10
by @oumfatima33
💞💞💞💞💞💞💞💞
*AMATURRAHAMAN*
_*By*_
*_OUM FATIMA_*
_*(Hakimar D. A. W. A)*_
💞💞💞💞💞💞💞💞
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S📚ASSOCIATION*_
_*TEAM*_
_*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*_
*BOOK 1*
*PAGE 10*
_*بسم الله الر حمن الر حيم*_
Lokacin da ta dawo daga Makaranta da murnar result ɗinta da ta amso ita ce ta ɗaya kamar yanda ta saba zuwa. Sai dai tana tura ƙyauren ɓangarensu murnarta ta koma ciki sakamakon ihun kukan Ya Nafi tana ƙwala kiran sunan Umma "Don Allah Umma ki tashi kar ki mana haka don Allah Umma ki tashi!." Ta faɗa cikin ƙarajin kukan daya saka Amaturrahaman hanstilar da result da jakar Makararantar ta shige ɗakin da gudu.
"Ya Nafi me ya samu Umman." Ta faɗa a gigice tana tattaɓa jikin Umman. "Kinga Amahh bata motsi, maza ki kirawo Aunty Rakiya tazo ta duba min ita!." Ko jira ta gama rufe baki bata yi ba ta ruga da gudu ɓangaren Kawu Isma'il tana ƙwala kira sunan Aunty Rakiya.
Da sauri ta fito tana tambayar "Lafiya Amatu? Irin wannan kiran haka."
"Aunty Rakiya don Allah kizo kiga Ummanmu bata motsi!". Ta faɗa cikin tashin hankali, da sauri Aunty Rakiya tayi gaba Amahh tana Binta a baya suka nufi ɓangarensu. Zuwa tayi tana taɓa jikin Umman tana jujjuyata. "Ta mutu ko?!" Amaturrahaman ta tambaya cike da raunin da tsoron amsar da zata samu.
"Bata mutu ba amma tayi nisa, maza ki taro adai-daita sahu a kaita Asibiti. Ta faɗa tana kallon Nafisa. Da sauri ta sauke kan Umman dake saman cinyarta ta fita da gudu don taro abin hawan.
Duk wannan abin da ake Kawu Isa na ɓangarensa yana jin kukan yaran amma ya kasa leƙowa yaga abinda ke faruwa sabo tsabar yanda mutane suka watsar da zumunci basu ɗaukeshi a bakin komai ba, ace ɗan'uwanka da kuka haɗa Uba ɗaya ya mutu ya bar iyali amma ka kasa kulawa dasu sabo da wani banzan dalili marar ma'ana. Koda matarsa Mariya tayi masa magana cewar "Malam kamar fa kuka nake jiyowa daga ɓangaren Asiya, kaje ka duba ko ƙarasawa tayi."
Cewa yayi "Ba zai wuce hakan ba, ai daman ƙarshen alewa ƙasa itama tabi sawun wanda ya jajiɓo ya goga mata. Ai daman duk wanda ya sai rariya ya san zata yi zuba don haka babu inda zani in ta wuce Allah ya ji ƙanta."
Shiru tayi bata ƙara magana ba jikinta yana yin sanyi, koda basa shiri tun farko daman mazanensu suka hana su mua'amala da iyalin Mukhtar sabo da ƙiyayyar dake tsakaninsu amma ai mutuwa ba abin wasa bace.
A dai-daita sahu Nafisa ta taro ta shigo gidan da gudu suka kama Umman ita da Aunty Rakiya sabo da kaɗaice bata ƙyamarsu a gidan, yanda kasan wani gajiyayyen tsumma haka suka ɗauketa suka saka aka nufi Babban Asibitin dake garin Matazu Aunty Rakiya na basu haƙuri akan bazata iya binsu ba bata faɗawa mijinta ba zai yi faɗa.
Godiya suka yi mata suka nufi asibitin domin burinsu a duba musu Ummansu da ita kaɗai gare su a faɗin duniyar nan.
Suna isa aka amsheta aka shiga Emargency da ita suka bi baya ko mai adai-daitan basu sallama ba sai yafe musu yayi ganin halin da suke ciki.
Bayan bata taimakon gaugawa da akayi aka ɗan samu kanta likita ya fito yana tambayar wanɗan da suka kawo ta "mu muka kawota doctor". Cewar Nafisa tana share hawayenta.
"Ku kaɗai!" Ya tambaya cike da mamaki. "Eh Mamanmu ce mu kaɗai gareta, ita kaɗai garemu." Ta ƙarasa a sanyaye.
"Ok biyo ni." Ya faɗa yana yin gaba ya nufi Ofishinsa "Amah ki zauna anan ki jira ni." Ta faɗa tana miƙewa tabi bayan likitan. Faɗa ya shiga yi sosai akan barinta da aka yi a gida har ciwon yaci ya cinye ta haka, bayan HIV ga hawan jini da ciwon zuciya ga Ulcer duk ita kaɗai.
