FANSAR ƘAUNA

9

by @princessdija

*FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA D. AUTA*

*AREWABOOKS: Princessdija.*

*Follow the D. AUTA NOVELS channel on WhatsApp: ***

*Na buɗe channel fatar za ku dinga leƙawa akwai wasu littafaina da zan saki ta can.*

*LAMBA TA TARA.*

Jikinsa ya yi sanyi ƙalau, saboda zubar hawayen Hajiya Mummy ba ƙaramin tashin hankali ba ne a wurin sa. Musamman a ce kuma shi ne ya yi sanadin saka ta kukan da babu farinciki a cikin sa. Ya jima a wurin bai motsa ba, zuciyarsa ta shiga saƙa masa abubuwa da dama. Kafin ya nisa cikin ƙaƙƙarfan sauti ya miƙe cikin sanyin jiki da na gwiwa. A haka ya ja ƙafafuwansa zuwa cikin ɗakin nata fuskarsa a yamutse. Saboda hango ta a bakin gado tana goge ƙwalla da gefen ɗankwalinta.

"Kukanki tamkar ɗigar dalma ne a jikina. Me ya sa kike so Allah ya yi fushi da ni Hajiyarmu?"

Ya yi maganar cikin sanyin murya a lokacin da ya kai gwiwowinsa ƙasa a gabanta ya dafa cinyoyinta. Sharr hawaye suka shiga malala a kan fuskarsa ba tare da ya damu da sharewa ba. Kansa ta dafa ita ma hawayenta bai daina gangara a kan fuskarta ba, amma hakan bai hana ta yin magana cikin muryar kukan ba.

"Duk abin da ka ga na yi ina yin sa ne saboda farincikinka Jamal. Ba burina ba ne saka ka kunci ko damuwa kawai don ina son ka yi mini biyayya. Idan ka riƙe Amina a matsayin mata in sha Allahu za ka yi alfahari da hakan ko a bayan rain...."

"Daina ambaton mutuwa Hajiyarmu...ba yanzu ba, kuma ba za ki mutu ki bar mu ba sama da shekaru masu yawa. Sai kin ga 'ya'yana da jikoki kamar yadda kika ga Amna kina shirin ganin aurenta da yardar Allah."

Shiru ta yi masa, saboda kukan da ke taso mata a zuciya tana ƙoƙarin dannewa. Idonsa a kan fuskarta ya ce, "Ina son Nur Hajiyarmu, amma tun da ba kya son na je neman ta ba zan je ba, sai zuwa lokacin da kika amince mini."

Gefen hannunta ta saka ta goge fuskarta sannan shi ma ta goge masa nasa hawayen tana cewa,

"Ubangiji Ya yi maka albarka."

Daga haka ya miƙe yana yi mata sallama, bayan faɗar amin a bakinsa ya fice gidan. Zuciyarsa cike da ƙuncin da bai san ina zai saka kansa ya ji sanyi ba. Hakan ya saka shi shawagi a saman tituna idan ya sauka wannan ya koma kan wancan. Ba tare da ya san ina ya nufa ba saboda kansa ya ƙulle ta yadda bai san abin da ya dace ya yi ba a lokacin. A ƙarshe tsayuwa ya yi a gefen titin wani junction, ya ɗora kansa saman sitiyari yana kukan zucin da babu hawaye ko sauti.

'Me ya sa Hajiya za ta yi mini iyaka da Nur?'

Tambayar da ya yi wa kansa kenan wadda babu mai ba shi amsa. Ya jima a duƙen yana nazarin yadda zai shawo kan Hajiya ta fahimci abin da yake ji a cikin zuciyarsa. Saboda yana da tabbacin ko mutuwa ya yi ya dawo duniya ƙaunar Nur ba za ta bar zuciyarsa ta huta ba.

Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi, sannan ya zare wayarsa da ke caji ya shiga danna wa Adamu abokinsa kira. Bayan barkwancin da suka fara ya katse shi da tambayar inda zai same shi, ya yi masa kwatance sannan suka yi sallama. Iska ya furzar mai zafi a jikinsa kafin ya buga motar ya sake hawa kan titin.

Tafiya yake yi a hankali har ya isa Jami'ar Bayero University ya yi parking a harabar makarantar. Wuri ɗaya ya ƙura wa kallo, kamar mai nazari a kan mabambanta mutanen da ke ta shawagi. Amma ko kaɗan zuciyarsa ba ta wurin, asali ma ba ya hangen kowa face fuskar Nur da sautin maganganun Hajiya. Kiran da aka yi masa a waya ya saka shi kai kallonsa a kan fuskar wayar. Ganin wanda ya zo nema ne ya saka shi hanzarin ɗauka yana faɗin,

"Kai nake jira."

