AMATURRAHAMAN

6

by @oumfatima33

💞💞💞💞💞💞💞💞

AMATURRAHAMAN

*By*

OUM FATIMA

*(Hakimar D. A. W. A)*

💞💞💞💞💞💞💞💞

*DASHEN🌲ALLAH*

*WRITER'S📚ASSOCIATION*

*TEAM*

*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*

BOOK 1

PAGE 6

*بسم الله الر حمن الر حيم*

Kai tsaye ɓangaren Mahaifiyarsa Hajiya Busaina ya nufa cikin taku irin na ƙaƙƙarfan sojan daya sha training. Jin tafiya a bayansa ya sashi dakatawa ya waiwayo don ganin wanda ke bin nasa, ganin Samuel ɗauke da jakarda ne ya bashi umarnin kaiwa can ɓangarensa dake a nan cikin gidan Iyayensa. Babban falo ne daya gaji da ƙayatuwa da kayan ƙawa da ake ƙawata falo dashi, sallamar daya furta cikin gwagwgwaɓar muryarsa mai razana marar jin magana tasa kyawawan ƴanmatan dake tafka musu akan wani Indian Film da suke kallo har basu ji shigowarsa ba natsuwa kowa tana gyara zama.

"Sannu da zuwa Ya ZAYYAD." Itace kalmar da gaba ɗayansu suke rigen furta wa. Kyawawan idanunsa masu ɗauke da wata irin baiwa dake saka ƴanmata da yawa faɗawa soyayyarsa lokaci ɗaya ba tare da sun farga ba ya zuba musu yana binsu da kallo, sai da ya kai kan budurwar da suke matuƙar kama wacce kallo ɗaya zai shaida maka cewar ita ɗin jininsa ce ya tsaida kallon "Ammah fa?" Ita ce tambayar daya jefa mata.

"Tana ɗaki." Ta faɗa tana nuna masa sama.

Bai ƙara kallon kowa ba a cikinsu ya nufi matakalar benen da aka mata wani irin shape mai birgewa ya shiga haurawa cikin kuzarinsa. Sai da ya ɓacewa ganinsu kafin suka shiga sauke ajiyar zuciyar samun nutsuwa kamar wadanda suka kubuta daga wani hatsari.

"Wai! Allah ya cecemu yau Banu da rabon shan wahala." Faɗin ɗaya daga cikin ƴammatan mai suna Amira.

"Ki bari kawai Meerah, kwata-kwata bamu ji tsayuwarsa ba, da ace ya ji akan me muke musun nan ai da kashinmu ya bushe yau, ni kam nayi nan gwara inje in yiwa Aunty ZAHEERA albishir ɗin dawowar sanyi idaniyarta, ko ba komai na samu goron albishir."

Fatima ta ƙarasa faɗa tana miƙewa. "Hm! Ni wallahi Aunty Zaheera tausayi take bani, ta ɗauki soyayyar wanda bai san tana yi ta saka a rai sai walaha take abin tausayi!"

Ameerah ta faɗa cike da jimami. "In dai Ya Zayyad ne tayi ta gama ƴar'walar!" Anisa ta faɗa tana ɓata rai fuskarta na nuna tsan-tsar kishi.

Gaba ɗaya ƴan'matan suka kalli juna suna taɓe baki kasancewar sun san cewa itama tana jikin jerin masu haukan son Zayyad ɗin, da haka suka fara ficewa bayan sun yiwa HANEEN data kasance ƙanwarsa ta jini sallama kowa ta nufi gidansu.

*** A bedroom ɗinta ya sameta tana amsa wayar ƴar'uwarta data kirata kan batun bikin yarinyarta da za'a yi. Da sallama a bakinsa ya ƙarasa ya zauna kusa da ƙafafunta saman lallausan Capet ɗin dake shimfiɗe a gaban gadon. Kyawawar mace ce mai kimanin shekaru arba'in da biyar (45 yers) wacce tsananin hutu da jin daɗi ya nuna a jikinta don bazaka taɓa cewa tayi waɗannan shekarun ba sabo da kyan jikin da take da shi da kuma iya kula da kai, fuskarta kawai zaka kallah ta shaida maka cewar ita ta haife shi, sabo da kamanninsa dake saman fuskarta. "Mutanen Abuja, saukar yaushe?." Ta faɗa tana kallon fuskarsa.

