin fi so raina ya ɓaci Joda?" Girgiza masa kai ta yi ya ce"good, saboda haka ki koma ciki nayi mikin alƙawarin zuwa na tafi dake kinji" sanin halinsa ya sanya ta gyaɗa masa kai kawai tana sake tusa kanta cikin ƙirjinsa, ɗago fuskarta ya yi ya shiga goge mata hawayen yana murmushi ya ce"ki daina rigima Joda" murmushi tayi masa ta ce"to yaya" peck ya yi mata a goshi sannan ya saketa
"Tafi"
Ya faɗa yana kallonta, kallonsa tayi sai kuma ta juya tafara tafiya toward direction ɗin gidan, tana zuwa ƙofar ta sake juyowa ta kalleshi taga ya ɗaga mata hannu. Ɗaga masa itama tayi sannan ta shige cikin gidan, wani zazzafan numfashi ya sauke sannan ya shige motarsa ya bar unguwar.
***Around 9pm ya shigo ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, amsa masa tayi idanunta ya kumbura, da mamaki yake kallonta ya zauna gefenta sake goge idanunta ta yi tana murmushi ta ce "sannu da zuwa"
"Mene ya saka ki kuka?
Girgiza kai tayi tana goge idanunta ta ce "abu ne ya faɗa min idona" hannunsa ya ɗora akanta ya ce" yanzu fa?" "Ya fita" ta faɗa da sauri, jinjina mata kai ya yi sannan ya zaro wata box a bayansa yana murmushi ya ce "gashi nan" karɓa tayi ta ce"mene ne?" Yunkurin buɗewa tayi ya yi saurin riƙe hannunta yana murmushi ya ce"no ki bari ba yanzu ba" murmushi tayi ta ce "Nagode"
"Saida safe"
Jinjina masa kai tayi ya tashi ya fice daga ɗakin, a ƙofar ɗakin ya tsaya ya jingina da bango ya yi shiru kamar wanda wani abu ke damunsa.
"Akhii me kake anan?"
Juyowa ya yi ya kalleta sai kuma ya yi murmushi ya ce"Maha rigima" murmushi kawai tayi ta ce"meke damunka?" "Me kika gani?" Shima ya bata amsa, girgiza kai tayi ta ce"shikenan kawai" tayi gaba bata sake cewa komai ba, da kallo ya bi bayanta sannan shima ya bar wajen.
A hankali ta tura ƙofar ɗakin ta shiga, zaune ta hangeshi gefen gado yana jan cazbahar hannunsa, sallama ta yi ya amsa ba tareda ya kalleta ba, ƙarasawa tayi ta tsuguna a gabansa cikeda ladabi ta ce "Barka da hutawa Ameer" kallonta ya yi fuskarsa a sake ya ce"Maha" "na'am Abbiey" murmushi Ameer ya yi ya ce"Masha Allah" shiru suka yi na wani lokaci, magana takeson tayi masa amma kuma nauyinsa da take ji ya hanata, kwarjinin Ameer ya hanata amayar da abinda ta ƙunso, ganin bata ce komai ba ya sanya ya yi gyaran murya. A ɗan firgice ta kalleshi sai kuma ta yi murmushi ta ce"daman zuwa nayi zan faɗa maka wata magana" gyara zamansa ya yi yana kallonta ya ce " Tom inaji" cikin sanyin murya ta fara magana a harshen larabci
"Ameer naga wani abu ne ko na ce naji wata magana ne wacce ta sanya naji tsoro, naji babu daɗi, na shiga ruɗani, hankalina kuma ya tashi,koda wasa ban taɓa tunanin hakan ba, meyasa Ameer?, meyasa?, why?, why??. Meyasa sai ita?, idan kace wata kakeso wlh babu wanda zai hanaka aure, tunda ba haramun bane, amma wai IMARA! IMARA!, IMARA matar Maheer, ita kakeso Ameer?, matar auren matar kuma ɗanka, why Ameer?, why? Wlh zuciyata gab take da bugawa, naji kamar na gudu na bar gidan nan, wane irin saɓon Allah ne Ameer?, da girmanka da mutuncinka, ka aikata irin wannan abun, me Shamma da Immi suka rageka dashi?, dame TA FI SU?