Daga haka bai sake cewa komai ba ya katse kiran, tare da bubbuga goshinsa yana hucin iska daga bakinsa. Buɗe motar Adamu ya yi yana 'yar dariya ya ce,

"Ango ka sha ƙamshi, na Amina ba da kanka a sare.."

Kallon da Jamal ya yi masa ya saka shi barin zancen ya koma murmushin yaƙe saboda fahimtar ba ya cikin yanayin mai daɗi. "Magana nake so mu yi mai muhimmanci, don haka ba na son abin da zai ƙara ɓata mini rai a banza, zancen ango ko wata Amina duka ka jingine shi a gefe mu yi abin da ya kawo ni."

"Ok tom, me ke tafe da kai?"

Adamu ya yi maganar cikin shiga nutsuwarsa. Nisawa Jamal ya fara yi mai ƙarfi sannan ya rungume hannuwansa a ƙirji ya ce, "Ina so na gama da Hajiya lafiya, amma ba zan iya yin abin da take so na yi ba. Wannan dalilin ya sa na taso ƙafa-ƙafa zuwa neman ka domin ka nemo mini mafita."

Kallonsa kawai Adamu ya yi ba tare da ya ce da shi komai ba, hakan ya bai wa Jamal damar sake cewa, "A wannan lokacin da muke ciki ko mace aka yi wa auren dole idan ba ta so za a ga ta'addanci ballantana ni ina namiji a nemi saka ni zama da wadda ba na so. Sannan idan ma aka jingine matsalar gefe raba ni da Nur tamkar saka almakashi ne a datse mini igiyar da nake shanya farincikina. Ba na jin zan iya yi wa Hajiya biyayya a kan rabuwa da son Nur ko da na yi haƙurin zama da Amina. Shin ya zan yi Hajiya ta gano illar abin da take ƙoƙarin yi ba abu ba ne mai sauƙi?"

Ya ƙare maganar cikin wata kalar murya mai ɗauke da yanayi mara daɗi tun a kan fuskarsa. "Hmmm!" Ajiyar zuciya Adamu ya yi kafin ya sake cewa,

"Babu abin da zan faɗa illa na ce ka yi haƙuri, sannan ka nemi zaɓin Ubangiji maji roƙon bawansa n.."

"Kalmar haƙuri ta yi kaɗan ta rarrashi zuciya Adamu. Don haka ban ji wannan ba, idan ba ka da wani abin faɗa sai haƙurin; to kawai mu bar zancen gabaɗaya."

Murmushi Adamu ya yi sannan ya yi magana cikin nutsuwar da ya gayyato ya yafa wa jikinsa. Saboda shi kansa ba ya jin daɗin halin damuwar da abokin nasa yake ciki. Hakan ya sa yake roƙon Hajiyar a kan ta sassauta ƙiyayyar da take yi wa Nur duk da ya sani abin da ta aikata dole ne a ji haushin ta.

"Lamarin iyaye ba abu ba ne na wasa, na sha sanar da kai Hajiya ba za ta so abin da zai ɓata maka rai da gayya ba. Saboda uwa ce, kuma irin wadda samun irin ta a wannan lokacin abu ne mai wahala. Ta ƙi aure tun tana da ƙurciya ta tsaya kai-da-fata a kanku duk don kada rayuwarku ta lalace. Me ya sa a yanzu ba za ka iya yi mata halacci ba? Ka ba ta dama a kan abin da take so sannan ka bi da addu'a in sha Allah komai zai warware cikin sauƙi. Don haka ka yi haƙuri ko ba ka son Amina ka karɓe ta a matsayin matarka, wataƙila alheri ce gare ka ba tare da ka sani ba."

"Idan na karɓi Amina na yi ya ya da Nur?"

"Lokaci zai sanar da kai makomarta a gaba. Don haka ka bar wa Allah komai shi zai yi maganin matsalolinka gabaɗaya."

Adamu ya yi maganar cikin yanayin da ke tabbatar da yin amanna da duk abin da yake hasashe. Jamal ya yi shiru tsawon mintuna kafin ya ce,

"Ni zan wuce, amma ban gama shawara a kan lamarin ba. Sannan zan yi cigiyar Nur ko a cikin gidana ba tare da na tsallake dokar Hajiya ba."

