🌸10
by @khanoum03
💝🌸HARAMTACCIYAR ALAƘA🌸💝
*Written by Fateemah MG
....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ
ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)
🌸Page 10
Shiru Wahidah tayi kafin tayi farr da manyan idanunta tace, "Koma meye? Yaya Irfaan na gida kuwa?" Taɓe baki Zaynoora tayi kafin tace, "Me zaki yi masa?" Juya idanu Wahidah tayi kafin tace, "Kar kice mun kishi kike yi da yayanki! Oho koma meye dae umma ce bata da lafiya!" Ɗauke kai Zaynoora tayi bata sake cewa komai ba. Ana tashi daga islamiya Raudah da Zaynoora suka sa kai suka fita daga islamiyar su biyu a tare, tana ɗaga kai taci karo da Ya Anwar a jingine da motarsa yana jiran fitowarta, tsaye sauran ƴan matan suka yi cikinsu har da Wahidah da ta kafe Anwar da manyan idanunta, ganin dae Zaynoora yake kallo yasa tayi tsaki tayi tafiyarta. Wani mummunar faɗuwar gaba Noor ta samu ganin Ya Anwar a tsaye kusa da Islamiyarsu, wani shu'umin kallo yake binta dashi wanda yasa jikinta ya fara rawa nan Raudah tace, "Waye shi?" Da rawar baki Zaynoora tace, "Abokin Ya Irfaan ne kuma wai sona yake yi!" Ganin tayi tsaye ta kasa motsi yasa ya tako har ya ƙarasa gurinta yace, "NOOR!" Murmushin dole tayi tace, "Ya aka yi kasan islamiyarmu?" Murmushi yyi tareda maida kallonsa ga Raudah yace, "Barka ƙawar Noor, nace dae kina kular mun da ita!" Ita kuma Raudah sae abun yyi mata citta tayi murmushi tace, "Yawwa barka, bari na baku guri!" Tana faɗan haka ta ɗan matsa can gefe tana duba musu ko magulmata na kusa dan ita kanta ta san halin Yayan Zaynoora, hannunta ya kama suka ɗan tsaya a wani guri da ke a ɗan keɓe amma still ta ƙi ɗaga kai ta kalleshi, murmushi yyi yace, "Noor ki kalleni!" Da kyar ta ɗago kanta ta zuba masa kyawawan idanunta dake cike da kunya da kawaici, murmushi yyi kafin ya lumshe idanunsa ya sake kafeta da su, hannunta ya kamo yace, "Na kasa samun natsuwa tunda na barki!" Saurin fusge hannunta tayi amma ya sake kamowa yace, "Mu tafi gidan tare toh!" Saurin ɗaga kanta tayi tace, "Aah, Yaya Irfaan yana gida ko ka manta abunda yyi maka?" Murmushi yyi sannan ya fara murza hannunta cikin wani salo mae kashe jiki yace, "I'll endure everything da Irfaan zaeyi mun saboda ke ko da kuwa kashe ni zaeyi!" Sosai ta sake tsorata dan ko ranar ma taji tsoro da tausayin Anwar ɗin, turo baki tayi tace, "Aah gaskiya, kasan Yaaya yana da fushi sosai!" Murmushi yyi ganin yanda take son zuba shagwaɓar nan yyi saurin cewa, "Toh ki bani phone numbern ki ko na bi ki har gidan yyi mun duk abunda zae yi!" Turo baki Noor tayi tace, "Ni dae gaskiya aah! Kuma ni wayata ta lalace!" Hannunta ya sake ya nufi inda yyi parking motarsa ya ɗauko wani ƙaramin jaka ya kawo mata, ɓata rai tayi tace, "Meye wannan ɗin? Ni bana so!" Ɓata rai Anwar yyi yace, "Ni ba Yayanki bane? Idan baki karɓa ba sae na bi ki gida!" Ganin ya fara yi mata barazana ne yasa ta turo baki kafin ta saka hannu ta karɓa, murmushi yyi yace, "Good girl, now look at me Noor!" Sae da ta lumshe idanu kafin ta ɗaga kai ta kalleshi bata ankara ba kuwa taji ya manne lips ɗinsu gurin ɗaya, quick kiss ya manna mata kafin ya ɗauke kansa yyi fuska kamar bashi ba, razana tayi gaba ɗaya har ta rasa mae zata yi tunani ko ta aikata, shi dae gashi ya fuske kamar bashi ba, cikin tunaninta na sakarci ta fasa yi masa magana ta bari wai idan ya sake zata ce masa bata so. Hannunsa ya zura cikin aljihu ya ciro wayoyinsa guda biyu, ɗaya babbar waya ce ɗayar kuma ƙarama ce mae buttons, miƙa mata wayar yyi dan dama bae cika amfani da ita ba kuma Irfaan ne kawai ya sanshi da layin dake ciki yanzu kuma sun ɓata so baya tunanin zae neme shi.
