SO da CIWO

24

by @maidambu41

❤️‍🩹SO da CIWO❤️‍🩹*

®©Ramlat A Manga

Mai_Dambu

500₦

*** Abdulrahman Ramlat Manga Opay

Shaida biya a turo ta wannan numbers din.

***

Or

***

Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76

Follow this link to join my WhatsApp group: ***

Dakata hajia💃💃💃💃💃 kin Dade kina Neman inda Zaki sai amintattun jaka, da takalma, sarkoki,masu kyau da quality cikin farashi Mai sauki❓

Ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,wannan gidan na RUMIEE UNIQUE BAG'S GALLARY na budeshi ne saboda na Baku damar siyan jaka,da takalma na Yara Dana manya masu kyau da quality da Kuma saukin kudi cikin aminci daga wajena.masu siyan daya da masu sari duk Muna mataba daku

Muna Kano Muna Tura kaya kowanne state da makotan Nigeria cikin yardar Allah,

Uhmm rigi-rigi ko kun san kayanmu sun iso like bags irin wanda Maamah take amfani da shi, Veils, Shoe's, more and more suna nan dasu...... Let go ❤️‍🩹💃🏻🐾

Paid book

24

Tunda muka isa Makka bayan mun bar madina, ban yarda na sake barci ba. Ina gaban dakin Ka'aba ina gayawa Allah abinda yake damuna. Bana ce na saka rai da zan yi escape daga auren sharahbil ba, amma nayi imani da wanda ya ajiye wanan dakin ya kuma umarci Annabi Ibrahim ya gina tare da Annabi Isma'il kamar yadda Alqur'ani ya fada, a kullum muna fita da wata mata wacce itama na lura kamar tana da nata matsalar da damuwar, yau ma ina fitowa ta fito murmushi tayi min, na maida mata cike da kunya don matar tana da mutunci duk da bata min magana ko wani abu ya haɗa mu da ita ba, kullum muka fita sai ta tsaya ta nima mana ruwa ko ta saya mana tea ko coffee. Duk da wanann abin da take ban tab'a karba sai da na ce mata nagode, yau ma dabino ta saya mana ta mika min. "Bana son abin da kike yi maza amsa, ina da Yaran nima ba zan iya cutar da ke ba, Ya sunanki?" Murmushi nayi na amsa ina me Bismillah na fara ci, "Rahmah ana kirana Maamah." "Allah sarki suna mai dadi, ni kuma sunana Hawwa'u amma ana kirana da Boɗɗo ko Innar Ayuba, zuwa na nan na uku kenan. Na zo aikin Hajji mijin Bintu Yayarki ta biya min, na biyu Umara nazo Yayanki Ibrahim ya biya min, yanxu na zo Umaran nan Ayubana ya biya min shima Yayanki ne, akwai Baban Yayanki shi yana raye ne ko yana mace ban tab'a cire da shi ba, amma ance ya mutu tun yana shekaru shida a duniya a wata gobara a garin Kaduna inda aka kai shi Almajiranci wannan shine labarin Innar Ayuba! Yawwa na rasa Babanku wato babansu Ayuba!" Sai na tsaya kallonta yadda take ta cewa ku. Murmushi tayi tana faɗin. "Ina ganinki kullum sai naga kin dace da Ayubana, sannan naga kina fita kullum da dare, nasan kina fita don Allah ya baki miji na gari ne ta fada bayan mun isa harami!" A hankali na kalli dabinon da bani, na saka a bakina na ce mata. "Ina addu'a ne Allah ya kawo min mafita Innarmu, sannan ina yiwa Mahaifiyata da tarasu addu'a wata biyu da suka wuce." Nayi shiru a hankali na ji idanuna ya cika da kwalla, ban san yadda aka yi na shiga bata labarin halin da nake ciki ba, murmushi