Haramtacciyar Alaƙa

🌸6

by @khanoum03

💝🌸HARAMTACCIYAR ALAƘA🌸💝


*Written by Fateemah MG


               ....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ

ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)


🌸Page 6


Salma na ƙarasawa ɗakinsa ta tarar dashi a zaune yana danna laptop, tana ajiye tray ɗin akan table ta koma gefe ta tsaya tace, "Yaya kana buƙatar wani abu kuma?" Lumshe idanu yyi kafin ya ɗago su yace, "Aah, zaki iya tafiya!" Bata ji daɗin maganarsa ba amma haka ta yi hanyar fita daga ɗakin simi simi kanta a ƙasa. Tana ficewa ya sauke ajiyar zuciya yau kwata kwata baya jin daɗi wanda ya rasa meya sa hakan ko dan su ɓata da Noorie ne shi kansa bae sani ba, gyara zama yyi ya fara cin abincin a hankali ba dan yana jin daɗin abincin ba.


Ɗakin Salma Aunty ta nufa ba tare da tayi knocking ba, tna shiga ta tarar da Salma a zaune rungume da pillow tana kuka, zama gefenta Aunty tayi tace, "Au kina nan kina kukan asara ne?" A hankali ta ɗago fuskarta tace, "Toh Aunty ya kike so nayi? Ko kaɗan Irfaan baya kallo na a matsayin mace sae kace wata gardi haka yake kallona fah..." wani kuka ta fara cigaba da yi, hannunta Aunty ta kamo tace, "Ke namiji fah kamar yaro haka yake sae yanda kika bi dashi, kuma da kike zancen gardi ba ke kike yin abu kamar gardi ba!" Da sauri Salma ta ɗago kai ta kalli Aunty da ta miƙe tsaye tana gwada mata tafiya, "ki kalli yanda nayi man, haka zaki rinƙa tafiya kina tafe kina karairaya haba man sae kace ba mace ba? Ɗan shagwaɓar nan duk ki rinƙa yi masa ko baki ga yadda yafi son shagwaɓaɓɓiyar autarsu ba duk cikin ƙannin nasa? Kema haka zaki riƙa yi masa ko zamu samu ya aure ki" dawowa tayi ta zauna gefen Salma tace, "Ya rage ga naki wallahi, kin dae ga yadda nake jin daɗi a gidan nan idan baki samu kinyi wuff da Irfaan ba ke kika sani, ni kin ga tafiyata!" Tana faɗin haka ta miƙe ta fice daga ɗakin ta bar Salma a tsaye sae aikin safa da marwa take.