Turo baki zata yi yyi saurin ce mata, "I'll kiss you idan kika yi mun musu!" Murmushi yyi ganin ta natsu sosai haka yake son mace mae tsoro da jin magana, ganin za'a kira sallar Magrib yasa yace, "I'll call you later, okay!" Waving ɗinta yyi kafin ya juya yyi saurin wucewa ya barta a tsaye, buɗe jakar hannunta tayi ta kalli chocolates ne a ciki da yawa sosai nan ta fara murmushi ita kaɗai, jin kiran sallar Magrib yasa tayi saurin dawowa cikin hankalinta nan tunaninta duk ya watse, ganin Raudah tayi tana tunkarota nan ta kama hannunta suka fara rusa sauri kamar an koro su, basu ƙarasa gida ba Zaynoora tace, "Dan Allah ki tafi da wannan jakan gidanku sae ki kawo mun gobe, ki ɗauki abunda kike so a ciki!" Tana faɗan haka kuwa har da gudu ta haɗa daya ke bbu saiti sosai ta shige cikin gida tana haki, tana hanyar shiga parlour tayi karo da Yaaya Irfaan, wani mugun bugawa ƙirjinta yyi nan tayi saurin ɗauke numfashinta tana jiran abunda zae ce dan fuskarsa a haɗe take sosai, giran sama a haɗe dana sama yace, "Ah ina kika tsaya ai kun tashi tun ɗazu!" Sosa ƙeyarta tayi tace, "Yaaya damaa... kaga sha...sharan class Mu'allim ya saka mu... shiyasa!" Kallon rashin yarda yyi mata inda tayi saurin sauke idanunta daga nashi tana jin kamar abu na shiga idanunta daga nashi. Tana shiga can cikin parlour har zata wuce part ɗinsu muryar Aunty ya fito tana faɗin, "Sae yanzu kika ga daman dawowa daga gantalin naki?" Turo baki Zaynoora tayi tace, "Ni bbu gantalin da nake zuwa!" Tana faɗin haka ta wuce part ɗinsu abunta tana jin gajiya na ɗibarta, taɓe baki Aunty tayi tace, "Wato itama yarinyar nan ta fetsare kamar Ayshatu kenan, ai shknn!" Tana faɗin haka ta shige cikin kitchen ta ɗaura musu abunda zasu ci tunda yaran gidan duk zama ƴan duniya.
Zaynoora na isa ɗaki ta murza wa ƙofar key, hijab ɗinta ta zare kafin ta wuce gaban mirror ta zauna, hannu ta kai ta fara shafan lips ɗinta tana sake jin ɗumin lips ɗin Ya Anwar a kan nata, bata yi expecting haka first kiss ɗinta zae kasance ba hakan yasa ta yi ta murmushi kamar sakarya, miƙewa tayi ta ciro ƙaramar wayar daya bata, a vibration ta saka kafin ta wuce toilet ta ɗauro alwala. Zama tayi ta zauna abunta tana jin kunya na rufe ta, sam har ga Allah baza ta iya haɗa ido da Ya Irfaan ba dan gani take kamar zae gane cewar tayi kiss da Ya Anwar a yau hakan yasa tayi zamanta a ɗaki da niyyar sae sun gama cin abinci zata ɗibo nata can dare.