(Upcoming novel) Yarinyar da ba kowan kowa ba, naji ba daɗi Ameer, kuma Wlh wannan abun ba daidai bane, na zaɓi nayi maganar da kai ne saboda naji ta bakinka, idan har ya tabbata kuma hakane wlh sai nafaɗa kowa yaji a fadar nan, gwara ayi duk abin da za'a yi da ku cigaba da wannan rayuwar, bazan bar maganar ba!, wlh bazan bari ba! Ka bani kunya Ameer!, ka ruguza soyayyar dake tsakanin mu, ka sanya shakku cikin zuciyata, wlh bana son ganinka! Banason ganinka Ameer!, banaso...bana...b"
Maganar ta maƙale saboda kukan da yaci ƙarfinta, tunda ta fara magana Ameer ke kallonta bazaka taɓa cewa dashi take ba yanayin nutsuwarsa bai sauya sai idanunsa da suka kaɗa sukayi jajur, jijiyoyin kansa sun firfito, ganin tayi shiru ya sanya ya kama hannunta jikinsa na rawa ya fara magana
"Karki yimin mummunar fahimta Maha, babu abin da ke tsakanina da IMARA, kawai dai nasan ina sonta, son da bansan dalilinsa ba!, tabbas ina ƙaunarta, inajinta har cikin raina, kuma wlh nafi Maheer sonta, nasan zaki fahimci Ameer ɗin ki, ina nan a matsayina na masoyinku, bazan taɓa canzaku ba dan Allah kuma karku canzani"
"Dole mu sauyaka domin bazamu cigaba da rayuwa da mahaifi irinka ba!, ba kada imani Ameer! Wlh bakada Imani!, bazan taɓa barin wannan cin amanar ba saboda haka zaka ga abin da zan aikata!, zan yiwa tufkar hanci, zan tabbatar ban bar wata alama wacce za'a gane ka ba, zan rufe maka sirrinka har abada" wata ajiyar zuciya ya sauke ta samun sauƙi ya miƙe yana kallonta ya ce" daman nasani ba zaki juyamin baya ba Maha, nasan kina tare da Ameer ɗinki" fashewa tayi da kuka ta shige cikinsa tana rawar murya ta ce"kayi haƙuri Ameer, wlh bazan jure ba, bazan iya yafe cin amana ba, ka yafeni Ameer, ka yafeni...wlh ina sonka..ina sonkaa..." Tayi baya tana cire jikinta daga nasa. Kallonta Ameer ya yi sai kuma ya kalli cikinsa wanda ke zubar jini kamar an buɗe famfo dafa cikin nasa ya yi ya ɗago yana ƙoƙarin yi mata magana daidai lokacin Imara ta shigo ɗakin, sandarewa tayi ganin Ameer cikin jini ya durƙusa da gudu ta tafi ta riƙe shi tana jijjigashi cikin tashin hankali take faɗin
"Ameer, Ameer!!!! Ameer!! Ka tashi kaji kada ka rufe idanunka, zan kira Maheer ya kai ka asibiti, karka rufe idanun Ameer, karka rufe don Allah!!!!" Ɗago idanunta tayi da niyyar yiwa Maha magana taga babu kowa a tsaye, a hankali kuma ta kalli gefenta taga wuƙar da aka kashe shi da ita, an ajiye mata jikinta kuma duk jinin Ameer ɗin, hannunta na rawa ta ɗauki wuƙar ta shiga juyata daidai nan kuma Shamma ta bude ɗakin ta shigo. Sakin wuƙar tayi ta sake riƙe shi tana jijjigashi cikin tsananin tashin hankali take faɗin
"Dan Allah Ameer karka tafi ka barni, ka tashi kaji, kasan me? Ina sonka wlh inama ina sonka ka tashi kaji!, zan dinga dafa maka abinci mai daɗi ka tashi kajii" gaba ɗaya ta fice a hayyacinta banda kiran sunansa babu abin da take, wani ihu Shamma ta saki wanda ya yi sanadiyar shigowar mutane ɗakin da gudu suka ƙaraso wajensa suna kallonsa
"Kika kashe shi?"
