27
by @maidambu41
❤️🩹SO da CIWO❤️🩹
®©Ramlat A Manga
Mai_Dambu
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
***
Or
***
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76
Follow this link to join my WhatsApp group: ***
Dakata hajia💃💃💃💃💃 kin Dade kina Neman inda Zaki sai amintattun jaka, da takalma, sarkoki,masu kyau da quality cikin farashi Mai sauki❓
Ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,wannan gidan na RUMIEE UNIQUE BAG'S GALLARY na budeshi ne saboda na Baku damar siyan jaka,da takalma na Yara Dana manya masu kyau da quality da Kuma saukin kudi cikin aminci daga wajena.masu siyan daya da masu sari duk Muna mataba daku
Muna Kano Muna Tura kaya kowanne state da makotan Nigeria cikin yardar Allah,
Uhmm rigi-rigi ko kun san kayanmu sun iso like bags irin wanda Maamah take amfani da shi, Veils, Shoe's, more and more suna nan dasu...... Let go ❤️🩹💃🏻🐾
27
Wannan gobarar da ta tashi ta d'aga hankalin kowa, ga Dadah da ta suma, haka yasa aka wuce da ita asibiti shi kuma Baffanmu da ya auna arziki, an fitar da shi da kyar bayan an sake same shi a sume. Wannan abin ya so saka Mama zaucewa. Haka yasa ana kawo shi asibiti, ta kalli yadda Allah ya mai da shi, juyawa tayi domin ba zata iya cigaba da kallonshi ba, inda Datti yake ta kalla tana faɗin.."Saboda ya bijirewa bukatarka zaka kashe shi? Saboda son zuciyarka Datti, Wai me kake so ne? Idan har abinda aka tara ne ya d'aga maka hankali mai zai hana ka fita ka nima, tunda ka iya cutar mutumin da ya baka yardan shi ai ba kome ba ne idan ka kashe dan cikinka, tunda ka kashe waɗanda basu ba basu gani ba ka tattara duk abinda kake bukata kayi yadda kake so. Datti a shekarunka lahira zaka nima ba kaunar da duniya ba, idan don Rahmah kake wannan abin lallai tabbas zaka kashe mu domin dukkanmu rayuwarmu zamu bata, Datti ina jiye maka ranar da zaka wayo gari aka jika cikin Kabari." "Mama!" "Kyale ni!" Ta fada tana kuka tana faɗin.."ranar zaka gane Allah da girmama yake." "Ke ni ban san kome ba, nima haka na ga wuta ta tashi a gidansa." "Kai ne sanadin wutar kai ne kayi sanadin wutar da baka kashe Rufa'i da Hannatu ba, mai zai faru? Da baka yi sanadin kama El Mansur babu abinda zai bibiye ka. Yanzu mutane uku suna gabbar mutuwa saboda da kai." Ta fada tana wani irin kuka. Domin nata laifin yafi na datti. Gani take kamar tafi kowa laifi. Haka yasa ta koma dakin da Maamah take, tana wani irin kuka me cike da tausayi Maamah.
Nayi barci kasancewar alluran barci da aka min, washi gari na tashi da sauki sosai. Dada na gani a daya gadon da yake dakina. "Abar kauna yaushe kika zo!" "Da asuba aka dawo da ni!" Dadah jarumar tsohuwa ce zai yi wahala ka ga tashin hankali a tare da ita, haka yasa nake bala'in sonta. "Dadah na me ya same ki?" Juya min baya tayi tana faɗin.."ke tafi can bera!" Ta juya min baya. Mama ce ta shigo fuskarta jajjur tayi kuka har ta godewa Allah. Sannan maganar gaskiya na ga kowa cikin tashin hankali. Wayar da Mama take yasa ni bin ta da idanu. "Eh Mehra kome yana son fita daga yadda ake tsammani, rayuwar Princess yana da muhimmanci, please kayi wani abu ko wani lokaci kome zai iya lalacewa, please save my Princess koda kuwa ace bana raye ina son ka tsaya akan Princess." Ta fada tana jan hancinta. "Ok In sha Allah!" Daga haka ta kashe wayar, tana me shafa kaina. "Baby girl!" Kallonta nayi ina faɗin. "Mama wani abu ya faru ne?" "Hawaye ne ya zubo mata." "Baffanku bai da lafiya daren jiya gobara!" Damke hannunta nayi idanuna waje.."don't tell me I lose my Dad!" Na fada da karfi ina sauka daga gadon, zubewa nayi a kasa. "Princess take it easy!" Mikewa nayi na ji na sake faduwa. "Please Mamana kai ni wurinshi." Na fada ina fashewa da kuka. Rungume ni tayi tana shafa bayana, a hankali naji wani irin karfi ya zo min janye jikina nayi na kama gadon na mike, "Baffanmu!" Na fada a hankali. Sannan na fita da sauri ina ji kamar iska zata dauke ni, kafaffuna babu takalmi kaina babu dan kwali, waige-waige na fara har na isa inda su Hamma Jamal