tayi tana share kwallanta tare da jan hancinta. "Jinin Yaya bai tafi a banza ba, Allah yana sane ya bar kowa yayi yadda yake so, zan taya ki addu'a in sha Allah kudirinta da alkhairin da ta nima a rayuwarki Allah zai cika mata, muna gaban mai dukka ne ya baki ya bamu ya hanaki ya hanamu, ki kwantar da hankalinki, matukar kika ga kin bar nan Allah bai cika miki burinki da na Yaya ba, akwai abin da ya zab'a miki ne, amma muna addu'ar ya zab'a miki abin da yafi alkhairi." Haka muka yi ya hira kafin muka yi alola muka shiga ibada har aka yi sallah asuba, sannan muka dawo gida a hanya muka hadu da Mama da Addah Jiddah. "Maamah wai fitar nan na meye haka ba zaki kwanta ki huta ba." Murmushi Mama tayi tana faɗin. "Ba zata yi barci ba, bayan tazo wurin mai abin." Uwani da take gefen Addah Jiddah ta ce mata. "Uwar dakina kin min addu'a Allah ya bani miji na gari!" Anan ne Innar Ayuba ta ce mana. "Ku kyale Daughter ta huta, alamar uwa ta gari kenan tana addu'a domin gobenta da abinda zata samu, nima take yi don haka barci ba nata ba ne, ina kwananku zan shige Daughter Ubangiji ya tashe mu lafiya!" "Amin Ya Allah, Innarmu!" Na fada ina kallonta har ta wuce dakinta, mu kuma muka wuce namu dakin, tunda na shiga na kwanta ina jin kamar zazzaɓi. Saboda sanyin da ake yi a garin Makkah. Mama ce ta shigo dakin tana kallon yadda nake jan bargo ina kokarin rufe kaina. "Baki jin dadi ne?" "Eh amma ba wani can ba!" Na bada amsa, zama yayi tana me ɗaukar remote din ac dakin ta rage sanyin. "Ina ta istahara wannan shine karo na uku da nayi amma ina jin kamar babu auren nan!" Kallonta nayi da son jin karin bayani. " Tunda aka ce Alhaji yayi miki magana akan auren nan Yaya Abidah tayi istahara amma ta ce min bata ji wani abu ba, sai nauyin da ta ji zuciyarta tayi, nima har sau uku ina yi. Allah bai taɓa sanya min haka ba sai yau da nayi, ina ranar da yan fashi suka shigo mana, Yaya Abidah ta gaya min cewa tayi istahara sau uku a lokuta mabanbanta, sai dai bata tab'a karo da wani abu da ya danganci auren ko a barci ko a wanj abu ba. Sai dai zuciyarta tana nauyi. Ta ce amma tayi mafarkin jiya kin zo gaban harami tare da wata mata kina da addu'a itama tayi yi. Kin rike hannun matar zuwa ga wani kofa, wanda yake rufe da kwado babba, anyi anyi kofar ya bude bai bude ba, sai da kika tab'a kofar ya buɗe. Ta gaya min haka ne ranar da zata rasu ta ce bayan kin dawo anyi yaki a cikin gida jini na ta zuba, sannan nime ki an rasa. Maamah jikina ya yi sanyi da ta bada wannan labarin. Mahaifiyarki tana da kusanci da Ubangiji, a yadda ya fada min kayan jikin matan farare ne, matar da na ganki da ita hijab dinta fari ne. Ta ce mace mai yawan fara'a. Maamah ki cigaba da addu'a ina taya ki Allah ya tabbatar da alkhairi shi muke bara." "Batun auren fa?" "Ta ce min ta ga gawar bata san na waye ba ne, amma ta ganki kina burgima da buge buge bayan auren, bata sani ba ko auren ne babu alkhairi kike ta wannan burgima da buge buge, amma tana nima miki rahamar Allah da sassaucinsa!"