A ɓangaren Zaynoora ma kasa bacci tayi har saeda dare ya raba sosai ta samu baccin ya ɗauke ta, da safe kuwa tana idar da sallar Asubha ta miƙe ta wuce kitchen, dan tasan yau Yaaya Irfaan zae wuce ABU da sassafe, tea ta haɗa masa ta saka a flask sae kuma golden yam da tayi masa, ta shirya komai a tray tayi hanyar part ɗinsa, knocking ta fara yi kafin ta tura kai ta shiga cikin ɗakin, har ya gama shiryawa tsab yaji knocking kafin aka shigo ɗakin, fitowa yyi cikin navy blue suit ta tayi mugun karɓarsa yyi kyau sosai ga gashin nan yasha gyara sae sheƙi yake yi, riƙe yyi da jakar laptop ɗinsa kawai sae wayarsa a hannu, yana fitowa ya tarar da Noor a durƙushe a ƙasa cikin wani zumbulelen hijabi mae ruwan ƙasa, ta jin fitowarsa tace, "Yaaya ina kwana!" Ko kallon inda take baeyi saema gyara cufflinks ɗinsa da ya fara yi, a dake kamar ba zae amsa ba yace, "Lafiya!" Yana gamawa ya saka wayarsa cikin aljihu kafin ya ɗago kansa yyi hanyar fita, sosai taji wani ƙulu a zuciyarta saboda tasan yaga trayn data shigo dashi, murya can ƙasa tace, "Yaaya breakfast na kawo maka!" Lumshe idanunsa yyi ya ko sake saka kai zae fice, kamar zatayi kuka muryarta ya fito tana cewa, "Yaaya dan Allah kayi breakfast tun Subh fa na tashi nake haɗa maka!" Jin muryarta kamar zatayi kuka yasa ya juyo ya zuba mata slender eyes ɗinsa. Ba dan yyi niyya ba kawai ya ɗauki ƙaramin flask ɗin yyi hanyar fita, daidai fitowarsu Salma ta fito daga part ɗinsu nan taga Zaynoora a bayan Irfaan tana binsa kamar bindi har waje, tsaye tayi bakin main door tace, "Yaaya Allah Ya kiyaye!" Bae kalleta ba yace, "Ameen!" Reverse yyi wa haɗaɗɗiyar motarsa ya fice daga gidan bayan buɗe masa gate ɗin gidan. Tsaye Salma tayi tana ƙunƙunin takaici, Zaynoora na dawowa ta shige part ɗinsa ta ɗauko trayn ta wuce dinning table, a zaune ta tarar da Aysha ta shirya har ta fito kwana biyun nan ana basu zafi dan tun kafin bakwai na safe take barin gidan, tana ƙarasowa da trayn Aunty ta fito daga part ɗin, lokacin breakfast bae yi ba amma duk sun fiffito, fuska a sake Zaynoora tace, "Aunty Ina kwana!" Banza Aunty tayi da ita tace, "Meye cikin kular hannunki?!" Aysha dake zaune dama tea take haɗawa tana sauri ta gama ta wuce school, murya a ƙasa Zaynoora tace, "Doya da kwai ne!" Taɓe baki Salma tayi nan Aunty tace, "Tih miƙo mun kular!" Ƙiris dama Aysha take jira aikuwa ta miƙe tsaye tace, "Ban gane ba a miƙo miki kular toh dan me?" Fusgar kular tayi daga hannun Zaynoora ta jawo plate ta juye a ciki dama abincin mutum ɗaya ne. Ɓata rai Aunty tayi tace, "Tunda mae baƙin hali ta kwace sae ki shiga kitchen ki soyo mini wanda zanci!" Kai a ƙasa Aysha tace, "Ke kika san wanda kike kira mae baƙin hali kuma Zaynoora aiki zan saka ta wallahi bbu girkin da zatayi!" Juyawa Aysha tayi ta kalli Zaynoora tace, "Ke ki wuce kije ki gyara mun kayana cikin wardrobe, kina jina kuma wallahi kar ki kuskura ki fita idan baki gama ba!" Kwalla ne suka cika idanun Aunty nan tace, "Aysha ni fa matar baban kice amma shine kike yi min rashin kunya?" Ɗago kai Aysha tayi tace, "Toh ina baban nawa yake yanzu ba an karshi ba toh me ake yi mana a gida?" Hawaye ne suka ɓalle idanun Aunty nan ta miƙe ta bar dinning table ɗin cikin kuka, Salma da ranta ya ɓaci ne tace, "Aysha ya ishe ki haka, wanne kalan rai..." bata ƙarasa Aysha ta nuna mata hannu alamun ta dakata kafin ta ɗago kai tace, "Ke ya isheki, da wacce ta auri ubana nake ba da ke ba karan kaɗa miya ba. Karki ɓata mun rai a gidan ubana kinzo kina cin arziki amma hakan bae ishe ki ba?Ki tsaya a matsayinki" tana faɗin haka ta duƙa plate ɗin doyan da cup ɗin tea ɗinta ta ɗauka ta wuce ɗaki tareda yiwa Zaynoora alamar ta biyo ta, ko kaɗan Zaynoora bata ji daɗin abunda Ya Aysha tayi ba amma ya zata yi tunda itace ƙarama, suna isa ɗakin ta samu guri ta zauna dan tasan Ya Aysha bata barin kayanta a hargitse bare tace wai da gaske zata yi gyara, suna zama Zaynoora tace, "Ya Aysha amma kinyi musu tsauri da yawa!" Wani kallon banza Aysha ta watsawa Zaynoora tace, "Shashasha toh ki zauna wallahi sae ta mayar dake ƴar aiki a gidan ubanki ai na san halinta sarai dan baki san iskanci da tayi wa Umma lokacin da take da rai bane!" Shiru Noor tayi nan Aysha ta tura mata plate ɗin dan dama ba dan tana son ci bane ta karɓa kawai dan neman magana ne. Tana yafa veil ɗin abayarta tace, "Saura ki kuskura ki fita daga ɗakin nan, ki kunna ipad ɗina akwai sweet a drawern can!" Ta faɗa tana nuna mata side drawer, murmushi Zaynoora tayi tace, "Ya sae dawo, take care!" Tana faɗin haka Aysha tasa kai ta fice daga ɗakin, tana fita waje ta shige mota driver ya wuce da ita school.