suke tsaye cikin tashin hankali. Yau ya dace ya koma aiki amma wannan tashin hankalin ya saka dole ya dakata ya ga halin da Baffanmu yake ciki. "Princess!" Suka kira sunana, kallonsu nake ina mai nuna musu kofar dakin, gyada kai suka yi da sauri na juya zan shiga Hamma Umar ya rike ni. "Sake ni, i say let go!" Na fada da karfi ina tirjewa dakyar na samu na gantsara mishi cizo na fada dakin a guje,.ina kallon yadda likitocin suka zagaye shi. Ga Hamma Abdulhameed tsaye ya kasa kome. "Baffanmu!" Na nufe shi "Baffanmu" na kara kiran sunanshi. "Baffanmu ka tashi ka tashi!" Na fada da karfi ta baya Hamma Abdulhameed ya rungume ni, "is okay!" "Not be okay!" Na fada ina faɗin. "Baffanmu ka tashi don Allah, ka tashi nace!" Na fada ina kwace jikina a wurin Hamma Abdulhameed, gadon na nufa ina me ƙoƙarin tab'a shi wani likita ya kai hannu zai rike ni, dafa shi ɗaya daga cikin likitocin yayi yana nuna mishi harbawan vital da pulse din Baffanmu. "Barta tayi mana abin da muka gaza. Alhamdulillahi! He recognized voice dinta, sauran aikin namu ne team a motsa. Princess cigaba da kiran Baffanmu har sai ya amsa miki!" Ai kuwa cikin kuka da sarewa na ce mishi.."idan ka tafi nima mutuwa xan yi don Allah ka tashi baffanmu Mama Yaya baffanmu yaki tashi." Ina yarinya baffanmu yana goya ni a a parlourn shi yana min doki, tow ranar ya gaji Yaya tayi tayi na hakura da dokin, amma naki shine suka kyale ni ya ce su bar ni, ai kuwa ya juya baya na hau ya fara min doki, ai kuwa ya zube a wurin. Wannan yasa nayi ta ihu ina kukan Mama yaya Baffanmu yaki tashi suna zuwa a rufe aka fara kokarin niman hanyar da zasu fitar shi ya ce musu.."nifa lafiya ta lau idanuna biyu!" "Baffanmu cheat is bad." Na fada ina kuka. "Baffammu ka tashi kayi hakuri ka tashi nayi maka alƙawarin maka kwalliya." Bani mantawa ina yarinyar na tab'a zuwa ka kwaso kayan kwalliyar Addah rukayya kafin aurenta na shiga dakin Baffammu yana barci na haura gadon na fara mishi kwalliya. A ranar yaya ya zane ni sai da zazzabi ya rufe ni, shima kuma ranshi ya b'aci akan me zata zane ni, ai a ranar ya sayo min kayan kwalliyar ya ce na cigaba da mishi kwalliya idan yana barci. "Baffanmu don Allah ka farka!" Na juya ja fita da sauri. Haka nayi ta bi room ina tambayar kayan kwalliya, wata mata ce na samu a wurinta na dawo zan shige Hamma Jamal ya rike ni, ihu na saka ina fadin. "Wayyo Allah na Wayyo Baffana, wayyo Baffana wayyo Allah ka kyale ni ko ja cije ka." Na fada ina kokarin nufar kanshi.."kyale ta Hamma!" Inji Hamma Abdulhameed, shiga nayi da gudu na koma kan shi. "Baffana zaka tashi bari na maka kwalliya zaka tashi, Baffana ka gaya min idan zan yi aure kai zaka kai ni dakin Mijina, baffana ka gaya min baka tab'a give up akai na ba!" "Baffana ka tashi ka ji zan auri Sharahbil ba zan kara fadar wani abu ko na ji haushi Baffana nayi maka alƙawarin ko kuka ba zan yi ba, Baffana ka tashi ka ji kada ka mai dani marainiya Allah ka san bani da wani Jarumin Ubana sama da shi Allah idan ka ɗauke shi yadda ka ɗauke Yayata ciwon zai min yawa ina jin ciwo sosai a raina, Allah ka dauki tawa ka bar min Baffana." Na fada ina kuka. "Allah kai ne Allah Allah na yarda kai ne Allah, Allah nayi imani da kai sama da yadda nayi Imani da Baffana, Allah ka tashi kafadarshi, Allah kada ka raba ni da masoyana da nake sonsu. Allah ga Baffana a gabanka, Ya Allah ina cikin maraici da kaɗaici Ya Allah ka bar min Baffana ba don halina da kome ba. Allah!" Dafe kirjina nayi kamar ana dakatar da fitar numfashina. "Alhamdulillahi!" Iya abinda na iya furtawa kenan, daga nan na ga dakin yana juya min. Daga nan ta tafi zan zube, rike ni Hamma Abdulhameed yayi ya fitar dani daga cikin dakin, ana fitar da ni yana jan wani irin numfashi da kiran "Rahmah!" "Alhamdulillahi! Daddy girl tayi mana mai wuyar, yar baiwa kenan." Doctor Sharif ya fada yana gyara tsayuwarshi kafin wani lokaci sun tsaya akan aikinsu, babu wani kunnar da yayi hayakin da ya shaka ce ta cika mishi cikinsa. Don haka suka shiga zukee hayakinki.
