9
by @oumfatima33
💞💞💞💞💞💞💞💞
*AMATURRAHAMAN*
_*By*_
*_OUM FATIMA_*
_*(Hakimar D. A. W. A)*_
💞💞💞💞💞💞💞💞
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S📚ASSOCIATION*_
_*TEAM*_
_*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*_
*BOOK 1*
*PAGE 9*
_*بسم الله الر حمن الر حيم*_
...Cikin matuƙar farin ciki ta shigo ɗakin nasu "Umma albishirinku na samu aiki a wani gida can bayan layinmu za'a rinƙa biyana dubu talatin!." Nafisa ta faɗa bakinta har kunne tsabar farin ciki.
Ta san dai in sha Allah dubu talatin ɗin ba ƙaramin taimako zata mata ba, sosai Umma tasa albarka tayi mata nasiha akan yin aikinta da amana ba tare da ha'inciba. "A kullum ina horar daku kuji tsoron Allah a duk inda kuka tsinci kanku, ku sani ku marayu ne baku da wani gata sai na Allahn daya halicce ku. Don haka kuji tsoron Allah ku riƙe maraicinku, ku min alƙawarin cewar duk yanda rayuwa ta kai ga yi maku tsanani zaku riƙe mutuncin ku zaku guji haramun komai ƙanƙantarta. Idan kuka kiyaye dokokin Allah zai kula daku ya baku mafita a lokacin da baku tsammata ba!."
Shiru tayi tana ɗauke hawayen dake gangaro mata yayin da su Nafisa ke kuka har da shesh-sheƙa.
Washe gari Nafisa ta shirya tunda safe ita da Amaturrahaman suka fice bayan sun gyara gidansu Nafisa ta taimakawa Umma ta gyara jikinta sun bata koko da Nafisar ta aiki Amahh ta sayo masu suka sa a cikin su. Sai da ta raka Amaturrahaman har makarantar da ita tuni ta hakura da zuwa kafin ta wuce gidan Alhaji Tanimu ta kama aikinta.
Cikin farin ciki da karsashi Nafisa ta fara aikinta sai dai matsalar data fara fuskanta daga yaron gidan mai suna Gaddafi. Tantirin yaro ne marar kunya da gata ya lalata shi, Alhaji Tanimu da matarsa Hajiya Asabe irin mutanen nan ne masu shegen son yaransu da ba ruwansu da kwaɓar yaro duk abinda yayi dai-dai ne.
Tunda Gaddafi ya ɗora idonsa akan Nafisa ya ƙwallafa rai da ita ya kuma yi alƙawarin duk rintsi sai ya cika burinsa a kanta. Tun daga nan ya fara bibiyarta da zantukan rashin ɗa'a, abin ya fara isarta ta rasa yanda zata yi. Tana so ta sanar da Hajiya Asabe sai dai tana tsoron halinta da masifa.
A hankali aikin ya fara fita ranta sabo da tsoron abinda zai faru da ita matuƙar taci gaba da zuwa gidan nan, don ranar da ya rutsa ta a bayan gidan tana shanyar kayan su Muhsin da ta wanke. Bata ankara ba kawai sai jin mutum tayi a bayanta yana ƙoƙarin taɓa mata jiki, a firgice ta juyo suka yi ido huɗu da shi "Ya dai?, muje daga ciki mana!" Ya faɗa cike da iskanci yana ɗaga mata gira.
Hawaye Masu zafi suka riƙa zubo mata ta buɗe baki tace "Don Allah kayi haƙuri ka barni in tafi!."
Ta faɗa cikin tsananin kuka "Ina,!!! zance ne wannan, ai bazan taɓa barin wannan damar ta wuce ni ba." Ya faɗa yana ƙoƙarin damƙota Allah ya bata dama ta danƙara masa cizo a dansten hannunsa na dama. Azabar zafin daya ziyarci ƙwaƙwalwarsa ce tasa shi sakinta ba shiri.
Tana samu ta kuɓuce ta kwasa da gudu ko tsayawa ɗaukar hijabi batayi ba ta nufi gidansu cikin tsoro da ruɗanin abinda yake shirin faruwa da ita.
A zaure taci karo da Kawu Isa bata ko tsaya ba ta shige ciki a guje tana kuka "Ikon Allah wato ita ma wannan layin Ubanta zata bi wato karuwanci, ai dama barewa ba zata yi gudu ɗanta yayi rarrafe ba." Shine abinda ya faɗa ya ƙara gaba abinda ba tare da damuwa da bincikar abin da ya faru ba a matsayin sa na Uba a gareta.