"Yanzu na zo Ammah, na sameku lafiya?." Ya faɗa cikin natsuwarsa da kamewa, mutum ne shi mai tsananin kamewa da tsentseni wanda ko Ammah da take Mahaifiyarsa baya iya sakewa sosai a gabanta kasancewarsa ɗan fari da take masa alkunya, itama bata wani sakewa dashi sosai. Sai dai fa hakan bai hana soyayyar Uwa da ɗa shiga tsakaninsu ba, musamman Zayyad da yake tsananin son mahaifiyarsa, itace Mace ta farko da yake tsananin so a duniya sannan Mahaifinsa da ƴan'uwansa, a ɓangarenta hakan take shine ɗa mafi doguwar a zuciyarta, sai dai tana ƙoƙarin dannewa a zuciyarta sabo da kara da kuma alkunya.

"Kaje kayi wanka ka huta , zan sa Haneen ta kawo maka abinci." Ya tsinci muryar Ammah tana faɗa.

"To Ammah na barki lafiya." Ya faɗa yana miƙewa, har ya kai bakin ƙofa ya juyo ya tambayeta "Abby fa?."

Sunje Matazu wani ɗaurin aure da Baba Alhaji ya tura su su wakilce sa shida Uncle ɗinku."

"Ok" Kawai ya faɗa yayi gaba, ɓangarensa dake can farkon shigowa gate ɗin gidan nasu ya nufa, inda ya tarar da komai a gyare tsaf yanda yake buƙata, kayan jikinsa kawai ya cire ya shige toilet don watsa ruwa yayi haramar sallar la'asar da ake gab da kira.

****

A Asibiti kuwa jikin Abba (Mukhtar) kamar yanda yaranta suke kiransa yayi tsanani sosai, abin duniya ya taru ya yiwa Umma yawa. Ta rasa inda zata saka kanta taji daɗi, gashi Kawu Isa ya tsere ya barta ita kaɗai ke fama dashi ga kuɗaɗen hannunta na gab da ƙarewa, ga damuwar halin da yaranta suke ciki. Ta san zuwa yanzu ɗan abinda ta bar musu ya ƙare, ko a wane hali suke ciki? Allah masani.

Wannan dalilin ne yasa ta yanke hukuncin neman sallama ta tattara su koma gida su zubawa Sarautar Allah ido. Yau da suka cika sati ɗaya a Asibitin ta yanke hukuncin in likita yazo duba su zata ce ya sallame su, sai dai kafin likitan ya ƙaraso Allah ya karɓi ran Mukhtar bayan ya ƙara neman gafarta.

Ta shiga tashin hankali sosai inda tayi kuka har ta gode Allah. Ta rasa yanda zata yi ga bata da waya bata riƙe lambar kowa ba bare ta sami aron waya ta kira gida azo a ɗauki gawar ba.

Wasu bayin Allah da suka ga halin da take ciki ne tana ta kuka suka taimaka suka samar mata shatar Mota suka biya kuɗin aka ɗauketa ita da gawar da rakiyar mutum ɗaya suka nufi Matazu.

Dokajo Mansion...

A bedroom ɗinta ta sameta ta ɗaura waya a jikin Ring light ta kafe Camera tana bin wani sabon challenge daya fito a TikTok sai iyayi take, a lumshe ido a mele baki duk don a birge mutane.

"Aunty Zaheera albishirinki!". Fatima ta faɗa lokacin data matso kusa da ita, bata kulata ba don kar ta ɓata mata videonta sai da ta kammala tayi posting kafin ta jiyo wurin Fatima data shaƙa sabo da ƙyaletan da tayi.

"Ya aka yi?." Ta tambayeta tana harararta.

"Na fasa faɗa tunda kika share ni!". Ta faɗa tana tura baki, wani tunani ne yazo zuciyar Zaheera sanin da tayi cewar Fatima ƙawar Haneen ce kuma yanzu haka daga gidansu ta dawo, kila labarin sanyin idaniyarta zata bata.

"Zo ki faɗa min, kika sani irin kyautar da zan baki idan labarin ya min daɗi?."

"Ya Zayyad ne ya dawo yanzu." Ta faɗa tana miƙa mata hannu don ta san babu labarin da yafi wannan daɗi a wurin Yayarta. Ai kuwa ihu Zaheera ta saki tana juyi. "Dan Allah? Yaushe ya dawo?, wayyo Allah zama bai ganni ba!." Ta faɗa tana nufar hanyar toilet.

"Dawo ki sallame ni." Cewar Fatima.

"Ɗauki duk abinda kike so." Ta faɗa tana shigewa don yin wanka ta sake sabon shiri.

"Yes!!" Fatima ta faɗa tana nufar gaban mirrow ɗinta, wani ɗan boxs ɗin da take aje sarƙoƙinta ta buɗe ta ɗauki sabon set ɗin sarƙar da ta sayo jiya da taje shopping, tun jiya take ƙwawar ta bata su ta hanata shine yanzu da ta bata damar ɗaukar abinda take so tayi ciki dasu...