Ita dai ba abinda take yi daya wuce kuka sai da ya gaji da faɗan ya saurara. "Ina ƴan'uwanku suke? Idan Babanku ya rasu ai yana da ƴan'uwa, ko ita Maman taku ina nata ƴan'uwan da zasu barta cikin wannan halin?!" Ya ƙare maganar furiously.
"Basa sonmu ne, sun tsane mu, Mamanmu kuma marainiya ce bata da kowa don Allah likita ka taimake mu ka mata magani ta warke, idan muka rasata itama shiga uku zamu yi!". Ta faɗa cikin tsananin kuka da fargabar abinda zai faru danƙare a zuciyarta.
Shiru yayi na ƴan lokuta yana nazarinta kafin ya janyo takarda yayi rubutu ya bata yace "Kije pharmacy ki sayo waɗan nan yanzu." Karɓar takardar tayi tana juyawa gabanta na tsananta faɗuwa don sai a lokacin ta tuna Naira biyar basa maganinta, ashe ko mai adai-daitan daya kawo su basu biya shi ba. Ganin taƙi tashi sai juya takardar take ya sashi faɗin "Kije mana ki sayo idan ba so kike Mahaifiyartaku ta mutu ba."
Da sauri ta miƙe jin abinda yace ta nufi ƙofar fita jikinta na yin sanyi sabo da tunanin inda zata samu kuɗin da za'a buƙata. Wani shegen kallo ya bi bayanta da shi yana lumshe ido ƙasa-ƙasa ya furta "Bala'i! Yarinya ƙarama da ƙirar manya, wannan da alama zata bada abinda ake buƙata".
Pharmacy ɗin ta nufa ta miƙa takardar tace a duba mata kuɗin magungunan, manyan magungunan da allurai ne da kuma ƙarin ruwa ake so a fara treating ɗinta dasu kafin ayi mata gwaje-gwajen da suka dace.
"Naira dubu hamsin da bakwai da ɗari uku." Matar ta faɗa mata tana miƙa mata takardar data kasa amsa sabo da tashin hankalin jin kuɗin da ake magana ita da ko sisi bata da ita ba kuma ta ba wani ajiya ba. Wullo mata takardar da aka yi ne ya maido ta cikin hankalinta ta damƙeta ta juya, inda ta bar Amaturrahaman ta nufa. Anan ɗin ta sameta ƙofar ɗakin da aka kwantar da Ummansu.
Ya ake ciki Ya Nafi?." Amaturrahaman ta tambaya cikin ƙaguwa, bayanin halin da ake ciki tayi mata nan da nan itama hankalinta ya tashi. "Yanzu yaya zamu yi Yaya Nafi?". Ta tambaya tana amsar takardar.
"Kinga ki zauna wurin Umma ki kula da ita zanje in roƙi likitan ya mata maganin kafin in samo kuɗin." Kai kawai ta gyaɗa mata ta kasa cewa komai har ta wuce.
Ƙwan-ƙwasa Office ɗin likitan tayi aka bata izinin shiga, samun shi tayi yana haɗa kayansa zai wuce gida ta zube ƙasa tana cewa. "Don Allah doctor ka taimake mu kayi mata aikin, in sha Allah zanje in nemo kuɗin in kawo maka."
Kallo irin na ƙurullah ya bita dashi yana wani mici-mici da ido yace "Ai Kinga bani nake sayar da maganin ba bare na baki, sai dai idan kina so in baki kuɗin da zaki saya ɗin?" Ya ƙare maganar ta sigar tambaya yana ɗage mata gira.
Da sauri tace "Eh don Allah ka taimake mu likita."
"Ok to amma fa kema sai kin biya da wani abun." Cikin rashin fahimta take duban shi "Eh in sha Allah zan nemo maka kuɗinka in kawo maka."
Wata shegiyar dariya ya saki yana nunata "ashe dai yairnya ce ke to bari in fito maki a mutum, ba kuɗi zaki biyani ba haɗin kai kawai zaki bani muji daɗinmu." Ya ƙare maganar yana wani kashe mata ido cike da iskanci. "Innalillahi wa inna ilaihirraju'un!" ta shiga maimaitawa saboda gano abinda yake nufi. Tsoro da mamakin halin mutane ya mamayeta. Shikenan su basu da wani abun daya wuce su wulaƙanta mutuncinsu, kuka ta fashe da shi tana ja da baya har taje bakin ƙofa ta juya ta murɗa ta fice da gudu tana jin yanda yake mata wata shaƙiyiyar dariya yana nunata.