Bata tsaya ko ina ba sai a gaban Ummanta ta ƙara fashewa da kukan daya daga hankalin Umman da kuma Amaturrahaman da dawowarta kenan daga makaranta tana cire Uniform ɗin ta "Ya Nafi menene?, waye ya dake ki?." Amaturrahaman ta tambaya hankalinta na tashi ganin irin kukan da Yayarta ke yi.
"Me ya faru Nafisa?, kiyi mana bayani." Umma ta faɗa tana yunƙurawa ta tashi zaune tana dafa kafaɗar ƴarta. Sai da tayi kuka sosai kafin ta share fuskarta ta shiga yiwa Umma bayanin abin da take fuskanta daga wurin Gaddafi ɗan masu gidan da take aikin da suke rufawa kansu asiri da abinda ake biyan ta da kuma abincin da ake bata tana taho musu da shi.
Wani irin tsoro da fargaba ne suka dira a zuciyar Ummah lokaci guda, kar dai ace ayace zata tabbata akan ƴa'ƴanta, kar dai ace mummunan abinda Mukhtar ya aikata ne zai shafi ƴ'aƴanta da basu ji basu gani ba "Innalillahi wa inna ilaihirraju'un!" Ta shiga maimaita wa hawaye na wanke ramammiyar fuskarta da babu mama ko kaɗan.
"Kin tabbata babu abinda yayi maki?". Umma ta tambaya cikin tsoron da ya gama kama zuciyarta.
Kai kawai ta iya gyaɗa mata. Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace "Ba zaki ƙara komawa gidan ba Nafisa, daga yau na soke aikin."
"Amma Umma idan ban koma ba ya zamu yi? Kina ganin ko lomar abinci babu mai bamu a gidan nan in ba Aunty Rakiya ba, itama kuma a ɓoye in ta samu dama. Wannan aikin yana rufa mana asiri Umma ko don a samu a tara kuɗin da za'a kai ki asibiti da kuma yiwa Amahh hidimar makaranta."
"Mutuncinki na gaba da duk abubuwan da kika lissafo Nafisa, bana ƙaunar abin da zai taɓa mituncinku koda bana raye, bakin da Allah ya tsaga ba zai hana shi abinda zai ci ba".
*****Tun daga ranar Umma ta hana Nafisa komawa gidan Alhaji Tanimu aiki, abinda ya rage a albashin wata biyu da aka biyata suke aje wani abu domin kai Umma asibiti su ta ɗauko taje ta haɗo kayan awara ta fara soyawa a ƙofar gida. Amaturrahaman taci gaba da zuwa makarantar boko da islamiyya, idan ta dawo ne take taimakawa Yayarta da hidimar awara.
A wannan lokacin sosai ƴammatanci ya gama haɗa Nafisa gata kyakykyawa ba laifi duk da ana cewa Amaturrahaman ta fita kyau amma ita a lokacin ƙaramar yarinya ce duka shekarunta goma sha ɗaya, yayinda Nafisa take da sha bakwai sabo da shekara shida ta bata.
Sosai samari suka taso ta a gaba danma tana kame kanta bata basu fuska amma basu rabu da ita ba, rabi daga cikin samarin ba tsakani da Allah suke sonta ba sai don su lalata mata rayuwa. Daga cikin su akwai Sule ɗan Kawai Isa dake farautar Nafisar, abin yana matuƙar damunsu musamman ma Umman su, duk sanda tayi yunƙurin kare martabarta sai a riƙa kiranta da munanan kalamai ana cewa duk ƙaryace ai itama abinda take yi kenan, waye bai san Babansu mazinaci bane ƙarewa ma cutar ƙanjamau ce ta kashe shi take shirin kashe Uwarsu, shine zata riƙa nunawa mutane ita ta Allah ce.
Wannan na ɗaya daga cikin dalilin da yasa Umma hanata siyar awarar a waje sabo da nan ake taruwa su sule da ƴan iskan abokansa suna ci mata mutunci, idan ta kai ƙaransa wurin kyawun nata sai dai ya korota da zagi yana faɗin "Ai ba sharri aka maki ba, wannan gantalin da kike da sunan aiki idan ba iskancin ba me kuke yi, aikin banza aikin wofi."