Ajiyar zuciya na sauke ina faɗin. "Yaya ta rasu amma wani abu kamar a mafarki ya faru." Na fada a hankali ina lumshe idanuna, domin na fahimci aurena da sharahbil babu makawa tunda ko labarin da Mama ta bani bata ce min auren ba sai yiwu ba, ta gaya min abinda ta ji a bakin Yaya ne, sannan ita wancan matar da mika hadu Innar Ayuba, tana da kirki idan ita ce wacce na budewa kofa a mafarkin Yaya tow me haka yake nufi, lumshe idanun nayi barci yayi gaba da ni. Ban san fitar Mama ba, har wurin karfe sha biyu ina barci koda zasu tafi massalaci basu tashe ni ba Uwani ta ce mata. "A tashe ta?" "A'a bakonta ne zai zo take zazzaɓi." "Ayya yarinyar kirki ruwan zafi ya kamata ta sha yau bakiɗaya!" Inji Addah Jiddah, haka kuwa ya faru suka tafi. Karfe daya na ji kamar nayi fitsari ina jin haka na ji wayata tana ringing, dubawa nayi aka rubuta the day. Tashi nayi da kyar bayana da cikina ya rike. A daddafe na shiga ban daki nayi wanka na fito na gyara gadon na kwanta. "Allah sarki Yaya!" Na fada a hankali ina jin kwalla yana cika a idanuna, buga kofar aka yi na tashi a hankali na nufi bakin Kofar a daddafe da cikina, bude kofar nayi ina kallonta. "Innarmu!" "Ki da lafiya ne?" Gyada kai nayi ta shigo dakin,.ganin yadda nake rike da marata ta ce min. "Date dinki ko?" Kunya ta sa na lumshe idanuna, a hankali ta nufi wurin wayar dakin ta dauka kiran number office din MD na hotel din tayi ya gaya mishi akwai mara lafiya ko za a zo da likita. Can kuwa sai gasu yadda take Larabci ya bani mamaki, amma yadda nake fama da matsanancin ciwo ban iya magana ba, suna zuwa da likita mace ce, haka yasa aka duba ni aka min allura da yar karamar roban ruwa saboda rashin karfin jiki, gyara dakin aka kuma aka wanke zanin gadon da na fara wankewa, barci me nauyi yayi gaba da ni. Innar Ayuba tana dakin har la'asar su Mama suka dawo, gaisawa suka yi tana basu labarin yadda ta same ni ina ciwon. Murmushi Mama tayi tana faɗin. "Mun gode sosai, Allah ya saka da alkhairi."