Can around tara na dare Irfaan yyi zauna yana ɗan danna wayarsa, a hankali Salma ta turo ƙofar ɗakin bayan tayi knocking, murmushi tayi a gajiye tace, "Yaaya Irfaan!" Gyara zamansa yyi ya bata guri ta zauna mae kyau, tana zama ta sauke wata ajiyar zuciya, lumshe idanunsa yyi kafin yace, "Me yake damunki?" Runtse idanunta tayi cikin kissa kafin ta buɗesu akanshi tace, "Yunwa nake ji!" Zaynoora na zaune a ɗakinta da plate ɗin jollof spaghetti zata ci kenan taji ringing ɗin tsohuwar wayarta daya lalace, taɓe baki tayi ta miƙe ta duba callern, ga wayar dae zata kawo kuma kira zae shigo amma babu halin picking saboda screen ɗin wayarne ya tashi aiki gaba ɗaya, da sauri ta fice daga ɗakin nata ta wuce part ɗin Yaya Irfaan, tana ƙarasawa ta tarar da Ya Irfaan a zaune a gefen Salma yana tambayarta wani abu can masu dae, turɓune fuska Noor tayi ganin bae ma san ta shigo ba saboda kasancewar Salma a ɗakin, sosai Noor taji takaicin ganinsu tare wanda ita ma yaso ya ɗaure mata kai amma bata damu bade ai yayanta ne sae da amincewarta ya kamata ya zaɓi mata saboda duk na baya basu yi mata ba, gyaran murya tayi kafin tace, "Yaaya gani!" Kamar baza tayi maganar ba amma dae dole tayi, ko kallan Noor bae yi ba yace, "Abinci zaki kawo mun!" Taɓe baki Noor tayi kafin ta juya ta wuce kitchen dan zartar da umarninsa, a hanyarta ta dawowa da tray a hannu ta tarar da Aunty tana shiga part ɗin Irfaan ɗin, shiga Noor tayi ta ajiye abincin akan tray idanu Yaaya ya zuba mata nan dae ta daure ta zuba mata abincin dan ta riga tasan na waye. Wani wayyo wayyo Salma ta fara tana wani juyi da murƙususu kamar macijiya, ƙarasowa Aunty tayi tace, "Likita ya jikin nata?" Kai ya ɗaga ya kalle Aunty kafin yace, "Bazan ce komai ba yanzu gaskiya sae bayan taci abinci sae na duba ta!" Shi dae yyi specialising a surgery amma yasan sauran fields ɗin though ba kamar Cardiology daya karanta ba, ajiyar zuciya Aunty ta sauke kafin tace, "Tun rana take abu ɗaya wallahi kuma tana shan wahala!"