A razane Imara ta ɗago idanunta tana kallon Maha, kafin tayi magana Immi ta ce"inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun, ta kashe shi, wlh ta kashe shi, shikenan ta kashe Ameer" bin su kawai Imara ta shiga yi da kallo kafin ta miƙe tsaye daidai nan Maheer ya shigo dakin, da gudu ya ƙarasa wajen Ameer ɗin ya rungumeshi yana jijjigashi ya ce"Buddy, ka buɗe idanun, stay still, zan kai ka asibiti" hannun Ameer na rawa ya ɗora kan fuskar Maheer yana ƙoƙarin goge masa hawayen fuskarsa. Maha ce ta riƙe Imara cikin faɗa take faɗin"me mahaifin mu ya yi miki da zaki kashe shi?, saboda kina gudun ya tona miki asiri?, ke wace irin mara imani ce?, me ya yi miki IMARA! Me ya yi miki?" Girgiza kai Imara ta shiga yi tama kasa furta koda kalma guda ɗaya, hannunta ta kalla taga duk jinin Ameer tamkar ita ce wacce tayi kisan da gaske, wani irin sarawa kanta ya yi tayi saurin ɗora hannunta aka tana sakin wani firgitaccen ihu kafin ta juya da gudu ta fice daga ɗakin.
Ɗakinta ta koma ta shiga tana dube-dube kamar mahaukaciya, wajen dressing mirror taje ta barbazo da kayan dake wajen, juyawa tayi zata fita sai kuma ta dawo da sauri ta buɗe wardrobe ɗin ta daidai nan Maheer ya shigo ɗakin. Akwatin daya bata ta ɗauko da sauri ta fara ja da baya tana kallonsa cikin tashin hankali take cewa
"Wlh bani ba ce!, wlh bani ba ce!, ban kashe Ameer ba!, bani ba ce wlh!, tafiya ma zanyi" kallonta kawai Maheer ya yi bai ce mata komai ba ya ɗauki car key ɗinsa ya yi waje da sauri, da gudu ta tafi daga ɗakin ta sauka ƙasa bata ko ganin gabanta, fita tayi daga fadar har sannan bata daina gudun ba, da mamaki Maids ɗin fadar ke kallonta ganin kamar bata hayyacinta ta fice daga gidan gaba ɗaya.
***Tunda ya fito yake yawo ba tareda ya samu inda ake sayarda irin abincin ba, shi kaɗai yake jan tsaki yana dukan sitiyarin motar, tun daga nesa ya hangota tana gudu kamar wata mahaukaciya taɓe bakinsa ya yi a ransa ya furta
"Nonsense!"
Kamar wasa yaga tana ƙara yo inda yake duk ƙoƙarinsa na son ganin ya taka burki kasawa ya yi bai yi aune ba sai gani ya yi ta faɗi ƙasa, sai a sannan yaja wani dogon birki ya fito yana hargitsa sumar kansa wacce ta barbareje. Gabanta ya ƙaraso ya tsaya ya riƙe ƙugunsa wanda ya zamar masa jiki, ɗan siririn tsaki yaja sannan ya sunkuya dan ganin ko tana numfashi, da sauri ya kalleta ganin ta riƙe hannunsa bakinta na rawa ta furta
"Papaa..."
Sake kallon fuskarta ya yi jin sunan data ambace shi dashi da kuma muryarta, a ɗan razane ya durƙusa gabanta ya ɗago kanta waro idanunsa ya yi cikin wani irin yanayi ya furta
"*IMARA*"
*End of free pages 🤪💃*
*Wacece IMARA?*
*Da gaske Maheer ya mutu?*
*Wace rayuwa Imara zata faɗa bayan faruwar wannan al'amari?*
*Akwatin me Maheer ya bata?*
*Wacece Jadda kuma mene alaƙarta da Qatar?*
*Wane ne Abaan?, mene alaƙarsa da Joda?*
*Mene ne alaƙar Abaan da IMARA da har ya furta sunanta?*
*Idan Dameer ba ɗan Ameer bane to ɗan wane!?*
*Wacece Katalina kuma mene alaƙarta da IMARA!?*
*Mene ne abin da ya raba Shamma da ƴaƴanta?*
*Shin za'a kama Maha ko kuwa ba za'a ganeta ba?*
*Me IMARA ta rasa a rayuwarta da har ta faɗa wannan ƙangin?*
*IMARA💋*
*Domin samun amshoshin waɗannan tambayoyin ki biya Naira ɗari biyar kacal ₦500 via 7041901078 Hauwa Adamu lawan opay sai a turo da shaida ta *** Nanameera, masu Arewabooks kuyi following ɗina Nanameera08 zan dinga posting a can a matsayin
VIP*
*Note:*
*Littafin nan ₦500 ne idan zaki biya ki biya dan Allah 🙏 Ba zanyi ragi ba!, ki biya ki karanta cikin salama da kwanciyar hankali.*
# *Bestnovel*
# *2025*
# *Ameenatou*
# *IMARA💋💋*
***
Chat me to subscribe yours.