Za a iya cewa Alhamdulillahi, domin kuwa a cikin kwanakin abubuwan da suka faru suna da yawan gaske, amma kuma kome yazo da sauki tunda an tsira da rai, a cikin kwanakin da basu haura sha daya ba, aka gyara gidan tare da zuba sabin furniture, Kai Alhamdulillahi, a bangaren Maamah barci take tayi na tsawon kwanaki goma sha ɗaya, yarinyar damuwa tayi mata yawa haka yasa ake ta mata alluran barci akai a kai, domin zuciyarta ta huta. Baffanmu ya farka kamar ba shi ba, da ake tambayarshi musabbabin gobarar ya ce shi bai sani ba, domin yana dakin. Uwani aka tambaya ta ce ita ma gaskiya ba zata ce ba, domin bata ji motsin shigowa gidan ba, sai da ta fito ta ga gidan ya cika da hayaki. Yasa aka cigaba da bincike amma babu wani abu da ya bada damar fahimtar saka wutar aka yi ko kamawa tayi, Datti ma da ake zargi Dada ta bada shaidar ta bar shi a parlour kuma bai fita ba, wannan abin ya dami kowa, a wannan lokacin kowa yaga Raheemah sai ta bashi tausayi domin kullum tana asibiti wurin Maamah, kowa ya yarda Duk abinda ya faru ya wuce yanzu ta rayuwar Maamah suke, haka yasa ta shiga zuciyar kowa.
A bangaren Iyayen Sharahbil shima suna kokarin ganin sun nima mishi magani, sannan sun tanadi wasu fake results na test saboda tsaro ba don tsoro ba.
***
Kano
Innar Ayuba.
Tunda ta dawo a kano ta sauka gidan Bintu, lamarin Maamah ya dame ta kamar ta koma ta dauko ta son yarinyar take daga zuciyarta. Murmushi tayi kafin ta kalli Bintu ta ce mata. "Naga yarinyar da ta dace da Ayuba, sai dai akwai damuwa sosai akan Yarinyar."
"Inna Ayuba yana da wacce yake so, kuma take sonshi." "Ikon Allah, tow wallahi yarinyar tayi min, shi kenan dama itama aure za a mata bata son Mijin, Allah sarki Auta naga samu na ga rashi Ubangiji ya kawo miki sauki a lamarinki, Ya Allah kada ka kunyata Hajiya Abidah, Ya Allah ka amshi addu'ar Hajiya Abidah ka bawa Yarinyar nan miji na gari." "Innar Ayuba kishi nake da yarinyar nan da ta kwace mana zuciyarki!" Murmushi Innar Ayuba tayi tana faɗin. "Amma dai Bintu Allah ta shirya ki, Yarinya ce fa wannan sai dai na kirata da Autana!"
"Allah Innar Ayuba, tow shi kenan!" "Yaranki biyu, amma kina abu kamar yar shekara biyu." Murmushi tayi tana faɗin yarinyar ce tana cikin kewar rashin uwa." Ta fada a yanayin damuwa. "Innarmu ki rufa min asiri kada ki saka damuwar wata can, ki zo mu rasa lafiyarki." Murmushi yayi tana faɗin. "Tunda na rasa mahaifinku da Yayanku ban shiga damuwa ba gaya min wani gwagwarmayar ya rage ban gani b....