Shiru yyi mata bae bayar da amsa ba, magana Irfaan ya fara yiwa Salma a murya mae taushi, "Ki tashi kici abinci kinji shine zaki warke!" Wani ajiyar zuciya ta sauke mae ƙarfi kafin tace, "Ni bazan iya ci ba!" Ɗauke kansa yyi kafin yace, "Tashi ki zauna toh!" Nan ma shiru tayi masa sae murƙususu da ta cigaba akan gujerarsa dan tuni ya koma ƙasa a tsugune, muryar Aysha ce ta shigo cikin parlourn cike da wahalar school tace, "Meye kowa ya tare a part ɗin Yaya?" Kallon banza Aunty ta watsa mata tana tunanin yanzu ne lokacin daya kamata tayi wa Aysha nata tuggun, "Ke domin Allah sae yanzu kike dawowa gida kusan tara na dare? Kin kyautawa Yayanki kenan?" Cikin mamaki Aysha ke kallon Aunty dan ta ma rasa mae zata ce jin furucin Auntyn, shima Irfaan yana ji amma ya basar bae ce ƙala ba, cigaba Aunty tayi tace, "Ni kam idan gantali zaku riƙa yi da sunan karatu kawai ku bari sae ku cigaba idan kunyi aure, ai da auren kika yi da mun huta ma ai!" Ɓata rai Aysha tayi dan sae yanzu ta fahimci inda maganar ta dosa, murmushi tayi tace, "Aure ko? Wallahi bazan yi ba sae na dire Masters a gidan nan tunda gidan Ubana ne. Maganar aure ma ai bata taso ba tunda kema bazawara ce me kike yi bbu aure a gidan matacce bayan baki da gado?" Sosai maganar ta ƙona wa Aunty rai dan reshe ya juye da mujiya nan ta fara kukan ƙarya tace, "Ayshatu yanzu ni kike faɗawa maganarnan? Ko shi Irfaanu da yake ciyar da ni bae ce komai ba sae ke?" Hannu ta kai ta fara share hawayenta nan ran Irfaan ya ɓaci sosai ganin yadda Aunty da ta riƙe su kamar ƴaƴanta tana zubar da hawaye saboda Aysha, ɓata rai yyi ainun yace, "Ayshaaa, Ayshaaa..." ɓata rai Aysha tayi dan ta fice tun kafin ya fara kiranta tace, "Yaaya wallahi na gaji kuma yunwa nake ji!" Tana ficewa abunta Aunty tace, "Yanzu duk bautar da nake yi a gidan nan Ayshatu bata gani?"
Ajiyar zuciya Irfaan ya sauke yace, "Aunty kinsan na sani matuƙa, Allah ne kawai zai biya ki!" Yana faɗan haka Aunty ta juya ta fice tana cigaba da kukan ƙarya har ta shige part ɗinta, Zaynoora dae na tsaye abunta tana jin kamar shekara bakwai tayi a tsaye tsabar gajiya, Salman ma shiru tayi ta gama jin abunda ake faɗi sae da aka gama ta fara wayyo wayyo tana juyi, hankalin Irfaan ne ya koma kanta gaba ɗaya nan ya jawo Stethoscope ɗinsa ya maƙala a kunne, akan ƙirjinta ya kai zae saka nan Salma ta ɗan nutsu tace, "Ba nan bane zuciyar, kayi ƙasa kaɗan!" Saura ƙiris Noor ta kwashe da dariya saboda tsab Salma ke nuna bariki a halayyarta amma ita meye nata, kuma da alama ta manta cewar Surgery akan zuciya da abunda ya shafe ta ne ɓangaren Yaya Irfaan, kaɗa kai tayi zata tafi taji muryarsa yana cewa, "Waya ce ki tafi?" Tana juyowa ta zuba masa fararen idanunta kafin ta koma baya ta tsaya mae kyau, yana cikin jin heartbeat ɗin ne Salma tayi wani motsi tareda juyi, dama gaba ɗaya wata banzar rigar bacci da wando ne a jikinta wanda yasa motsin da tayi ya bayyanar da saman boobs ɗinta, Noor na tsaye tana kallon komai bakinta a taɓe kamar an manna mata laka, shi dae Irfaan lokaci ɗaya yaji hannayensa suna gogayya da soft boobs ɗin Salma, jin goosebumps sun fara ziyartar jikinsa ne yasa yyi saurin zare hannayensa daga kan ƙirjinta, da sauri ya ɗaga kansa ya zube idanunsa akan Zaynoora dake tsaye tana kallon komai, shi a yanzu ko da kowa zae ɓata shi bazae dame shi ba amma idan da za'a ce Noor ta fara yi masa wani kallo toh da sae ya fi kowa ɓakinciki kaf faɗin duniya.
* Let's keep the vote count please!🥹❤️
©️Fateemah MG