Zaheera ƴace ga doctor Hashim Muhammad Dokajo ƙani a wurin Alhaji Muhammad M Dokajo wanda ya kasance mahaifi a Wurin Marshal Zayyad M Muhammad Dokajo. Zayyad shine ɗa na farko a wurin Mahaifinsa wanda Matarsa ta biyu ta haifa masa bayan tsawon shekaru da suka ɗauka da Matarsa ta farko Allah bai basu haihuwa ba, Allah ya haɗa shi da Barrister Busaina Bello ƴa ga Aminin Mahaifinsa Alhaji Tahir. Basu wani tsaya ɓata lokaci ba bayan fahimtar juna da suka samu ya gabatar wa Mahaifinsa ita a matsayin wacce zai aura.

Muhammad Dokajo wanda suke kira da Baba Alhaji yayi matuƙar farin ciki da jin hakan, don haka ba ɓata lokaci ya shaida ma Amininsa. Shima jin daɗinsa ya nuna don haka sati biyu aka saka yana zuwa kuwa aka ɗaura musu aure. Uwar gidansa Hajiya Ruƙayya tayi baƙin ciki da wannan auren don ba abinda ta tsana a rayuwa irin kishiya, sai dai ba yanda ta iya tana ji tana gani aka ɗaura auren aka kawo amarya gidanta. tsana da kishi muraran take nunawa amarya musamman data samu ciki daga zuwanta kuma ta haifi ɗa na Miji wanda hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba, a ɓangaren Alhaji Muhammad da kuma Mahaifinsa ba ƙaramin farin ciki sukayi da samun wannan ƙaruwar. Don haka suka ɗauki soyayyar duniya suka ɗorata akan Zayyad musamman Baba Alhaji daya kasance jika na farko a wurinsa, don haka abin ya matuƙar tsayawa Hajiya Ruƙayya a rai.

Tofa tun daga nan ta ƙara lunka tsana da ƙiyayyar da take yiwa Ammah da ɗan data haifa. Tun daga haihuwar Zayyad sai haihuwar ta dakata daga kansa sai da ta shekara huɗu kafin ta sake samun wani cikin, inda itama Hajiya Ruƙayya ta samu nata rabon wanda ba ƙaramin murna tayi ba. Tun cikin yana ƙarami ta ɗauki son duniya ta ɗora masa ta kuma yanke hukuncin cewar na miji zata haifa. Sai dai lokacin da cikin ya isa haihuwa sai ta haifi ɗa na mijin amma sai bai zo da rai ba.

Ba ƙaramin baƙin ciki tayi ba da faruwar wannan lamari ba, inda ta tada rikici akan cewar Hajiya Busaina ce ta shiga ta fita ta kashe mata ɗanta tun kafin yazo duniya. Da ƙyar dai Abby ya kashe wannan rigimar ba don ta haƙura ba, daga nan ta ƙara kullatar ta a rai.

Sati ɗaya tsakani Hajiya Busaina ta ƙara haife ɗanta na miji wanda hakan yaso tada ƙurar da aka kashe da ƙyar, ranar suna aka raɗawa yaro suna Muzaffar.

Ba'a wani ɗau lokaci ba Hajiya Ruƙayya ta ƙara samun wani cikin wanda take taka tsan-tsan a cewar ta kar a ƙara kassara mata ɗanta, wacce take ɗaukar alhakin nata bata damu ba sai dai tayi murmushi kawai ta barta da halinta.

Cikin ikon Allah Hajiya Ruƙayya ta haifi ɗa na miji kamar yanda take buri, kuma take ganin wato dabarar ta ne yasa ta haife shi lafiya. Ranar suna yaro yaci suna Salim, cikin ikon Allah kuma tun daga nan haihuwa ta buɗewa Hajiya Ruƙayya sai da ta haifi yara huɗu Mata bayan haihuwar Salim akai-akai, inda ita kuma Hajiya Busaina sai da ta ƙara shekara biyar bayan haihuwar Muzaffar kafin ta haifi aurarta Haneen.

Wannan kenan...

A ɓangaren Zaheera kuwa wanka tayi ta tsara kwalliya taci ado cikin ɗinkin doguwar rigar atamfa fitet wacce tsabar yanda ta matse jikinta da kyar take iya tafiya, kiching ta shiga ta samu mai aikin da tasa ta haɗa mata abinci ta gama haɗa komai kamar yanda ta buƙata. Don haka ɗauka kawai tayi ta nufi ɓangarensa zuciyata cike da ɗokin ganin kyakykyawar fuskarsa da tayi matuƙar kewa. Sai dai kuma deep down tsoron yanda zai karɓe ta ne ke kai-kawo cikin ranta don bata manta irin wulaƙancin ɗaya mata ba a wancan dawowar da yayi taje don masa sannu da zuwa...

# Oum Fatima