"Allah Ya zaɓa abin da ya fi alheri."

Adamu ya yi maganar tare da miƙa masa hannu suka yi musabaha kafin ya fice yana ƙara jaddada masa komai zai wuce idan an saka wa zuciya haƙuri. Kai-tsaye ya koma bakin aikinsa, kasancewarsa ɗaya daga cikin malaman Jami'ar kuma masu ruwa da tsaki a cikin makarantar.

Jamal ya ja motarsa zuwa wani masallaci ya yi sallar Asr, sannan ya zarce wani gidan abinci, sai da ya yi ƙat sannan ya riƙo abin da yake buƙata ya nufo gida yamma sakaliya. Zuciyarsa a cunkushe saboda ya kasa nutsuwar da zai yarda da tsarin Hajiya.

Misalin ƙarfe shida saura ya shiga gidansa, hannu kawai ya ɗaga wa maigadi sannan ya shige da ledodinsa a hannu. Minal ya gani tsaye a falon tana cika tana batsewa alamun jiran shigowarsa take yi. Amma ganin ta bai saka shi bi ta kanta ba ya nufi hanyar shigewa ɗakinsa.

"Malam, wayata za ka ba ni."

Ta yi maganar a sama saboda ta zo wuya a kan takaicin yadda ya saka ta zaman kaɗaici bayan zaman ƙuncin da take yi a gidansa. Bai nuna ya ji abin da ta faɗa ba, ballantana ya tsaya tankawa. Ɗakinsa ya shige da guntuwar sallama ya ajiye ledodin hannunsa ya faɗa toilet. A gurguje ya yi alwala ya fito babu shiri ya yi turus saboda ganin ta a tsakiyar ɗakin riƙe da ƙugu tana jijjigar jiki. Yi ya yi kamar bai gan ta ba ya zagaye ta yana mayar clips a hannun rigarsa.

"Ka ba ni wayar akwai abin da zan yi."

Ɗakin ya buɗe yana ƙoƙarin ficewa ba tare da ya bi ta kanta ba, caraf ta riƙe masa riga ta baya hawaye ya fara wanke mata fuska ta shiga rera kukan da ya saka shi daskarewa a wuri ɗaya, ya kasa gaba kuma ya kasa juyowa.

"Duk girman ƙiyayyar da kake yi mini ba ta isa ba sai ka ƙara saka ni a damuwa? Mene ne laifina bayan ba ni ce na maƙalaww wa kaina zama da kai ba? Me ya sa ba za ka tausaya mini ba, bayan ka sani ni ma ina da wanda nake so.."

Maganarta ta ƙarshe ba ƙaramin duka ta yi wa zuciyarsa ba. Hakan ya saka shi waigowa idonsa a kanta cike da wani irin sabon yanayin da ya shige shi a lokaci ɗaya ya yi magana cikin wata kalar murya.

"A cikin gidana kike zancen kina da wanda kike so?"

"E, kamar yadda kake son Nur haka ni ma nake son Aminu. Don haka babu adalci idan ka ce za ka hukunta ni a kan laifin da ni ma an yi mini, kuma zaman maneji nake yi da kai ba don ina sonka ba..."

A hargitse Jamal ya sake jifar ta da wani kallon mamaki ya yi magana cikin raunin zuciya ya ce, "Ba kya so na?"

"Babu ranar da zan iya son ka Jamal. Saboda ba ka cikin kalar mazan da na tsara wa kaina rayuwar aure da su."

Murmushin takaici ya yi, kafin ya kalli kansa ya koma ƙare mata kallo sama da ƙasa ya ce, "Mace irin ki ba isa ta faɗar ba ta so na b.... don haka ko da wasa kika sake yi mini zancen wani a cikin gidana; wallahi sai na nuna miki ba iri na ake yi wa iskanci b.."

"Gaskiyar kake so na daina faɗa ko son Aminu zan cire a zuciyata a cikin gidan nak..."

Karaf ta ji saukar yatsunsa biyar a gefen fuskarta, yana huci ya shiga nuna ta da hannu idonsa a zare ya fara magana a birkice sannan cikin ɗaga muryar da ta ƙara saka ta jin tsoron sa ta fashe da wani sabon kuka.

"Ba ki isa ki saka ni gaba kina faɗar abin da kika ga dama ba, kuma ba ki da matsayin da za ki yi mini abin da kike so! Ba Aminu ba ko sunan anta na ji kin sake faɗa a cikin gidana sai na zare harshenki na datsa shi gida biyu!"