Kai tsaye bakin gate ta nufa cikin rashin mafita, dole dole ne ta samo waɗannan kuɗaɗen sabo da bazata bari su rasa Mahaifiyar da ita kaɗai garesu a wannan duniyar da babu abinda mutanen cikinta suka sani sai son zuciya. Hannu tasa ta ɗauke hawayen daya silalo daga kwarmin idonta.
Sanin cewar bata da ko sisi yasa bata tari abin hawaba ta miƙi hanya kai tsaye ta nufi gidansu don zuwa ta jaraba roƙon Kawunnanta ko zasu ji ƙanta su taimaka musu.
********Amaturrahaman kuwa jin kamar kakari na fitowa daga ɗakin da Ummansu ke kwance yasata miƙewa mijinta a sanyaye ta murɗa ƙofar ta shiga, da sauri ta ƙarasa gaban gadon jin yanda Umman take jan numfashi da ƙyar. Hannunta da babu tsoka ko kaɗan sai ƙashi lulluɓe da fata ta riƙe tana faɗin "Sannu Umma, Allah ya baki lafiya!." Ta ƙare tana share hawayen tsananin tausayin halin da Mahaifiyarsu ke ciki na tsananin azabar ciwo.
Tunawa da tayi Ance Abbansu ne ya sanyata a wannan halin yasa taji wani irin ɗaci yana tasowa tun daga ƙasan zuciyarta. Gaba ɗaya ji take ta tsani ko wane namiji sabo da kuɗin goro da zuciyarta tayi musu, a ganinta su ɗin azzalumai ne marasa tausayin Mace. Tunda ta fara wayo take jin yanda mutanen gudansu ke yamaɗiɗi da maganar abinda Babansu yayi da irin wahalar da Umma tasha sabo da shi sai abin ya zauna a zuciyarta ta riƙe shi.
Ga kuma irin rayuwar ƙunci da suke yi a gidan da irin yanda ƴan'uwan Mahaifinsu suka wofantar dasu suke fafutukar rayuwa sai abin ya samu matsuguni a zuciyarta ta riƙe su take ƙallonsu da abin. Hannunta da taji Umma ta riƙo ne ya maido ta hayyacinta.
Da ƙyar ta iya buɗe bakinta tace "Amah in..., ina ƴar'uwarki."
"Taje ta samo kuɗin da za'a sayo maki magani Umma."
"Ki..., ki kirawo min ita kinji ko Amah... Ina son yin magana daku, ba lallai na ƙara samun lokacin da zan iya buɗe baki nayi magana ba."
"Kiyi haƙiri Umma Ya Nafi ta tafi nemo kuɗi, in sha Allah zaki samu lafiya."
Hannu tasa ta share hawayen dake gangarowa saman fuskar Umma amma nata hawayen na sauka saman fuskar Umman na tsananin tausayin Mahaifiyarta da kuma tashin hankalin abin da zai iya faruwa. Ɗan motsa bakinta tayi alamar murmushi wanda kwata-kwata bai yi kama da murmushin ba tace "Allah ya muku albarka ya kare ku daga dukkan wani sharri, Allah ya kula da rayuwarku yasa ku rayu cikin aminci. Abinda zan jadda a gareku shine kuji tsoron Allah a duk inda kuke, ako wane irin hali kuka tsinci kanku ku tuna Allah yana tare daku, ku zamo masu gaskiya da amana, ina roƙon Allah ya baku ikon jure duk abinda zai fuskanto rayuwarku a lokacin da bana kusa daku. Ku haɗe kanku ku ƙaunaci junanku ako wane irin yanayi rayuwa zata kaiku. Kece ƙarama Amaturrahaman ki yiwa Yayarki biyayya nasan zata kula dake, tana da saurin fushi da rashin haƙuri, ke kuma kina da haƙuri da juriya sannan da zurfin tunani. Kiyi ƙoƙarin maidota saman hanya idan kika ga ta kauce, ita kaɗai gare ki itama ke kaɗai gare ta don haka ku kula da kanku Allah ya maku albarka na yafe maku duniya da lahira, a duk lokacin da kuka tuna da ni da Mahaifinku kuyi mana addu'a ku roƙa mana gafar Allah!". Ta ƙare maganar da ƙyar.
Tunda ta fara maganar Amaturrahaman ke wani irin kukan da yake fitowa daga can ƙasan zuciyarta yana galabaitar da ita, tsoro da fargaba nasihar Umma ke saka mata. Duk addu'ar da yazo bakinta ita take karantawa. Wani irin karkarwa da jikin Umma ya kama ne yasata fita da gudu ta kirawo likita tana ta sharɓar kuka.
Koda suka dawo Umman tayi laƙwas idanunta a kafe suna kallon sama, ƙarasawa likitan yayi ya dubata. Gani tayi yaja farin zani ya rufe ta ya juyo ya kafe ta da ido cike da tausayawa.....
Oum Fatima