Zaune Salma tayi a gefen Aunty dake ta huci kamar zakanya, ajiyar zuciya ta sauke kafin tace, "Lallai yarinyar nan bata da kunya ko kaɗan kuma wallahi sae nayi maganinta!" Salma take tsaye tace, "Aunty ta ya?" Cize bakinta tayi tace, "Da yayanta zan haɗata, sae nasa ya tsane ta tunda har ta isa tazo tana sa'insa dani zata gane shaye ruwa ne wallahi!" Dariya Salma tayi tace, "Aunty taya zaki haɗa jini ɗaya faɗa kuma kiyi tunanin har zae tsane ta?" Dariya Aunty tayi tace, "Ke dae ki tsaya ki gani ki ɗauki darasi cikin kissar mace!" Dariya Salma tayi tace, "Dama zata yi aure be da mun huta!" Taɓe baki Aunty tayi tace, "wannan ƴar iskar yarinyar ce zatayi aure? Ai baza tayi ba ko dan ta hana mu jin daɗin zaman gidan nan!" Dariya Salma tayi kafin ta kalli agogo dake manne da bangon ɗakin tace, "Bara na samo mana abunda zamu ci nikam yunwa nake ji!" Dariya Aunty tayi tace, "ƴar bantan uba kar ki samu ki aure Irfaan ki cigaba da jin daɗi ko zaki iya komawa gida ne?" Dariya Salma tayi tana sauke kanta ƙasa tace, "Taya zan koma na riƙa cin tuwan dawa? Ai bazan iya ba yanzu kam jiba yanda fata ta tayi haske tayi kyau!" Dariya suka kwashe dashi su biyu har suna tafawa kafin Salma ta fice daga ɗakin zuwa kitchen nan Aunty ta kwanta akan gadonta tana nazarin yadda zata ɓullowa lamarin Aysha.


A ɓangaren Irfaan kuwa tunda yyi parking motarsa ya fito ƴan mata suka fara juyowa fah, sosai aka kafeshi da idanu saboda ba ƙarya gayen ya haɗu sosai ga wani ƙamshi da yake fitarwa idan yana tafiya, bae yi nisa ba lecturers biyu da dean suka iso dan su tareshi, suna gama gaisawa suka wuce hall room dashi yana binsu a baya, students ɗin already sun halarta suna zaune suna jiran shigowar baban baƙonsu dan sun daɗe suna jin labarinsa gurin ex students amma yau zasu haɗu da prof da kansu. Dean da kansa yyi introducing Irfaan gurin students ɗin kafin suka samu guri a can ƙarshe suka zauna dan ganin performance ɗinsa da na students ɗinsu. Tsaye Irfaan yyi a gaban students ɗin da basu ƙarasa ɗari ba, agogonsa ya duba yaga takwas har ta ɗan gota, laptop ɗinsa ya buɗe yyi connecting da projector, glasses ɗinsa ya ciro na karatu ya maƙalata a idanunsa kafin ya fara, "I'm Professor Irfaan Umar Abdallah as your dean mentioned earlier!" Ya fara kenan wata ta shigo cikin ajin tana kame kame cikin jin kunya amma haɗaɗɗiya ce bbu ƙarya gata kyakkyawa sosai, gaba ɗaya ta ɗauke hankalinsu amma bayan ta zauna sae kowa ya natsu, orientation ya fara musu akan importance ɗin Masters ga masu buƙatar cigaba da karatu, yana gamawa ya fara yi masu wani special lectures da baya cikin syllabus ɗinsu.


Zaune Asmah tayi a office ɗin Dr Haulat kamar zatayi kuka tace, "Haulat yau Irfaan bae shigo ba!" Cikin rashin fahimta Haulat tace, "Irfaan kuma, ohhh Director wai? Eh bae shigo ba kinsan ya je ABU Zaria yau!" Shiru Asmah tayi kafin tace, "Haulat Abba ya saka min rana da cousin ɗina!" Shiru Haulat tayi kafin ta tashi ta zagayo ta zauna a gefenta tace, "Ina taya ki murna Asmah gara kiyi settling wallahi dan ni banga amfanin bibiyar Director da kike yi ba bayan kinsan baya da interest akan ki!" Ɓata rai Asmah tayi tace, "Haulat wallahi ina son Dr Irfaan sosai, Haulat ko ganinsa kawai nayi baki san kalan farinciki da nake ji ba!" Ajiyar zuciya Haulat ta sauke tace, "Asmah wallahi ba son Dr kike yi ba, ki yarda kawai tunda har ni na faɗa miki a matsayina na ƙawarki tun yarinta!" Haɗe gira Asmah tayi tace, "Mey kike nufi Haulat, idan ba sonsa nake ba toh me nake?" Dariya Haulat tayi tace, "Asmah sha'awar Dr kike yi ba sonshi kike yi ba, nina lura da hakan!" Shiru Asmah tayi kafin tace, "Ko ma meye dae!" Matsowa Haulat ta sake yi tace, "Asmah ki ɗauki shawarata ki rabu da Dr kinsan baya sonki, kiyi haƙuri ki kai mutuncinki gidan Faisal ko mai banza zae ga mutuncin ki!" Shiru Haulat tayi kafin ta miƙe ta fice daga office ɗin Haulat fuuuuu, ajiyar zuciya Haulat ta sauke tana jin tausayin Asmah ɗin dan ta zubar da kanta duk saboda Director amma shi baya gani saboda bata gabanshi, ƙasƙanci ne ace mace mae ji da kai kamar Asmah tazo tana aiki a asibiti a matsayin nurse amma ko ma meye dae ita Asmah ta jawa kanta saboda Babanta zae iya samar mata wani aiki mae kyau da mutunci.


Comment🌸🤝🏻