Yana ƙare maganar ya kai mata harbi da ƙafa kafin ya buɗe ƙofar ya fice daga ɗakin zuciyarsa tana tafasa. Tsabar takaicin rainin da take son kawo masa bayan ɗaurin talalar da Hajiya ta yi wa rayuwarsa a kanta. A hargitse ya yi sallar ya dawo gida bayan sallar Isha. Saboda har lokacin bai daina jin zafin kushen da ta yi masa a kan wani ƙaton banza ba. Kukanta da ya tarbe sa bayan dawowarsa ya ƙara dagula masa lissafi. Hakan ya saka shi zama falo ya yi kwanciyarsa ganin har lokacin tana cikin ɗakin nasa ba ta fito ba. Tv ya kunna aka yi dace MBC Action suna wrestling ya miƙa hankalinsa a kan kallon, amma zuciyarsa ba ta daina jin zogin abin da Minal ta yi masa ba. A gefe ɗaya kuma ba ya jin daɗin sauraron kukan da take yi, don gabaɗaya ta lalata masa kuzarin jiki.

Tsawon awa ɗaya tana kukan kafin ta rarrashi kanta ta miƙe a ƙufule ta fito daga ɗakin. Kai-tsaye kitchen ta nufa saboda ta gama kaiwa maƙura a kan halin damuwar da take ciki. Wuƙa ta zaro sabuwa fil ta fito jikinta yana tsuma ta isa kansa ta tsaya. Idonsa a kanta Tv bai ɗauke kansa daga kallon ba, duk da ya ga wuƙar a hannunta amna hakan bai saka shi razana ko ya ji tsoron abin da take ƙoƙarin aikatawa ba. Haushin ko-in-kular da ya yi hakan ya ƙara rura wutar tashin hankalin da take ciki.

Hannunsa ta damƙa tare da cusa masa wuƙar a ciki hawaye yana zarya a kan fuskarta ta ce,

"Ba don na san hukuncin wanda ya kashe kansa ba, da tuni na kashe kaina na huta da zaman ƙaddarar da nake yi. Don haka ka taimake ni ka kashe ni kawai ka huta da gani na, zan fi farinciki da hakan fiye da abubuwan da kake yi min..."

Ta durƙushe a gabansa tana wani irin gunjin kuka tamkar wadda aka lakaɗawa mugun duka. Ido ya bi ta da shi cikin wani yanayi mara misali, saboda jikinsa ya yi sanyi ƙalau kuma kukanta yana taɓa masa zuciya. Zumbur ya miƙe ganin tana ƙoƙarin karya masa zuciya ta ƙarfi, da wuƙar a hannunsa ya nufi kitchen ya kwashe duka sauran wuƙaƙen da ke nan. Zuciyarsa cike da tsoron tsautsayi ya sa ta kashe kanta ta jiƙa masa aiki ya koma masa sabo, don komai ya faɗa ba zai goge kansa daga zargi ba. Saboda ko Hajiya ba za ta yarda a kan ba shi ne ya kashe ta ba.

Ɗakinsa ya shige ya datse ƙofa, sannan ya ɓoye wuƙaƙen sannan ya zauna yana furzar da iska daga bakinsa. Ya shiga tunanin yadda zai rabu da Minal cikin sauƙi ba tare da ya cutar da rayuwarta ba. Ya miƙe cikin sanyin jiki ya ɗauko wayarta a inda ya ajiye ta, tun bayan ɗaukar ta saboda binciken da yake so ya fara yi domin ya tabbatar akwai hannunta a cikin guduwar Nur ko babu.

Kai-tsaye ya shiga binciken saƙonnin da ke cikin wayar, tun daga kan waɗanda take turawa har waɗanda ake turo mata. Jikinsa ya yi sanyi ƙalau ƙirjinsa ya hau bugawa, saboda cin karo da saƙon da ta tura wa Gwaggo salame a kan ta zo zai kashe ta. Hamdala ya yi ga Ubangiji a kan dabarar kwashe wuƙaƙen da ya yi, amma hakan bai saka shi nutsuwar zuciya ba, sai da ya ajiye wayar ya fito ya same ta a inda ya bar ta har lokacin ba ta daina kukan ba.

Tsaye ya yi a kanta hannuwansa zube cikin aljihu ya yi gyaran murya sannan ya ce,

"Ki tashi ki zauna za mu yi magana."

Ga link;

Follow this link to join my WhatsApp group: ***

Masarauta group ne ga masu tambayar a saka su group da masu buƙata su ma su yi joining.

D. AUTA CE ✍️