HAWAYEN ZARGI

9-10

by @fadilalamido

HAWAYEN ZARGI

By

Fadila Lamido

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Page 8-9

Fashewa Habibullah ya yi da dariya a lakacin da ya ji ta duru kanshi cikin sauri ya ture ganganjikin katuwar yar baby kasa tare da rungumo Habiba zuwa jikin shi, ita ko kakarin lekawa take domin tabbatarwa idonta, ganin tabbas yar baby ce ta fashe da kuka tare da cigaba da kaiwa Habibullah duka, karewa yake cikin kyalkyalewa da dariya daker ya samu ya kwantar da ita sannan ya haye kanta ya sakar mata nauyin shi tare da cewa "Wai! azaba, Allah ya huci zuciyar ki, wasa ne."

Tureshi take iya karfinta tare da fadin "Innalillahi wa Inna ilahir raju'un, na shiga uku"

"A'a ki nutsu mana meye haka ki ke yi? haba mana tsaya kiji, daga wasa sai ki birkice min."

"Ni bana so Habibullah karka sake min irin wannan wasan kasan me na ji kuwa?"

"Nasan me ake ji Habibty, na bari bazan kara ba kinji ko, yau kin karya tarihi bantajin kin kirani Habibullah gatsai ba, ba Yaya ba Daddy Khalil bare kuma ya Habibi."

"Ai kaine ka tayar min da hankali na."

"Yi hakuri tashi ki zauna in gaya miki abin da yasa nai miki haka."

"Tashi ta yi ta zauna tana binsa da kallon cikin kosawa."

Yana kallon tsakiyan idonta ya ce "Ai na ce miki in dai zaki hau motar wani bani ba ki dinga zama a baya amma kinki jin magata."

"Abban Khalil Sadam din kanina ne fa."

"Ke fa kin faye son girma, kanin ki ko kodai yayan ki? duka duka shekaran ki nawa ne yanzu Habibty, kina da son girma tsiya fa."

"Amma dai ai dan uwanane ko?"

"Shikenan dai mubar maganar"

Tagumi Habiba ta yi tare da cewa "In Allah ya yadda zan kikaye"

"Sannan karki kara saka gyale in dai ba tare zamu fitaba."

Komawa Habiba ta yi ta kwanta sannan tace "To ni ma bana son irin wannan wasan indai ba kana son zuciyata ta buga ba."

"Shikenan zan kiyaye."

Dukan kirjin shi ta yi tare da cewa "Kuma nima sai na rama."

" Zaki rame dai" Habibullah ya fada yana dariya, suna rungume da juna suka yi bacci Habiba kuwa kusan kwana ta yi tana sauke ajiyan zuciya, tun da tazo kullum manne suke da juna har suka cike sati dayan suka dawo, gida su suka sauka, misalin biyar na yamma Habibullah ya fito dauko yara, yana makarantar aka tashe su cike da kewan yaran ya sakko ya rungume su suna tafe a hanya yaga kiran Abba dauka yayi cikin nayin kidima Abba yace "Ka dawo ne Yaya?"

"Eh, na dawo na manta ban kiraka bane."

"To nazo daukan su Najma ne aka ce baban su ya zo."

" Eh ka koma gida abin ka ina nan zuwa gidan."

Acan bangaren Abba kuwa bayan ya sauke wayar tsaki yaja tare da cewa "Ji wani abu dan Allah" Goshin sa ya daka sannan ya sake jan tsaki cikin takaici.

Khalil da Najam kuwa yau bakin su yaki rufuwa tsalle tsalle suke yayin da Habibullah ke taya su.

Bayan sati daya da dawan su Habiba ta shirya rama abin da Habibullah ya yi mata ranar da taje Abuja, fuskarta dauke da murmushi ta kira Sadam bayan ya dauka tace Sadam dan kira ya Habibi kace mishi nakira ka nace bazan sami zuwa ba banda lafiya.

Yar karamar dariya yayi sannan yace "Me hakan ke nufi?"

"Ina ruwan ka? Ka ji min dan rainin wayau" Habiba ta fada cikin kosawa

"Da ruwana mana in taje ta dawo min fa? wannan jarabben mijin naki ni banson fada fa."

"Kudai kuke kallon sa a haka, kirashi kaji nasan in kace mai hakan zai kirani ne."

"To ke ki kirashi mana in haka ne."

"Sadam so nake ya dawo gida kashe wayar zan yi ko ya kirani bazai samu ba."

Lallai, ni gaskiya ba ruwana yau fa daya kai su Khalil makaranta saida yazo gidan Daddy saboda ya kwana da fushin su Aminu ya rutsasu basu zata ba yaita hargagi sannan ya fito ya wuce."

Cike da Mamaki Habiba tace "Me suka yi?"

"Ni ina nasani wata kilama ba wani laifi bane kawai duk yabi ya takura mana shi lokacin shi waye ya takura mishi."

"Ka tambaye shi mana, yanzu dai zaka kira shi ko bazaka kira ba?"

"Bazan kira ba..."

Katse wayar ta yi cikin jan tsaki sannan ta danna wata number tasa a kunne zuwa can tace "Abba."

"Na'am Anty Habiba"

"Dan kira Ya Habibi kace mishi na kira ka na ce banda lafiya bazan iya zuwa gidan ba."

"Toh a nawa? Anty kun yi zaki zo ne"

"Eh, nawa zan baka to."

"20k zaki bani."

Dariya Habiba ta yi tare cewa "Har 20k Abba, zan tura maka 10k."

"Anty yafi haka gaskiya"

"Babu fa abin da zai faru"

"Aini koma me ye zai faru ki tura min 20k din kawai."