"Kai haba nima Uwa ce ina da yaran ko min kashin alkhairi kayiwa dan.wani Allah sai ya mai da kan naka, shi yasa nake kwadayin wannan gwagwabar ladan domin ko bayan raina Allah zai duba bayana." Kallon Innar Ayuba Mama tayi, tana murmushi a hankali ta juya mata fulatanci, ai kuwa Innar Ayuba ta cabe, ba dai ga Fulani sun sauya harshe ba, abu daya kenan aka yi ana karawa, anan Mama take bata labarin rasuwar Yaya Innar Ayuba bata nuna mata ta sani ba ta mata ta'aziya sannan ta ce mata. "Yarinyar nan tana fama da kaɗaici da kewa na wanda ya rasa Uwa, ki nutsu ki fahimta ki janyota a jiki sosai yadda zaki rufe mata gurbin da ya ta rasa. Kiyi hakuri Hassanah Rahmatullah tana kewa shi yasa bata barci kamar yadda kuke korafin tana fita rashin tayi ne yasa take fitan, ko godewa Allah da yasa tana da sanin ya kamata, sannan kana ganinta kaga ga wacce ta samu tarbiyya, ban sani ko akwai baikon wani akanta domin samun ta a matsayin suruka abin alfahari ne, don mace ta gari na hnago a wurin." Shiru Mama tayi cikin jin wani irin abu da ya dinga motsi a zuciyarta bata san yadda akayi ba ta bude bakinta ta gayawa Innar Ayuba silar zuwan su Umara ba, murmushi yake Innar Ayuba tayi tana faɗin. "Nayi takaici tunda ta amince, Allah yasa haka shine mafi alkhairi, idan kuma tana cikin a rabon zuri'ata Ubangiji yayi sanadin alkhairin da zai hada mu, Hajiya Yarki ce Rahmah ki ji a ranki kece kika haife ta, ki dauka Yaya rikonta kika bata, zata yiwa Yaya addu'a ne don ita ce mahaifiyarta ke zata kaunata har zuwa lokacin da Allah ya daura mata. Uwa take nima nayi mamaki da kika ce bata cika shekaru sha bakwai ba ta iya jure wannan kamar ba kome ba, nasan Yaya Abidah ta bar miki ita ne amma bata tsammaci zaki gaza fahimtar yarki ba, kiyi nazarin abinda na faɗa,ina magana ne as a teacher and Mother wacce ta damu da iyalinta, a Koyarwamu an koya mana sanin ilimin dan Adam, kin ja baya da Rahmah kamata yayi ki rungume ta kamar yadda ba zata kara waiwayen kome ba, idan baki tallafi rayuwarta ba haka zai kashe ta har ranar da zata mutu, domin kaɗaici da damuwa yana haifar da babban ciwon damuwa wnada yake kai yara aikata abinda ba shine ba, Allah ya sawwaka ba fata ake ba, auren nan kun san bata so? Idan ta gudu ta bazama duniya fa? Idan tayi yunkuri kashe kanta fa? Kin ga akan bar halak don kunya amma ba wasa da rayuwar mace karama irin Rahmah da ace bayan rasuwar Abidah kin jajjurce tow ba zaki tab'a jin kamar kin gaza rikon amanar da Abidah ta baki ba. Ni mijina na rasa na rungume Yarana, kin ga tafin hannuna. Waɗannan sune tabon da na same su ta hanyar gina gobe Yarana. Alhamdulillahi babbar Yata tana auren wani Yaron da kusan nice komensa, na biyun yana aiki da CBN, na ukun kwallon kafa yake shi ya biya min zuwa nan, sanadin Yaran nan da na gina su nake nan cike da alfahari, ki fahimci wani abu Allah yana son mu da jin kai yasa ya bamu aron rayuwa, ki yarda da cewa Allah ya barki ne domin ki zama madadin Abidah, ban sani ba ko akwai wani abu a ranki amma na hadaki da Allah kada ki cutar da wani.daga cikin macen da tai gwagwarmaya domin Yaranki, idan kuma babu cutarwa ki tashi kada ki damu da maganar kowa ki cika alƙawarin da ta baki a lokacin da jininta yake zuba daga zuciyarta, ni zan tafi ga wannan a canza ayi mata abinda duk wata uwa take yiwa yarta nawa gudummawar ce idan kuma tana cikin rabon zuri'ata Allah ya kawo sanadin da zan yi alfahari da samunta a matsayin Surukata kuma Y'ata ki gaya mata bayan Yayanta da Mama tana da Innar Maamah daga yau na cire ayuba domin na samu auta. Na gode da yarda da tayi da ni da tayi!" Ta ajiye dala duhu biyu da dari biyar sannan ta fita ta bar Mama tana kuka, ita kanta ta san ta gaza rike Maamah ta rasa mene mata ya sa ta kasa rike Maamah Jiddah da Uwani suna tsaye haka Hamma Umar da Salim da suka zo masaukin suna jin kome, murmushi Innar Ayuba tayi ya ce mishi. "Nuna mata soyayya shi ne abin da zaku yi, ku cika alƙawarin mahaifiyarku da wasiyyarta, Maamah ita ce rayuwarku idan wani abu ya same ta, dukkanku zaku sha wahala!". murmushi tayi tana juyawa ta kalle ta, "Da inda hali da babu abinda zai saka na barta a wannan yanayin, Ina sonta tun daga zuciyata har rayuwata. Ku shafa min kanta Umar kai ne Umar ko?" Ta nuna Salim nuna mata Umar yayi da yake kuka. "Kada ka damu ka koma baya tace ko irin fadar da kuke kun daina wannan fadar zai dawo da ita nutsuwarta. Ki karfafa mata gwiwa ku tsaya kamar Yadda Jarumar uwa ta tsaya mata ku tayata yaƙi, amma sai kun tsaya da gaske domin zaku ga abinda baku tab'a gani ba. Kowa yasan ita ce zuciyarku sannan idan za a yaki Yaya dole sai da Maamah ita ce rayuwarku." Ta juya tana kallon Mama murmushi tai ta ce mata. "Kin zata Yaya ta tafi ita aka zo kashewa ko? Tow idan yadda kika bani labarin yakin naki ne, ba na Yaya Abidah ba. Kuma ki shirya daga yau har zuwa ranar da Mamaki zai zagaye ki, Yaya ita ce garkuwarku a zuriar Datti, idan aka tab'a wani zata tsaya idan aka tab'a ta zata yi hakuri Hassanah kiyi lissafi duk wanda ya kashe Yaya Abidah ba ita ba ce abar harinsa kece maganar Maamah ya shigo ne ya zama riga malam masallaci. Abinda tayi iya nata kuma Yaranta suna cikin kariyar Allah, kece zaki tashi. " Murmushi Innar Ayuba tayi sannan ta ce musu. "Shekaru kusan talatin da takwas nayi ina girban kishin Uwar mijina, ba ni ba ce abin harin ni wanda ake hari na zauna da shi har ya mutu babu abinda aka fasa, makiyinka yana tare da kai yana kwana a gefenka, har Yarona na fari aka kashe saboda kishin Kakarshi da Ubanshi so i learn more about hatred kiyi kokarin kare Yaranki." Daga haka ta bar dakin tana musu fatan Alkhairi da zaman lafiya a zuriarsu...