Wannan halin ƙuncin da rashin mafita da suke fuskanta yasa jikin Umma ƙara rikicewa, damuwa tabi tayiwa Nafisa da Amaturrahaman yawa wanda abin ya kai har Amaturrahaman ta fahimci akan me ake zagin su kullum har abin yayi tasiri a zuciyarta taji ta tsani Mahaifinsu. Ƙwaƙwalwarta ta gama yanke mata cewar duk abinda ke faruwa da rayuwarsu shi ya janyo musu, laifukan daya shuka ne ya bari suke girbar sakamakon.
Sabo da a halin da ake ciki yanzu har ita ba'a bari ba hari ake kawo mata, don haka ta saka tsananin son yin karatu a ranta. So take ta zama lauya ta hukunta duka waɗanda suka cutar dasu ciki har da dangin Mahaifinsu da suka wulaƙantar da rayuwarsu suka bada ƙofar da ko wane kare da doki ke ƙokarin taka mutuncinsu sabo da an san basu da wanda zai tsaya musu.
Ba ƙaramin kuka suka ci ba a ranar da Sule ya tare Nafisa a zaure ya kusa keta mutuncinta Allah yasa Amaturrahaman ta dawo daga aiken da Nafisa tayi mata ta sayo masu gari da sigar su sha taga n shi ya tareta a lungu suna ta kokowa tana son ƙwatar kanta.
Ƙara ta ƙwalla wanda ya jawo hankalin mutane aka cika wurin. Ana tambayar abinda ya faru sai sule ya juya maganar yace ai ita ta tareshi take neman shi sabo da ya bata kuɗi. Ba wani bincike Kawu Isa ya yarda ya ƙara kammama maganar akan ba yau ta fara neman sulen ba, tana ji tana gani aka ƙulla mata sharri kowa ya tafi yana zaginta da Allah wadai da ɗabi'ar ta.
Sosai abin ya taɓa su gaba ɗaya har Amaturrahaman ya kuma tsaya a zuciyarta.
Tun daga nan fita ma ta fara gagarar su don suna fita za'a fara nuna su ana zaginsu da cewar sun yi gadon Ubanne shima da yayi iskancin ƙanjamau ce ta kashe shi kuma ita zata ƙarasa Uwar.
Haka suka ci gaba da rayuwa cikin azaba da tsananin ƙunci ba cin yau bare na gobe, babu sutura kirki ga umma ta koma kamar wata aljana tsabar rama. Bayan ƙanjamau hawan jini da ciwon zuciya sun kamata ga azababbiyar Ulcer da babu wanda bai da ita a cikinsu.
Amma sabo da naci na Amaturrahaman haka taci gaba da zuwa makaranta har ta gama firamare ta shiga Sakandire ta gwamnati, da jacen Uniform na Nafisa da ta daina zuwa kwata-kwata tun da rayuwa ta fara musu tsanani. Haka suka ci gaba da lallaɓa rayuwar sun zama tamkar mujiyoyi a cikin gidan Ubansu tamkar ba dangin su ba haka suke hantarar su, ƙarfi da yaji Nafisa ta zama baiwar su take musu bauta don su samu abin sakawa a bakin su.
Sosai girma ya fara zowa Amaturrahaman don yanzu tana da shekara sha huɗu ne, tana J S S 3 a makarantar secondary wacce ta kawo matsayin hakan da ƙyar da suɗin goshi, ba Uniform ɗin kirki babu littattafan kirki wasu sai ƴan ajinsu sun canza sabi suke bata tsofin musamman ƙawarta ɗaya da take iya sakewa suke mua'amala mai suna Hasina.
Ya zuwa wannan lokacin Ummansu ta zama abin tsoro domin kuwa ko tashi zaune bata iya yi sai sun kwantar sai sun tayar, maganar kyan kamanni ma babu ita don ba wanda zai ganta yanzu yayi tunanin waccen Asiyar ce ta shekarun baya. Wannan dalilin ne yasa Amaturrahaman ke nacin karatu sabo da a ganinta ita ce hanya ƙwaya ɗaya da zata ɗaga darajar ta ta bata damar da zata taimaki mahaifiyarta da kuma ƴar'uwarta da ta sadaukar da komai nata don ganin ta cika wannan burin, shi yasa bata taɓa saka nuƙatarta a gaba sai ta saka tasu farko koda a cikin addu'arta ne.
Sai dai Hausawa suka ce wai kana naka Allah na nasa, nashin kuma shine dai-dai....
#Oum Fatima