Dariya Asma'u ta yi tare da cewa "To zan tura maka yanzu."

Sauke wayar ta yi tana dariyar Abba da shegen son kudin sa, nan take ta tura masa sannan ta kirashi tunkafin ta ce wani abu ya ce na cika aikin, sallama suka yi bayan ya mata godiya ta kashewayarta gaba daya.

Misalin karfe biyu na rana Habibullah ya iso gidan, cikin sauri ya fito cikin motar ya nufi cikin gidan tun daga falon ya fara kwala mata kira ya isa kofar dakin baccinta, takalmin da ya gani a wurin ya sashi waiwayawa dan dawowa baya yayi kadan tare da kurawa takalmin ido sam ba nashi bane ba don haka ya dan shiga mamakin abin da zai iya kawo talmin wurin, jin kamar ana magana a cikin dakin yasa shi waiwayawa ya kalli kofar, ahankali ya karasa bakin kofar cikin nishadi yake jiyo muryan Habiba tana magana tana dariya sai dai ya gaza jiyo ko kalma daya daga cikin mgnr da take yi.

Kumawa da baya ya sake yi a karo na biyu sai dai wannan karon tsugunawa ya yi ya dauki takalmin ya juya bayansa, sabo ne dal ba a taba sakawa ba, wani gauron a jiyan zuciya Habibullah ya sauke sannan ya juya ya nufi dakin yana rike da warin takalmin

Tsayawa yayi cak jin dariyar Habiba a toilet runtse idonsa yayi bayan wani lokaci ya bude domin zuciyar shi taki yadda da abin da idon shi ke son tabbatar mishi, Kirjin shi ya dafe da hannun sa daya sannan ya karasa gaban gadon ya jawo jallabiyar dake kan gadon ya kura mata ido, fara ce kar cikin sauri ya kaita hancinsa babu abin da take banda kamshin sabunta, jifa yayi da ita kasa sannan ya sake kallon kofar dakin da har yanzun dariyar Habiba ke tashi tare da kuskus din magana, cikin sauri ya sake mika hannun shi ya dauko hular can tsakiyar gado, itama sabuwa ce dal neman dalilin ta na yin haka ya shiga yi nan take ya tuna yadda suka yi daren da taje Abuja tare da kalmarta na karshe da tace saita rama, kallon kofar yayi tare da cewa amma har yanzu yarinta na damun Habiba, jifa yayi da hular sannan ya finciko rigar itama yayi jifa da ita, zama yayi bakin gadon ya fesar da iskar baki tsawon lokaci, tuni idon shi ya kada yayi jawur rasa abin yi yayi tsawon lokaci zuwa can ya mike ya nufi bayin.

Bude kofar yayi da karfi azabure Habiba ta kalle shi ganin inda ya tsaya cak ya na kallonta yasata fashewa da dariya, koda ta ga ya daure fuska tamau bata dauke cewa wai ya dago jirginta bane don haka ta nufoshi da niyyar sanar masa ramuwa ce ta yi sai dai tana karasawa gabanshi ta bude bakin kafin tace wani abu ya wanke mata kumatu da wanni lafiyayyen mari wadda har saida taga taurari suna yawo a bayin.

Dafe kumatun ta yi yayin da ta ke jin idonta na gefen kamar yana duran ruwa, duk son da take tai magana kasawa ta yi, daker ta isa bakin gadon ta zauna tsawon lokaci ta kasa bude idonta bayan kusan minti sha biyar ta bude idon ta saidai abun mamaki babu shi a dakin kofar ma abude ya barta ga kayan da ya yasar nan a tsakar dakin.

Mikewa Habiba ta yi da sauri ta fito har falon bude ya barshi ya fice don haka ta nufi kofar saidai ko motar sa babu a farfajiyar gidan, da alama ya fice ne ma gigan baki daya, sosai ahankali Habiba ya tashi komawa ciki ta yi ta dauki waya kiranshi taita yi amma be daga ba don haka hankalinta ya kara tashi nan ta shiga dana sanin data barshi ya fita bata gaya mishi wasa take mishi ba, kasa hakura ta yi da kiran nashi duk da cewa ba dauka ya ke yi ba sai dai har aka kiran sallah la'asar be dauka ba don haka hankalinta ya yi mummunan tashi.

Ganin bata da mafita ta mike ta ta dauro alwala tana shinfida sallayar tana tunani duk wadda ta tuna zata iya kira sai ta tuna dokar Habibullah sam be amince wani ya san sirrin cikin gidan shi ba haka ya koyar da ita tun farko beson wani yasan tsakanin su dan haka yanzu bazata iya kiran abokanshi ba duk da tasan cewa suna tare a daidai wannan lokacin yin haka na iya kara jawo wata matsalar.

Bayan ta gabatar da sallah addu'oi ta yi tana me rokon Allah ya kawo mata mafita, fuskarta kuwa tuni ta yi zuciya ta kunbure gaba daya, data sanin ta yi shi yafi a kirga ganin har shida ta yi bashi ba yara hankalinta ya sake tashi, wayar shi ta cigaba da kira har a ka kira sallar mangariba be dauka ba don haka ta hakura ta sake dauro alwala, wannan karon ma bayan ta idar addu'a ta yi sosai sannan ta yi lamo kan sallayar tana mai ji a ranta tunda tai aure bata taba shiga cikin damuwa irin na yau ba.

Karan bude get din gidan yasata kasa kunne jin ana shigowa da mota yasata ta tashi da sauri ta mike tana sauke ajiyan zuciya tare da kokarin fita da saurinta...

*** Fadila Lamido